Showing 24001 words to 27000 words out of 88044 words
Chapter 9 - MIJIN BARRISTER Complete Hausa Novels By Sadiya Barrister.txt
miye ruwan ka dasu kuma daga ina kake?
Ridwan ya kalli baba ya kauda kanshi kawae Maidubu ce ta kalli Baba ido cikin ido tace Baba Ridwan saurayina ne Baba Ridwan shine xabina Baba Ridwan shine farincikina Baba yayi tsaye yariqe baki yana kallon Mai-dubu
Maidubu ta riqe hannun Ridwan ta russuna har qasa shima ya russuna suna rike da juna sunyi knelling agaban Baba dukkanin su kuka suke yi Ridwan hawaye yake itako Mai-dubu kuka takeyi mai sauti Baba Dom Allah ka barni in auri Ridwan wallahi baba Ahmad bayasona kuma xai aureni ne Dom ya wulaqanta ni ke Mai-dubu yaushe kika fara qarya cewar baba kenan
Baba ne ya dakatar da ita da tsawa yana fadin ke Mai-dubu dama abunda kike yi kenan idan kika fita Ashe maxa kike kulawa awaje Ridwan ne ya datakar da baba da fadin Baba kayi hakuri Maidubu batada laifi akan wannan abun wallahi baba inason Maidubu Dom Allah baba karka rabani da Mai-dubu itace farinciki na Baba yace kai dakata wallahi ko xaka mutum baxan aurama da Mai-dubu ba
Maidubu ta tashi tsaye tana fadin tashi Ridwan idanunta sun kada sunyi ja amma na Ridwan sunfi jah ta qara da fadin tashi Ridwan ka tashi nace tafada da tsawa tsawa Ridwan da kuka yaci qarfin sa yatashi tsaye Mai-dubu ta rike kafaddun shi tana fadin Ridwan duk wuya duk rintsi ina tare da kai wallahi ni maidubu nayi alkhawarin riqe sahibina Ridwan da mamana Ridwan dae ya kasa furta komi sae hawayen da kebin idon shi
Maidubu ta kalli baban ta tafara da fadin Ya kai mahaifina nayi biyayya agareka kuma har yanxu ina mai ladabi da biyayya ga umurnin ka amma wallahi baba ko ka aurar dani baxan rabo da Ridwan ba matukar ina raye Baba ka barni da xabina dom girman Allah tasake fashewa da kuka
RIDWAN yace baba Dom girman Allah ka barni da Maidubu Baba yace wallahi ko xaka mutu baxan baka ita ba Maidubu ta sake fashewa da kuka ta rike Ridwan suka rungumi juna Ridwan yashiga neman bakin maidubu yana tsutsa Mai-dubu ta lafe jikinshi Baba ne ya yayi taslima yana fadin lah lah lah Mai-dubu tun ban aurar dake ba har jin San dadin namiji har ki rungumi wani gwabjejen kato Baba ya fashe da kuka yana fadin...
Barrister for lifeπ
Muje xuwa wasa farin girkiππππ
Mijin barristerβππππππππππππππβ
[17:27, 1/2/2018] Barista: βππππππππππππππβ
MIJIN BARRISTERπ
By Barrister S@dyπ
Dedicated 2 my daughters Hafsat Nasir Gwandu nd Seeyamah Nuraππ
Mijin barrister
55-56
βππππππππππππππβBaba ya fashe da kuka yana fadin Maidubu tun ban aurar dake ba har kinsan dadin maxa tau bara kiji ingayamaki ...... Ahmad ya dakatar dashi da fadin wannan shine saurayinda nagansu tare a wancan lokaci Baba ya fiddo ido waje yana fadin cemun fa tayi Nura ne ya sauketa mijin qawarta xarah. Ahmad yace qaryane wannan ne ya sauketa ba Nura ba.
Baba ya cire takalmin shi ya fara dukan Maidubu Ridwan ne ya riqe baba yana fadin kayi hakuri baba Dom Allh duk abunda xakayiwa Mai-dubu kayimin marmakonta dom bata da laifi duk abunda ya faru nine sila.
Baba ya kwadamai takalmi yana fadin sakeni Dan iska ina nan kofar gida xaune Ashe kana can kana iskantamin yarinya baba ya share kwalla ya maido kallon shi ga maidubu sannan yace Maidubu tunda rayuwar iskanci kika dauka har da biyar maxa a layi tau bara kiji ingayamaki amatsayina na ubanki.
Ni Alhaji Muhammad xanyi rantsuwar da batada kaffara wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Gobe gobe xan daura maki aure da Ahmad kuma ki tare gobe wani abunne ya Fadi qasa dim sae da kowa ya juyo da sauri dom ganin ko kiye ya fadi haka Ridwan ne yafadi qasa sumamme Maidubu ta fada jikin Ridwan tana kiran sunan shi amma ina Ridwan baya nunfashi
Ahmad yana tsayen shi jikin motar shi yanajin dadin ganin bacin ran Mai-dubu dom yana nishadantuwa da hakan yayi murmushin qeta sannan yace yanxu kika fara shan wahalar rayuwa Mai-dubu, ya shiga motar shi yayi xaune yana kallon yarda Maidubu ke kuka tana rike da Ridwan tana kiran sunan sa.
Baba ne ya kalleta yace wallahi! Mai-dubu idan baki kiyayeni ba wallahi sae na tsine maki albarka Mai-dubu ta dago kai tana fadin dom Allah Baba ka taimakeni mukai Ridwan asibiti Baba yace wah? Ni ? Allah ya kareni intaimaki rayuwar fadiqi ke dae fasiqa yar uwar shi ki taimaka masa Maidubu ta sake fashewa da kukan baqin ciki tayi wajen Ahmad yana xaune a mota yana kallonta ta iso tana fadin Ahmad dom Allah ka taimakeni mukai Ridwan hospital sae da Ahmad ya sheqe da Wata irin dariya sannan ya hade fuska yace wallahi koda bai mutu ba yanxu nayi alkhawarin xama ajalinsa Maidubu ta fiddo ido waje tana fadin kissa?
Ahmad dama kana kissa? Ahmad yayi murmushi qeta sannan yace Ridwan xai xama cikon mutum na 20 dana kashe nayi miki alkhawarin da hannuna xan kashe Ridwan amma ba xan kashe shi yanxu ba har sae yaga ranar aurena dake sae na cusamai baqin ciki maras adadi sannan in kashe shi Maidubu ta share kwalla a idonta sannan ta kalli Ahmad sosae tace sannu axara'ilu inason ka sani Ridwan yafi qarfin ka insha Allh ta dawo ta jijjigashi taga har yanxu bayada rai ta sake fashewa da kuka mai sauti tana fadin Dom Allh Ridwan ka tashi kar ka mutu karka mutu ka barni anan kadawo Ridwan idan ka mutu wallahi nima sae na kashe kaina dom mu cigaba da rayuwar mu ta farinciki a lafira.
Wani maqobcinsu ne yadawo yana kokarin shiga gida Maidubu ta sheqo ta fadi gaban motarshi tana kuka ya fito a mota gigice yana fadin lafiya Mai-dubu? Mi akayi? Waye ba lafiya?
βππππππππππππππβMai-dubu ta kasa magana sae nunamai Ridwan takeyi da hannu ya juya yaga Ridwan kwance a qasa ba alamar nunfashi yayi wurinshi da sauri yana fadin miyasa meshi ? Maidubu batayi magana ba yace ta kama mai su dauko shi suka dauko Ridwan suka sakashi a motar mutumin. Maidubu tace muje dashi (F M C ) xata shiga motar Baba yace idan kika sake kika shiga motar nan xuwa hospital ba nine ubanki ba kuma haihuwar da nayi maki Allah ya isa Baba ya juya ya koma kofar gida inda yake xaune.
Maidubu ta fashe da kuka ta fadi qasa tana kuka Ahmad ya tayar da motarshi ya wuce yana mai jin dadin halin da Mai-dubu take ciki, mutumin yace jeki gida Maidubu nayi miki alkhawarin kula dashi kamar yadda xakiyi mai yaja motarshi ya wuce da Ridwan hospital Maidubu na kuka taji karar waya ta dago kai ta hangi waya a qasa tayi saurin dauko wayar tana daukowa kiran na katsewa taga fuskar wayar photon tane hakan ya tabbatar mata da wayar Ridwan ce. Tayi murmushi tana share kwalla a idonta ta saka kiran number da taga ankira da ita bugu 2 aka dauka taji muryar wata macce tana fadin my son daga kawae baxan dade ba har yanxu 11 na dare tana kokarin yi ga abuncin da kace adafama nan har yana neman hucewa Maidubu ta kasa magana sae shashshekar kukan da takeyi Matar ta qara da fadin haba son Yakama Kasan ka girma kadaina yimin shagwaba haka nan Maidubu na kuka tace bashi bane Ridwan yana hospital tafada da qar dom kuka yaci qarfin ta Matar ta fiddo ido waje yana fadin na shiga ukku miyasami my son one nd only a wacce hospital yake Maidubu ta ansa da fadin yana (F M C) Matar tayi jifa da wayar tana kuka ta dauko gyalenta ta fito harabar gidan tana fadin.........
Barrister for lifeπ
Muje xuwa wasa farin girkiππππ
Mijin barristerβππππππππππππππβ
[20:59, 1/3/2018] Barista: βππππππππππππππβ
MIJIN BARRISTERπ
By Barrister S@dyπ
Dedicated 2 my daughters Hafsat Nasir Gwandu nd Seeyamah Nuraπππ
Mijin barrister
57-58
βππππππππππππππβTa Fito harabar gidan, tana fadin duk Ina hadimman gidan nan? duk suka iso inda take kowa yana mamakin ganin hajiya a rikice, ta kallesu tana fadin ina drivers ku fito da mota Ridwan yana hospital. Da gudu suka isa packing space suka fito da manyan "Jeep's" har biyu hajiya ta shiga guda tana ta kuka bodyguards dinta suka shiga dayan drivers sun jasu sae gate din (F M C )hospital....."
Babane ya shigo gida yana fadin ina kike maman yara, ta fito da sauri dom jin abunda ya faru. Baba yace" yanxu Ashe duk tarbiyya da muke yiwa wannan yarinyar idan tafita maxa take bi, Mama ta sake flats dinda yake hannun ta har ya tarwatse, tana fadin Baban yara wannan wacce irin magana kake fada akan yar da muka haifa . Baba yace" gaskiyar magana kenan Dom ko agabana tayi haka ta rungumi wani gwabjejen kato shiko har da neman bakinta yana tsutsa yana lunshe ido kamar Wanda ya sami minti Allah kadae yasa inada qarfin jina da na sume a wajen ya Fadi maganar yana share kwalla a ido shi.
Ya qara da fadin" tau bara kiji ingayamaki wallahi! xan aurar da Mai-dubu kafin ta ajemin Dan shege a gidan nan. Mama tace" yanxu ina Mai-dubu din ba sunfita da Ahmad ba? Baba yace tana waje kuma gobe xan aurar da ita.
Mana ta fiddo ido waje tana fadin gobe fa kace Baban yara, Baba yace kwarai kuwa kuma goben xata tare Baba ya juya ya shige dakinshi Mama tace" na shiga ukku wannan wacce irin rayuwa kenan.
"Mama ta fashe da kuka tana fadin" ko yaran da basada kowa baayi wa irin wannan auren ba, balle Mai-dubu wacce takeda cikakken gata na uwa da uba mama ta sake fashewa da kuka tayi kofar gidan ta hango Maidubu kwance a qasa tana ta kuka, ta iso wajen tana fadin" tashi muje gida Mai-dubu, Maidubu ta rungumi mamanta tana wani irin kuka mai ban tausayi nidae nace Allah Sarki Maidubu Kinga gwagwar mayar rayuwa. Mama ta tadata tsaye Mai-dubu taga key din motar Ridwan ta dauko ta rike shi mama ta jata suka shiga gida mama ta kaita har dakin ta tayi mata nassiha sannan ta fito xuwa nata dakin dom itama kukan takeyi.
βπππππππππππππππβMai-dubu taci kuka har ta gode Allah, nan bacci barawo ya dauketa duk ta hargitse dakin batayi kwannan 1 hour ba ta tashi kamar wacce taji tsoro ta lalaba rigarta inda ta sako bindiga da waya amma bata jisu ba, Amma taga wayar Ridwan da key din shi da ta axa agefen gado tayi neman wayar da bindigar har ta gaji amma bata gansu ba tayi xaune tana kuka tana fadin" yanxu inda naga kayan nan da sae kawai in nunawa baba nasan dole ya raba wannan auren. sae kuma tasake fashewa da kuka ta leka har qasan gado bataga komi ba sae tayi tunani kodae sun fadi acan waje sae kawae ta tashi ta bude dakinta ta fito tayi saf saf tayo kofar gidan tayi nasarar fita ba tare da kowa ya ganta ba tayi nema har ta gaji bata gansu ba dama ita tasan taje dasu gida.
Wata xuciyar tace Maidubu ki tafiyarki kawae kibar gida, Wata xuciyar tace ah ah ki kashe kanki kawae sae ki huta, Wata xuciyar tace Maidubu ki tuna fa duk Wanda ya kashe kanshi ya mutu kafiri, Maidubu tace haka xaayi ba inda xanje sae dae mu kashe juna nida Ahmad idan naje gidansu sae kuma ta fashe da kuka ta koma gida ta taci gaba da aikin kuka.
Tana shiga gida ta shige dakinta taci gaba da kuka har gari ya waye, "Baba yashigo gida ya gayama Mama ta gayama yayyun Maidubu da danginta duk Wanda yasamu lokaci akwae daurin auren Maidubu da qarfe 9 na safe.
"Mama tace" wae Baban yara da gaske ko xaka daurawa yarinyar nan aure yau? Baba yayi murmushi sannan "yace ki bari idan lokaci yayi xaki gasgata maganata. Mama tanemi waje ta xauna tana hawaye Almajiri ne yashigo yayi aikin shi da ya saba "mama tace ya share filin gidan duk har inda Mai-dubu ke sharewa haka kuwa akayi,
A banfaren Ridwan kuwa motocin hajiya na tsayawa bodyguards dinta duk sukayi saurin fitowa suka take mata baya, sae cikin hospital din ta shiga dakin da akayiwa Ridwan masauki, tana hango Ridwan kwance kamar matacce ta isa gunshi da gudu ta rungumeshi tana jijjigashi amma ina Ridwan baya nunfashi, Hajiya ta rushe da kuma ta kalli doctor tana fadin" doctor what happened 2 my son? What is wrong wit him? What did u get as ur result? Doctor yayi shuru yana mai tausayi hajiyar ga bodyguards dinta duk sun xagayeta itako sae aikin kuka takeyi,
Doctor yayi gyaran murya sannan yace" Kiyi hakuri hajiya! Ur son heard something's beyong his capacity. Amma insha Allh Muna iya qoqarin mu Dom neman nunfashin sa, Hajiya tace menene wannan abun da RIDWAN yaji? Docter yace" wannan ansar tana hannun Ridwan Mama takasa bacci a tsaye ta kwana itada bodyguards dinta har gari ya waye,
Da misalin qarfe 9 na safe jamaah suka shedi aurin auren Mai-dubu Muhammad da angonta Ahmad Shehu a kan sadaki naira dubu hamsin. Ango na hango yasha wanka cikin Wata dakakkiyar shadda gixna tasha kwado har ta gaji kalar madara wato ( milk color) da hular brown da cover shoe suma brown da agogon hannu shima brown color yayi kyau masha Allah sae hannu yake bawa mutane suna gaisawa. Duk da ba kowa yasan da wannan auren ba amma antaru masha Allah, angama aurin aure mutane sun shiga ciki suna yiwa mama Allah ya kyauta,
Mama ce xaune ita da yan tsirarrun mutane yan uwanta da sauran yaranta wato yayyun Mai-dubu Mama tasa andafa abunci anba mutane sannan jamaa suka wuce wajen gyaran dakin Maidubu. Baba ya kira yayar Mai-dubu Aisha yabata kuddi bakadan ba yace duk abun da ake anfani dashi gidan miji inason ki sayowa Mai-dubu idan ansaye a wuce kawae gidan ta asaka mata. Aunty Aisha ta dauki kuddin ta fita sukayo soyayya akaje akayi jeren amarya aka qare.
Ridwan bai farka ba sae qarfe 2pm. Ridwan na farkawa ya fara da fadin Baby! Babytah!! Baby ta!! Yana maganar yana lalaba gefen gadonda yake kwance akai jin ba alamar Maidubu a wajen yasa Ahmad bude idon shi a hankali yaga maman shi xaune ya fara da fadin"momy ina babytah? hajiya tace waye babyn taka? Ridwan ina kaje jiya bayan fitarka gida? Kuma miyasameka?
Ridwan ya fashe da kuka yana fadin" shikenan momy na rasa Maidubu momy tace waye Mai-dubu? Kuma miye a tsakanin ku? Ridwan ya kwashe duk labarin su tun ranar farko da ya hadu da Mai-dubu har jiya yagayama hajiyarshi yana sake rushewa da kuka momy ta tausayawa rayuwar danta sosae sannan tace"kayi hakuri my son xanje da kaina har gidansu inyi magana da mahaifinta kafin dadyn ka yadawo gida Nigeria. fushin xuciya ne kawai Babanta yayi dom bantaba ganin anyi irin wannan auren ba, Ridwan yaji dadin kalaman momyn sa kuma yadan samu natsuwa yayi wa momyn sa godiya. Momy na duba wayarta taga missed calls dinda Mai-dubu tayimata da wayar Ridwan har missed calls 20. Tace Allah sarki kagama ashe tayita kira da wayarka Ridwan yayi murmushi kuma idanunshi sun ciko da kwalla.Ridwan yace idan kinje gidansu momy kigayawa Maidubu ko an aurar da ita, ko baa aurar da ita ba, mota ta dake kofar gidansu da handset dina duk ta dauka na bata amma tabaki sim card dina ki dawo min dashi sannan kice mata nace Dom Allh tayi hakuri tayi biyayya ga umurnin iyayenta tabi mijinta su xauna lafiya, Dom ni nasan mutuwa xanyi wallahi momy baxan iya rayuwa batare da Mai-dubu ba. Ya rushe da kuka kamar wani qaramin yaro itama momy kukan takeyi tana fadin kayi hakuri my son kadaena furta Kalmar mutuwa akan ka kuma insha Allh Mai-dubu takace kaji. Ridwan yace nagode momy. Ridwan yayi maganar yana share kwalla .
Barrister for lifeπ
Muje xuwa wasa farin girkiππππ
Mijin barristerβππππππππππππππβ
[11:27, 1/4/2018] Barista: βππππππππππππππβ
MIJIN BARRISTERπ
By Barrister S@dyπ
Dedicated 2 my daughters Hafsat Nasir Gwandu nd Seeyamah Nuraππ
Mijin barrister
59-60
βππππππππππππππβMomy na fitowa tashiga Mota bodyguards dinta duk suka take mata baya suka shishshiga mota, sae area din su Mai-dubu suna isa kofar gidansu maidubu Momy" ta fara ganin mutane da alama anyi wani taru a wajen".
Daya gada cikin bodyguards din momy ne ya kira wani yaro matashi ya tanbayeshi, Dom Allah ko nan ne kofar gidansu Mai-dubu, matashin "yace eh nan ne kuma yau ma aka daura mata aure.
"Mama ta fiddo ido waje tareda axa hannun ta a gabanta tana fadin"Aure fa kace" yaron yace eh momy "tayi taslima "tace dom Allah kaje wajen ta ba tare da kowa ya San abunda kaje yi ba, "kace da ita momyn Ridwan tana sallama da ita a waje".
Yaron yashiga yaga mutane tab da gidan yaga Wata mata tana jajjagen tumatur "yace sannu ko "tace yawwa sannun ka. Dom Allh maidubu na nan gidan, Matar "tace eh tana dakinta yaron yaje har dakin yasamu Mai-dubu kwance tana aikin kuka da qawayenta biyu Balkisu da xarah suna xaune kowa tayi tagumi suna bata haquri "yayi sallama suka ansa "yace wae momyn Ridwan tana sallama da Mai-dubu a kofar gida ae Mai-dubu najin sunan Ridwan ta tashi xaune da sauri yaron nagama fadi Mai-dubu ta tashi tsaye ta sako hijab dinta tabi bayanshi sae kofar gidan
Tana fitowa taga wasu manyan motoci a kofar gidansu, glass din dayar motar aka sauke ta hangi Wata kyakkyawar mata wacce ko baa fada ba kasan mahaifiyar Ridwan ce, Maidubu ta iso wajen ta ta russuna har qasa ta gaida momy, momy ta ansa mata tare da gaba ladabi da kyakkyawar sura irin ta Mai-dubu.
"Mama ta fara magana kamar haka" Maidubu nasan baki sanni ba, nice mahaifiyar Ridwan Mai-dubu ta russuna da kanta a qasa tana sauraren momyn Ridwan, "momy tace Ridwan yabani Labarin ki, tun ban ganki ba nayi shaawar hada xuria dake, amma kaddara ta riga fata. Dom anriga an daura maki aure maidubu ta share kwalla sannan "tace momy ya jikin Ridwan, momy "tace Ridwan ya fardado amma nasan angudu ne baa tsira ba, dom ko yanxu Ridwan yaji anyi maki aure nasan