Showing 57001 words to 60000 words out of 88044 words

Chapter 20 - MIJIN BARRISTER Complete Hausa Novels By Sadiya Barrister.txt

15 Nov 2025

1938

ba kenan kamar yarda bakyason ganina nima na yarda da in axaftar da xuciyata da rashin ganin abunda tafi muradi a rayuwa.

Ridwan ya bude mota ya dauko ATM dinshi yace ta amsa tana amsa yace wannan ATM dina ne xaki iya anfani da kuddin dake ciki akwae insan million 70 ciki basan xasu isheki hidimar biki idan ma basu isheki ba kigayawa Nura kawae dom insha Allah baxaki sake ganina ba sae ranar da wani event din auren mu zai hadamu daga nan kuma sae ranar da aka daura auren mu, ranar da nakeda ""absolute right over u".

Ridwan ya bude motarshi zai shiga Barrister Maidubu ta.....

Barrister for lifeπŸ’‹

Muje xuwa wasa farin girkiπŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„

Mijin barristerβš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–
[14:00, 2/9/2018] Barista: βš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–
MIJIN BARRISTERπŸ’‹

By Barrister S@dy😘

Dedicated 2 my daughter's Hafsat nd Seeyamah ina sonku yarana Allah yayi muku albarka.πŸ’‹πŸ˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜


This page is urs Samira Malami ( Mrs Mukhtar) Thank for ur love nd sport dear.πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Mijin barrister
107-108

βš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–"Ridwan zai shiga mota Maidubu ta riqe hannunshi bai juyo ba amma ya tsaya haka tayita bashi haquri harda kukan shagwaba Ridwan naji dadi ba kadan ba, Dom ko bakomi yasan zata girmamashi tunda har take iya bashi hakuri idan tayi ba daidai ba. ba kamar sauran matan ba.

"" suke laifi kuma su jira abasu haquri. ""ya juyo fuskarshi ba yabo ba fallasa itako sae shagwaba take xuwa mai, kuma gata riqe da hannunshi tana bubbuga qafarta a qasa na fulaninta sae kadawa suke ae bashiri Ridwan yasaki murmushi yana "fadin na haqura wallahi na haqua.

"Yace ke daina wannan bubbuga qafar da kike yi ina ganin abubuwa ae sae kimin illa, dariya tayi itama, shikenan suka shirya ta bashi ATM dinshi amma yaqi karba "yace idan akwae abunda take bukata basae ta jirashi ba.

βš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–
""JAN HANKALI""
"Yaku yan uwana mata shin ko kunsan mutuwar auren mu yana yawan faruwa ne akan rashin biyayyar aure?. idan kikayi laifi bakya iya bawa miji haquri wae zai raina ki wanne raini? Idan miji ya raina ki wallahi kece kika raina kanki, ko kice idan kina binshi zai gane kina mugun sonshi ya wulaqanta ki.

Tau gara kiji yar uwa rashin bada haquri idan kinyi laifi yanasa miji ya tsaneki dom kin rainashi bayan yatare maki duk Wata bukata taki sannan kuma bakya darajja shi kai mata muyiwa kanmu fada wallahi.

"Allah da kanshi "yace da xan yi umurnin ayiwa wani sujjada bayanni,"" da nayiwa "mace umurnin tayiwa mijinta sujjada. Wannan kadai ya isa ya nunawa duk wata mace mai hankali girman da Allah ( S.W.A) yaba miji ga matanshi.

""Mata mu kiyaye, kullum Muna adduar shiga aljanna dami namu kenan xamu shiga aljanna? biyayyar mu ko rashin biyayyar mu ga Allah da miji.
Haba mata muyiwa kammu fada.
βš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–

"Dady ya fito yayi mamakin ganin part din Ridwan a kulle kuma ba bodyguards dinshi a gidan ko daya momy ta kira wayarshi suka gaisa ya shaida mata yana Nigeria, dady yaje tareda baba sukayi sayayyar kayan da xasuyi hidimar biki. aka hadowa Ridwan Kala 50 manyan shaddodi ne kawae.

Yau takama Lahadi su dady sun gama shiri kaf suka shigo "jet dinsu sae gida NIGERIA "jet ya tsaya a compound din gidan dady suka fito.

Suka shiga ciki dama sunyi odar abunci daga "daula restaurant" suka kare cin abunci suka Dan huta sannan dady yabada Driver sabowar mota kirar ( Land Cruiser) "yace wa driver yakaisu sabon gidansu kuma idan yakaisu yabarmusu motar.

Dady yashigo falon "yace wa su baba driver yana mota haka suka fito gaba daya Dom yiwa su Baba rakiya Baba da mama suka shiga mota su dady suka koma gida.

Su mama da momy basuji dadin rabuwa da juna ba. Dom shaquwa ce mai qarfi tashiga tsakaninsu.

Driver nakai kofar gidan yayi "hone "gate man" yabude suka shigo daga ciki baba da mama sae kallon juna suke, "dady ne "yace kai malam ina ne ka kawomu nan kaida aka ce kakaimu gidanmu.

"Driver "yace nan gidan dady ne kuma shi yayi min umurni da in saukeku a nan! gidan! kuma "yace har wannan motar in barta a nan! mama ta kalle gidan, gidan sama ne har hawa 6 sae kawae ta fashe da kuka ""dady "yace kamaidamu wajen shi muyimai godiya Dan Allah.

Driver din yace ah ah Alhaji yace duk yarda kukayi karna dawo daku kuyi xamanku ku huta. baba yace lallah munyi haihuwa maman yara godiya sukayi ga Allah ma daukakin sarki. sannan suka shiga gidan ae basu yi murna ba har sae da suka shiga gidan baba ya kira dady yayimai godiya tare da yimai dukkan fatar alkhairi.

"Su maidubu angama raba invitations har friends dinta na India sae da tagayyata Gobe ne "kamu" mama tanemi Maidubu tadawo gida yau tunda tayi sati daya a gidan qawarta zarah tare suka dawo itada Balkisu .

Ba karamin mamaki maidubu tayi ba da ganin gidan da suka dawo Dom mama ta gayamata amma bata dauka kyawon gidan yakai har haka ba .

Da gudu ta shiga gidan tana kai wani falo ta hango mama da gudu ta isa wajen ta ta rungumeta.

Yau Yakama "Monday da misalin qarfe 8pm naga anyiwa Amare shiri cikin Wata atamfa super exclusive mai ruwan fari da marrow ta sako farin gyale fararen shoe sarqa da mundayenta suma fari batayi Wata kyalliya ba a fuskarta suka shiga mota ita da Balkisu da qawayensu sannan sauran jamaar suka shiga motaci aka wuce wajen "kamu" a harabar gidan yaya Bello akayi "kamun" Dom harabar gidan tanada girma akalla xata dauki mutum Dari 9,

Akayi "kamu" aka sako waqarsu ta "kamu" daya daga cikin waqoqin da akayimusu Dom ko wanne "event! da tashi waqar.

"Waqa ce mai sanya da shiga rai sae da maidubu tayi kuka sosae har balkisu. aka yayyafa musu ruwan xam-xam akayi kade kade Harda na gargaji makada kam sunsha liqi ga dangin Amare da angwaye. Motoci sun daukosu sai gida.

"Barr ta kwanta amma bacci ya gagareta sae tunani take wae tayi kusa aure sae can bacci ya dauketa Kiraye kirayen sallar asuba ne ya tada ta. Ta tashi ta tada Balkisu sukayi sallah wayarta ce tayi ringing! koda ta duba taga Ridwan ne ta daga Daren jiya xuwa asubar Ridwan yayi mata kusan 18 missed calls ta dau wayar suka gaisa suka Dan taba fira sannan sukayi sallama.

Da misalin qarfe 4 na rana naga mai kwalliya ta chan cha dawa amare Barrister da Balkisu kwalliya ba Kadan ba sukayi shirin xuwa (friends day) Barr tayi shiri cikin wani yadi Goldin color da marrow flowers. tasaka marrow gwaggwaro da shoe marrow sarka da yan kunne da yan hannu suma marrow tasaka sunyi kyau masha Allah.

Haka akayita events masu qayatarwa Ridwan kullum sae yayita kiranta a waya Dom mai gyaran jikin ta hana Maidubu fita ko ina sae in xasu je event kawae take bari su fita ridwan yayi missing din babynshi ba Kadan ba.

Ridwan ya anso dinkunan shi na biki har da masu babbar riga Riga da wando da babbar Riga.

Kuma ko pics dinta aunties dinshi sunqi bari yagani haka ya daure Dom yasan dae duk qarewa ake abashi amaryarshi.

Yau takama Friday Ranar daurin auren Barrister Maidubu da Ridwan kuma ranar "dinner" din aurensu. Ridwan kasa bacci yayi har asuba sae xumudi yake yatashi yayi sallah ya kira madam dinshi Dom jin muryarta .

Barrister na kwance itama yau kasa baccin tayi sae tunani takeyi tana kuka wayarta ce tayi ringing ta duba taga RIDWAN ne sae da ta share kwalla sannan ta dau wayar tana fadin........

Barrister for lifeπŸ’‹

Muje xuwa wasa farin girkiπŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„

Mijin barristerβš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–
[14:02, 2/9/2018] Barista: βš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–
MIJIN BARRISTERπŸ’‹

By Barrister S@dy😘

DEDICATED 2 ALL WORLDS MIJIN BARRISTER FAN'S LOVE U ALL 😍😍😘😘

"Where re u my blood sister? Hauwa Muhammad Sanusi, here is ur page (Mrs Nasir Gwandu) u means so much 2 me, can't express how much I love u sistoπŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Mijin barrister
109-110

βš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–"Barrister na daukar wayar da sallamarta, sae da ridwan ya lunshe ido sanadin jin daddadar muryar babynshi. ""Ya fara da "fadin! ran Barrister nah ya Dade. "Tace amin tare da na angon Barrister! murmushi sukayiwa juna Ridwan ""yace......

Ridwan yace baby wallahi farin cikana na yau baya misaltuwa kan xumudin xuwanki gidana yau ko bacci kasawa nayi murmushi maidubu tayi. "wayar Balkisu ce tayi ruri itama Farouq ne ta dauka sukasha soyayya mama ce tashigo dakin nasu da sallamarta suka kashe wayoyinsu suka gaida ta mama tayi murmushi tace tau arage waya dae na tsawon lokaci Dom tana affecting kunne dariya sukayi.

"Yau takama Friday ranar weddings fatiha nasu Barrister kenan.kuma ranar dinner.

Mama tace ku tashi ga mai gyaran jikin ku nan tana Kiran ku, suka tashi sukabi bayan mama akayimasu gyaran jiki akayimasu dilka akayimasu turaren tsugunno akayimasu turaren jiki Wanda akalla zai iyakai Wata daya mutum yana qanshinsa

"Amare sunyi kyau masha Allah mai qunshi taxo tayimusu lalle irin na amarenda suka anshi sunan su tana yi ana videoting din qunshin.

"Ridwan ne yafito daga wanka yana daure da towel ya dauko wani qaramin towel ya goge kanshi yashafa mai a jikin shi, momy ce tashigo dakin da sallamarta tayi dress tayi kyau sosae itama tashigo tana fadin my son katashi kafara shiri fa time is going .

"Momy na ganin Ridwan har yayo wanka sae kawae tabishi da ido tana kallon shi, batare da tayi magana ba "" Ridwan ne yace momy lafiya sae kallona kike ? Momy ko har kin fara missing dina tun ban tafi ba? "momy tayi murmushi tace My son yau ranar farin ciki ne Dom Allah karka sani kuka kaji ..

Murmushi yayi sannan yace tau momy nah.. momy tace najika shuru na dauka ko bacci kakeyi shine nazo du baka Ashe wannan angon kan Dan gidimine har yayi wanka dariya Ridwan yayi yace Allah sarki momynah ina xan iya bacci a yau wallahi momy ko baccin dare banyi ba yau murmushi momy tayi tace ina kayanda xaka saka? Ridwan ya nunamata.

"Wata dakakkiyar shadda ce na hango akan bed dinshi light brown wace tasha kwado dark brown da hula dark brown momy ta taimakamai yagama shiri cikin wannan shadda Riga da wando da babbar Riga ( Jamfa) yasako hula yasako cover shoe suma brown color da Wrist watch dinshi ( Rolex watch) yayi kyau sosae masha Allah angon Barrister kenan.

"Momy bata ganin girman Ridwan dom har yanxu tana taimakamai wajen shiri idan yayi wanka.

A bangaren Farouq shima haka yayi kyau sosae.

Momy tafito taje bedroom dinta ta dauko turarukkanta masu tsadar gaske takoma part din Ridwan tayimai barin turaren a jikin shi ta fito ta wuce part din dady shima shirin yake ta taimakamai yagama shiri shima tayimai barin turaren tafito xuwa part dinta gidan yau ya cika maqil da mutane yan yinin biki.

"Dady yagama shiri yafito shima Ridwan yagama shiri yafito amma bayasom ya wuce har sae yaga momynshi yayi. part din momy da sauri sauri Dom har friends din shi suna mota, shi kawae suke jira su wuce wurin aurin auren.

Momy takoma bedroom dinta tayi xaune tayi tagumi tana hawayen rabuwa da danta a yau. RIDWAN ne yashigo har bedroom din da sallamarsa momy ta kawar da kanta a gefe ta share kwalla sannan ta amsa mai sallamar yashigo Ridwan ya russuna har qasa yana fadin momynah xamu wuce kiyimin fatar alkhairi idonshi sun kada sunyi jah momy tace Ridwan Allah yadawo daku lafiya yace amin momy nah yatashi yafita momy tabishi da ido.

Da misalin qarfe 3:00pm dinbin jamaar Kebbi da kewayenta suka shaida aurin auren RIDWAN Justice Aliyu & Barrister Maidubu Muhammad akan sadaki naira dubu goma sha biyar .Dana Balkisu Abdullahi & Farouq Umar Farouq akan sadaki naira dubu goma sha biyar itama. Mai martaba sarkin Makkah ne yabiya kuddin sadakinsu su duka.

Qa idar baba ne sadakin yaranshi baya tsada Dom neman albarkar aure.

Jamaar da suka shaidi aurin wannan auren sunfi a qirga akalla xasu iyakai mutum dubu biyar 5 Dom ko a titi motoci basa gudu Go Slow ne ake Dom garin Kebbi yacika maqil da jamaa duk wani hotels na Kebbi da sokoto Ridwan yakamasu Dom yiwa baqinshi masauki duk da haka sae da wasu suka kwana a Abuja suka biyo jirgin safe Dom halartar aurin auren.

Angon na hango sae hannu yake bawa mutane suna gaisawa ta ko ina kiranshi ake photo kam yashashi ba adadi duk wani juyin da Ridwan zai yi photo akeyimai wasu mutanen baima sansu ba amma suna fadin a kanshi suka xo Ridwan da Farouq suka tsaya akayi musu photo tare suka sake tsayawa da Ridwan da dady da baba da Abban Balkisu da Farouq da mai martaba sarkin Makkah akayi musu photo sannan suka sake tsayawa dady kawae da ridwan akayimasu su biyu .

Matane sae shaking hands suke da ridwan sunayimai fatar alkhairi taro yayi taro dady yashi mota tare da mai martaba sarki bodyguards dinshi suka shiga nasu motocin suka wuce Ridwan sae gaisawa yake yi da jamaa.

Da qir yasamu mutane suka bari yashiga mota shida friends dinshi bodyguards dinshi suka shiga motocin su suka dau hanyar gida.

Makadane ba Kadan ba suka taru a gate din gidansu Ridwan aka bude masu suka shigo sae kade kade suke da bushe bushe motarsu Ridwan na isowa makadan sukayo kanshi suna yimai kade kade.

Ridwan yafito mota shida friends dinshi RIDWAN yafitar da bandur din yan dubu dubu ya fara yimusu kari sae da suka kare ya fitarda wani bandur yakarar dashi dady ne yaja hannunshi don ya lura idan ya kyale ridwan ba karamar riya zai yi ba. dady yaja hannunshi wani makadin yace Allah yabarka da barrister har mutuwa ae Ridwan sulale hannunshi yayi daga rikon da dady yayimai ya dauko bandur biyu dubu Dari biyu kenan yamiqawa wannan makadin.

Dady yasamu ya sake riqo hannun Ridwan shida friends dinshi suka wuto Dom shiga main falon gidan Dom dady ya hada liyafa a gidan momy suka hango nafito wa a bangaren ta an turomata wani baro maqil da kaya tana tafiya ana Binta da baron.

Dady ne yace wify ina xuwa kuma haka? Tace husby zan je harabar gidannan ne Dom nuna farin cikina dady yace miye wannan kayan momy tace lace ne da shaddodi da materials da atamfa xan rabasu ne ga wadanda suka xo tayamu murnar wannan ranar.
sorry fa husby dole ne yau mu batama naira rai dolene mu fidda naira dole ne muyi abunda yakama ta katuna ko kai waye Kaine fa JUSTICE ALIYU niko JUSTICE HUWAILA.

Kuma dolene jamaa Susan anyi bikin yan gata RIDWAN JUSTICE ALIYU DA AMARYARSHI BARRISTER MAIDUBU dady yayi murmushi yace Allah ya kyauta.

Ridwan yace nagode momynah sae momynah Allah yakara nisan kwana sae da tadan yi rawa tun a gabansu duk sukasa dariya ta wuce.

Kade kade da bushe Bushe kawae kakeji haka momy tashigo filin tafara wasa da naira tana yiwa makada liqi da turame .

Wani makadi ne yafara rera Wata qawar wace sae da momy ta juyo da sauri Dom ganin ko waye momy ta fara yimai liqi tayimai karin turamen atamfa sunfi 10 aunty Sarah ce tace momy kinfi yiwa wannan kari fa.

Momy tace waqar da yakeyi tanada matuqar muhinmanci agareni irinta akayi min a ranar a xaa kawoni gidan dadynku momy tace I really miss dat day. aunty Sarah tayi dariya..

A bangaren amare kuwa su baba nafita kofar gida Dom dauro aurensu. Barrister ta ruga da gudu tashige daki tafada kan bed tafashe da kuka Balkisu ta fada kan bed din itama tafashe da kuka akayi ta aikin rarrashi amma sunqi yin shuru har mama tayi tayi sunqi daina kuka haka ta haqura ta kyalesu.

Har Mai gyaran kai taxo sae da akayi daqir sannan suka fito akayimasu gyaran gashi.

Mama ta dauko mai turaren gidan har Dubai. aka kaita gidan maidubu tayi mata turaren gidan ba gidan Amarya ba kawae har shiyar baki daya sae da tadau qanshin turaren aka kaita gidan Balkisu tayimata itama.

Da misalin qarfe 8 na dare akayiwa amare shiri dom xuwa dinner daga can kuma sae gidajensu na aure.

Mai kwalliya tayimusu kwalliya sunyi kyau ba Kadan ba Barrister tayi shiri cikin yadin amare Sky blue da farin gwaggwaro fararen shoe sarqa da yan kunne da yan hannunta suma farare da farin Net ta axashi akan gwaggwaron ta tayi kyau Masha Allah.

Wata qanwar mama ce tashigo taja hannun amare xuwa falon Baba. Baba yayiwa amare hudubar xaman aure su Maidubu ansha kuka ba Kadan ba. inna tayimasu tata hudubar itama sunyi kuka har inna mama tana part dinta taqi fitowa wae bata iya ban kwana da yaranta.

Baba da kanshi yaje yafito da ita mama tayi xaune kawae takasa magana Dom kuka yaci qarfinta sosae baba yace idan bata iyawa a wuce xasu kawae.

Maidubu ta rushe da wani sabon kuka har baba sae da yayi kukan Maidubu ta russuna har qasa tace ya mamanah Dom Allah kiyimin hudubar da ko wace uwa take yiwa yarta kuma ki yafemin duk wani laifin da nayimaki a iya rayuwata mama ta sake fashewa da kuka aka tadasu har sunkai kofar falon mama tace Maidubu !

Maidubu ta juyo tana kuka sosae itada Balkisu mama tace hudubar da xan yimaki shine kibi Allah kibi mijinki

Ita ce Hudubar da manxon Allah (S.A.W) yayiwa yarshi fadimatu bintu Rasulu ta qarshe kibi Allah kibi mijinki.

Maidubu ta fashe da kuka itada Balkisu suka suka rungumi juna mama tace duk abunda kikayimin daga ranar da kika xo duniya har yau na yafemaki Allah ya yafemana baki daya.

Qanwar mama da aunties din Maidubu suka jasu aka fito xasu maidubu kuka take kamar ranta zai fita mama ma kuka take sosae Dom duk yaranta tafi shaquwa da Barrister dangin Amarya Maidubu Dana Amarya Balkisu Dana angwayensu suka shiga mota Dom kai amare gidansu daga can a wuce dinner.

Motocine na rikan amare a gate din gidansu Barrister sunfi hamsi 50 mota daya suka shiga Barrister da Dr innah tayimasu rakiya har mota da kanta ta kulle masu mota sannan ya juya takoma gidan Dom mama ta mayarda innah a nan gidan.

Motocinsu sun shiga layi sun hau hanyar gidan Ridwan ga kida na tashi a motocin har suka iso gate din gidan Ridwan......

Barrister for lifeπŸ’‹

Muje xuwa wasa farin girkiπŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„

Mijin barristerβš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–
[14:04, 2/9/2018] Barista:

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login