Showing 30001 words to 33000 words out of 88044 words
Chapter 11 - MIJIN BARRISTER Complete Hausa Novels By Sadiya Barrister.txt
ukku itama Mai-dubu ta mutu ko malam?
Malam shehu yace aa tana da rai, saedai bata hayyacinta har yanxu, ya nuna masu dakin da akayiwa Mai-dubu masauki mama tayo dakin da gudu tana kuka,
Baba yabi motarsu Malam shehu aka wuce da gawar Ahmad sae da suka kaishi dakin malam shehu sannan jamaar gidan suka dau kuka suna fadin yau bangon jingina ya fadi, kasancewar Ahmad shi yake dauke da nauyin kowa a gidan, har mahaifinsu dom yayi retire, Alhj Muhammad "yace xai koma hospital tunda (funeral) din Ahmad sae gari ya waye.
Baba ya koma hospital yashiga room din da Mai-dubu take yasamu mama har yanxu kuka takeyi Baba yayi tsaye yana fadin wallahi nayi danasin haihuwar maidubu, mama dae bata tanka shi ba.
Ana fara kiraye kirayen sallar asuba, maidubu ta fara bude idonta a hankali tana fadin dom Allh muyi hakuri karku kashe shi, nashiga ukku ni maidubu Dom Allh karku kashe shi, sae kuma ta fashe da kuka mama ta riqeta tana "fadin Mai-dubu! maidubu!! Mai-dubu!!!, maidubu "tace waye? mama "tace Maidubu nice mamanki! "maidubu tace mama ina ne nan? Mama tace hospital ne! Mai-dubu ta fashe da kuka tana Fadi mama ina Ahmad? duk da batason Ahmad bata qaunarsa amma taji tausayin rayuwa.
" Baba ne yashigo room din ya dauke maidubu da mari, "yana fadin wa kike tanbaya ina Ahmad, ae kinfi kowa sannan kun hada kai keda wannan tsinan nan yaron Ridwan kun kashe Ahmad, sae kuma baba ya fashe da kuka yana fadin Mai-dubu idan dae nine ubanki na roqi Allah ya tsine maki albarka, kuma wallahi sae dae ki nemi wani uban bani ba. Mama "tace ashsha haba Baban yara 'yar, da kuka Haifa kake tsinewa, baba "yace 'yar da kika haifa dai, amma nikam Mai-dubu ba ya ta bace.
Maidubu ta tashi ta sauko akan gado tana kuka mai sauti ta russuna gaban baba tana "fadin yakai mahaifina dom Allah ka saurareni ka fahinceni,
βππππππππππππππβMai-dubu "tace wallahi baba banada masanniya akan kisan Ahmad. Baba yayi wa Mai-dubu wani wawan shuri har saeda takai ga bango, ta fadi qasa sumammiya kanta ya fashe sae jini yake fiddawa.
Baba ya maido kallon shi ga mama wacce tayi gurin mai-dubu ta rungumeta tana kuka sosae tana jijjigata, Baba "yace ke tashi muje gida! mama ta dago kai tana "fadin baxan je ba, ba inda banje in bar ya'ta a wannan halin.
Baba "yace tau bara kiji wallahi idan har nakai gate din hospital, kina nan wallahi bakin aurenki, mama ta dago kai da sauri tana karewa baba kallo "tace maganar saki fa kakeyi baban yara? "yace kwarai kuwa ya juya ya wuce huuu.
Mama ta fashe da kuka sosae, sannan ta kalli Mai-dubu tana kuka "tace Mai-dubu ni! mahaifiyarki, na yarda dake, kuma na yarda da Bakida sa hannu akan mutuwar Ahmad, Mai-dubu Allah ya tsaremin ke aduk halinda zaki sami rayuwar ki, sae kuma mama ta sake fashewa da kuka tana "fadin Mai-dubu Allah yayimiki albarka! Allh yabaki Wanda zai taimakeki, ya taimaki rayuwarki, taimakon da mu iyayenki muka kasa yi miki, duk wannan maganar da mama keyi Mai-dubu bata sani ba, Dom tana kwance ne qasa sumammiya, mama ta fito tana kuka sosae, ta shiga mota suka wuce gida, koda suka isa gida har 6 na safe tayi sannan sukayi sallar asuba.
Da misalin qarfe 8am akayi "Funeral" din Ahmad aka kaishi gidan shi na gaskiya, sae da aka bixne Ahmad, sannan malam shehu ya kalli inda aka saka sanshi sae kawae ya fashe da kuka sae da aka rikashi suka koma gida. Allah Sarki duniya!
Jamaar gari sae jimamin mutuwar Ahmad suke yi wasu na "fadin wannan mutuwa ta Ahmad tanada sa hannun Ridwan saurayin maidubu wasu na fadin har duka momyn Ridwan tasa anyi mai jiya kuma gashi antashi yau da gawar shi kuma duk bodyguards din ta suna da bingida shima ahmad kuma da bingida ne aka kasheshi har (Police) sun baxa tsaro sosae a garin, ba shiga ba fita, duk inda ka dubu police ne.
Mutuwar Ahmad ta karade garin kebbi da kewayenta. mutane sae xuwa gaisuwa sukeyi gidan iyaye Ahmad har wadanda basada alaqa dashi gidan iyayenshi ne ake xaman makoki dom gidan shi bakowa sae maigadi.
Wata doctor "ce ta shigo room din Mai-dubu, taganta kwance cikin jini, ta karaso da sauri, tana fadin subhanallah!!! ta kira wani doctor suka maida maidubu akan gado, suka shiga bata taimakon har ta farfado.
Doctor ta koma office dinta, Mai-dubu na farkawa ta tashi ta leko bataga kowa a ajen dakinta ba, ta fito tana ganin juwa. har tasamu ta kawo titi da qar tashiga napeep tana nazarin ta inda zata fara sae ta tuna batada wasu kayan sakawa a gida bayan na jikinta sae kawae ta kwatantawa mai napeep gidan Ahmad, tace ya kaita can, suna isa ta kwankwaso gate din gidan maigadi ya leqo, yana ganin Mai-dubu yayi saurin bude gate din gidan, Mai-dubu ta shigo gidan taga bedroom din duk digaggan jini ne, taga duk dakin hargitse ga bulalar da yayi mata duka, da ita ajiye, sae kawae ta fashe da wani sabon kuka, tayi kneeling tana kallon gabas tana fadin,
Ya Allah ga boyarka a tsananiπ Ya Allah nasan baka kuskure, ya Allah nasan duk abunda kayimin gata ne agareni, Ya Allah kafiddani cikin wannan tsakanin rayuwarπ Ya Allah ka fiddani ga zarginda mahaifina kemun, Ya Allah ka jarabceni da auren dole na rungumi wannan qaddarar. Ya Allah ka jarabce mahaifina da qiyayyata na rungumin wannan qaddarar. Ya Allah ka jarabceni da ganin mutuwar Ahmad kuma a dakin auren mu daga ni sae shi, Ya Allah kai kadaine shaidata akan banada hannu akan kisan Ahmad, sae kuma ta fashe da kuka sosae tana "fadin Allah ka fiddani a wannan qangin ka fidda masoyina RIDWAN Ya Allah kabani ikon cin wannan jarabawar da kayimin ta Fadi maganar tana kuka sosae.
Kuyi hakuri da jina da kukayi silent yau nasamu kaina busy ne da fatar an yimin afuwa.
Barrister for lifeπ
Muje xuwa wasa farin girki ππππ
Mijin barrister βππππππππππππππβ
[19:49, 1/7/2018] Barista: βππππππππππππππβ
MIJIN BARRISTERπ
By Barrister S@dyπ
Sadaukarwa ga Zahra Muhammad mahmud surbajo kina raina day nd night da sonki nake kwana dashi nake tashi ππBarrister ta gaishekiπ
Readers kuyi hakuri da masu fadin basuji dadin mutuwar Ahmad ba sunso yaga auren maidubu da Ridwan, da masu fadin kwara da Ahmad ya mutu Dom ta auri Ridwan duk wacce taga rashin dai daina tayi hakuri, inada labarin ne daga farko har qarshe kuma a tsarin littafin dolene Ahmad ya mutu, reader's kuyi hakuri da writtersπ
Mijin barrister
65-66
βππππππππππππππβMaidubu ta tashi ta janyo akwatinta sae lokacin ta tuna da inda Ahmad ya nunawa yan fashinnan inda ya aje jakar taje ta dauko ta tasaka ta a dayan akwatinta, ta fito tana kuka ta shiga napeep sae kofar gidansu, ta shiga gidan ta samu mama na kitchen baba bayanan, ta wuce dakinta ta aje kayanta ta cigaba da neman wayar da bindigar, amma bata gansu ba tana cikin neman ne taji motsi a waje tana fitowa suka hado ido ita da mama ae ko mama ta karaso da gudu ta rungume yar'ta Mai-dubu kuka mama kuka.
Baba ne ya shigo gidan, jiki a sanyaye yana ganin Mai-dubu bacin ranshi ya qaru, baba ya hade fuska sosae kamar bai taba dariya ba.
Ya fara da "fadin ke wa yayi miki ixini xuwa nan gidan? Mi kikaxo yi? ko muma din xuwa kikayi ki kashemu ?tau bara kiji wallahi! Kiyi maxa kibar gidan nan, Maidubu ta kalli Babanta tana share kwalla "tace baba nan ne gidanmu, kuma kaine mahaifina idan nabar nan gidan ina zanje?
Sae da Baba ya cije bakinshi ya kwadawa Mai-dubu shoe din shi a kai inda akayi mata dinki ya sake faccewa sae jini yake fiddawa Kasancewar shurun da yayi mata daxun sae da akayi mata dinki .
"Baba yaci gaba da fadin ni ba ubanki bane, Allah ya tsaran in haifi dan da ke neman ganin bayan raina, kije dae can ki nemi ubanki, da kika tanbeni inda zakije ki bi duniya mana, na fiki sanin inda ake xuwa ne dom sayarda mutunci, ga gidan karuwwai nan daban dabam kisamu Wanda kikayi joining mana, kuma ki fita idona wallahi Kiyi maxa kibar gidan nan kafin in kasheki, dom rayuwarki batada wani anfani a garemu Mai-dubu sae aikin kuka takeyi.
Baba shiga daki da alama abun bugu zai daukko mama ta kalli maidubu "tace Maidubu ban yafe maki ba kibi duniya kamar yarda babanki ya furta, inason Kiyi hakuri ki jure wuya da duk tashin hankali da kika sami kanki, kije gidansu Balkisu ki xauna har babanki ya gama fushinshi, nasan da kanshi zai nemeki maidubu ta dauko hijjab dinta ta kulle dakinta ta rike key a hannunta.
Baba ya fito rike da bulala yana fadin tau tunda makyajin magana ki jirani inxo, yana sako shoe din shi Mai-dubu ta kalli mama "tace yake mahaifiyata nasan idan kowa yakasa fahinta ta nasan ke kin fahinceni, kuma kin yarda da tarbiyyata wallahi mama ban aikata ba, kuma banada sa hannu a kisan Ahmad ta fashe da kuka .
Mama "tace nafi kowa sanin baki aikata ba, ya'ta, Mai-dubu "tace mama zan tafi kuma nayi maki alkhawarin kare mutunci na aduk inda na sami kaina Mai-dubu ta riqe mama itama ta riqeta duk suka sa kuka.
Baba ya iso wajen yana shirin dukan Mai-dubu, mama ta riqe shi tana "fadin dakata baban yara ko baka qaunar maidubu ni ina qaunar ta! kuma Wallahi sae haqqin wannan yarinyar ya bika, baba "yace kice in mutu yau din nan sannan insan naci amanar maidubu kuma ki saki bulalar nan ko in dakeki wallahi .
Maidubu ta russuna har qasa ta kalli babanta "tace kayi hakuri yakai babana bantaba ganin sabaninku ba, Dom Allh kuyi hakuri karku fara akaina. baba "yace idan ma bamu taba yi ba, ae munyi a zamanin ki tsinanniya kawae,
Maidubu "tace baba zan tafi kamar yarda kayimin umurni, kuma insha Allh baxan qara dawuwa nan gidan ba, har abada. baba "yace da kin kyautawa kanki.
Maidubu taci gaba da "fadin baba inason kasa a Ranka har yau banada sa hannu a kisan Ahmad, kayi hakuri baba banyi rashin kunya ba idan nace lokacin da zakayi da kasani wulaqanta yar'ka da kanka! yana nan xuwa, sae dae zuwa lokacin nadamar ka bata da anfani .
Baba ya fashe da kuka yana "fadin tsinuwar da nayi miki akaina ta fara aiki kenan maidubu, keda idan ina magana bakya tada kai sae na qare yau ni kike gayawa sae nayi nadama, lallai ni Alhaji Muhammad nayi baqar haihuwar.
Tau wallahi kibar gidan nan tun ban kiramaki police ba .
Mai-dubu "tace yi hakuri baba idan na batama sannan ta maido kallon ta ga mama ta bata key din dakinta "tace mama Dom Allh kayimin alkhawarin duk wuya duk rintsi baxaki bar kowa ya shiga dakina ba da hakan zan tabbatar da har yanxu kina qaunata. ta fashe da kuka ta fita.
Mama ta rushe da kuka itama "tana fadin zama da kai ko hasara wallahi ayau din nan nayi danasanin auren ka kuma ba dom mahafiyata "tace idan na kuskura na bar gidanka ba tare da kai ka koreni ba ko tana lafiya bata yafemin ba shine maganarta ta qarshe dani Allah ya dauki ranta. da yau din nan nabar gidanka baba dae bai tanka ta ba yashige dakin shi .
Maidubu na fita tayi gidansu qawarta balkisu, tana shiga inna ta qaraso wajen ta da sauri, "tana fadin Mai-dubu lafiya? Miyasameki haka? Inna ta cire Dan kwallin Mai-dubu ta daure mata inda jini ke fita, Maidubu ta fashe da kuka ta rungumi inna, sannan ta kwashe duk labarin abunda ya faru ta gayama inna, inna ta dau taslima hawaye nabin idonta duk Wanda yasan maidubu ya ganta yanxu da qar ya ganeta Dom tayi baqi tayi rama amma har yanxu kyanta yana nan. inna ta xaunar da ita "tace zasu xauna da ita har babanta yadaina fushin da ita, ko idan gaskiya ta bayyana Mai-dubu "tace inna ko angane gaskiya baxan koma gidanmu ba, dom baba baya qaunata nima bana qaunar..... Inna tayi saurin dakatar da ita da "fadin 'kul maidubu kar ki bari kiyi qusquren furta mummunan kalami akan mahaifinki.
"Jita jitar da mutane keyi akan Ridwan da momyn shi, wae sunada sa hannu akan mutuwar Ahmad yakai ga yan sanda kuma qanin Ahmad yayi alkhawarin ko duk dukiyar da Ahmad ya bari zata qare sae sun nemo mai haqqinshi, na kisan da akayiwa yayanshi. sae ankama wadanda suka aikata wannan kisan ko su waye, yakai report ga police Dom yaji labarin Ridwan har dukan da momy tasa anyiwa yayanshi Ahmad, sae dae police na hangen matsala daya xuwa gidan JUSTICE ALIYU DA JUSTICE HUWAILA.
Wani daga cikin police din ya dauki report din qannan Ahmad yakaiwa Commissioner of police, tare da neman ixinin xuwa kamun Ridwan Dan gidan JUSTICES ALIYU DA HUWAILA sae da Commissioner ya tashi tsaye da sauri ya doki tebur yana fadin nop!!! kar Wanda yayi kuskuren xuwa gidan JUSTICE ALIYU Dom kamun dansu shida JUSTICE HUWAILA tau bara kaji in gayama JUSTICE HUWAILA kadai ta isa tasa duk kanninmu a sallamemu akan wannan kujerar dom haka kujira sae na kira JUSTICE ALIYU dom neman ixinin shiga gidan shi, dom kamo dansu RIDWAN.
Barrister for lifeπ
Muje xuwa wasa farin girkiππππ
Mijin barristerβπππππππππππππβ
[11:16, 1/8/2018] Barista: βπππππππππππππβ
MIJIN BARRISTERπ
By Barrister S@dyπ
Sadaukarwa ga Zahra Muhammad Muhmad Surbajo π€π
Mijin barrister
67-68
βππππππππππππππβCommissioner ya daga waya ya kira "JUSTICE ALIYU" suka gaisa cikin ladabi da girmamawa. Commissioner yayi shuru dom yama rasa ta inda xai fara yiwa Justice bayani, Justice "yace uhim ina jinka commissioner! ya kayi shuru.
Sannan Commissioner "yace sir, "sir Ridwan" ne ake xargi da kisan wani Ahmad Wanda sukayi neman yarinya daya. Justice na kwance yana hutawa jin abunda commissioner ke gayamai yasashi tashi tsaye da sauri yana fadin qarya ne! wallahi qaryane! Ridwan ko tsuntsu baya kashi balle mutum, wannan kawae bita da kulline kuma ni ake yiwa Dom na gagara ne aka juya ga dan da nafiso dan da nakeso fiye da rayuwata amma ba komi.
JUSTICE "yace commissioner mi kuke buqata ne yanxu? commissioner "yace "am sorry sir, permission dinka muke nema Dom xuwa kamun RIDWAN, sae da JUSTICE ya runtse idonshi Dom jin maganar zaaje kamun RIDWAN sae da idanunshi suka cika da kwalla.
JUSTICE "yace Commissioner U re permitted amma inason kasani wallahi! koda alama kar wani yayi qusquren dukan RIDWAN ko yimai mummunan kallo duk Wanda ya taba lafiyar Ridwan! yasani ya taba kujerar sa. Commissioner "yace ok sir, thank you sir, JUSTICE ya kashe wayar shi ya kira wani bodyguard din shi "yace ya hada musu kayan su kuma kowa ya hada nashi kayan zasu koma gida Nigeria yau din nan.
Bodyguard din "yace ranka ya Dade Nigeria fa? JUSTICE "yace eh ko mu barka nan ne? Bodyguard din "yace No sir, Sorry Sir .
"Yafita yasami sauran yayi musu bayani duk suka shirya" jet "dinsu kawae suke jira yasha mai su diru Nigeria.
Motocine na police har guda 3 ko wacce cike take da police, suka wuce gidan JUSTICE. suna isa suka fara firfitowa ko wannen su da bindiga a hannun shi, suka zagaye gidan wasu suka shiga gate din farko, suna shiga gate na biyu Wanda ke sadaka da cikin gidan,
bodyguards suka taresu police suka fiddo bindigoginsu suma bodyguards suka fiddo nasu dom sun aje ne da subasu damar shiga cikin gidan gara kawae suyi farin wuta kowa ma zai mutu ya Dade bai mutu ba.
Daya daga cikin police din ne yayi wa police, umurni da kowa ya sauke bindigar sa. DA alama shine babbansu. Ya maido kallon shi ga bodyguards din momy "yace salamu Alaikum. suka ansamai da Amin waalaikassalam. Dom Allh ku yi hakuri nasan kuna Bakin aikin ku ne nan muka sameku amma yanxu mun gane kuskuren mu naqin neman ixinin ku. kuyi hakuri kuyi mana sallama da yaron gidan nan Ridwan. Bodyguards suka ce, Ridwan bayada lafiya.
"Police din "yace OK momyn shi fa? Daya daga cikin bodyguards dinne ya kira wayar momy ya sanar da ita xuwan police din. Momy ta fito tagansu ba Kadan ba, haka kuma taga bodyguards dinta suma duk sun halarci Copound din gidan Dom jin meke tafe da police a gidan.
Dayan police dinne yayiwa "momy bayanin abunda yakawo su, momy ta fiddo ido waje "tana fadin qarya, Ridwan ko tsuntsu baya kashe balle mutum, Dom haka kuyi gaggawar barin gidan nan tun Muna gane juna.
Police din ya koma gefe ya kira Commissioner ya gayamai abunda momy "tace. Commissioner "yace kar wani yayi qusquren jayayya da ita, mubani 2 minute inyi waya da mijinta. Police din "yace OK sir.
Commissioner ya kira "JUSTICE ALIYU" ya gayamai. Justice Aliyu ya kira Matar shi, justice HUWAILA "yace da ixinin shi akaxo kamun RIDWAN momy "tace da ixinin ka fa kace? "yace ki basu shi kawae.
" momy tace haba husby, ya axayi inbari a fita da RIDWAN gidan nan bayan nasan bayada laifin, justice "yace "wify idan har na isa dake ki basu dama su fita da RIDWAN,
Kuma karki damu ina hanyar Nigeria. momy "tace baka ce sae kayi 3 month acan ba justice "yace dolene in dawo yanxu karki manta Ridwan bayada kowa sae Allah sae mu. Momy "tace wishes u safe trip husby" Justice ya ansa da "thank you wify".
Momy "tace ina shaidar ku ta Kama my son suka bata warrant of arrest ta ansa ta karanta sannan tace su shiga dom RIDWAN bayada lafiya har baisan ko waye a kanshi ba. Ta shiga gaba tana fadin follow me, suka bi bayanta suka shiga room din momy dom ta maidashi dakinta tunda bayada lafiya.
Ridwan ne kwance baya ko motsi kuma ba suma bane yayi ba. dom wani lokacin yakan bude ido yabi momy da kallo idan "tace yadae my son sae ya lunshe ido batare da yayi magana ba.
Suka ganshi