Showing 15001 words to 18000 words out of 88044 words

Chapter 6 - MIJIN BARRISTER Complete Hausa Novels By Sadiya Barrister.txt

15 Nov 2025

1924

ma karama mana Ahmad yayi maganar cikin tsawa yana rike da kolar rigar maigadi tsohon sae kuka yake yana fadin Dom Allh alhaji kayi hakuri duk da bansan abunda nayima ba Ahmad ya sake wanke tsohon da mari yana fadin ohhh bakasan abunda kayimin ba ko yasake wanke shi da mari sae da tsohon nan ya Fadi kasa malam shehu ne ya iso wajen yana fadin subhanallah Ahmad mi maigadin nan yayi ma wai malam naxo gate inata yimai hone har na tsawon minti 3 sannan ya budemin gate

Malam shehu yace haba Ahmad wannan wanne irin rashin kunya ne gareka ina ganin ka girma Ashe kai har yanxu bakada hankali ya xaka daki tsohu kamar wannan da koni ubanka yayi kusa haifata Ahmad yace haba malam ya xaka tsayarda ni agaban talakkana wanda ke cin abunci a qarqashina kana yimin fada gaskiya malam banaso idan fada xakayimin kabini cikin gida mana idan naje dakina basae kabini acan din kayimin fada ba malam dae da mamaki yayi wa yawa tsaye kawae yayi yana kallon Ahmad maigadi ko na duqe kuka kawae yake Dom baa taba dukanshi haka ko sanda yana yaro balle kuma yanxu malam yabashi hakuri ya wuce masjid

Ahmad ya shigo dakin shi ko kayan jikinshi bai rage ba yahaye makeken gadonshi yana huci kamar wani xaki yana tuno abunda Mai-dubu tayimai tun ranar da suka hadu har yau da tasake marinshi ya tashi tsaye yana fadin ko namiji baya ja dani balle macce na daki maxa amma sunkasa daga hannu su rama sae macce macce ma yarinya tabbas kinyi baban kuskure Wata xuciya tace Ahmad karka bari wannan yarinyar tasaka ma ciwon.....

Barrister for life馃拫

Muje xuwa wasa farin girki馃憚馃憚馃憚馃憚

Mijin barrister鈿栶煄€馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰鈿�
[16:41, 12/27/2017] Barista: 鈿栶煄€馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰鈿�
MIJIN BARRISTER馃拫

By barrister s@dy馃槝

I dedicate dis page 2 my lovely sisters
Ummu Abbakar gari (maman musty)馃槝
Sumayya Alkhali Bello馃拫
Amina Umar limanci馃槏
Rakiya Isah馃槝
Love u all 馃拫馃拫馃拫馃拫


Mijin barrister
39-40

鈿栶煄€馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰鈿杒ar tasa ciwon xuciya ya kamaka Wata xuciyar tace Ahmad kaje kawae ka kasheta yace yes har ya tashi Wata xuciyar tace ah ah Ahmad kar ka kasheta yanxu sae ka aureta ka mureta sannan ka aiwatar da nufin ka a kanta yace wannan kuma gaskiya ne yayi kwance akan gado tsanar maidubu sae karuwa takeyi a ranshi

bangaren Mai-dubu kuwa tana shiga gida ba kowa a filin gidan ta wuce kawae dakinta tana shiga ta rage kayan jikinta ta kwanta amma ina bacin rai ya hanata bacci sae kawae ta tashi tai toilet ta dauro arwallah ta fito ta shinfida darduma ta dauko Qur'anin ta ta fara karantawa ae ko ba jimawa taji duk bacin ranta ya gushi Qur'ani kenan waraka akan duk Wata damuwa

Yau takama Wednesday maidubu na hango a skul da frnds dinta na skul kasancewar qawarta xarah har yanxu tana sokoto suna fira da sauran frnds dinta har malamar su tashigo suka fara daukar darasi har aka tashi baba yaje ya dauko maidubu suka dawo gida

Akwana atashi na Allah ne yau takama ranar Friday da xaayi baikon Mai-dubu da Ahmad Maidubu na tashi bacci ta nuno yau ne Ahmad xai fara taka mataki na farko na mallakar ta sae kawae ta fashe da kuka tana fadin ya Allh gani gareka Allh kayimin mafita akan wannan qangin rayuwa Mai-dubu ta shiga toilet tai arwallah ta fito tayi raqaa biyu ta idar tana addua tana kuka har gari yawaye ta fito ta gaida iyayenta ta koma daki ta share dakinta ta fito ta share na mama sannan almajiri ya share filin gidan maidubu ta shiga kitchen ta hado kayan breakfast ta kaisu akan dinning table ta sakawa kowa suna ci suna fira itadae maidubu taka sa cin komi amma bata bari iyayenta suka gane hakan ba har suka kare

Da misalin qarfe 5 na yamma na hango qawayen Mai-dubu a gidan Kasancewar xarah ta dawo jiya da yamma suna xaune suna yiwa Mai-dubu tsiya wae amarya itadae ta kasa ko tanka su Baba ne ya shigo da mutane ba Kadan ba sae Allh ya kyauta suke Fadi mama ce xaune a falo itama da ita ne da qawayenta Mai-dubu najin ana fadin Allh ya kyauta Allah ya nuna mana ranar biki hankalinta ya kara tashi ta fashe da kuka na ban tausayi qawayenta ne suka taso suna bata hakuri qawarta baliksu da qawarta xarah har suka samu ta natsu akayi sallar magarib kowa tayi gidansu aka bar Mai-dubu kawae a dakinta ta kara fashewa da kuka tayi mai Isar ta sannan tayi bacci

Auren xarah ya qaraso Dom yau takama Monday su Mai-dubu qawayen amarya ba xama hidimomi sunyi yawa Dom har sun fara raba invitation ga qawayensu na kusa Dana nesa aka fara shagalin biki anyi biki sosae anyi lafiya anqare lafiya amkai amarya a gidan mijinta Nura sae xumudin xuwan amaryar shi yakeyi abokkanshi suka rikashi har dakin amaryar sa

鈿栶煄€馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰鈿朩ashe gari tunda safe xarah ta fara kiran qawayenta tana yimusu sannu da hidima tana kuma cewa yaushe xasu xo Dom Allh suxo da safen nan sukace OK

Xarah ba taga qawayenta ba har 12 na rana sannan sukaxo suka yita yiwa amarya xarah tsiya wae ansha first night xarah dae sae dariyar su takeyi tana fadin kujira naku lokacin hardai ke Mrs Ahmad maidubu tayi dariya tace wanne ahmad ae koshi yasan ko yana hauka baxan yarda dashi ba har in bashi kaina Allh ya kikaye duk suka sa dariya xarah tace tau gamu gani suka ci kaxar amarya sannan suka anshi kayan girkin angwayen suka je suka hado abunci naji da gani da drinks suka dawo gidan amarya da kayan

Magarib nayi angon xarah da frnds din shi suka xo cin abuncin amarya frnds din amarya sukayi serving din ango da frnds din shi sukaci abinci kuma suka yaba da irin dadin da abuncin yayi suka bada tukuicin girki na 2000k suka tashi daga nan naga daya daga cikin abokan ango duk inda maidubu tayi yana biye da ita da ido har ta lura da irin kallon da yake yimata sae kawae ta tashi ta shege warta dayan dakin xarah tayi xamanta acan

Abokin angon nan ne yaga har suna xancen tafiya amma baiganta tafito ba sae kawae yakasa jurewa ya kalli duk jamaar wajen yace shin banga dayan qawarki ba amarya xarah tayi dariya sannan tace ohhh maidubu kenan tanacikin daki yace xan iya shiga inganta xarah tace why not yayi dariyar jin dadi sannan yace thanks u amarya duk suka sa dariya suna fadin ko har kakamu ne dariyar yayi shima sannan yace sosae ko nakamu wallah dom wannan kamun baixo da sauqi ba duk suka sa dariya bai jira ansar su ba ya shige dakin

Ya shiga da sallamar sa Mai-dubu na kwance akan dayan gadon xarah Dom gado biyu aka yimata masha Allah Maidubu tayi saurin gyara kwanciyar ta sannan ta ansa mai sallamar ya shigo da murmushi shi sannu yan mata yawwa sannun ka yadae kika shige daki kekadae mutane na falo ko bakida lapia ne Mai-dubu tace ah nop lafiyana qalau wllh kawae dae bancika son hayaniya ba shiyasa OK gud

Yahau bed side drower ya xauna yana qarewa Mai dubu kallo tare da yaba kyakkyawar surar da Allh yayi mata sae murmushi kawae yakeyi sae da Mai-dubu ta gaji da kallon da yake yimata tace yadae amma ko mutsawa baiyi ba ta qara magana nan ma ba ansa sae da ta furamai iskar bakinta mai sanyi da qanshi nan fa ya lunshi ido ya bude su yana fadin wow Dan qara sae da kunya ta kama Mai-dubu tayi murmushi ta dauke kanta sauran abokkan angon ne suka ce wae xaka fito mu wuce ko sae mun tafiyar mu ya tashi tsaye yana murmushi yana kallon ta sannan yace pls can I hav ur phone number baby Mai-dubu tace nop yace why banada waya yayi dariya sannan yace Haba baby yana yuwane Allh banada waya tau miyassa dadynah ne bayason inyi wayar yanxu sae na kammalah karatu na yace akwae wayar da xan iya samunki da ita tace aa Haba baby karki saka rayuwata a garari fa wallahi inason ki kuma da aure nakeson ki idan ina tunanin wani abun ki bani damar ganin magabatan ki nayi miki alkhawarin yau din nan xanje kuma banqi a aura aurenmu a gobe ba ........

Tau fa ga qoshi ga kwanan yunwa koya Mai-dubu xata kaishi gidansu ohooo

Barrister for life馃拫

Muje xuwa wasa farin girki馃憚馃憚馃憚馃憚

Mijin barrister鈿栶煄€馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰鈿�
[21:56, 12/27/2017] Barista: 鈿栶煄€馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰鈿�
MIJIN BARRISTER馃拫

By Barrister s@dy馃槝

Sadaukarwa ga Mijina 馃槝 Masoyina angona馃槝 nurul hayat 馃槝nurul qalbina馃槝 farincikina馃槝 abun alfahari na 馃槝Allah yabar mu tare har abada 馃憦Allh yabar so da qauna na haqiqa馃憦 I love u wit all my heart dear soulmate .......馃槝

Mijin barrister
41-42

鈿栶煄€馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰鈿朚aidubu na komawa gida tunanin wannan mutumin ya hanata sukuni sae ganin murmushi sa take yi a duk wani mutsi nata tsakani da Allh gayen ya hadu sosae masha Allh

A bangaren abokin angon xarah kuwa ya koma gida yakasa yin komi ba abunda yake Gani sae maidubu a idonshi ba abunda yake muradin sake gani sae maidubu haka yakwana har asuba baiyi bacci ba tunanin Mai-dubu kawae yakeyi Dom shi tsakani da Allh yakeson Mai-dubu ae ko yana qare sallah yadan yi breakfast ya kira ango da waya hello abokina naam abokina ya gida Alhmdllh yawwa ya madam tana qalau gud kai ina qawar nan ta amaryar ka wacce naji suna kira da maidubu sae Nura yakatse shi da fadin ohhh wacce kabiya daki jiya duk sukasa dariya yace yawwa abokina wallahi abokina yarinyar nan taje dani sosae fa jiya fa wallahi banyi bacci ba nura yace lallai abokina ashe akwae maccen da xata hanaka sukuni har haka wallahi Mai-dubu ta hanani kuma gani nan xuwa yanxu sae ka rakani gidansu muje wajen mahaifinta kawae Nura yace ok sae ka shigo

Nura ne yagayama xarah yanda sukayi da abokin shi xarah ta fiddo ido waje tana fadin yanason Mai-dubu fa ta danyi shuuuu sannan tace kagayamai kawae yayi hakuri Dom wallahi baban Mai-dubu baxai yarda ba hasali ma Kasan anyi baikonta ranar Friday ko Nura yayi shuru yana naxarin wannan alamari

Suna hakan akayi sallama wani mutum naga ya shigo gida Nura ya fito sukayi hannu suna dariya ko baagayama ba Kasan abokin Nura ne suka shiga falon tare xara taxo suka gaisa ta koma daki ya kalli Nura yace muje ko Nura yace tunda safen nan eh Kasan yarda na kwana ne halan wallahi abokina ko bacci kasa wa nayi duk akan yarinyar nan ta hadu fa nura dae sae dariyar abokin shi yakeyi

鈿栶煄€馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰鈿朜ura yace abokina kayi hakuri da abunda xan gayama gaskiya baban Mai-dubu yayimata miji ae bai jira nura ya rufe bakinshi ba shiko yafara da fadin wallahi wallahi ko xan rasa raina a sanadin soyayyar wannan yarinyar na amince da hakan abokina ka taimaka min wallahi har ga Allh inason Mai-dubu daga jiya xuwa yau banajin xan iya cigaba da rayuwa idan babu maidubu kuma wallahi ko waye mijin da akayimata dole ne yayi hakuri ya barmin Mai-dubu Dom dani tafi dacewa kuma wallahi ina kishinta batuqa

Nura dae sae kallon ikon Allh yakeyi wanne irin some abokin shi yakamu dashi haka ya qara da fadin Nura ka taimakamin yana maganar idonshi cike da hawaye Nura yaji tausayin abokin shi sosae ya xaunar dashi yana bashi hakuri ya qara kallon Nura yace Nura what is the way out tell me pls my friend Nura yadan yi shuru sannan yakira xarah taxo yace xarah inason ki kiramin Mai-dubu yanxu ki bani wayar xarah ta dauko wayar ta ta kira number din maman Mai-dubu mama ta dauka Nura ya ansa batare da xarah tayi magana ba Nura yafara da fadin ina wuni mama lapia qalau yace Nura ne tace mijin xarah yace eh tace Allh Sarki ya gida ya xarah yace hmmm ae itace ba lafiya shiyasa nakira Dom Allh mama adan aramuna maidubu taxo tadan taimaka mata mama taji tausayin xarah sosae sannan tace ina gaidata kuma ga Mai-dubu nan xuwa yanxu insha Allh Nura yaji dadin kalaman mama sukayi sae anjuma ya katse wayar

Ya kalli abokin shi yace abokina kayi hakuri Mai-dubu na hanya yanxu insha Allh yaji dadin kalaman Nura da qoqarin da yayimai suna xaune sukaji sallama suka ansa Mai-dubu ce tashigo daga ita sae Riga da sket na atamfa sunkama ta sosae dom duk sharp dinta ya bayyana rabin na fulaninta duk a waje suke ga hips dinta masha Allh da Dan karamin gyale fuskar ta ba kwalliya da ganin maidubu kasan babu nutsuwa a tare da ita dom tunda akace qawarta xarah batada lapia hankalinta ya tashi sosae tana shigowa falon tagansu duk a xaune harda qawarta xarah ta karaso wajen xarah tana fadin qawata what is wrong with u meke damunki xarah ta riqe hannun Mai-dubu tana fadin qawata lapia ta qalau Nura ne ya tashi yana dariya yace lallai maidubu nason ki xarah akan ance bakyada lapia bakiga ko gaisuwar ta bamu samu ba sae lokacin Mai-dubu tayi dariya sannan tace kayi hakuri Nura wallahi ban gan ka bane Nura yace gaskiya ne baki ganmu ba kenan duk suka sa dariya
Nura ne ya kalli Mai-dubu ya fara fadin Mai-dubu Kiyi hakuri nace maki Xarah batada lpia ko axahirin gaskiya lpiar Xarah qalau sae dae ga Wanda bayada lafiya nan Nura ya nuna abokin shi da hannu Mai-dubu ta kalli wajen sae yanxu taga Ashe akwae mutum a wajen Nura yace Mai-dubu ta ansa yace Mai-dubu abokina ne bayada lapia kuma kece sila amma dae tunda gashi kusa sae yayi miki sauran bayani Nura ya dauki amarya shi kamar karamar yarinya yana fadin madam muje daki inbaki sweet ko suka shige dakin akabar Mai-dubu tsaye da abokin Nura a falon .......

Barrister for life馃拫

Muje xuwa wasa farin girki馃憚馃憚馃憚馃憚

Mijin barrister鈿栶煄€馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰鈿�
[08:40, 12/28/2017] Barista: 鈿栶煄€馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰鈿�
MIJIN BARRISTER馃拫

By Barrister s@dy馃槝

Dedicated 2 all writers of novels more especially sis Maryam muktar d writer of nidah ya fauxan sis I love u Lodi lodi馃槝馃槝馃槝馃槝馃拫

Mijin barrister
43-44

鈿栶煄€馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰鈿朚ai-dubu ta gaidashe ya ansa bakinshi har rawa yake yi yakasa furta komi dom tunda yaga maidubu yakara ganin kyakkyawar surar ta duk hankalinshi ya kara tashi sunkai minti 5 ba Wanda yayi magana, sae can ya kalli Mai-dubu sannan ya fara da cewa

Babynah mai-dubu ta daga kai dom ganin waye yashigo sae taga ba kowa ya kara kiran baby cikin Wata irin siga wacce sae da tsikar jikin Mai-dubu tayi tsam . Dom Allh ki karbi soyayya ta kuma karki ce dani ah ah Mai-dubu tayi shuru tana kallon shi kallon tausayi sae magiya yake yimata akan ta yarda dashi Mai-dubu tace baxan boyema ba inada miji kuma har anyi baikona dashi karatuna kawae ake jira in kammala ayimin aure sae yatashi tsaye yana fadin kina nufin abunda Nura yafayamun gaskiyane kenan? Baby kina nufin ke ta wani ce bani ba ? Baby bantaba soyayya ba bantaba son Wata yarinya ba sae ke kuma wallahi! Banajin xan iya rayuwa da wata idan bake ba, Sae ya share kwalla itama mai-dubu kwallar ta share sannan ta fara da cewa kayi hakuri nasan akwae xafin rashin abunda mutum keso amma wallahi! Nayi imanin ko xaka rasa rayuwar ka babana baxai baka ni ba da fatar xaka fahinceni har Mai-dubu xata wuce ya rike hannun ta yana fadin ina xakije tace gida tana share kwalla a idonta yace idan kikaje gida nifa ina kikeson inje maidubu ta ansa mai da gidanku mana yashiga girgixa kai yana fadin qarya ne baxanje gida ba wallahi baby sae dae muje gidanku Mai-dubu ta fiddo ido waje tana fadin gidanmu kuma? Yace sosae kuwa .

Mai dubu dae tayi tsaye tana kallon shi a ranta take rayawa kodae wannan senseless ne maidubu bata gama tunani ba ya qara magana dom Allh baby wallahi ina sonki Mai-dubu na tsaye xarah ta fito ita da Nura tana fadin qawata ga mama ta kira waya maidubu ta ansa tana fadin hello mamana.

鈿栶煄€馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰鈿朚aidubu kixo gida Ahmad yayi waya yace yana hanya kixo gida idan ya wuce sae ki koma ki taimaka mata ko! Maidubu ta ansa da tau mama ganinan xuwa ya rike Nura yana kwalla yana Fadi abokina baby bata sonah! Nura yace wae hakan Mai-dubu itama maidubu kwalla ta sake sharewa sannan tace Nura kasan inada baikon wani akaina Nura yace wannan gaskiya ne amma kuma nasan bakyason mijin da akayi miki baiko dashi Dom haka idan har abunda abokina ya Fadi ba gaskiya bane tau ki bashi dama mana maidubu tace Nura ko na bashi dama babana baxai yarda ba Kiyi hakuri dae kibani damar kinji baby ta maidubu ta kalleshi ido cikin ido tace nabaka damar yace Nura ina gabas Nura nunamin gabas Nura ya nunamai yayi sujudul shukhri duk suka sa dariya har Mai-dubu xata fita yace baby ataimakamin da nom ko tace sae dae inbaka ta mamana amma karka kira idan na anso wayar a hannun ta xan kira xarah sae Nura ya gayama ina tare da wayar sannan ka kira yace duk da da baki tanbeni ba sunana (RIDWAN ALKHALI ALIYU) nasan bakyada lokacin jin tarihina Dom naga mama ta kiraki amma xamuyi wannan maganar daga baya Maidubu tayi musu sallama ta fito shima ridwan ya take mata baya yayi mata kariya Dom yayi yayi ya sauketa gida amma taqi yarda suna fito wa gate din gidan xarah suka yi ido 4 da Ahmad yana tsaye a bakin motar shi a kofar gidan xarah ......

Barrister for life馃拫

Muje xuwa wasa farin girki馃憚馃憚馃憚馃憚

Mijin barrister鈿栶煄€馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰鈿�
[21:25, 12/29/2017] Barista: 鈿栶煄€馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰鈿�
MIJIN BARRISTER馃拫

By Barrister s@dy馃槝

Dedicated 2 all writers of novels more especially sis Maryam muktar d writer of nidah ya fauxan sis I love u Lodi lodi馃槝馃槝馃槝馃槝馃拫

Mijin barrister
43-44

鈿栶煄€馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰鈿朚ai-dubu ta gaidashe ya ansa bakinshi har rawa yake yi yakasa furta komi dom tunda yaga maidubu yakara ganin kyakkyawar surar ta duk hankalinshi ya kara tashi sunkai minti 5 ba Wanda yayi magana, sae can ya kalli Mai-dubu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login