Showing 12001 words to 15000 words out of 91879 words

Chapter 5 - MATAR KA KO MATATA COMPLET BY Khadija S Dogarai (Lipton girl).txt

18 Nov 2025

2788

Dogon Nunfashi ta ja ta cigaba da shafa masa kai
"Shawaran da zan baka ka manta da maganar Aminu Kada ka taba. Sa Wanan a cikin ranka I am sure Aneesha ba zata cuce ka ba saboda yarinyar tana da hankali ga kuma tunane uwa uba tarbiya bana tunanin gidan da ta fito za'a koya mata yaudara da dai sauran abunda ba shi da kyau and you know what your choice is the best"
Dago wa yayi ya kalle ta "thank you mom you are the best"
Duk maganar da sukiye Aneesha tana jin su Hawaye ne suka zuba a idon ta wanda bata san ko nami ne ba koma wa tayi cikin daki ta kwanta
"Ka kwantar da hankalin ka kaje ni zan wuce"
Tashi tayi ta fita shikuwa ya koma cikin daki ganin matar tasa tana bacci ya sa ya dauki ta ya nufe Bathroom da ita tayi kamar bacci taki ye Ruwa ya Hada kamar jiya sanu sanu ya saka ta a cikin ruwa bude idanun ta tayi ganin ta cikin ruwan gulbe ta bakin Aneesha
Ta buga kuwa
"Wayoo yarima pls ka fida ni a ciki ko jiya fa sai da nace maka bana son wanan ruwa Meyasa ka kawo ni anan??



Murmushi yayi wanda ya kara fitar da kyawun sa

"Bacci ki yayi yawa har mom ta shigo ta fita baki sani ba ta zo ta ga ko kina lafiya ama ki kina nan kina bacci uhmm Gimbiya"
. reki kunen ta tayi "kayi hakuri Yarima"
"Ba kome kiye wanka ki fito kinsan yau sauran kwana daya"
Kallon sa tayi "kwana daya kuma"
Daga mata kai yayi yana nunin ta, ta fuskan ce abunda yaki nufe tayi saurin rufe fuskan ta
Ita bata Meyasa Yarima baya jin kunya gaya mata duk maganar da ta fito masa a baki ba
"Kiye saure fa ki naki jira ina jin yunwa idan kuma baki ta shi ba ni na fara wanka.. Ko in zo muye tare? Ya daga mata gira
Da saure tace "Aa kowa yayi shi ka dai"
Kafadar sa ya daga "as you wish " ya fita ya bar ta kamar yanda taye jiya haka tayi wanka ta ta fito shima din shiga yayi ya watsa ruwa ya saka kaya ita ma ta saka wata jalabiya Pink wada taje aikin Dusuna farare
Jirawa sukaye suka sauka kasa Kuyangu sun jira masu abince Kalla Kalla Kallon su yayi ko bai fadi ba sun san abunda yaki nufe suka bar su suka dai kuyan ga guda ta tsaya don ta zuba masu abinci
Ja mata kujera yayi ya zauna da ita shima din ya zauna kuyanga ta shiga bude abinci ta fara serving in su Aneesha kuwa kallon abinci ta ki ye
Yarima kuwa har ya fara ce ganin bata ce yasa ya dago kansa ya ce mata "me kiki jira baki fara cin abince ba??

A shagwaban ce tace "Yarima Bazan iya cen wanan abince ba"
Zaro ido yayi "meye matsalar wanan abince Uhmm "
Kallon sa tayi "jifa yanda yaki wani yafke kamar wanda yayi kwana biyu "
Kallon kuyanga yayi ita ma ta fita
"Haba Gimbiya wanan fa pizza ne sai kuma wanaan shawar ma da meet pie sai samosa sune kuma ba zaki iya ce ba"
Turo baki tayi "Nifa ba zan iya cin su ba bansa ba da su ba Inda zan samu kunu ko tuwo nace yafi man wanan
Zaro ido yayi "Tuwo fa kika ce kuma anan gidan??

"Eh manah to meye matsala "
Buga masa Teble ta kama ye "Ni gaskiya Bazan ce wanan abun ba a san yanda za'aye da ni don yunwa naki je"
Karamen Murmushi yayi "Gimbiya yaki ki son nayi na shiga kitchen na dafa maki abinci???
Turo baki tayi "Haba Yarima wai Meka mai dani ni wada bata ita girki ba baka san a kauyen mu ba Nafi kowa iya girki. Idan baka yarda ba yanzu nan zan dafa maka kace "

Kallon ta yayi "ki da kan ki zaki shiga kitchen????

"Sosai kuwa"


"Yarima ina kitchen "ta dafe cikin ta

Tashi yayi ya jawo Hanunta ya kai ta kitchen kallon kitchen in taki a ranta kuwa ta ce "Ae ko nan zaka iya kwana saboda girman da yaki da shi"
Taba ta yayi.. Sa'an ta dawo daga zurfin tunanen ta da taki ye

"Yarima yanzu nan zan Hada mana kunu da ko sai.. Sai dai ban iya aiki da wanan ba ta nuna cocker

"Don't worry baga ni ba ae sai na nuna maki"
Murmushi tayi Yarima ya Kira kuyanga Aneesha ta gaya mata abubuwan da taki buka ta.. Ta nuna mata ta wuce war ta

Nan fa Aneesha ta shiga fara girki bayan ta gama kunun geda ta yi k'o sai Yarima kuwa ba abunda yaki sai kallon ta yaki suna gama wa suka zuba a cikin food flask Suka koma Diner area ta jaye duk abince da akaye masu ta zuba ma yarima kunu
Kallon ta yayi "meki ki nufi da Hakan???
"Haba yarima har sai nagaya maka kai ma shi zaka sha "
Ta Washe hauru.
Zuba masa tayi ita ma ta zuba ma kan ta fara sha ta yi ajiyan zuciya tayi "Yauwa yanzu kam zan karya "
Kallon shi tayi "Bisimillah manah kace kayi shiru sai kallona kaki ye"
Murmushi karfin Hali yayi don tunda yaki a Rayuwar sa bai taba shan kunu da kosai ba...
Gani ba ce zai ye ba ya sa ta tashi Ta dauki kosai ta saka masa a baki kunu ta debo ta bashi
Ae kuwa nakin yaje dadi.. Sai yaje kamar duk abince da yaki ce bashi da dadi wanan yafi dadi
Koma wa tayi ta zauna ta cigaba da cin nata Yarima ma haka
"Uhmm Yummy Gimbiya ashe haka kika iya girki"
Dariya tayi "ae daman na gaya maka ni gwana ce a fanin girki"
Daga Kansa yayi "Na yarda da Hakan"
Haka suka ce abinci su suna hira har suka gama...


Aneesha kuwa Ita da kanta ta dauki kunu cikin flask sai kosai cikin kulla suka nufi bangaren Mom in Yarima waton Aisha

Da sallama suka shiga ko da suka shiga tana zaune tare da mai martaba suna breakfast domin shi mai martaba bai yarda ya ce abinci a fada ba ya fi son yaci tare da matar sa domin kuwa tana da haki akan sa
Aneesha Har kasa ta kai ta Gaida su cikin sakin fuska suka amsa.
Ajiye kayan da ki Hanunta tayi
"Mama ga girki da nayi"
Kallon ta tayi "Aneesha Meyasa kika shiga kitchen ina Kuyangu suki????
"Suna nan , kwai bana iya cin abinci da suka dafa shiyasa na ye kunu da kosai tau shine nace bare na kawo maku idan kuna so sai ku ce"
Ajiye na hanunta tayi ta zuba kunun ta fara sha domin kuwa ita ma tana son shan shi Mai martaba aka zuba ma shi ma ya sha ae kuwa sun yabe ta sosai kuma sun yaba da hankalin ta sun san ko bayan ransu ita da Yarima zasu iya reki masarauta
Koma sa sukaye bangaren su Dakin ta ta shiga don tana jin bacci kwanta wa tayi yarima kuw ya shigo cikin daki

Kokarin kwanta wa ya kiye busan jikin ta tayi sauren jaye wa
"Yarima wai Dan Allah meye haka.?? Duk wanan gurin ba zai ishi ka ba sai ka kwanta a jiki na???
Kallon ta ya ki ye karamar yarinya sai iya magana
" a jikin ki na naki son kwanta wa "
Kallon mamaki taki ye masa domin wata magana idan ya fadi ta yana bata mamaki
Nuna shi tayi "A jikin ka"
Ya nuna ta "eh a jiki na"
Taba shi tayi ta kwance kanta ouch ta furta
Kallon ta yaki ye
Murmushin takai ce tayi "Meyasa baka je zafi ba in jikin ka ni"
Dariya ya kama ye "Gimibiya kina bani dariya Allah"
Ita kuwa bata ga abun dariya ba a ciki
Jeyo wa tayi ta kwanta
Ya jawo ta ya manata a kirjin sa
Turo baki tayi "Yarima pls ka saki ne ina jin bacci"
Kyaleta yayi kamar bai je tana magana ba haka ta daure ta kwanta kan jikin shi har tayi bacci..... Su a basu tashi ba sai da aka kusa Sallah Azahar

Yarima ya fita ita kuma ta sauka kasa Kuyanga ta Kira tace su zauna suye hira
Ita kam mamaki taki ye ita zayayi hira da Gimbiya
Ae kuwa Aneesha ta fara bata labare yanda kauyen su yaki abunka da mai surutu....

Yarima ni ya shigo cikin gidan Ganin kuyanga Aneesha tana ta zuba wa
Tashi tayi ta zube kasa tana Gaida shi daga mata hanu yayi da saure kuwa ta fita
Aneesha ta kara so kusa da shi
"Sanu da zuwa Yarima yaushi ka dawo?? Meyasa ka kore kuyanga baka ga muna hira bani???

Murmushi yayi "lokacin da na dawo kina nan kina zuba wa"
tabe baki tayi "To Allah ya bani baki me zanye kuwa in ba zuba wa ba"
Dariya yayi ya dauki ta
"Yarima meye haka wai Meyasa kaki. Son mai dani kamar wata jariri ya"
Tafiya yaki ye yana Kallon ta
"Ae jariri ye kiki"
"Pls ka sauki ni"
Kallon ta yayi "yaushi kika iya pls "
Dariya ta aza
"Kaji ka idan ban iya pls ba ae ba matar ka naki ba tunda baka da aiki sai turance wani lokacin ma sai naga kamar kana zagina tunda ban iya ba"
Kallon ta yayi ya aza ta kan gado
Reki hanunta yayi
"Taya zan zagi Gimbiya ta "
Murguda masa baki tayi na sani

"Tau ki sani ba zan iya zagin ki ba"

"Gobe yaushi zaki ye wanka"
Kallon sa tayi
"Meye matsala ka da wanna na"
Ki dai ki bani Amsa
Shiru tayi kamar mai tunane "Zuwa 2 ina ga"

"Ohk ni zan fita zan je gidan Abokina Aminu "
Murmushi tayi "Allah ya tsare ya kai man ka lafiya "
"Ameen matata"
Ya jawo ta ya fara mata kiss
Ture shi tayi
"Wai kai yarima kome sai ka hada bakin ka da nawa"
"Eh manah ae shine soyaya da kuma zam aure don haka ki shirya gobe"
Ya fita ya bar ta cikin tunane

"Shine soyaya??? Kuma shine zaman aure???
Tambayar kan ta ta kiye wanda bata da amsa


Yarima kuwa bai dawo ba har kusan 8 na dare ita kam ta gaji da jiran sa shiyasa tana cin abinci tayi baccin ta koda ya dawo har tayi bacci dan karamen bakin ta ya Kalla mai shigin surutu ya jawo ta suka ye bacci tare


Basu falka ba sai da safe Yarima ni ya wuce massalaci suka gaba tar da sallah Kamar dai jiya haka yayi ya koma bacci Sai kusan 9 ya tashi yayi wanka ya dauki Aneesha har suka kai Bathroom idanun ta a rufe suki.
Cikin Ruwa ya Kada ta
Ae kuwa ta bude ido tana mai da nunfashi
"Yarima zaka kashi ni ne??? Wai haka aki tada mutum idan yana bacci
Murmushi yayi mata "Eh haka aki ye tunda mata ita ki tada miji ama ni matar tawa bata tada ni shiyasa ni kuma naki tada ki ta haka.. Oyah kiye wanka ni fita zanye kuma ba zan dawo ba sai dare"

Kallon mamaki taki ye masa "sai dare fa kace Yarima lafiya kuwa?? Ko dai na bata maka rai ni???

Kallon ta yaki ye "ba abunda kika ye man"
"Ka gaya man gaskiya domin mallamin mu yana cewa Kada mu taba bata ma mijin mu rai"
Dan murmushi yayi najin dadi
"Baki ye man komi ba kinje akwai aikin da zanye shiyasa ba zan dawo ba sai dare"

Kiss yayi mata a goshi ya fita a ranta kuwa tace ae kara ma ka fita ni ko zan samu sauki ka dai na taba ni wanka tayi ta na gama wa ta saka kaya ko yau ita ta dafa ma kan ta abinci Gashi ta gaji da zama ita ka dai Inda ma yarima yana nan da zai cire mata kewa haka tayi ta zama ita ka dai har dare yayi..........


Yarima ni ya shigo dauki da Leda a hanunsa zaune taki kan gado
Tana Ganin sa ta Turo baki
"Sanu da zuwa Yarima"
"Yau yar Albarka na jima ko"
"Eh kam tun fa safe ka fita ama sai yanzu ka dawo"
Jawo ta yayi "Sorry my wife aiki ya reki ni kinye sallah???
"Eh nayi "
"Masha Allah "
Ya dauko Leda ya zuba masu a plate ae kuwa tana Ganin Kaza ta fara jin dadi
"Laaa yarima kaza ka seyo men"
Kallon ta yayi
"Wanan nawa ni "
Zaro ido tayi "Yarima Rowa zaka yi man????

"Eh mana bakin ci jikin ki naki ni ba ni kuma kazata tawa ce"
Tabe baki tayi ta kara So kusa da shi "Wasa nakai Yarima pls ka bani nace"
Dariya yayi "kin gan ki wanan dan tsiton baki akwai shi da kwadai"
"Na dai je ni dai a bani"
Plate in ya tura mata ae kuwa ta fara ce
Shi kuwa ba abunda yaki sai Kallon ta
Dago wa tayi ta kalle shi Yarima Gashi
"No kice kwai"
Tura masa tayi a baci haka yace tayi ta bashi yana ce sai da suka gama sa'an suka shiga toilet don su wanki Hanu...........



*Lipton girl*๐Ÿ’™
[11/3, 2:16 PM] Lipton Girl Mrbcy: *MATAR KA KO MATATA*
๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน

*Daga alkalamen*โœ๐Ÿป

*Khadija S dogarai (Lipton girl)*๐Ÿน

*A short Story* ๐ŸŒคโ˜€๐Ÿน

*Dedication*

*first Love (Mom) Allah ya Kara maki lafiya*๐Ÿ’—โ˜€๐ŸŒค๐Ÿน

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~โœ๐Ÿฝโœ๐ŸฝGOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ~*




*~We are bearer's of so golden pen๐Ÿ–Š~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden penโœ,behold our words.~*

*~A product of our pen๐Ÿ–Š,savour our words, for it will cause you no pain.~*

๐ŸŒคPage 20&25...๐Ÿน


^^^^Tashi tayi ta kai plate a kitchen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login