Showing 1 words to 3000 words out of 85380 words

Chapter 1 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3851

??ࡱ?>?? E???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????B????

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?FFWordDocument????1T0Table????????p Data
???????????????????? P?8
KSKS?1T?????????rr????????kD??J J J J J J J J L $??a *r??J J ????J ? ??? J ?J ? ?J J ?? KRB2P001
Arewabooks@nanahaleema11

FaWuwar da Narma tayi a wajan shi ya Wauke hankalin su daga kan su Omar aka yi kanta a guje ana jijjigata amma Narma ko numfashi bata yi. Hankalin su ya tashi matu?a aka Wauki Narma aka tafi zuwa asibiti da gaggawa. Sen takaicin duniya ya ishe shi, ji yake kamar ya je ya saka wuyan Omar a gabas ya yanka kowa ya huta. Kowa ka kalli yanayin fuskarsa a cikin su kasan baya cikin walwala, ransu duk a Sace yake da abinda ya faru.

Sai da daddare Narma ta buWe ido ta kalli iyayen nata guda biyu da suke zaune kusa da ita, ta kalli ?an uwanta suma da suke gefenta. Murya a sha?e ta ce, "Dad Faruk ya tafi ko?." Maganar da tayi ne ya saka suka fahimci ta farka duk suka kalle ta.

Sen ya ja tsaki bai ce komai ba ya fita daga Wakin, dan in ya cigaba da zama bai san abinda zai aikata mata ba. Mum ce ta ?arasa inda take ta ri?e hannunta tace, "Narma ki yi shiru da maganar nan mu koma gida, yanzu kina kwance asibiti ne." Narma ta ce, "Mum in na rasa shi mutuwa zan yi." Ran Mum ya Saci amma bata nuna ba ta ce, "na ce ki yi min shiru ko?." Narma ta yi shiru tana tuna abubhwan da suka faru kanta ya yi nauyi sosai.

Babu jimawa suka nemi tafiya gida dan dukkan su basu da nutsuwa, ganin Narman ta dawo daidai ba laifi sai suka bar asibitin zuwa gida. Babu wanda ya yi mata maganar kowa Waki ya shiga dan ya huta dole itama ta kwanta amma ba dan tana son yin bacci ba.

Mum ta shiga wajan Sen ta same shi a tsaye a jikin window yana amsa waya yana cewa, "kayi duk abinda ya kamata ka yi, ni fa da zan samu dama direct prison nake so a kai shi, bana son wani Sata lokaci wallahi."

Daga cikin wayar aka ce, "Calm down Sen, ba a kai mutum prison kai tsaye ba tare da laifin komai ba." A fusace ya ce, "ba na faWa maka har gida sha?e ni ba?."
"Wannan ma hujja ce da za a Waure shi life in prison ba, kuma dole kotu ce zata yanke hukunci." Sen ya ce, "Kaga ni bana son wani long process, me za a yi yanzu?."

Ya ce, "ka bar komai a hannuna, zan haWa masa sharrin da bazai iya fitar da kansa ba. Sunan ka ma bazai fito ba, domin zamu saka masa cocaine a jikinsa mu sake shi, in ya fita kan titi sai mu tura masa Ndlea su kama shi. Da sun kama shi zan san abinda zan yi a mi?a shi kotu, daga nan sai a yanke masa hukunci a matsayin mai safarar cocaine, kaga shikenan sunan ka bai fito a maganar ba."

Dad ya yi tsaki ya ce, "Kana ji, ka killace min shi a wani waje, sannan ka tabbatar da anyi masa horon da hannunsa ma bazai iya Wagawa ba. Ka yi masa horon da zai kasa banbance a duniya yake ko a lahira, ka tabbatar da ya kasa koda motsa yatsun hannunsa. Su kuma sauran biyun ku barsu su tafi, ina so su je su isar da sa?on Tiger bazai sake komawa Kano ba har abada!" Yana gama faWar hakan ya yanke wayar ya juyo yana kallon Mum da take kallon sa.

"Tun farko ai na faWa maka kar ka haWa min ?ata da Wan daba amma ka ?i ji, har ka ke ganin zai yi maka aiki da hukuma baza tayi maka ba. Yanzu ga abinda ka jawo mana, wannan babban cin mutunci ne ga family. ?ar da na haifa namiji kamar sa ya zo har gidan nan ya ce yana so, saboda akwai ka bashi fuska da sake har yake ganin mu dashi Waya ne" Mum ta faWa a fusace tana kallon Dad dan ita gabaWaya laifin sa take gani.

Sen ya ce, "Nayi kuskure, ban Wauka abin zai zo da haka ba, amma yanzu zan gyara komai."
"Ko ka gyara ai an riga da an aikata, yaro yazo har gidan nan kana faWa yana faWa kamar sa'ansa?. Sannan ya kalle ka ya ce yana son ?arka, akwai abinda yafi wannan cin fuska ne?."

Sen ya yi shiru bai ce komai ba amma shi kaWai ya san zafin da yake ji a zuciyarsa. Mum ta sake cewa, "yanzu ya zamu yi da Narma? Na tabbatar asiri ya yi mata, tunda ya samu damar hawa mota tare da ita ba dole ya yi mata abinda zata haukace haka a kansa ba. Ka duba yanayin da take ciki, ga zafin zuciya, ga zafin asiri, ga zafin marin da ka yi mata Wazu."

Sen ya ce, "London zan tura ta taje ta huta. sannan maganar Ashraf zata dawo, dama tun asali shi take so, aikin asiri da ya yi mata ne ya saka tace bata sonsa. Yanzu kuma maganar zata dawo, da zarar ta huta ta dawo zan aura mata Ashraf." Mum ta ce, "ya dai gama cutar mu wallahi, ya lalata mata tarihi gabaWaya. Wai Narma yake so, just imagine" ta faWa cikin da takaici tana kallon sa.

Sen ya ce, "zan tabbatar masa da tayi masa nisa, zan tabbatar masa da iya furta wannan kalma da ya yi guda uku ta ina sonta sai ya yi dana sani yafi sau dubu uku, zan nuna masa ni ba kanwar lasa bane, duk isakancin da yake ji dashi na dame shi na shanye. Zan tabbatar masa da ruwa ba sa'an kwando bane, zan lalata mara rayuwa, zan saka shi ya ji zafin da naji a zuciyata, zan saka ya WanWana irin zafin da ya saka Narma tana WanWanawa."

Mum a fusace ta ce, "meyasa ba za a Satar dashi daga duniyar ba gabaWaya? In aka kashe shi an kashe banza da wofi, zamansa a duniya tamkar cin fuska ne a gare mu." Dad ya girgiza kai ya ce, "ki barni dashi akwai, mutuwa ai mai sau?i ce ga rayuwarsa, in ya mutu yanzu ai ban ci riba ba, ban saka masa abinda ya saka min a zuciyata ba. Sai na gana masa azabar da zai manta a wanne gari yake sannan komai ya biyo baya." Zaman kurame suka koma a Wakin, Mum tana nata tunanin haka shima Sen Win shiru ya yi yana tunani mai cike da dana sanin duk abinda ya aikata a baya, tabbas da bai haWa Narma dashi ba da yanzu hakan bata faru ba, duk kuskurensa ne amma zai gyara.

Da safe haka suka tashi duk fuska babu walwala, Narma bata fito daga Waki ba sai da taji duk suna falo sannan ta fito tana takowa kamar kazar da ?wai ya fashewa a ciki. Duk da kallo suka bita kafin Dad ya ri?o hannunta ya zaunar da ita kusa dashi yana kallon ta.

GabaWaya ta rame a lokaci Waya, tayi wani iri kamar ba Narman sa ?ar gayu ba, tsana da takaicin Omar suka sake yi masa dirar mikiya, suka dabaibaye masa zuciyar sa. Kallon Mahaifin nata ta yi kamar yadda yake kallon ta kafin ya ce, "Ya jikinki?."

Narma cikin sanyi murya mai Wauke da rauni ta ce, "Dad babu sau?i. Dad Ina son Faruk a yadda yake, Ina so na rayu dashi. Kuma Dad zaka iya mayar da Faruk yadda ka ke so, zaka iya sakawa Faruk wani abu kamar yadda ka ke buri. Ni ban damu da bashi da abinda ka ke faWa ba, shi nake so kuma shi nake so na aura Dad" ta faWa tana kallon sa kamar yadda yake kallon ta. Ya gama gasgatawa asiri ya yiwa Narma hakan ya saka ya kwantar da murya ?asa ya ce, "Daughter ki daina wannan maganar kinga baki da lafiya, ki bari ki samu lafiya zamu tattauna."

Narma ta ce, "Dad bazan taSa dawowa daidai ba indai baka amince da aurena da shi ba. Dad ni na fara furta Ina son Faruk, a hankali shima ya fara sona, Dad Meyasa zaka ce bazan aure shi ba?. Don Allah Dad kar ka bari a cutar dashi kaji...." ta faWa cikin karyewar murya tana kallon mahaifin nata. Rungumeta ya yi a jikinsa tana kuka sosai, cike da tausayi yake shafa bayanta dan ya san ba yin kanta bane aikin asiri ne.

Nabil ya ce, "zai biya bashin asirin da ya yiwa Narma, Dad bai kamata a bar shi ba" ya faWa cike da damuwar halin da take ciki. Narma ta Wago daga jikin Dad ta kalli Nabil ta ce, "ni bai yi min asiri ba, ni ce na dinga bibiyarsa har sai da ya fara sona. Ba asiri ya yi min ba, haka kawai nake sonsa. Najwa ta ce, "daman haka zaki tunani ai, haka zaki Wauka babu abinda ya yi miki dan ba yin kan ki bane, ya saka miki soyayyarsa zuciyarki ta hanyar asiri, ke bazai fahimci ba asiri bane ba ai.."

Narma ta kalli Dad ta ce, "Daddy kana ji suna cewa asiri yayi min ko? Kuma ba asiri ya yi min ba Dad, ni ina sonsa ne kawai. Har yanzu ina ?aunarsa, shi kaWai nake so na aura, in ba shi ba ni bazan auri kowa a duniya ba zan mutu a haka. Dad Ina ka saka aka kai shi?." Bai bata amsa ba ya kalli Najwa ya ce, "Najwa ki shirya zaku tafi London this week."

Narma ta ce, "Dad babu inda zan je, babu inda zan je na bar Faruk Wina a Nigeria. Ni dashi zan rayu, aurensa nake so nayi da shi kaWai zan iya rayuwar duniya. Dad in kace bazan aure shi ba zaka iya rasa ni! Zan iya mutuwa na bar muku duniyar gabaWaya." Babu wanda ya iya tanka mata a cikin su, tausayi take basu gabaWaya sun san aikin asiri ne ba yin kanta bane.

Mum ta taso ta ri?e ta tana rarrrashi itama kuma tana kuka sosai. Mum da kanta ta bata tea ta sha, sannan ta bata maganinta na jiya ta sha, ta kaita Waki ta kwnatar da ita a kan gado tana shafa kanta. Narma sai magana take yi ita kaWai idanunta a rufe kafin bacci ya Wauketa.

Fitowa Mum tayi bayan ta yi bacci ta kalli Sen ta ce, "ya faWa musu inda ya kai Narma aka yi mata asiri, yayi gaggawar warware asirin kafin ya kai ga yin dama sani!" Mum ta faWa ido na cikowa da ?wallar tausayin Narma. Dad bai ce komai ba amma tabbas zai san abinda zai yi akan asiri nan da ya yiwa Narma, dole ma ya warware shi kafin ya rasa ?arsa.

*Kano.*

Didi tun a daren jiya da ta ga dare ya yi babu Omar babu labarinsa hankalinta ya tashi, ta kira wayarsa yafi sau babu adadi ba a Wauka, ta kira ta su Bashir duk a banza bata samu hakan ya Waga mata hankali sosai. Har sha biyu na dare ta kasa bacci, ko ya ta Win ji motsi zata firgita ta kalli ?ofa amma babu Omar babu alamunsa. Gashi ta san shi mutum ne da duk inda yaje komai dare a gida yake kwana, baya kwana a wani waje in ba gida ba. GabaWaya hankalinta ya tashi, bata da nutsuwa bacci ko kulle ido bata yi ba tana tunanin dawowar sa.

Rashin baccin da bata yi da wuri ba ya saka ta makara sallah asuba, sai shida ta farka a firgice ta fito ta shiga Wakin Omar amma baya ciki. Salati take yi a zuciyarta, ta kira wayarsa zuwa lokacin ma wayar a kashe take. Da?yar ta iya yin sallah dan ba nutsuwar kirki gare ta ba, tana idarwa ta sake kiran su Bashir amma suma duk a kashe.

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Allah yasa ba masu garkuwa da mutane ne...." Sai kuma bata ?arasa ba jikinta har rawa yake kamar mazari saboda tashin hankali. Ta rasa wanne tunani ma zata yi ta ji daWi, ta damu da rashin Omar matu?a, inda ya saba kwana a wani waje ne ma da sau?i, to ta san duk daren duniya Omar sai ya dawo gida hakan shine yake Waga mata hankali.

Taci kukan ta ta gode Allah, fuskarta tayi ja sosai ta kasa aikata komai a gidan gabaWaya jikinta a sanyaye yake. Gashi an wayi gari juma'a bata da karsashin iya yin abincin sadaka dan ta tabbatar bata da wannan ?warin guiwar shiyasa ma bata yi tunanin yi ba.

Karfe sha daya na safe tana zaune a falo ta zuba uban tagumi ta jiyo sallama, ai a haukace ya fito tsakar gidan idon ta ya haWu da na Goje ya yi wujiga-wujiga. Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "Alhamdu lillah! Meyasa ku ka tayar min da hankali ne Bashir? Meyasa baku kira ni kum faWa min a can zaku kwana ba?. Ina Omar Win yake?." Bashir ya kalle ta ya ce, "Didi ba tare muke da Damisa ba" Didi da mamaki ta ce, "Kamar ya kenan? Ba tare ku ka tafi ba?."
"Tare muka tafi Didi."
"A Ina ya tsaya shi?." Bashir ya sauke numfashi ya ce, "Didi mahaifin yarinyar nan ne ya saka aka kama Damisa."

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ya saka aka kama Omar kuma Bashir? Akan wanne dalili? Laifin me ya aikata masa aka kama shi?. Bashir ka bani amsa, Mustapha ku nake saurare ku faWa min!"Ta faWa a gigice tana kallon su. Goje ya ce, "Didi bai masa laifin komai ba, kawai saboda ?arsa tana sonsa shiyasa ya yanke wannan hukunci. Ya saka a kama shi da laifin wai yazo har gida zai kashe shi kuma zai sace masa ?arsa. Mu kan mu damu aka kama gabaWaya, Sanata Win ya saka a sake mu wai dan mu zo mu sanar daku Omar bazai dawo ba har abada."

Jiri ne ya fara Waukar Didi tayi saurin dafa bango tare dur?ushewa a wajan tana kuka sosai. Kuka take yi wanda ya hanata magana, kuka mai sauti mai nunu da tsantsar damuwar da take ciki. Ta ce, "Bashir sai da na ce masa kar ya je, sai da nace masa kar ya je yarinyar nan tafi ?arfinsa amma Omar da yake baya jin magana sai da yaje. Sai da nacewa Omar kar ya yi wannan gangancin amma Omar ya ?i jin maganata. Da ya ji maganata da yanzu muna tare dashi babu abinda ya same shi, da ya ji maganata da yanzu ba a kama shi ba" magana take cikin fitar hankali tana kuka sosai hakan ya karya zuciyar Bash da Goje.

"Ki yi ha?uri Didi, zamu san yadda zamu yi ya fito, mun san manya da yawa zamu je mu saka su shige mana gaba a fito da Omar."
"Bashir babu lallai su amince, amfani kawai suke yi daku amma in kun shiga matsala baza su iya shige muku gaba dan warware ta ba. Bashir in akace Omar baya nan ya zan yi? In aka ce Omar bazai dawo ba ya zanyi?. Ta ya zan iya rayuwa bana ganin Omar? Ya rayuwata zata kasance Omar yana wani waje ana bashi wahala ni ina nan?."

Goje ya ce, "ki kwantar da hankalin ki Didi zai dawo in sha Allah, zamu san abinda zamu yi. Zamu bi duk hanyar da zamu bi dan dawo dashi. Ba ke kaWai zaki shiga damuwa ba in baya nan, har damu Didi." Bata kula shi ba sai kuka kawai da take yi, Goje ma kukan yake yi ya fita dan fara neman mafitar dawo da Tigar ko ta hali ?a?a.

Didi sai da tasha kukan ta son ranta sannan ta iya tashi jiki a sanyaye ta shiga falo. Babu wanda zata faWawa damuwarta, ta saba su biyu suke solving matsalar su basu da wasu dangi da suke warware musu matsala balle ta ce zaje ta faWa masu. Hajja ce ta faWo mata a rai, ta mi?e da sauri ta saka hijjabi ta fita zuwa gidan Hajja.

Hajja da take zaune ita da Salma ganin yanayin Didin duk sai suka kalle ta dan sun san ba haka ta saba shigowa ba. Wajan Hajja ta nufa ta dur?usa kusa da ita kawai ta fashe da kuka. Hajja hankalin ta ya tashi ta ce, "Aisha lafiya? Me ya faru kike kuka?." Bata daina kukan ba sai da ta gaji sannan ta kalli Hajja ta ce, "Hajja Omar."

Hajja cikin tashin hankali ta ce, "me ya same shi?." Didi cikin kuka ta faWawa Hajja duk abinda ya faru sannan ta ce, "Hajja yana can Abuja sun kama shi, Hajja ya zanyi? Na rasa inda zan saka raina. gabaWaya hankali a tashe yake."

Hajja ta ce, "Hasbunallahu wani'imal wakil! Amma Ummaru ya yi ganganci."
"Hajja babu yadda ban yi dashi ba amma ta?i ji, Omar in yaso yin abu ko duniya bata so in dai shi yana so sai ya yi, na bashi shawara akan haka amma ya?i saurarena. Hajja in wani abun ya same shi ya zanyi?" Ta ?arasa faWa murya na rawa. Hajja ta ce, "ki daina kuka ki kwantar da hankalin ki, in sha Allah zai fito."

Didi ta ce, "ta ya zai fito Hajja? Ta ya ya Omar zai fito bayan furucin da Sanata ya yi a kansa?. Hajja Sanata ne fa ya saka aka kama shi, dawowar Omar gida abu ne mai matu?ar wahala." Hajja tayi ajiyar zuciya ta ce, "kar ki damu Aisha, zan yiwa mahaifin salma magana ko ya san Sanata Win. ?an kwangila ne wata?ila suna da wata alaqa dashi. Ki kwantar da hankalin ki mu bi komai a sannu kar ki damu." Didi ta goge idanun ta ta ce, "to Hajja. Na rasa inda zan kai kuka na shiyasa nazo gare ki." Hajja ta dafata cikin tausayi ta ce, "kar ki damu, in sha Allah yadda kika kawo min kukan ki zan zama silar share miki hawaye. Salma bata ruwa ta sha" ta faWa tana kallon Salma. Salma ta mi?e ta kawo mata ruwa ita kanta tausayin Didi take ji.

Ruwa ta sha tana jan numfashi cikin tashin hankalin da take cikii,Hajja ta dinga rarrashin ta tana bata baki har ta Wan nutsu sannan ta ce bara ta koma gida ta dawo. Bayan ta fita Salma tayi tsaki ta ce, "Wannan Omar da Waukar dala ba gammo yake, Ina shi ina soyayya da ?ar Sen Sagir banda Wage irin na sa?. Haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login