Showing 57001 words to 60000 words out of 85380 words

Chapter 20 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3839

min waye shi" yana faWa ya yanke wayar ya cillar da ita a kan gado zuciyarsa na yi masa zafi.

Babu abinda ya Sata masa rai a abinda Nayla ta turo masa kamar da tace tayi zata iya barin kowa saboda Omar, In ya tuna irin kalaman da ta yi amfani dasu wajan a sa?on da ta turo masa sai yaji kamar ana soka masa kibiya a zuciyarsa saboda Sacin rai da ba?in ciki da takaici.
Ranar a gidan gabaWaya kowa zuciya babu daWi, Mama ce kawai take farin ciki amma dukkan su babu wanda yaji daWin abinda Nayla tayi.

Washe gari.

Wai me Nayla ta aikata ne? Wanne irin sa?o ta turowa Abiy haka? Ina su Abiy zasu je?......A kafta=؃? KRB2P020
Arewabooks@nanahaleema11

?arfe takwas na safiyar ranar juma'a Abiy ya sakko daga sama yana Waura agogo a hannunsa. A ?aramin falon ?asa ya tarar da Mama ta kalle shi ta ce, "Ina zuwa haka da sassafe? Kun yi magana da Nayla kuwa? Ina kiranta har yanzu bana samu." Abiy ya kalle ta ya ce, "ba mu yi waya ba, bana bu?atar yin wayar da ita. Ina su Jawad?." Mama ta ce, "suna main parlor tun Wazu." Abiy bai ce komai ba ya wuce zuwa falon.

Yana shiga duk suna tashi suna kallon sa suka gaishe shi ya amsa kana ya ce, "Ku zo mu je." Ba musu duk suka bi bayan sa. Jawad ya shiga mota mazaunin driver Abiy ya shiga baya Yaya ya zauna a gaba suka fita daga gidan. Sai da suka hau titi sannan Jawad ya ce, "Abiy ina zamu je."
"Kano" ya bashi amsa ba tare da ya kalle su ba. Basu tambaye shi ba kawai Jawad ya Wauki hanyar fita daga Kaduna.

Nayla kuwa a lokacin idanunta biyu ta kasa komawa bacci, ganin ?arfe tara na safe tayi sai ta mi?e tayi alwala ta tayar da sallar walha. Sai da tayi raka'a ashrin sannan tayi addu'a zuwa lokacin har goma na safe ta kusa. Wayarta jawo dan tun jiya bata duba ba ta shiga WhatsApp Winta. Abin mamaki an yi hacking account Winta, tsaki tayi ta fita ta shiga Google ta duba yadda zata dawo da account Win tana karanta yadda zata bi ta dawo dashi.

Salma ce ta shigo hakan ya saka ta ajjiye wayar ta ce, "wai WhatsApp Wina aka yi min hacking." Salma ta ce, "ai zaki iya dawowa dashi ba wahala ne dashi ba, ki dai yi gaggawa kar a fara tambayar mutanen contact Winki kuWi." Nayla ta Wauki wayar ta ce, "bara na gani" ta faWa da tana bin steps Win da ta gani a google har ta dawo dashi. Tsaki tayi ta ce, "ikon Allah, an goge min wasu messages Win, suka sani dai" ta faWa tana ajjiye wayar a kusa da ita.

Kallon Salma tayi da take kallonta sai ta ce, "yaushe zamu je gidan Didi? Ina so naje kafin na koma Kaduna." Salma ta ce, "sai muje anjima in zaki iya. Amma kafin nan Nayla me yake damunki?." Nayla ta ce, "Salma nima bana ce ba wallahi, komai baya yi min daWi. Babban abin tashin hankalin ma Abiy ya san maganar Omar." Zaro ido Salma tayi ta ce, "mun shiga uku! Kamar ya ya sani? Ta wacce hanya ya sani?."

"Ashe lokacin da muke maganar nan a gidan mu na Kano Mama taji. Mama tana goyan bayana akan soyayyata dashi, hakan ya saka ta sanar Abiy shi nake so ko zai amince. Hmmm Salma! Abiy bai taSa yi min faWa kamar lokacin ba, kai tsaye ya ce min Hauwa sunan da bai taSa faWa ba."

Salma ta dafe ?irji ta ce, "Innalillahi wa'jnna ilahir raji'un!. Yanzu ya ake ciki?."
"To bana ce ba dai, ya ce dai duk yadda zan yi nayi na fitar da mijin aure in ba haka ba zai bani wanda ya ga dama. Daman na san bazan taSa mallakar abinda nake so ba Salma, shiyasa ni zan bawa Abiy ha?uri ya zaSa min duk wanda ya ga dama. To Mama ce take bani bani ?arfin guiwar zai iya amincewa da Omar."

Salma ta ce, "Gaskiya Abiy bazai amince da Omar ba, gwara ma ki daina yaudarar kanki. Duk dani shaida ce Omar ba kamar da ba yake ba yanzu ya canja, harkar sana'arsa yake yi kuma Allah ya saka masa albarka. Ke in kika ga takalman da Omar yake yi sai abin ya baki mamaki, sai kin ce daman yana da wannan talend Win ya zauna yana Sata rayuwarsa a banza da wofi.....huhh amma duk da haka rayuwarsa ta baya zata saka a ?i bashi aure Nayla. Musamman auren irin ki, mai ilimi, nasaba, kyau da sauran su."

Nayla ido ya kawo ruwa ta zubawa Salma ido ta ce, "da gaske kike yanzu Omaar ya koma yin sana'a sosai?."
"Da gaske nake wallahi, bara na nuna miki handles Win su da suke posting kayan. Naga didi ta saka a status, shine naje na gani ke baki ga abu ba baza ki Wauka Omar yana da wayewar yin abubuwa haka ba" Tana faWa tana danna waya tana duba page Win.

Nuna mata wayar tayi ta ce, "kin gani.. wannan shine irin takalman da Omar yake yi yanzu. Shiyasa zaman unguwar nan ma yanzu ba yi yake yi sosai ba, ko yaushe baya nan suna shago suna aiki." Nayla kalla take yi zuciyarta na rawa sosai kafin ta sauke kai ta yi ajiyar zuciya ta ce, "wata?ila babu Omar a cikin ?addarata."
"Calm down, ki cigaba da addu'a komai zai wuce. Kuma ba kince Mama na supporting Winki ba?."
"Ita kaWai ba, Yaya cewa ya yi a bashi ni mu tafi Lagos sai na dawo hankalina na dawo gida. Yaya J ma da yake aminina shima yana bayan Abiy. GabaWaya jina nake wani iri wallahi."

"Ki dai yi ha?uri. Yanzu ki tashi kiyi wanka, kiyi break sai mu je gidan Didi." Nayla ta ce, "Ina so naje gidan Twiny ma."
"To ki tashi mu shirya." Nayla tayi ajiyar zuciya ta tashi ta shiga banWaki cikin damuwa mai yawa.

Su Abiy lokacin da suka shigo Kano umartar Jawad ya yi da su wuce gidan su na Kano. Kai tsaye nan suka wuce kamar ko yaushe. Mai gadin gidan jin ana horn ya buWe ya ?araso ganin mai gidan ne da kansa ya saka ya buWe suka shiga cikin gidan. Falon gidan suka shiga bai yi dauWa ba sai dai ?ar ?ura kaWan mara yawa.

Abiy ya kalle su ya ce, "ku huta zuwa sha biyu da rabi zamu fita." Amsa masa suka yi ya shiga ciki. Ahmad ya kalli Jawad ya ce, "Wai me yake faruwa ne? Me muka zo yi Kano?."
"Wallahi ban sani ba Yaya, abinda na sani kawai jiya Nayla ta bar gida ta taho nan Kano. Da Fari na Wauka gidan Hajja Win zamuje sai naji ya ce mu zo nan." Da mamaki Yaya ya ce, "ta bar gida ta taho nan? To Akan me?."

Jawad ya ce, "Akan wannan yaron mana, ran Abiy ya Saci matu?a a jiya da daddare."
"Daman Nayla bata da hankali ban sani ba? Ana ganin ta mai kirki da hankali ashe itama ?ar iska ce?. Ta taho na saboda ance bazata aure shi ba ko me?." Jawad ya ce, "nima ta bani mamaki wallahi, ban Wauka zata aikata haka ba. Ashe macijin sari ka no?e ce, a haka sumi-sumi da ita kamar bazata aikata ba."

Yaya ya girgiza kai ya ce, "Lallai tana bu?atar duka, dan sai na zane mata jikinta sannan zata fahimci kuskurenta. Bara Abiy Win yazo, Wauketa zan yi wallahi mu tafi lagos na koya mata hankali a can tunda ita shashasha ce" ya faWa yana fita zuwa Wakin da suke zama a cikin gidan.

Ba su jima sosai ba Abiy ya yi musu waya ya ce su fito, suka fito suka tarar dashi a bakin mota suka shiga kai tsaye ya ce su wuce unguwar Kundila. Can suka nufa Abiy yana basu address yadda aka faWa masa suna tafiya sai gasu har ?ofar gidan Kawu.

A ?ofar gidan suka faka motar Abiy ya kalli gidan da aka tabbatar masa nan ne gidan Kawu. Babban gida ne mai kyau kana gani ka san mai shi yana da abin hannu so??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????sai. Abiy ya kalli Agogo ya ce, "mu ?arasa masallaci muyi sallah in ya so sai mu dawo." Da to suka amsa suka ?arasa masallacin da yake kusa suka yi sallar juma'a sannan suka dawo mota.

Abiy da kansa ya tambaya aka nuna masa Kawu da yake tahowa yana amsa waya zai shiga gidan ya dawo daga masallaci. Abiy ya ?arasa ya ce, "Assalamu alaikum." Ya dakata da wayar ya amsawa Abiy suka yi musabaha kafin Abiy ya ce, "na san baka sanni ba, ba?o ne in babu damuwa Ina so zamu tattauna." Kawu ya ce, "to bismillah shigo." Abiy ya yi musu magana alamun su shigo suka biyo bayan Abiy.

A wani babban falo ya sauke su wanda maza biyu suke a zaune ya kalli Abiy ya ce, "?an uwana ne, Ina fatan babu damuwa." Abiy ya ce, "babu damuwa. Na ji daWin hakan sosai." Kawu ya ce, "Da yake yau muna Wan ?aramin taro, an kawo kayan lefen ?ar wajan ?anina gashi a zaune shiyasa muke gabaWaya" ya faWa yana nuna masa Kawu Yusuf. Abiy ya ce, "Allah ya sanya alkhairi."

"Amin ya Allah. sai dai ban sanka ba." Abiy ya ce, "Sunana Alhaji Abdullah Ahmad, ni mazaunin garin Kaduna ne. Nazo wajanka ne akan Wan ?aninka Omar ?anin Aysha." Kawu ya gyara zama ya ce, "to Allah yasa ba laifi ya yi ba." Abiy ya murmusa ya ce, "ba laifi ya yi ba, na zo ne ina nemawa ?ata aurensa a yanzu in hakan zai yu."

Duk mutane wajan mamaki ya kama su, suka bi Abiy da kallon mamaki ba tare da ya basu damar magana ba ya ce, "na san komai, kar ku tambaye ni dalili ko meyasa, ina sane duka abinda nake yi. Kawai in zai yu ina so zan bashi aurenta a yanzun nan a Waura auren. Tunda ku ne waliyansa ga nata waliyya a zaune" ya faWa yana nuna su Jawad da suka yi mutuwar zaune.

Kawu ya ce, "To ai ka kulle mana baki ne, wai ka san wanne Omar ka ke magana akai kuwa?."
"Na sani, tunda kaji har nayi maka kwantacesa da Yayarsa ai ka san na sani. Ni sirikin Hajja ne ma?ociyarsu."

Kawu ya ce, "?warai na san Hajja, har gaisheta na taSa shiga nayi sau biyu, kuma Ina jin labarin alkhairinta sosai a wajan Aisha." Abiy ya ce, "na auri ?ar Hajja kafin mutuwa ta raba mu, yarinyar da zan aura mata ?ata ce ta cikina kuma jikar Hajja. Amma naga kamar kuna tantama, in kuna so ku tabbatar ku kira Aisha ku tambayata ku ce ta san Nayla."

"Assalamu alaikum, Kawu ashe ba?i ne da kai bara na koma" aka faWa daga bakin ?ofa ana ?o?arin komawa. Kawu ganin Didi ce sai ya ce, "Aisha shigo mana." Didi ta juyo tana takowa a hankali har tazo tsakiyar falon. Kallon Abiy tayi cikin mamaki ta ce, "Abiy! Ikon Allah kaine a nan?" Ta faWa da fara'a tana kallon sa. Abiy ya murmusa ya ce, "ni ne Aisha."

"Barka da rana."
"Barkan ki, ya gida?."
"Lafiya lau Abiy, ya su Nayla? Tana lafiya?."
"Lafiya lau." Didi ta kalli Kawu ta ce, "Kawu mahaifin jikar Hajja ne Nayla, kuma shine wanda ya karSo Omar daga hannun Senator kwanaki da abin nan ya faru."

Kawu ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "ya yi min bayanin komai Aisha. Wata magana yazo da ita mai girma, wai yana so a yanzu a Waura auren ?arsa da ?aninki Omar." Wara idanu Didi tayi tare da dafe ?irji cikin mamaki ta ce, "Aure Kawu!?." Ya Waga mata ka ta juya ta kalli Abiy ta ce, "Abiy auren Nayla da Omar?."
"Haka nake so, yanzu kuma babu Sata Lokaci."

Jawad da yake gefe ya ce, "Amma Abiy...." Dakatar dashi yayi ta hanyar Waga masa hannu ya ce, "kar wanda ya yi min magana yanzu" ya kalli Aisha ya ce, "Auren zai yu?." Didi ta kasa magana sai kallon Abiy da take yi dan ta rasa abinda zata ce. Abiy ya ce, "in bazai yu ba ki faWa min kawai." Didi cikin kiWima ta ce, "Abiy ni wallahi ban san me zance ba, abin nake ji kamar a mafarki. Meyasa ka ke son aurawa Nayla Omar?. Abiy na san ka san Omar ba sai na faWa maka ba, meyasa haka kwatsam zaka yanke wannan hukuncin?."

"Haka nayi ra'ayi" ya bata amsa a ta?aice.
"Amma Abiy Nayla ba sa'ar auren Omaar ba ce, ka san halin sa ba sai na faWa ba, kowa ma a nan ya san halinsa ba sai an maimaita ba. Meyasa ka ke son aurawa ?arka shi don Allah?" Ta faWa a sanyaye tana kallon Abiy.

Abiy yayi ajiyar zuciya cikin Sacin ran da yake ciki, danne Sacin ransa kawai yake yi yana magana amma Allah kaWai ya san irin yadda zuciyarsa take tafasa akan abinda Nayla tayi masa wanda bai yi tunani ba. Ya ce, "Aisha ki amsa min tambayata kawai, in auren zai yu to in bazai yu ba ki faWa min."

Didi ta sunkuyar da kai dan bata san me zata ce ba, auren Nayla da Omar kuma...? to akan wanne dalili kenan? Kuma ta tabbatar Omar Win ma bai san labarin ba, aka Waura auren sa bai sani ba ai an shiga tashin hankalin faWansa, dan tsaf zai saka yi ya?in duniya. To ita Nayla Win ta sani ko bata sani ba..? Meyasa lokaci Waya Abiy zai zo da wannan maganar?.

Kawu ya katse shirun ya ce, "zai yu mana tunda kana so, amma ka san waye Omar kuwa?." Abiy ya ce, "kaf labarin Omar na sani, har wanda baku san dashi ba na sani, har wanda kuke tunanin ban sani ba shima na sani, yanayin alaqarku da duk abinda yake yi na sani. Kawai ina so ku amince min ne yanzu babu Sata Lokaci."

Kawu ya kalli Didi ya ce, "Aisha ya ki ka ce? Kece uwar Omar, kina ganin kin amince?." Didi tayi ajiyar zuciya bata san abinda zata ce ba wallahi, in ta amince kamar ta cutar da Nayla ne duk da bata san dalilin Abiy na aura mata Omar rana tsaka ba, in bata amince ba kuma kamar bata kyautawa Abiy ba duk da tarin taimakon da ya yi mata bai cancanci haka ba. In ta amince ma aka Waura auren da wacce fuska Omar zai karSi auren?.

Numfashi ta sauke a hankali ta ce, "Ayi abinda Abiy yake so." Abiy yayi murmushi ya ce, "na gode. A yanzu nake so a Waura auren nan babu Sata lokaci."

Kowa mamakin Abiy yake yi kawai kallon suke yi, a take aka kira mazan gidan cousins Win Omar kenan aka tara shaidu Kawu ya bada sadaki naira dubu Wari biyu. Abiy ya umarci Jawad da ya je mota ya Wauko goro da alewa ba jimawa ya kawo aka shaida saurin aure a wajan. Didi dai tana zaune tana kallon su kamar a mafarki take ganin abin, wai yanzu Nayla ta zama matar Omar, ko da wacce fuska zai karSi auren ma oho, ko meyasa Abiy ya yiwa Nayla haka oho.

Bayan an Waura auren Abiy ya kalle su ya ce, "Na gode sosai da karamcin ku a gare ni, duk da baku sanni ba amma ku ka amince ku ka ?ulla a?alar aure dani, naji WaWi sosai Allah ya saka da alkhairi ya ji?an mahaifa. Sannan zaku iya tambayar kowa a garin Kaduna waye Abdullah Ahmad, in sha Allah zaku samu magana mai kyau a kaina."

Kawu Mamman ya ce, "Ni na sanka, mun taSa yin wani taro an gayyato ka matsayin babban ba?o. Na san labarinka kaf, suma baza su rasa sani ba ai kai ba Soyyayen mutum bane." Murmushi Abiy ya yi ya ce, "Na gode. Sai a fara shirin tarewar amaryar nan da kwana biyu masu zuwa in sha Allah."

Kowa kallon Abiy yake yi dan gani suke kamar yana da taSin hankali ko kuma ba ?arsa ba ce. A haka yayi musu sallama cikin mutunci tare da karSar number juna suka rako shi har harabar gidan yana kallon su.

Jawad suna so su yi masa magana amma ya ?i bada fuska dole suka ri?e bakin su suka bari aje gida. Didi ce ta biyo bayan Abiy ta samu har sun fita zasu shiga mota ta ce, "Abiy." Ya jiyo yana kallonta ta ce, "Don Allah meyasa ka yanke wannan hukuncin akan Nayla?."

Abiy ya murmusa cike da takaici da Sacin rai ya ce, "ki kwantar da hankaliki babu komai, ki fara shirin karSar amarya ranar lahadi jibi kenan, ranar Nayla zata tare a gidan mijinta" ya faWa yana shiga mota suka suma suka shiga suka bar unguwar.

Didi ko da ta koma su Kawu tsare ta suka yi da tambayar anya Abiy yana da hankali kuwa, Didi ta ce, "wallahi yana da shi, mutum ne na gari dattdijo ban san meyasa ya aikata hakan ba. Kuma baka ji Kawu ?arami ya sanshi ba? Babban mutum ne mai kuWin gaske a Kaduna, zan iya cewa kaf garin Kaduna an sanshi."

Kawu ya ce, "Nima na san shi Aisha, yana da manya-manyan store a garurun dake cikin ?asar nan. Kawai tantama nake yi akan anya yana da hankali? In kuwa yana dashi anya ita Hauwa Win ?arsa ce?."
"Wallahi ?arsa ce wacce yake matu?ar ?auna, kaf yaransa ma babu kamarta."
"Iko sai Allah, to yanzu shi Omar Win ya san labarin nan?."
"Wallahi bai sani ba Kawu, tashin hankalina bai wuce Omar ya sani ba. Ban san da wacce fuska zai karSi auren nan ba."

Kawu ya ce, "kuma ke zaki faWa masa ba, Haka zaki same shi ki sanar dashi zai iya fahimtar ki. Sai a fara shiri tunda ya ce jibi zata tare." Didi ta ce, "to Kawu ina Omar yaga gidan ma da zai saka amarya?."

Kawu ya ce, "wannan ba abin damuwa bane, ki san yadda zaki yi dashi, akwai gidan da na siyawa ?aninki mai sunan Omar Baba kenan, an gyara shi anyi komai babu abinda ba a saka ba, hatta solar an haWa 24/7. Da yake Allah bai nufa zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login