Showing 42001 words to 45000 words out of 85380 words

Chapter 15 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3850

da daddare ya ce yau ki faWa min waye zaSinki a cikin samarin nan guda huWu."

Zuciyar Nayla bugawa take yi matu?a ta kalli Mama da? itama ita take kallo. Mama ta ce, "Ina jin ki, wa kike Wauka ki ke ganin zaki iya rayuwar aure dashi?." Numfashi ta sauke tare da yin ajiyar zuciya a sanyaye ta ce, "Mama ni...." Sai maganar ma ma?ale saboda bata san ne zata ce ba. Mama ta ce, "Ke me? FaWi ina saurarenki."
"Mama ni ban san ne zan ce ba." Mama ta ce, "to haka zan faWawa mahaifinki baki san ne zaki ce ba?." Nayla ta girgiza kai alamun A'a Mama ta ce, "to faWa min, a wannan lokacin bazai ?yale ba Nayla sai kin fitar da gwani dan burinsa a yanzu bai wuce auren ki ba. Ya ce ya gaji da ganin samari har huWi a matsayin masu neman aurenki, wannan rashin lafiyar da yayi ko wannen su babu wanda bai zo ba kuma ya yi hidima. Har gwara shi Abbas daman ko babu soyayya Wan uwanki ne amma sauran fa?."

Nayla tayi shiru cikin rashin sanin mafita. Ita bata san abinda zata ce ba dan dukkan su babu wanda take so babu kuma wanda take ji zata iya zama dashi a zuciyarta. Zuciyarta mutum Waya take so kuma bayan shi babu wanda zata iya bawa dama. Mama ta katse mata tunani ta ce, "ko na ce masa ya sake baki lokaci?." Da sauri ta Waga kai alamun eh ta ce, "E Mama, don Allah ki ce ya sake bani lokaci har yanzu babu wanda nake ji a cikin zuciyata. Dukkan su bana sonsu."

"Omar ma?ocin Hajja kike so ko!?." Tambayar ta zo a bazata da sauri ta kalli Mama Gabanta na faWauwa sosai, tsoro ya bayyana akan fuskarta ?karara dan bata san ya aka yi Mama ta san labarin ba. Mama tayi murmushi ta ce, "kina mamaki ya aka yi na san waye a zuciyarki Nayla?. Hmm Nayla kenan, kar ki manta ni fa uwa ce a gare ki." Nayla ta sunkuyar da kai cikin bugun zuciya da tsoron bayyanar sirrin zuciyarta ga mutanen gidan su.

Mama a tausashe ta ce, "A da in kin dawo daga Kano labarin Yayarsa kike yi ba shi ba, in hirarsa tazo cikin labarin kina sako shi ne kina tsaki saboda tsoro da haushi yake baki. Amma daga baya sai hirar ta zama hirarsa kawai kike yi, kina bada labarin yanayin yadda yake kyau in yana murmushi. Daga lokacin da akace an kama shi hankali ki ya tashi kika yi ruWewar da baki san kin yi ba. Muka je Kano bikin Shayida kika kusa yin accident a mota saboda kina so kizo ki samu mahifinki da maganar kina so a fito dashi. A yadda kike yiwa Abiy bayani kowa zai fahimci rauninki a kansa ne ba akan Yayarsa ba, kowa zai fahimci kina ro?on a fito dashi ne saboda shi kike so ba dan kina tausayin Yayarsa ba. Da Abiy ya amsa har ya kira Senator a lokacin farin cikin ki ya kasa Soyuwa akan fuskarki. Daga lokacin da akace ya dawo a ranar ke kuma ki ka dawo gida gabaWaya rasa nutsuwar kiki yi Nayla, har wayata kin karSa kin kira Salma saboda bata Waukar kiranki ke kuma kina so ki ji ko ya dawo."

Mama ta ri?e hannunta sosai ta ce, "tun daga lokacin na saka alamar tambaya akansa a zuciyarki. Abinda ya saka na tabbatar da zargina a kanki lokacin da suka zo gidan nan, kin ruWe gabaWaya, duk da ciwon da kike ji wanda ya hana ki zuwa aiki a ranar nan da nan kika neme shi kika rasa. A nan na tabbatar da Omar ma?ocin Hajja shine wanda kike so."

Kawai sai ta fashe da kuka ta kifa kanta a hannun Mama tana kuka sosai. Mama ta dinga shafa bayanta a hankali tana murmshshin da ita kaWai ta san ma'anarsa. A sanyaye ta ce, "Ki yi shiru mana Nayla, ba ga ni ba? zan tsaya a Sangarenki wajan ganin kin samu abinda ke so. Ki nutsu mu yi magana bana son yawan kukan nan naki."

Ta Wago fuskarta ta ji?e da hawaye ta ce, "Mama in Abiy ya ji wannan maganar fushi zai yi dani, Bazai amince da zancen nan ba kawai gwara abar maganar Mama." Mama ta shafa fuskarta ta share mata hawaye ta ce, "FaWa min gaskiya kina son Omar so na aure ko bakya sonsa?." Nayla ta kalli Mama sai ta sunkuyar da kai ta ce, "Mama faWar bashi da amfani."

"Ni nace ki faWa min, zan kuma tabbatar miki da amfaninsa yanzu ko nan gaba." Nayla ta ce, "Ina sonsa Mama, wallahi Ina sonsa son da ban san yawan sa ba. Kuma...kuma....ni ban san lokacin da na fara sonsa ba, haka kawai na wayi gari naji Ina jinsa a zuciyata. Ban san me zan yi ba Mama, na rasa mafita ki taimaka min" ta faWa a raunane tana kallon Mama.

Mama ta girgiza kai ta ce, "to naji, nutsu mu yi magana." Nayla tayi ajiyar zuciya Mama ta ce, "kuma zaki iya aurensa a yanayin da yake ciki?." Nayla ta sauke jiyar zuciya t ce, "Mama bana kawo hakan a zuciyata gaskiya."
"Ina tambayarki, in kika samu dama zaki aure shi?."
"Mama ai bazan samu ba ma." Mama tayi murmushi ta ce, "ki amsa min tambayata mana, in kika samu dama zaki iya auren shi?." Nayla ta Waga kai alamun eh tana kulle idanunta.

Mama tayi ajiyar zuciya ta ce, "shikenan share hawayenki zan taya ki da addu'a, sannan zan san yadda zan yi Abiy ya amince da aurenki da Oamar." Da sauri ta kalli Mama cikin tsoro Mama ta Waga mata kai ta ce, "kar ki damu, zan tabbatar da kin samu abinda kike so kedai ki bani haWin kai kar ki bani kunya. In mahaifinki ya ji maganar ya tambayeki kar ki ce masa a'a, ki faWa masa abinda yake zuciyarki, mahaifinki yana sonki kuma na tabbatar da zai amince da abinda kike so. Sannan duk abinda nace kiyi, ta haka ne zaki samu cikar burinki."

Nayla kallon Mama kawai take yi amma a zuciyarta tana jin kamar hakan bazai yu ba. A sanyaye ta ce, "Mama hakan zai yu kuwa? Ni da zaki bar maganar kawai zan ha?ura na Wauki mutum Waya a cikin wanda Abiy ya ce na aure shi."

"Haka zaki zauna da wanda bakya so? Gangar jikinki fa kawai ya aura zuciyarki na tare da Omar. Baza ki iya yi masa biyyaya ba saboda ba shi kike so ba, ke kin san auren wanda baka so kuwa? Ko me mijinki zai miki bazai burge ki ba, tunanin Omar kawai zaki dinga yi kina Waukarwa kanki zunubi." Nayla ta ce, "To Mama ya zanyi? Abiy bazai amince ba."

Mama ta ce, "zai amince. Kin san mahaifinki ba kuWi ne a gabansa ba, bai saka a zuciyarsa lallai sai kun auri masu kuWi ba, tunda kina aikin ki kuma kina da shago wannan bazai dame shi ba. Kuma in ya so zai iya mayar da Omar yadda yake so, yana da dukiyar da zata azurta Omar. To mahaifinki ba haka yake so ba, ba gidan kuWi yake burin aurar daku ba, a ri?e masa yarinya kawai shi yake buri da ra'ayi."

Nayla ta girgiz kai ta ce, "ni dai Mama tsoro nake ji." Mama ta ce, "ki daina jin tsoro ina tare dake, Ke dai kiyi duk abinda na ce zaki mallaki Omaar in sha Allah." Nayla ta ce, "Mama Wan daba ne fa, taya Abiy zai amince?."
"Da ya ke Wan daba ai, ba naji kuna waya da Salma tana tabbatar miki har shago ya buWe na sana'a ba?." Nayla ta Waga kai ta ce, "eh Mama."
"To kar ki damu, labarinsa na baya ya wuce labarin yanzu ake yi. Kedai ki kwantar da hankalinki, wannan kukan ne bana so na ga kina yi, bana so na ganki cikin tashin hankali. In mahaifiyarki na raye na tabbatar zata yi duk abinda zata yi wajan ganin farin cikin ki, to nima haka take a wajena. Kar ki damu zan san abinda zan yi dan ganin kin yi farin ciki."

FaWawa jikin Mama tayi ta rungume ta yana hawaye, Mama tayi murmushi tana shafa bayanta tana murmushin da ita kaWai ta san manufarsa, dan wannan dama ce da ta jima tana nema yanzu tazo mata cikin sau?i. Ta Wago ta daga jikinta ta shafa fuskarta ta ce, "ki kwantar da hankalinki, Ina tare dake a ko yaushe." Nayla tayi murmushi cikin farin cikin da take ji a zuciyarta ta ce, "Na gode Mama." Mama taja hancinta ta mi?e ta fita ta bar Nayla na murmushi ita kaWai kamar zararriya.

Mama tana fita daga Wakin tayi dariya ta ce, "Nayla kenan, na samu dama a hannuna ba tare da na sha wahala ba zan aikata duk abinda zan aikata. Zan tabbatar da na yi abinda nake so cikin sau?i ba tare da tashin hankali ba. Mu je zuwa" ta faWa tana murmushi ta bar ?ofar Wakin zuwa Sangaren Abiy.
KRB2P016

Da sallama Mama ta shiga Sangaren Abiy yana zaune yana duba littafi a hannunsa, ya kalle ya amsa yana cigaba da duba littafin. Zama tayi ta ce,  A kawo kunun gyaWar?. Abiy ya ce,  A a barshi sai anjima. Ya kuka yi da Nayla?. Mama tayi ajiyar zuciya ta gyara zama ta ce,  yanzu muka gama magana da ita. Abiy ya kalle ta ya ce,  to Ina jinki. Mama ta ce,  Abiy ka ?ara mata lokaci saboda yanzu& . Ya katse Mama ya ce,  kamar ya na ?ara mata lokaci, wanne irin lokaci yake so na ?ara mata?. Auren ne bata so ko me?.

Mama ta ce,  A a ba haka bane&  Nan ma ya katse ta ya ce,  to yane? FaWa min waye zaSin taa cikin mutane huWu?. Mama ta kalle shi ta ce,  babu wanda take so a cikin su. Abiy ya ajjiye littafin hannunsa ya kalli Mama da mamaki ya ce,  babu wanda take so a cikin fa ki ka ce? duka mutane huWun babu wanda ya yi mata?. Mama ta Waga kai ta ce,  babu, shiyasa nace maka tana bu?atar lokaci.

 Wannan ma ai shirmen banza ne da wofi, dan tsabar rainin hankali samari har huWu ta ce babu wanda take so a ciki dan ta raina ni ta mayar dani ?aramin mutum?. Mtsw! Yaja ?armain tsaki yana Waukar waya ya saka a kunne ya ce,  Nayla zo falon sama ki same ni.

Nayla da ta samu kiran Abiy gabanta ya faWi tsoro ya mamaye zuciyarta kar taje Mama ta faWa masa halin da ake ciki. A sanyaye ta nufi ?ofar da zata kai ta falon sa na sama, ta shiga da sallama ya amsa yana kallon ta. Yanayin fuskarsa da take a Waure ya saka ?irjinta cigaba da bugawa, ta taka a sanyaye ta shiga ta zauna a akan carpet ta ce,  Abiy gani. Ya kalle ta ya ce,  Naji sa?onki akan samarin da suke naman aurenki, ki ka ce babu wanda kike so a cikin su?.

Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba. Abiy ya ce,  ke nake saurare. Nayla ta yi gyara zama nan ma bata ce komai ba. Abiy ya ce,  magana nake miki, da gaske babu wanda kike so a cikin su?.

Ta Waga kai alamun eh, yayi tsaki a Wan fusace ya ce,  magana zaki yi min!. Murya a sanyaye ta ce,  E Abiy.
 To wa kike so?. Gabanta ya faWi ta sauke kanta ?asa bata ce komai ba. Abiy ya sake cewa,  In ina tambayarki kina yi min shiru ranki ne zai Saci. In bakya sonsu wa ki ke so?.

Nayla ta ce,  Babu kowa Abiy. Abiy ya ce,  to ki tabbatar da kin samu wanda zaki so a cikin kwana biyu, na baki nan da jibi kizo ki faWa min wa kika Wauka a cikin su in ba haka ba zan aura miki duk wanda naga dama. Na gaji da wannan shirmen naki, gabaWaya kin canja kin koma wata shiru-shiru, da kin dawo daga aiki kika shiga Wakin bakya fitowa. An tambaye ki damuwarki kin?i faWa, likita ya ce kina da damuwa amma kin ?i faWar abinda yake damunki. Dan kinga na ?yale ki shine kuma zaki kawo min iskanci? To baki isa ba, nan da jibi ki tabbatar da ko ma waye kin zaSa an sanar dani in ba haka ba kuma ranki zai Saci wallahi. Na gaji da lallaSaki, yau ciwon kai, gobe zazzaSi, jibi ciwon ?irji. Dan kin raina mu kuma kin kalle mu kince baki da damuwa.

Nayla jin Abiy yana faWa abinda ba sosai yake yi ba sai tayi sanyi ta ce,  Kayi ha?uri Abiy. Abiy ya ce,  Nayi yanzu, amma ki sani jibi bazan yi ha?urin ba.
 To Abiy.
 Tashi ki bani waje. Ta mi?e a sanyaye ta fita cikin rashin sanin abinda zata yi.

Ya kalli Mama ya ce,  ke kike goya mata baya take abinda take so, ki faWa mata wannan karan bazan Waga mata ?afa ba wallahi, na gaji da wannan yazo tace bata so dole ta zaSi Waya daga a cikin waWanan huWun in ba haka ba ni zan aurar da ita ga wanda nake so. Mama ta ce,  in sha Allah hakan bazai faru ba, zan mata magana in sha Allah.
 Ya fi muku ya faWa yana Waukar littafin da ya ajjiye yana cigaba da dubawa.

" " " " " " "

Narma tunda lokacin da suka sauka a Texas cikin ?asar America tana yadda take bata canja ba, ko yaushe tana cikin Waki a zaune tana aukin tunani ko magana ba ta haWata da Ashraf. Shi kuwa yana sane ya ?yaleta dan ta Wan nutsu amma yaga abin nata ya yi yawa ha?urinsa ya fara ?arewa, ko magana bata yi masa balle ya saka ran wani abun daban.

Kamar ko yaushe tana sanye da ?aramar riga iyakar ta guiwa mai siririn hannu tana kallon taga, kasancewar lokacin snow ne ko Ina a garin ya lulluSe da ?an?ara sanyi yayi yawa sai da taimakon wood stove da take Wumama Waki. Shigowa Ashraf yayi ya kalle ta tun daga gashin kanta da yake a buWe har ?afar ta da take sanye da room slippers.

Abinda ya saba ji a kanta yaji yana jansa zuwa gareta, a hankali yake takawa inda take har yazo daf da ita ya le?e kansa ta kafaWarta yana kallon window Win da take kallo. Hannunsa ya saka ya riko cikinta ya jawo ?ugunta ya haWa shi da jikinsa yana kallon gefen fuskarta.  My love tunanin me kike yi? Ya faWa a kunnenta yana kallon fuskarta. Bata motsa ba dan Omar Winta take tunani har lokacin zuciyarta ta gaza karSar Ashraf a matsayin mijinta, Omar Win dai shi ne a zuciyarta.

Kiss yayi mata a wuyanta hakan ya saka ta kalle shi suka haWa ido ya ce,  Haba my love kina wahalar dani, kin san Ina sonki fa, please daina wahalar dani. Hannunta ta saka ta cire hannunsa gaga cikinta ta ce,  I need rest, please leave! ta faWa a sanyaye tana ?o?arin barin wajan. Ri?o hannunta yayi ya dawo da ita baya yazo daf da ita yana kallon idanunta ya ce,  i don t want to leave your side, ina sonki sosai Narma. Allow me to show you how much you mean to me ya faWa tana ri?e wuyanta yana shafawa a hankali har gashin kanta.

 Kai ka ce zaka iya zama dani a ko wanne irin yanayin ko? To bani bu?atar your love or time and whatever, ka ?yale ni a haka, haka nake son zama bana son takura ta faWa tana janye jikinta ta fita ta bar masa Wakin. Girgiza kai yake yi cikin Sacin rai ya ce,  No Narma baki isa ba, baki isa ki dinga saka ni a damuwa da yanayi mara daWi ba. I feel your desire a strongly, and i want to satisfy, tun kafin na aure ki nake jin son kasancewa dake a zuciyata. Yanzu matata ce ke baki isa ki yi min iyaka da jikinki ba ya faWa shi kaWai yana shiga toilet. Koma meye sai dai ya faru bazai sake barin ta haka yana kallon ta kamar wacce ya dasa yana jiran ta girma ba.

Narma falo ta koma ta Wora ?afa kan Waya tana kaWawa cikin tunani. Yanzu in ta kira Omar sau dubu bata shiga ma balle ta same shi, ta gwada WhatsApp duk a banza. Gashi iya WhatsApp ta san yana yi bata sani ba ko yana da wani handle a social media platform. Ajiyar zuciya tayi ta Wauki wayarta tana duba hoton da ta yi masa tana murmushi cikin soyayya.

KarSar wayar taji an yi suka haWa ido ta ga ya Waure fuska ta sauke kai ya ce,  Narma bazan juri wannan shirmen naki ba fa, da aurena a kanki ki dinga kallon hoton wani banza?. Narma ta kalle shi ta ce,  kar ka sake ce masa banza, ai na faWa maka daman bana sonka kace ka shirya aurena, to gani ga ka ai.

A fusace ya yo kanta ya ce,  na rantse da Allah bazan juri wannan shirmen naki ba, na juri iya abinda zan iya yanzu bazan jure ba. Mijinki ne ni dole ki yi abinda nake so. Narma kallon sa take yi kafin ta ce,  ni bani da wani miji in ba Faruk ba, don haka ka daina wahalar da kanka baza ka taSa samu na a matsayin matar ka ba. Ya Waga idanunsa ya kalle ta ya ce,  au haka ne? Zan tabbatar miki da ni ne mijin ki ba shi ba, kuma zan nuna miki nike da iko dake bashi ba, kuma har abada bazaki aure shi ba. Wuce shi ta yi zuwa Waki dan lokacin sallar azahar ya yi.

Sai da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login