Showing 3001 words to 6000 words out of 85380 words

Chapter 2 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3823

kawai ya tayarwa da baiwar Allah hankali bata ji ba bata gani ba." Hajja bata ce komai ba ta san Daddy zai zo tunda juma'a ce tayi alqawarin yi masa magana in yana da hanya a fito da Omar ko dan saboda Didi Win.

Da yamma kuwa sai ga Daddy bayan sun gaisa da Hajja take yi masa bayani akan Omar. Daddy ya ce, "wanne Sentor Win kenan?." Hajja ta kalli Salma ta ce, "Salma meye ma ta ce sunansa?." Salma ta ce, "Daddy Sen Sagir Sani take nufi." Daddy ya ce, "Kai! Shi ya saka aka kama shi?." Hajja ta ce, "eh shine. In kana da hanya ka yi masa magana don Allah ya sako shi ko dan ?ar uwar sa da bata da kowa sai shi, ta shiga damuwa sosai Allah, kaWai ya san halin da zata iya in akace Omar bazai dawo ba."

Daddy ya ce, "Hajja na san shi, amma bani da wata kyakykyawar mu'amala dashi gaskiya saboda mutumin bashi da kirki ko kaWan. Bashi da kirki bai san kirki ba kuma bashi da Waga ?afa kwata-kwata. Amma zan bincika a mutanena ni akwai wanda yake da mu'amala mai kyau dashi sai ayi masa magana, ko Ali zan tambaya ko shi ko Khabir. amma fitowarsa gaskiya da wahala." Hajja ta sauke numfashi ta ce, "Don Allah ka hanzarta."
"In sha Allah zan yi Hajja."
"Yauwa Allah ya yi albarka."
"Amin Hajja. Batun tafiyar ku umra yaushe ki ke ganin zaku je?." Hajja ta ce, "Duk sanda aka ce a shirye nake." Daddy ya ce, "Shikenan Hajja, zaki ji ni in sha Allah." Ta amsa tana ta addu'a yana amsawa shi da Salma. Hajja ta ce, "na san Ali ma yana hanya, wannan karon ka yi masa shigar saurin kaini Saudia. Khabir daman shi ya ce England zai kaini, na ce Khabiru nayi me a can, wai ki huta." Daddy yayi dariya ya ce, "Wan rigima kenan." Daga nan suka yi sallama Daddy ya tafi.
KRB2P002
Arewabooks@nanahaleema11

Bayan sallar magriba Hajja ta tura Salma ta kira mata Didi suka dawo tare. Hajja ta bita da kallo ganin duk ta firgice ta ce, "Aysha ki kwantar da hankali ki don Allah, kalli yadda ki ka firgice lokaci Waya." Didi ta zauna kusa da Hajja tana murmushi kaWan-kaWan. Hajja ta ce, "Nayi magana da mahaifin Salma, ya ce min shi bashi da wata alaqa mai kyau da Sanata, amma akwai wanda zai yiwa magana zai same shi in Allah ya taimaka za a dace. Amma ya maimaita min bashi da kirki sai dai mu dinga addu'a kawai."

Didi tayi ajiyar zuciya cikin sanyi ta ce, "Allah ya sa Hajja.." Hajja? ta ce, "amin. Sannan ki Wauko abinda zaki Wauko a gidan ki taho nan ki kwana, in aka farga Omar baya nan akwai masu jin haushinsa da yawa zasu iya cewa zasu shigo gidan ku. A san bai saaba tafiya ya bar gida ba, in aka lura da baya nan za a iya samu damuwa." Didi ta ce, "To Hajja, amma babu abinda zai faru."
"A'a dai, gwara dai ki dawo nan Win hankalina zai fi kwanciya." Wayar Didi ce take ?ara ta duba taga AbdulHamid ne yake yi mata waya, ta kalli Hajja ta ce, "Hajja AbdulHamid ne yazo."

Hajja ta ce, "to ya shigo gidan nan sai ku tattauna, shigar sa gidan ku ke kaWai babu daWi." Didi ta ce, "to bara na kira shi sai yazo nan Win." Ta faWa tana Waukar wayar ta sanar dashi inda zai zo kafin Hajja ta tura Salma ta shigo dashi. Da sallama ya shigo cikin kamalar sa ta ko yaushe, Salma tayi masa iso har falon Hajja ya shigo ya gaishe da Hajja da girmamawa ta amsa tana cewa, "Yau ai wajan uwar gidan kazo ko?." Murmushi ya yi ya ce, "Daman yau zuwan na ki ne."

Hajja ta ce, "Haba shiyasa ka sha kwalliya mana, dan wannan kwaliyya bata amarya ba ce." Murmushi ya yi yana kallon Didi da bata da walwala sosai duk fuskar ta ta canja. Hajja ta ce, "ya shirin biki? Saura kwana nawa ya rage ne?."
"Saura sati shida. Yanzu ma nazo akan batun gidan da za a je gani saboda shirye-shirye." Hajja ta ce, "kai har saura mako shida? Lallai abu yazo. Allah ya nuna mana ya tabbatar da alkhairi." Ya amsa da amin.

Hajja ta ce, "gashi tana cikin yanayi na damuwa. Omar ne aka kama shi Abuja ba tare da laifin komai ba." AbdulHamid ya ce, "Subahanallah! Yaushe hakan ya faru?."
"Jiya."
"Bata sanar dani ba, na dai damuwa a muryar ta." Hajja ta ce, "wallahi shine ya canja ta gabaWaya."

AbdulHamid ya ce, "Ya aka yi hakan ya faru?." Labari Didi ta bashi muryarta har rawa take yi saboda damuwa, ya sauke numfashi bayan ta ya ce, "case ne na manya gaskiya tunda da kansa ya saka aka kama shi, amma a shari'ance bashi da hurumin kama Omar dan bai yi masa laifin komai ba. To matsalar itace yadda ?asar mu take sai a hankali." Hajja ta ce, "Wannan gaskiya ne, amma zamu san abinda zamu yi in sha Allah."

AbdulHamid ya ce, "nima zan yi ?o?ari daga Sangarena in sha Allah. Kar ki damu kin ji?" Ya faWa yana kallon Didi. Kai ya girgiza kai bata ce komai ba. AbudlHamid ya ce, "Amma ba ke kaWai zaki kwana a gidan ba ko?." Ta Waga kai ta ce, "Hajja ta ce na zauna a nan."
"Gaskiya haka ya kamata, za a iya amfani da rashin Omar don cutar da ke." Hajja ta mi?e ta basu waje daman Salma ta shige ciki tunda ta ajjiye masa ruwa da lemo.

Rarrashin Didi ya dinga yi har sai da ya ga ta Wan kwantar da hankalinta, maganar gidan da ta kawo shi ma basu yi ba dan ya san ba a nutse take ba sai ta dawo hankalinta sa tattauna. Bai jima sosai ba ya saka ta kira masa Hajja suka yi sallama yana godiya sannan ya tafi.

Didi ta ce, "Hajja bara na je gida na kashe kayan wuta na dawo." Hajja ta amsa mata sannan ta fita. Ba jimawa ta dawo gidan bayan ta kulle gidan ta dawo falon Hajja ta zauna amma gabaWaya bata jin daWi.

Sallamar Bashir ta ji daga gate Win Hajja, ta tashi da hanzari ta je ta ce, "Bashir ya ake ciki?." Ya kalli Didi ya ce, "Didi Ina ya bincikawa, na dawo Goje ya ce min kina gidan nan shine nazo na ji lafiya. Ko akwai wanda ya shiga gidan?."

"Babu kowa. Hajja ta ce na dawo nan na kwana ne saboda gidan babu kowa."
"Haba Didi, muna nan fa, wallahi ko kuWa bazai taSa ki da niyar cutarwa ba." Didi ta ce, "Gwara dai na zauna a nan Win Bashir. Don Allah duk abinda ake ciki ka yi min waya." Bashir ya amsa sannan ta dawo gida wajan Hajja gabaWaya bata da nutsuwa.

Hajja ta ce, "Salma kai ta Wakin Nayla ta huta." Salma ta raka Didi Wakin Nayla da yake shirye tsaf sai khamshin turarenta yake yi. Murmushi tayi tunawa da Nayla, ta zauna a gefen gadon tana kallon kan mudubin Nayla da yake ajjiye da kayan kwalliya kamar a gidan take rayuwa. Murmushi tayi ta kalli Salma da ta kawo mata abinci ta ce, "Salma ni fa ba ba?uwa bace, ki daina hidima haka."
Salma tayi dariya ta ce, "na sani Didi, hutar dake nayi." Didi ta ce, "na gode. ?akin ?anwata Nayla sai ?hamshi, ga kayan kwalliya kamar tana ciki."

Salma tayi dariya ta ce, "Aljanar kwalliya kenan." Didi tayi murmushi kawai bata ce komai ba Salma ta fita ita kuma ta Wauki abincin ta fito ta zauna kusa da Hajja tana ci suna ?ar hira kaWan.

Washe gari.
Abuja.

? ? ?? "Daddy Ina aka kai Faruk? Daddy a dokance baka da right Win da zaka saka a kulle shi ba tare da ya yi wani laifi ba. Yana da damar da zai kai ka ?ara court kuma dole a yi maka hukuncin aikata haka" Sai kuma ta daidaita murya ta ce, "Dad Ina yake? Don Allah ka faWa min inda aka kai shi" ta faWa tana zamewa a wajan tana kallon mahaifin na ta.

Shi tausayi take bashi sosai, gabaWaya ta fita daga hankalinta ta koma wani iri kamar ba Narma ?ar gayu mai aji ba. Kallon Mum ya yi da take kallon sa kafin ya sake kallon Narma ya ce, "Narma ki nutsu." Narma cikin kuka ta ce, "bazan iya nutsuwa ba Dad, bazan iya nutsuwa ba Ina so na ganshi. Ina kewarsa, don Allah Dad kar ka cutar dashi. In aurena dashi ne baka so zan ha?ura dashi amma kar ka yi masa komai don Allah Daddy, bashi da laifin komai ni ce na fara son sa."

Sen ya kalle ta ya ce, "na ce ki nutsu ko?." Zama tayi tana share hawaye ya kalle ta ya ce, "Ranar monday zaki jinginar da duk abinda ki ke yi zaki tafi London." Da sauri ta Wago kai ta kalle shi murya na rawa ta ce, "Daddy London..? Me zan yi a can?."
"Ina so ki je ki huta hankali ki ya dawo jikinki daga baya za a san abinda za ayi."
"Dad i can't go anywhere without knowing where Faruk is. Where you have take to him?. Dad wallahi bai yi deserving wannan hukuncin ba, it's his fault for falling in love with me?. Kuma Daddy kai ka yi min al?awari zaka bani duk wanda nake so, na kuma kawo maka shi ga sakamakon da ya biyo baya."

Dad kallon ta ya ke yi kamar bata cikin hankalinta, sai magana take yi mara kan gado kamar ba ita ba. Sai ya yi shiru bai ce mata komai ba. Narma ta ce, "don Allah Dad ka taimake ni ka bar Faruk ya tafi, ka ?yale shi na yarda na ha?uta dashi bazan sake cewa Ina sonsa ba." Mum ta kalli Dad sai ta mi?e kawai ta bar wajan jim kaWan sai gata ta dawo. Ba jimawa sosai sai ga wani saurayi ya shigo Mum ta taso ta ri?e Narma ya yi mata allurar bacci.

Mum ta kalli Dad ta ce, "ni na kira shi, na lura Narma ba ta cikin hankalinta. Ya gama lalata min tunanin yarinyata, ya gama cutar da ita. Na rantse da Allah na tsane shi bana sonsa, bana so ya rayu a cikin duniyar nan." Dad ya kalli Narma da tayi bacci a wajan ya kalli Mum ya ce, "sai a hankali zata dawo daidai, ita da ganin sa kuma har abada" yana gama faWa ya fita dan ya zama dole ya canja shiri akan Omar.

Narma bacci tayi na sama da awa bakwai, dan tun safe take bacci har bayan sallar la'asar sannan ta farka da weaknesses joints. Da?yar ta iya wanka ta fito tana kallon kanta a madubi, key Win mota ta Wauka bayan ta shirya ta fita daga gida.

Kai tsaye wajan Wan sanda da ya zo ya kama Omar ta je ta ce tana so ta ga Omar. Da kamar bazai kai ta ba amma ya ga ta dage sai ya saka aka raka ta inda aka ajjiye Omar.

Can ?auyen Abuja ne, cikin wata unguwa da bata taSa zuwa ba, aka buWe mata wani wula?antaccen gida ta shiga ana biye da bayanta. Kallon gidan take yi tana hawaye, wai Omar Win ta ne a cikin nan ba tare da ya yi laifin komai ba.

Da ta shiga waje mai kyau aka ajjiye ta, inda masu azabtar dashi Win suke nan suka bata ta zauna. Bouncers Win da suke gidan kaWai abin tsoro ne, Narma sai kallo su take yi domin kana ganin su ka san basu da imani, in ka shiga hannun su sai sun karya ka. Ita kam ta kasa zama sai zagaye take yi, tana ji an buWe ?ofa da sauri ta kalli wajan. Ajiyar zuciya ta sauke ganin Omar da kayan jikinsa da suka zo amma kayan sun yi ba?i, duk da ba Saki sosai ba amma sun yi duhu. Fuskarsa babu walwala ko kaWan, sannan wahala ta bayyana ?arara akan fuskarsa. Da gudu Narma ta taho inda yake zata rungume shi ya motsa ya Wan ja baya kaWan sai ta kalle shi tana kuka.

Zubewa tayi a wajan ta ce, "im sorry Faruk! I'm sorry!!" Ta faWa tana kuka sosai tana dur?ushe a gaban sa. Bai ce komai ba bai ma kalle ta ba idanunsa a rufe babu abinda yake addabar zuciyarsa kamar Sacin rai, babu abinda yake damunsa kamar halin da Didi take ciki. Zaman inda yake da wahalar da ake bashi baya damuwan sa kamar barin Didi da ya yi a gida ita kaWai. Ya san tana can tana kuka, ya san tana can hankalinta a tashe saboda rashin ganinsa. Wannan tunanin yafi halin da yake ciki ?una da raWaWi a zuciyar sa.

Narma ta ce, "Na yi maka alqawari zan yi duk yadda zan yi wajan ganin ka bar wajan nan, zan yi iyakar iyawata wajan tabbatar da Dad ya ?yaleka. Ni lawyer ce, zan yi duk abinda zan yi saboda kai Faruk." Sam kalaman ta basa kwantar masa da hankali dan gabaWaya ma baya so yaji koda maganarta, ba wai dan ya tsane ta ko dan yana jin haushinta ba, sai da tsantsar ba?in cikin da yake zuciyarsa.

Narma ta sake cewa, "kayi magana Faruk, ka ce wani abun ko zan ji daWi." Sai a lokacin ya sauke shanyayyun idanunsa a kanta, haWa ido suka yi ya kalle ta na sakan biyar kafin ya janye idanunsa. Tabbas ta rame kana ganinta ka san tana cikin damuwa. Damuwarta bata dame shi ba, inda zai iya yi mata magana da ya yi magana akan Didi, amma baya tunanin ko waye yazo a wannan lokaci zai iya buWe bakinsa ya yi magana, shirun shine alkhairi a gare shi.

Omar da kansa ya juya ya koma inda aka ajjiye shi, Narma na kiransa amma ya yi mata banza ko juyowa bai yi ba. Bashi da nutsuwar da zai iya kallon ta har ya yi mata magana shiyasa bai ce komai ba.

Narma da hawaye shaSe-shaSe ta fito ta shiga mota ta fizgi ta da ?arfi zuwa gida. Tana tafiya tana kuka har ta je gida tana shiga falo ta zube a jikin Mum tana kuka mai sauti. Hankalin Mum ya tashi dan ita take nema tun bayan fitarta ta ce, "Narma Ina kika je? Kin san baki da lafiya kika fita ke kaWai?. Me ya same ki ke kuka haka?."
"Mum naje na ga Faruk, Mum gabaWaya an canja min Faruk Wina, Mum Dad ya saka ana azabtar min dashi. Mum abinda nake ji a zuciyata ji nake kamar na kashe kaina. Kinga bouncers Win da Dad ya ajjiye suna dukan Omar, kinga irin azabar da ake yi masa? Kashe kaina kawai zan yi!."

Hankalin Mum ya tashi da kalaman Narma, da hanzari ta dannawa Sen waya Allah ya taimaka bai yi nisa ba ya ?araso gidan.? A lokacim Narma take cewa, "Mum Ina sonsa, Ina ?aunarsa. Mum in Dady bai fitar dashi daga gidan da ya saka aka ajjiye ba ni zan yi da kaina, in aka hana ni zan yiwa kaina illa Mum, zan iya kashe kaina akan Faruk Mum...!" Ta ?arasa faWa tana jan sunan Mum Win tana kuka.

Sen ya ji ta ya ?araso ya tasar da ita tsaye ya rungume ta sai kuka take yi yana rarrashinta. Surutai take tayi masa barkatai akan Omar yana ta rarrashi yana shafa bayanta, sai da ya ga ta Wan yi sanyi sannan ya kalle ta ya ce, "je ki Waki ki huta." Zata yi magana ya ce, "kar ki ce komai Daughter, je ki" ba musu ta tafi zuwa Waki tana share hawaye.

Mun ta kalli Dad a ?ufule ta ce, "Tunda har ka san zata iya binciko inda yake har taje ta ganshi meye amfanin barinsa nan? Meyasa baka kai shi inda baza ta iya zuwa ba?." Dad ya ce, "shiyasa zan tura ta London."
"Saboda shi sai ta bar Nigeria? Kenan shi ya yi riba akan ta ko me?."
"Saboda ta samu peace of mind. Shi kuma zan ji dashi" ya faWa yana hawa sama ya bar Mum a wajan. Dole ya san abinda zai yi akan Omar kafin ?arsa ta rasa hankalinta akansa.

*Kaduna.*

Nayla na zaune sun gama magana da Twiny a waya sai ta kira Salma, tana Wauka ta ce, "Sis ya ki ke? Ya Hajja?." Salma ta ce, "lafiya lau Nayla, ya Mama da Abiy?."
"Kowa yana nan lafiya lau. Kin ga alert?."
"Eh naga kuWi ya zo, na ce Nayla kuWin wa ta saka min." Nayla ta ce, "KuWinki ne, first salaryna ya sauka."

Salma tayi dariya ta ce, "godiya nake ma'aikaciya." Murmushin ya?e Nayla tayi kafin Salma ta ce, "ya ki ke? Ina fatan yanzu babu damuwa ko?." Murmushi ta yi kawai bata ce komai ba dan maganar da suka gama da Jidda kenan. Salma ta ce, "Nayla don Allah ki kwantar da hankalinki, in kina tayar da hankali Abiy bazai ji daWi? ba. Yanzu kin samu magana dashi Win?."

Nayla ta ce, "Salma na faWa muku ni bana so ya san Ina sonsa, gwara ku taya ni addu'a kawai Allah ya kawo min ?arshen ko meye. Bana jin zan iya furta masa kalmar so gaskiya."
"Amma Nayla cutar da kan ki ke ke yi. Ni ki faWa min inda take a faWin Kano naje na same shi nayi masa magana, sai cutuwa ki ke yi a kansa, ba ke kika sakawa kan ki ba Allah ne, meye aibu dan an faWa masa?." Nayla ta murmusa ta ce, "Salma sanin waye bashi da wani mahimmaci, koda yana sona ma aure na dashi bazai yu ba. Na tabbatar Abiy bazai aura min shi ba."

Da mamaki Salma ta ce, "kafiri ne?." Nayla ta ce, "musulmi ne yana sallah kamar kowa, kawai dai aurena dashi na san bazai taSa yuwa ba. Balle kuma ni bazan faWi suna ba, kuma sannan bazan ce Ina sonsa ba." Salma tayi shiru kafin ta ce, "Nayla kar ki cutar da kan ki, ni na san Abiy indai kina sonsa shima zai so shi Nayla." Nayla bata ce komai ba Salma ta ce, "kin yi shiru."

"To me zan ce miki Salma? Asalin gaskiyata nake faWa miki Salma, na san Ina sonsa, Ina ?aunarsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login