Showing 12001 words to 15000 words out of 85380 words

Chapter 5 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3824

mata dukan tsiya." Ya kalli Didi ya ce, "kina jina? Ki tabbatar da kin saka ya karya asirin da ya yi mata, in ba haka ba kema bazan bar ki ba wallahi, sai na saka miki ba?in ciki a zuciyarki." Didi murya na rawa matu?a ta ce, "to a ina zan ganshi balle ya karya asirin?."

Mum ta kalli Dad ta ce, "in dai yana kusa a haWata dashi su yi magana, ya tabbatar ya karya asirin in ba haka ba wallahi bazai fita ba." Dad ya kalle ta ya ce, "Ina zuwa" ya faWa yana Waukar waya yana dannawa kafin ya kara a kunne ya yi magana. Babu wanda ya sake yi mata magana har wani ya shigo falon da girmamawa. Dad ya kalle shi ya ce, "gata nan, ku je tare." Mum ta mi?e tsaye ta ce, "nima zan je."

Dad ya ce, "me zaki je ki yi?."
"Ina so nayi magana dashi ne."
"Akan me?."
"Ni dai ina so naje nayi magana dashi." Dad ya mi?e shima ya ce, "mu je tare gabaWaga." Mum shiga ciki kawai tayi ta Wauko mayafi suka shiga bayan wata mota, ita kuma Didi suka ce ta shiga motar Escort Win Dad. Didi a motar ta yiwa Bashir text ta faWa masa.

Tafiya suka yi mai Wan nisa kafin su ?araso wani babban waje aka yi parking da motar suka fito suka shiga. A wani babban waje suka zauna Didi dai tana tsaye bata iya zama ba buri take ta ga Omar. Kallon inda aka buWe ?ofa tayi ta ga Omar Winta ya shigo cikin yanayi mara daWin gani.

Kayan jikinsa gabadaya sun canja kala fuskarsa ta cika da gashi haka kansa ya taru da gashi, da ganin yadda yake tafiya ka san ya wahala ko yana kan wahala, idanunsa sai lumshewa suke yi saboda wahalar da take Wawainiya da gangar jikisa. Kai kana ganin sa ka san bayan wahala ma akwai yunwa a tare dashi, ya canja gabaWaya kamar ba shi ba.

Kayan jikinsa sun yage kaWan musamman rigar jikinsa, ana iya hango fatar jikinsa da ta koma wata kala ga shatin ciwo da alama dai duka ake masa da bulalai bama bulala ba. Kuka Didi ta fashe dashi ta ?arasa inda yake ta ce, "Omar!." Jin muryar Didi sai ya Waga idanunsa da suka yi masa nauyi ya kalle ta, a iya laSSansa ta ga ya furta sunanta hakan ya saka ta rungume shi tana kuka sosai.

?agowa tayi tana kallon sa ganin yadda ya dake kamar ba dashi ne yake cikin wannan yanayi ba, fuskarsa har Wan washewa tayi saboda ganin rabin ransa. Muryarsa a Wan dashe kaWan ya ce, "Didi me ki ka zo yi nan? Kina lafiya? Babu abinda ya same ki?" Ya faWa yana kallon fuskarta.
"Omar haka ka koma?." Murmushin ?arfin hali ya yi mata ya lumshe ido ya buWe ya ce, "Ina lafiya kar ki damu. Waye ya kawo ki nan? Ina fatan ba ke kaWai ba ce ba ko?. Babu abinda yake damun ki?."

Mum ta mi?e tana hararar Omar bayan ta sauke facemask Win da ta saka a hanci ta ce, "bazan iya zama mai yawa tare dashi ba, gabaWaya dashi da wajan abin ?yama ne" ta faWa tana yatsine fuska tana kawar da kai. Ta kalli Dad ta ce, "Dear ka yi abinda ya kawo mu kawai." Kallon Omar Senator ya yi ya ce, "ga Yayarka nan tazo bada ha?uri dan a fitar da kai, ka faWa mata inda ka binne asirin da ka yiwa Narma ta je ta tona shi a karya, daga nan sai nayi tunani in zan iya yafe maka."

Kallon sa yake yi dan saboda shi ya dake kamar yana lafoya duk da abinda yake ji a jikinsa. Murmushin rainin hankali yayi ya ce, "?arka ai bata kai matsayin da zan yi mata asiri ba." Mum ta kalle shi ta ce, "ai ba jayayya aka zo yi da kai ba, ga Yayarka nan in baka karya asirin nan ba wallahi akanta komai zai ?are. Na lura itace weekneess point Winka, to wallahi duk azabtar da kai Win da ake yi ita sai mun ninka mata."

Didi ya kalla da yaji ta ri?e hannunsa alamun kar yace komai, yaga ta marairaice tana hawaye sai ya ce, "Didi baki ji abinda suke faWa ba ne? Ni wanne asiri na yiwa ?atsu? Har ta kai matsayin da zan yi mata asiri ne????? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?. Wallahi bata kai ba, irin ta dubu basu isa nayi musu asiri dan su soni ba. Sai dai in ?arsu ce tayi min asiri amma ba dai ni nayi mata ba."

Kulle ido tayi ta buWe jin ya riga dai ya faWi abinda bata so ya faWa Win ta kalli Sen ta ce, "Kuyi ha?uri don Allah, tun farko na faWa daman babu abinda ya yi mata, amma tunda kun dage a kan hakan zan koma duk yadda zan yi zan yi wajan an karya asirin."

"Didi ban san ki da ?arya ba, dan kare ni kar ki faWi abinda bazai faru ba. Babu asirin da na yi musu balle a karya shi. Ba ?arsu ba, ko su Win ne da kansu basu isa nayi musu asiri ba wallahi, zuciyar Omar ta wuce wannan mataki, babu wata halitta da zan iya yiwa asiri a duniya. ?arsu Win banza da wofi, wacce ita da har ni Omar zan yi mata asiri?."

Mum ta fusata sosai ta kalli Dad ta ce, "ka ga rainin da ka jawo mana, anya escort Win na suna akin su kuwa? Tunda har yake tsaye akan ?afarsa wallahi bai sha wahala ba" ta juyo ta kalli Didi ta ce, "kince yana jin maganar ki gashi kema ya nuna mana jahilcin nasa bai bar ki ba. Ki ja masa kunne a tabbatar an karya asirin nan in ba haka ba wallahi zaku yi dana sani gabaWayan ku."

Didi zata yi magana Omar ya rigata ya ce, "Jahili shine wanda bai san abinda yake yi ba, ni na san abinda nake yi kuma ban yi dana sanin zuwa gidan ku a matsayin mai neman auren ?arku ba. Ina alfahari da hakan ko babu komai zan shiga cikin tarihin rayuwarku, har abada baza ku manta da mai suna Omar yazo har falo ya ce yana son ?arku ba. Jahilin da ku ka raina shine soyayyarsa ta hargitsa ?arku har kuke tunanin an yi mata asiri. ?arfin tasirin Omar kenan ku ka gani, ?ar da kuke ji da ita zuciyarta ta gama narkewa a soyayyar wanda ku ka raina ku ke kallon sa ?as?antacce. Sai dai a yanzu ta makara, lokacinta ya wuce, domin in Omar ya yi gaba baya juyawa baya, Omar in ya tsallaka baya sake tsallakowa, Omar in ya tafi baya dawowa. Ku bata ha?uri, ba wai na ?ita bane kawai akwai abinda ya fita mahimmaci a gabana yanzu. Ku yi mata addu'a Allah ya bata ikon jure rashina. Na san zaku sha matu?ar wahala kafin ta jure, dan nima tasha wahala kafin na fara ko da Waukar kiran wayarta."

Sen ya fusata da jin kalaman Omar, ransa ya Saci sosai ya ce, "?arya ka ke yi, ?ata ta wuce ta fara soyayya da irin ka wallahi, sai dai aikin asiri. Kuma wallahi ka yi gaggawar sanar da ?ar uwarka inda ka Soye asirin, in ba haka ba kana gab da aikata aikin dana sani." Zai yi magana Didi ta riga shi ta ce, "Ku yi ha?uri don Allah, ku bani shi mu tafi zamu tattauna dashi zan yi iya ?o?arina wajan ganin an karya asirin."

Omar ya kalle ta da mamaki ya ce, "ki daina faWar wannan maganar fa, babu abinda na aikata kin sani. Ita tazo har gida ta zube a gabanki tana ro?onki ki saka na sota, na ji tausayinta saboda raunin da take tare dashi har naji a raina zan iya taimaka mata na saurarenta..." ya faWa yana kallon su Mum da suke kallon sa.

Ya sake kallon Didi ya ce, "Dan na taimaka mata na bata aron kaWan daga cikin lokacina sai ya zama nayi mata asiri?. Didi kar ki damu dani, ai ba yau na fara shan wahala ba, ba yau aka fara dukana ba. Wannan kaWan ne ba mai yawa ba, kar ki da wannan komai zai wuce. Amma na ?ara ilimi, na kuma ?ara sanin meye duniya, na kuma gasgata zancen da ki ke yawan faWa min a kullum. Ko a nan zan gama rayuwata zan tabbatar miki da Omar Win da kika sani a baya yana nan, hatta shi Senator bazai manta da Tiger yana da rai ba."

Mum ta kalli Senator cikin Sacin rai bata sake cewa komai ba ta fice shima bai yi magana ba ya fita. Omar ya yi murmushi dan so yake ya cusa musu haushi a zuciyarsu kuma ya yi, ya kalli Didi ya ce, "kar ki damu, babu abinda zai same ni zan kuma fito na dawo na zauna tare dake in sha Allah. Ki je kawai."

"Wahalar da kai suke yi ko Omar? Naga nan bai yi kama da gidan yari ba, Ina ne nan?."
"Ai daman ba prison suka kai ni ba, wani gida suka fara kaini kafin su kawo ni nan. Duk ?arfin mulkin da suke ji dashi basu isa su kaini prison ba tare da laifi ba, in nayi laifin ma sai dai kotu ta tura ni prison ba dai su ba. Amma zasu iya yi min sharri in suka ga dama, ban san meyasa basu aikata ba har yanzu. Ki kwantar da hankalinki Omar Winki zai dawo." Hawaye ya share mata da hannayensa da suka yi duhu ga farce ya taru.

Didi kuka take yi sosai ta ce, "Duk yadda zanyi dan ganin na kuSutar da kai zan yi Omar."
"Kar ki wahalar da kan ki Didi, ki kwantar da hankalin ki. Tare da wa ku ka zo?."
"Bashir da Tukur, Hajja ce ta bada mota aka kawo mu. Omar murmushin ?arfin hali ya yi ya ce, "shikenan ki je kawai." Didi ta ce, "Bana so na barka a nan Omar." ?arfin hali yake yi kawai yana yi mata magana saboda kar ya sakata a damuwa. Da?yar ya ce, "Ki je Didi." Fita tayi tana kallon sa shima a lokacin suka koma ta inda suka fito.

Didi da ta fito bata ga motar da suka zo ba hankalinta ya tashi gashi bata san gari ba, ta fito bakin titi ga taxi nan tana yawo amma bata san Ina zata ce zata je ba. Allah ya taimake ta da waya a tare da ita ta kira Bashir ta faWa masa, ta tura masa location ta whatsapp yadda zasu fi ganewa. Da yake driver Hajja ya san Abuja ba jimawa ya ?araso suka Wauki Didi zuwa inda suka sauka.
KRB2P005
Arewabooks@nanahaleema11.

Didi bata Soyewa su Bashir abinda ake ciki ba ta faWa musu yadda suka yi dasu, gabaWaya ta canja yanayin damuwa ta sake mamaye ta ba kamar in ta tuna halin da ta ga ?anin nata sai zuciyarta karye ta fashe da kukan tausayinsa. Washe gari da wuri suka Wauki hanyar Kano, da suka shiga cikin gari kai tsaye gidan Hajja suka shiga suka same ta a zaune da hijjabi ga kuma babban mutum a kan carpet a zaune yana gaisheta da matu?ar girmamawa.

A sanyaye Didi ta shiga falon Hajja ta bita da kallo haka Salma ma da take zaune. Abiy ya kalli wacce ta shigo, Didi ganin Abiy a zaune sai Didi ta gaishe shi a sanyaye ya amsa Hajja ta ce,  Aisha ce, Aisha ma?ociyarmu, Yayar Omar. Nan da nan fuskar Abiy ta washe zuwa fara a ya ce,  Allah sarki, na gane ta yanzu. Ina Omar Win? Yana nan lafiya?.

Hajja ta ce,  ba lafiya ba gaskiya, wata matsala ce ta saka har aka kama Omar Win a Abuja. Abiy ya ce,  Subahanallah! A Abuja kuma aka kama shi?. Hajja ta ce,  ?warai kuwa, hanyar da za a fito dashi ma muke so saboda bashi da laifin komai aka kama shi. Abiy ya girgiza kai zai yi magana aka kira shi a waya ya kalli wayar ganin kiran mai mahimmaci ne sai ya kalli Hajja ya ce,  Hajja zan koma ana kirana, Amma zan saka a bincika maganar Omar Win in sha Allah.

Hajja ta ce,  Allah ya yi albarka, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi. Da amin ya amsa ya ajjiye mata kuWi kamar ko yaushe, ya bawa Salma da Didi kafin ya tashi ya fita.

Kawai sai Didi ta fashe da kuka mai sauti Hajja ta ri?ota ta ce,  Don Allah ki bar kuka ki huta tukunna sai mu yi magana. Jikinki ma ya yi zafi sosai Aisha da alama zazzaSi yana damunki. Salma ta ce,  Da gajiya ma a zazzaSin da yake damunta Hajja, ta yi wanka ta sha magani ta kwanta zata ji daWi. Hajja ta ce,  kin ji abinda likita ta ce, don Allah ki yi shiru ki daina wannan kukan. Ba ki ji mahaifin Nayla ya ce zai san abinda zai yi ba? Na san zai yi, kuma da?yar in bai san shi Sanata Win ba.

 Hajja bazai amince ba, baza su bar Omar ba Hajja. Sun ce ya yiwa ?arsu asiri shiyasa take sonsa har ta fita daga hayyacinta. Wallahi Hajja Omar bai nata komai ba, har gida tazo tana yi min kuka na saka Omar ya sota. Kuskuren Omar da ya bari ya fara sonta, kuskuren Omaar da ya je ne gidan Sen. Hajja kin ga yadda suka mayar min da Omaar? Kin ga yadda ya koma Hajja& .? Ta faWa tana jan kalmar ?arshe tana kuka sosai.

Hajja ta ce,  ki yi ha?uri komai zai wuce in sha Allah, ki daina tayar da hankalin ki kin ji. Didi ta ce,  shi yake jawowa kan shi Hajja, a gaban su a jiya baki ji irin maganar da ya dinga yi ba, sam Omar baya ri?e maraicinsa, baya tuna matsayin da yake dashi. Na rasa wanne rashin tsoro ne haka da Omar bashi dashi, lamarinsa yana bani tsoro sosai. Kina ganinsa Hajja kin san yana cikin azaba, amma ya dake yana faWa musu maganganu masu ciwo. Hajja ta ce,  ni maganar ce bana so ki yi, ki je ki yi wanka ki huta kin ji?. Ba dan ta so ba Hajja ta saka ta shan tea sannan tayi wanka ta sha magani ta kwanta ba dan tana jin bacci ba. Haka Didi ta kwana da zazzaSi mai zafin gaske, sai da Salma ta yi mata allura sannan ta iya bacci a safiyar ranar jum a.

Nayla ta shigo garin Kano a ranar ana gab da shiga masallaci domin yin sallar juma a, gidan su na Kano wanda su Abiy suka sauka ta wuce ta ajjiye kayanta tayi wanka ko hutawa bata yi ba ta fito falo. Da Mama ta haWu ita da Jidda a zaune ta kalli Mama ta ce,  Mama zan je gidan Hajja sai zuwa dare zan dawo tunda event Win yau sai dare. Mama ta ce,  Baki huta ba fa Nayla, zuwan ki kenan kuma ki tafi gidan Hajja?.
 Bana so lokacin masallaci ya yi a rufe hanya ban tafi bane shiyasa.
 Baza ki yi makeup Win ba?.
 Bazan yi ba gaskiya. Twiny ta ce,  bara nazo na raka ki gidan Hajjan.

A motar Twiny suka tafi gidan Hajja lokacin ana ta sallah a masallaci. Bata Wauka zata tarar da Hajja ba dan tasan zuwa sallah duk sati da ita ake yi a masallaci, amma sai ta tarar tana nan ta tasa Didi a gaba tana ta rarrashinta. Shigar su falon ya saka Salma ta ce,  A a Nayla, saukar yaushe?. Duk sai suka kalle ta har Hajja, Hajja ta bita da kallo ganin ta yi wani iri itama kamar ba ita ba.

Fuskar Hajja ta washe ganin jikarta ta da kuma ?ar uwarta. Ta ce,  Hauwa u da Jidda, sannan ku da zuwa. Twiny tayi dariya ta ce,  Hajiya Hajja, barka da rana. Hajja ta amsa fuska a sake tana tambayarta Maman ta Jidda ta amsa da kowa yana lafiya. Da Didi suka gaisa ganin bata da lafiya sai tayi mata sannu. Didi ta kalli Nayla ta ce,  ?anwata Nayla ya kika tsaya?.

Nayla ta ce,  Hajja Didi bata da lafiya haka shine ba a faWa min ba?. Hajja ta ce,  kema ai baki da lafiyar, kalli yadda ki ka koma. Share batun Hajja tayi ta dawo kusa da Didi ta ce,  Didi sannu, me ya same ki haka?. Didi tayi murmushi ta ce,  ZazzaSi ne kawai Nayla, bayan shi babu komai.
 Sannu Didi, Allah ya baki lafiya. GabaWaya kin rame.
 Amin Nayla. Kema kin rame, na faWa miki ki daina cewa zaki rage ?iba, baki fa ?ibar kirki ki ce zaki rage? wallahi kin fi kyau da jikinki. Nayla tayi ajiyar zuciya kafin ta kalli Hajja da take kallon ta sai tayi murmushi ta ce, Hajiya Hajjata, na yi kewarki.

Hajja ta ce,  nima nayi kewarki Nayla. Amma me yake damunki haka?. Nayla ta ce,  Hajja na fara aiki fa, in na fita tun safe sai yamma nake dawowa, kin san ba wani abincin kirki na iya ci a waje ba shiyasa na koma haka. Hajja ta tace,  Mahaifinki ya faWa min ai zancen aurenki ake yi, yanzu haka ya baki lokaci ki fitar da gwani. Ni na san a cikin gwanayen naki babu Abbas ko?. Gabanta ya faWi sosai ta kalli Hajja bayan ta Soye damuwarta ta ce,  Hajja ni na barwa Allah zaSi, duk wanda ya zaSa min shine daidai da rayuwata. In Yaya Abbas ne Ina maraba dashi.

Hajja ta ce,  Gaskiya ne. Allah ya zaSa abinda yafi alkhairi. Ni daman so nake ki yi auren ai, an gama karatu aikin me za a tsaya yi? Me kika nema kika rasa?. Nayla tayi murmushi kawai kafin ta kalli Didi da take kallon ta. Didi ta ce,  Ashe ?anwar tawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login