Showing 27001 words to 30000 words out of 85380 words

Chapter 10 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3845

masa ya kuma ce in sha Allah na Wauka ya daina Win. Yanzu da ya dawo maganar yana so ya buWe shago na aikin takalmi yake min, har ya bada kudin siyan injin aikin takalmi."

Hajja tayi murmushi ta ce, "Alhamdu lillah! Wannan labari ne mai daWin gaske Aysha. Fahimtar kuskure sa da ya yi har yake so ya gyara babbar riba ce a rayuwarsa. Kin ga abinda nake faWa miki ko? Na kan ce miki Omar da?yar in ba mace ce zata yi silar nutsuwarsa ba, sai gashi ta dalilin mace abubuwa zasu canja."

Didi ta ce, "kuma na fahimci a gidan su Narma ne aka faWa masa maganar da yake ji a zuciyarsa zai canja, ya Wan faWa min wasu daga ciki kaWan amma bai faWa min duka ba, na kuma lura maganar tana damunsa a zuciyarsa."

Hajja ta ce, "kiran rabo da kiran canjin ?addararsa ne ya saka shi amsawa Narma. Kar ki yi mamaki in aka ce Allah ya shigo da Narma rayuwarsa ne kawai dan ya je gidan su a faWa masa maganar da zata farkar dashi daga dogon baccin da yake yi, kar yi mamaki in aka ce Allah ya yi haka ne kawai saboda Omaar ya nutsu ya zama mutum kamar kowa. Wata?ila amfanin Narma kenan a rayuwarsa, ta shigo rayuwarsa ta zama silar da ya je inda aka faWa masa abinda ya saka yake ji a zuciyarsa zai canja, ya amsa kiran rabonsa ta dalilinta, wata?ila ta fita kenan bazata sake dawowa ba har abada. Wata?ila kuma zata dawo nan gaba ta kasance matsayin matarsa. Ikon Allah ai girma gare shi, sai abu ya faru zaka tabbatar da in Allah ya yi nufin shiriya a lokaci Waya komai zai faru ayi a gama. Kai dai ka kasance cikin addu'a ko yaushe, duk ?an?antar addu'a bata faWuwa a ?asa wallahi."

Didi tana murmushi ta ce, "haka ne wallahi Hajja, Omar ya amsa kiran rabonsa ta silar Narma." Hajja ta ce, "wata?ila matarsa tana gefe zata shigo rayuwarsa ta wata fuskar, wata?ila kuma Narma Win ce matarsa, duk abinda iyayenta zasu yi sai dai su yi su gama amma sai ta aure shi. Allah ai ba abin wasa ba ne ba, in Allah ya rubuta babu wanda ya isa ya canja, In kuwa kaga ya canja to daman haka abin yake a cikin ?addararsa." Didi ta ce, "Wallahi Hajja na yi farin ciki, daWi nake ji sosai zuciyata wallahi."

Hajja ta dafata ta ce, "zaki fi kowa jin daWin canjin Omar a yanzu, ke kaWai ce uwa, uba, yaya, ?awa, ?anwa a gare shi. Allah ya baki lada Aisha, ya ji?an iyayen ku, ya Worar da zumunci da ?aunar da ku ke yiwa junan ku har aljanna."
"Amin Hajja. Amma yarinyar nan Narma tana bani tausayi, yanzu ta kira ni tana kuka kina ji kin san ba ?aramin so take yiwa Omaar ba. Abin har mamaki yake bani, ta rasa wanda zata yiwa wannan soyayyar mai zafi sai Omar, dole iyayenta su ce asiri ya yi mata."

Hajja ta yi dariya kaWan ta ce, "ita Narma ?addararta kenan soyayyar Omar, in Allah ya rubuta matarsa ce kamar yadda na faWa miki iyayenta basu isa su hana ba, duk matsayin da take dashi zasu manta su bashi aurenta. In kuma ba matarsa bace Allah zai sassauta mata abinda take ji tayi aure ta huta. Babu mamaki a cikin ikon Allah Aisha, bayan Narma sai ki ga Allah ya sake kawo wata da zata sake haukacewa akan soyayyarsa. Komai yana da sila, hatta mutuwa tana da sila, shi Omar silar soyayyar da Narma take masa ne ya saka ya amsa mata har yaje gidan su, ashe zuwa gidan na su shine silar canjawasa."

Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Allah ya sa mu dace, Allah ya tabbatar dashi akan tafarkin halak."
"Amin Aisha." Didi ta kalli Salma da take ta murmushi ta ce, "Salma zaki raka mu Kaduna jibi in sha Allah, zamu je mu yiwa Abiy godiya har cikin gida." Salma ta ce, "gidan su Nayla?" Ta faWa tana wara idanu. Didi ta ce, "can zamu je, amma kar ki faWa mata Ina so mu bata mamaki. Ki dai san yadda zaki yi ki tabbatar da Abiy yana nan zamu je a ranar mu dawo."

Salma ta yi dariya ta ce, "in sha Allah. Allah ya kaimu." Ta amsa da? amin Hajja ta ce, "Allah ya kaimu."
"Amin Hajja. Me ki ka san yana so da zamu siya daga nan mu kai masa?." Hajja ya ce, "kar ki takura kan ki Aisha, iya zuwan da zaki yi ya wadatar." Didi ta ce, "A'a Hajja, ai ya wuce na je gidan haka babu tsarabar Kano. Me zan tafi dashi?."

Salma ta ce, "yana son gurasar Kano, musamman ta gidan gurasa na nan baya, zaki iya yi masa ita kaWai ta isa. Dan indai Nayla tazo Hajja tana bayarwa a kai masa. Didi ta ce, "na gode Salma, zan saka a yi sabuwa wacce zamu karSa da safe sai mu tafi." Hajja ta ce, "Allah ya kaimu, sai ku je Sayyadi ya kai ku." Didi ta ce, "To Hajja, na gode Allah ya ?ara girma." Suka amsa da amin kafin ta ce, "Hajja sai magana ta gaba."

Hajja ta ce, "ina jinki." Didi ta ce, "magana ce akan kayan Waki da za a siya, Baba Adamu ya kira ni ya tabbatar min da shi ne zai yi komai na aurena, hatta cokali baya so na siya shi ne zai siya da kansa. Kawai abinda yake so na bashi makullin gidan zai zuba duk abinda ya kamata ace an zuba."

Hajja da fara'a ta ce, "kai amma ya kyauta, Allah ya bar zumunci." Didi ta ce, "amin Hajja. Babbar matsalar itace Omar, in yaji Baba Adamu ne zai yi komai wallahi bazai bari ba, in kuwa ya ha?ura ya bari to sai raina na dana Baba Adamu ya Saci. Yanzun nan kafin na fito maganar kayan yake min sai na ce masa zamu yi magana, na rasa ta yadda zan faWa masa sa?on Baba Adamu shima kuma Baban baya so Omar ya sani saboda tijarar Omaar. Ya dinga faWa kenan yana cewa an faWa musu bashi da kuWin da zai yi min komai ne, kai lefe ma da nace an kai gidan kawu ya yi min shiru ne amma zai nuna min yaji haushi nan gaba."

Hajja tayi dariya ta ce, "Omar kenan, Omar mazan fama, Omar carbin ?wai, ya ci sunan nasa damisa kamar yadda ake faWa masa." Didi ta ce, "wallahi na rasa abinda zan yi, ga makullin ya aiko min dashi amma na masa faWawa Omar saboda sa?on Baba. Shiyasa nazo na same ki don Allah ki kira shi ki ce masa kece kika Wauki nauyin abinda Baba zai yi, yana ganin girmanki sosai, ke kaWai ce kaf duniya zan ce kin yi bazai musa ba, duk da zai yi magana amma ?arama ce shikenan ya wuce. In na ce Baba Adamu ne ranar sai kowa ji kan mu dashi."

Hajja ta ce, "shikenan kin kawo dabara. Ki bawa kawun na ki makullin ni ki turo min shi in anjima. Kar ki damu ai an wuce wannan matsalar." Didi tayi murmushi ta ce, "Na gode Hajja. Kin kasancewa uwa a gare ni kuma kakata, bani da mai share min hawaye a duniya sai ke Win kawai. Allah ya shirya miki zuri'arki gaba da baya." Hajja ta yi murmushi ta ce, "Amin. Aisha ai an zama Waya kar ki damu." Didi tana ta murmushi suka Wan cigaba da hira kafin ta tashi ta koma gida.

Washe gari da safe take sanar masa da Hajja na son ganinsa, ya Wan yi jimm yana kallon ta kafin ya ce, "lafiya take son ganina?." Didi ta ce, "Omar
ya za a yi na sani? Ta ce min kawai na ce kaje." Ya Wan Wauke ido daga kallon ta ya ce, "to in na fita yanzu zan shiga." Bata sake kula shi ba kar tayi magana ya gano sai tayi shiru ta cigaba da aikin ta.

Kamar yadda ya ce da ya fita kam gidan Hajjan ya shiga da sallama, mai aikin Hajja ta amsa ta ce ya shiga ciki Hajjan tana ciki. Hajja ita kaWai a zaune tana lazumi, ta amsa sallamar ya zauna sai ta ajjiye carbin suka gaisa ta ce, "Ummaru daman na ce kazo ne akan batun kayan Wakin Aisha na aure. Na karSi makullin gidan da Aisha zata zauna a hannunta, ni nake so nayi mata komai na Waki a matsayina na uwa a gare ku. Shiyasa na ce ta turo min kai na faWa maka da kaina kar ka ji hakan a bakin ta bai maka daWi ba."

"Ina kallon ku matsayin jikokina ne, Aisha ta Wauke ni kamar uwa tana faWa min duk damuwarta. Ana zaman mutunci da amana shiyasa zan sauke ha??in da yake kaina matsayin uwa a gare ta. Ina fatan hakan bazai Sata maka rai ba." Shiru ya yi bai amsa ba Hajja ta ce, "Ummaru baka ce komai ba." Ya kalle ta ya ce, "babu abinda zan ce, tunda an yanke hukunci shikenan." Hajja tayi dariya kaWan ta ce, "an yanke kam, sanar da kai yanzu ma nayi ba neman shawara ba."

"Shikenan, an gode Allah ya saka da alkhari" ya furta a kasalance dan bai ji daWi ba. Hajja tana lura da yanayinsa tana girmama ?arfin hali irin na Omar, da gaskiyar Aisha da ta faWa masa asalin su waye suka yi da babu zaman lafiya.

Sallama ya yi mata ya fita ya koma wajan Didi ya shiga har cikin Wakinta ya samu tana mopping a lokacin. Kallon sama da ?asa ya yi ya ce, "Daman abinda aka tsara kenan shiyasa baki faWa min dalilin kiran ba?." Didi ta ce, "Shiyasa na ce ta faWa maka da kanta."
"Ai wallahi tunda naga kin kasa kallona kafin na fita na san akwai munafurcin da kika haWa, da farko nayi tunanin akan waWancan makiran ne ashe sabuwar gulma ki ka samo hanyar ?ullawa." Didi tana jinsa bata ce komai ba sai ma dariya da yake so ya bata.

Omar ya fusata ya ce, "Ni fa bana son shishshigi a cikin lamarin rayuwata, an ce mata bani da kuWi da zan iya yi miki ne da za a yi miki a waje?. Ba dangin iya babu na baba a ce itace tayi miki kayan Wakin auren ki haka daidai ne?. Salon nan gaba azo na yi min gori ace kayan Wakin Yayata ma ma?ota ne suka yi mata saboda na gaza?."

Didi ta kalle shi ta ce, "Omar kyautatawa ce fa ba wani abu ba." A fusace ya ce, "Allah ya tsinewa kyautatawar!." Didi ta yi shiru jin abinda ya ce. A kausashe ya ce, "in kyautatawar ce a yi ta wani Sangare mana lallai sai ta kayan Waki? Yanzu kaf unguwar nan sai a san itace tayi ko dan a faWa, ni kuma a cigaba da yi min kallon mara amfani tunda ni Allah ya Worawa yi miki ba wasu a waje ba."

Shiru tayi masa bata tanka ba kar ta tanka ta sake tsokano shi, ta san halin kayanta tsaf shiyasa take gujewa abinda zata sake tunzura shi. Shirun da tayi ma bai saka ya yi shiru ba ya ce, "wai komai na kayan Waki ita zata yi ko a matsayin ta na wa oho?. Nuna min ake yi ni bani da kuWin da zan yi kenan? ko ke kika ce mata bani da kuWin da zan yi miki ita tayi miki?."

Didi a sanyaye ta ce, "ni bamu yi haka da ita ba, abinda ta faWa maka shi ta faWa min." Omar ya yi ?aramin tsaki yana binta da harara ya ce, "To meyasa baki ce mata zan miki ba? Meyasa kika amince har ki ka ce ta faWa min da kanta?. Kenan kina tunanin bazan iya ba ko?." Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Nidai ban ce ba."

"Mtsw! Na rantse da Allah ba dan Ina ganin girmanta baza'a karSi kayan nan ba, to babu yadda zan yi mata ne amma da sai ta bar kayanta ai ba ro?a muka yi ba." Shiru Didi ta sake yi masa ta cigaba da aikin ta bata ce komai ba ya sake yin tsaki ya ce, "Abin haushi." Ita dai bata ce masa komai ba tana mamaki hali irin na Omar a zuciyarta, tabbas da ace ya san Baba Adamu ne ya yi ba Hajja ba da sai an yi ya?in duniya na uku saboda bala'i da masifar da zai dinga zazzagawa kowa.

Juyawa ya yi ya fita ta bishi da kallo ta ce, "Na kuSuta. Alhaji Omar manya, Allah ya shirya ka ya taimake ka a rayuwarka" ta faWa tana cigaba da aikinta tana dariya da tunanin irin kalar tizajarar da zai yi mata in ya san asalin su waye zasu yi kayan Wakin.

Haka ya wuni rai a Sace, ko kula ta ma bai yi saboda baya son maganar, gani yake kamar an raina masa hankali ne da za a ce wata a waje ce zata yi kayan Wakin yayarsa ba shi ba. Ita kuma tana sane ta share shi, tana yin magana zai sake yin sama ?arshe ma ya ce zai je ya samu hajja ya ce gaskiya bai yarda ba shiyasa ta yi masa banza.

Washe gari ?arfe bawai na safe ta buga masa ?ofa, da yake bacci yake yi a lokacin sai ya taso yana cewa, "Didi kin san ?ofar a buWe take amma sai ki ta buga min ?ofa kin san na tsani a buga min ?ofa amma sai kin yi, lafiya?." Didi ta ce, "na san a buWe take ai, shigowa ne bazan yi ba. Ka tashi ka yi wanka ?arfe takwas zamu wuce." Ya kalle ta ya ce, "Zuwa Ina?." Harararsa ta yi ta ce, "ban sani ba, ka koma ka kwanta in ka manta" ta faWa tana wucewa ta ?yale shi. ?aramin tsaki ya yi, dan kawai ya san mahimmacin alkhairi ne da bazai je ba wallahi.

Wanka ya yi ya shirya cikin ?ananun kaya a lokacin Didi ta fito daga falo shi kuma ya fito ta kalle shi ta ce, "Omar don girman Allah ka koma ka saka manyan kaya, ba dan ni ba, don Allah ka saka manyan kaya har hula ka saka." Bata barshi yayi magana ba ta dinga magiya dole ya koma tunda ba son magiya yake yi ba, ba jimawa ya dawo da shadda kalar blue mai haske har hula ya saka kamar yadda ta ce.

Murmushi tayi tana kallon sa ta ce, "Ko kai fa. Ka? ci abinci sai mu wuce." Shayi kawai ya sha aka kawowa Didi sa?on gurasar da ta bayar ayi, duk yana kallo ta juye a babban bokitin roba sabo dal da ta siya. Kallon sa ta yi ta ce, "ranka ya daWe in in ka gama sai mu tafi ko?."
"Ki jira na je na samo mai motar da zai kai mu ko?."

"Ai da driver Hajja zamu tafi." A kaikaice ya kalle ta ya ce, "Hajja dai?." Didi ta ce, "eh Omar, ita tace zata saka ya kaimu bazan ce mata a'a ba."
"Daman ai komai baza ki iya ce mata a'a ba tunda ga wacce ta haife ki, wallahi da na san haka ne bazan je ba."
"Shiyasa ban faWa maka ba, mu je" ta faWa tana fita ta bar shi kar tayi wani abun ya ce ya fasa.

Ransa a Sace ya fito zuwa ?ofar gidan ya kulle gidan ya tarar da driver Hajja ya fito da motar ga Salma a tsaye a jikin motar da alama tare zasu je. ?aramin tsaki ya yi lokacin su Bashir suka zo wajan ya tsaya yana yi musu magana, Didi ta shiga motar shima bai jima ba ya ?araso ya shiga gaba su kuma daman baya suka shiga, motar ya yiwa key bayan sun gaisa da Omar da Didi suka Wauki hanyar Kaduna ransa duk a Sace.
KRB2P0011
Arewabooks@nanahaleema11.

Sha Waya da mintina na safe suka shiga Kaduna, da yake gidan su Nayla ba ba?o bane a wajan driver Hajja ba Sata lokaci suka isa har ?kofar gidan ya tsaya yana danna horn. Didi kallon gidan ta ke yi tana girgiza kai, domin gidan yana da matu?ar girma da kyau. Duk da bashi da ?yale-?yale daga waje amma kana gani ka san gidan babban mutum ne ba gidan yaro matashi ba. Ko iya masu gadin da suke zaune a gate Win sun kai su biyar ko wanne da uniform kalar blue a jikinsa.

Ganin driver Hajja ya saka aka buWe musu gate na farko a nan suka ajjiye motar. Bayan ya faka Salma ta ce, "Mu je ciki" ta faWa tana fitowa tana Wan jijjiga hannunta dan ta gaji da zaman. Omar dai bai fito ba yana zaune Didi ta kalle shi ta ce, "ka fito mana." Ya kalle ta ya ce, "Sai na shiga gidan mutane babu izini? Ku je dai." Didi ta saki baki tana kallon sa ta ce, "ikon Allah! Sabon salo."

Salma tayi dariya ta ce, "Didi mu je zai shigo daga baya." Didi tabi bayan Salma suka sake shiga wani gate Win a nan wani mahaukacin parking space yake mai bala'in girma wanda aka tanadi rumfuna daga can gefe na ajjiye mota.

Didi kallon gidan take tana girmama girmansa da kuma ?arfin kirki irin na Nayla. Wanda ya fito daga wannan gida ba kowa ne zai yi mutunci har ya kalli na ?asa dashi ba. Ciki suke shiga Didi ta ga sai tafiya suke yi kafin a buWe wata babbar ?ofa su shiga sai gasu a wani babban falo mai bala'in kyau.

Babu kowa a falon sai mai aiki tana kunna turaren wuta Salma ta kalle ta ta ce, "Ina Mama da Nayla?." Ta ce, "Mama tana ciki, Nayla kuma tana sama bata sakko ba gabaWaya." Mama ce ta fito tana cewa, "waye yake nema na?." Ganin Salma sai tayi murmushi ta ce, "A'a Salma, ke ce tafe?." Salma tayi dariya ta ce, "Ni ce Mama." Zama suka yi har Didi suka gaisa da fara'a kamar ta san Didi kafin Salma ta ce, "Didi ce Mama, na san kina jin labarinta a bakin Nayla." Sai Mama ta sake yin dariya ta ce, "?warai kuwa in jin labarin Didi ma?ociyar Hajja ko?."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login