Showing 30001 words to 33000 words out of 85380 words

Chapter 11 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3849

Salma ta amsa ta ce, "itace. Ta zo wajan Abiy ne."

Mama ta ce, "ai kuwa yana falon sa kuma fita zai yi, maza jeki ki rakata dan na ji yana cewa cikin Zaria zai shiga, kuma ya kai yamma ko dare bai dawo ba." Salma ta mi?e tana cewa, "Nayla fa?." Mama ta ce, "tana sama yau ko sakkowa ma bata yi ba, bata jin daWi shiyasa ko aiki bata je ba. Jeki zan tasota sai tazo ta same ki." Tare suka fita da Didi da Salma. A harabar gidan wani Sangaren daban suka shiga, Salma ta buWe ?ofar da ta san nan ne falon Abiy na waje.

Ai kuwa yana zaune shi kaWai da alama ya gama cin abinci suka shiga falon da sallama, Jawad ne ya fito daga kitchen Win falon da ruwa a hannunsa ya ajjiyewa Abiy a gaban sa. Abiy ya amsa sallamar sai ya murmusa ya ce, "A'a Salma, ke ce tafe?." Salma ta ?arasa ta zauna a kan carpet ta gaishe shi ya amsa yana tambayarta Hajja da Daddy ta ce duk suna lafiya lau. Da Didi suka gaisa lokaci Waya ya gane ta, Salma ta ce, "Abiy Didi ce." Abiy ya ce, "Aisha dai, Ai na gane ta." Didi tayi murmushi tana sunkuyar da kai.

Salma ta ce, "ta ce na rakota wajan ka shiyasa muka taho yau. Tare mu ke da Omar ?aninta ma yana waje a tsaye." Abiy ya ce, "yana waje a tsaye? Kun yi wannan doguwar tafiya a barshi a waje? Jawad jeka ku shigo tare." Jawad ya tashi ya fita ba jimawa suka dawo tare da Omar harda driver Hajja. Gaisawa suka yi da Drivern kafin ya tashi ya fita Omar ya gaishe da Abiy cikin yanayin sa na kadaran kadahan.

Abiy da murmushi yana kallon sa ya ce, "Lafiya lau Omar, ya hanya?."
"Alhamdu lillah" ya amsa a ta?aice dan jinsa yake a takure. Wani irin girma yake ji Abiy ya yi masa a jikinsa da zuciyarsa, shiyasa gabaWaya ya kasa sakewa ya kuma kasa haWa ido da Abiy.

Didi ta ce, "Abiy mun zo mu yi godiyar alkhairin da aka yi mana, Allah ya saka da alkhairi ya biya ka da aljanna. Babu abinda zamu saka maka dashi sai addu'a. Ga Omar ya dawo cikin alfarmarka, Allah ya sa a fi haka, Allah ya kare ka, Allah ya shirya maka zuri'arka, Allah ya ?ara maka lafiya da tsahon rai mai amfani." Abiy yana ta murmushi cikin jin daWin addu'arta ya ce, "Amin ya rabbi. Tun daga Kano har Kaduna ku ka taho?."

Didi ta ce, "ai ya zama dole ne, dole mu zo mu yi godiya."
"Har gida kin je kin yi min godiya a lokacin, sai da ku ka sake Wauko hanya ku ka zo?." Didi ta yi murmushi Abiy ya ce, "Babu komai ai yiwa kaine. Kuma kafin na taimaki Omar ai shi ya taimake ni, na rama alkhairi da alkhairi ne kawai."

Omar wani iri yake ji a jikinsa, ba saba yiwa mutane godiya ya yi ba balle ya san irin addu'ar da zai musu, duk sai ya rasa abinda zai ce yake jin bakin sa kamar an Waure tamau. Gashi yana ji a jikinsa ya kamata yayi magana amma ya rasa me zai ce. Zai yi magana kenan Nayla ta shigo falon ba tare da ta lura da Didi ko Omar ba, a shagwaSe ta shigo ta san Abiy yana nan dan kawai Mama ta ce mata Abiy na kiranta bata san su waye a ba.

"Abiy" ta faWa tana ?arasowa inda yake. Ya kalle ta ya ce, "Mamana kin tashi? Tun Wazu aka ce bacci ki ke yi, ya zazzaSin?" Ya faWa yana ri?o hannunta ya zaunar da ita kan kujera yana taSa wuyanta. Abiy ya ce, "har yanzu jikinki da zafi. Mamana baki da lafiya gaskiya yana da kyau ki ga likita, gabaWaya kin rame sai yawan ciwo a kai akai-akai. Zan yi magana da likitan da zaki gani ki je gobe ya duba ki a san abinda yake damunki. Jiya Maman ki ta ce min harda ciwon ?irji ko?." Kai ta Waga alamun eh har lokacin idanunta a lumshe yake kafin ya ce, "Jawad gobe zai kai ki wajan likita, na lura kece bakya son zuwa."

"Hajiya Nayla" Salma ta furta tana kallon ta. Da sauri ta buWe ido tana kallon mutanen da suke zaune a falon. Dam! Gabanta ya buga haWa ido da suka yi da Omar da yake zaune daga gefe ya Wago kenan suka haWa ido. Wara idanu tayi ta kalli Abiy ta sake kallon su Salma ta ce, "Salma, Didi?." Didi tayi murmushi ta ce, "Na'am Nayla." Sai kuwa tayi ihu ta tashi a guje ta koma kusa da Didi ta ce, "Didi yaushe ku ka zo? Shine ba a faWa min ba?. Wai ko mafarki nake yi ne?."

Didi ta ce, "ba mafarki ki ke yi ba Nayla, ni ce yau a Kaduna." Nayla ta ce, "ikon Allah. Kuma Mama bata faWa min ba fa, ta ce min kawai Abiy yana nemana, ashe ku ne kuka zo. Sannu da zuwa."
"Yauwa Nayla, ya jikin na ki?."
"Da sau?i" ta faWa tana sauke da ido ?asa farin ciki yana mamaye zuciya ta ganin masoyin ta a zaune a falon gidan su.

Abiy da yake kallon ta yana murmushi ya ce, "ki tashi ki je ki saka a haWa musu breakfast sun yi tafiya mai nisa." Mama ce ta shigo falon da sallama ta ?araso ta zauna suka sake gaisawa da Didi shi dai Omar bai iya kallon ta ba sun gaisa kawai dan in akwai abinda ya tsana bai wuce gaisuwa ba.

Abiy ya kalli Mama ya ce, "wannan shine wanda ya taSa taimakon Nayla a Kano shekarun baya....Kin tuna?." Mama ta ce, "Allah sarki na gane shi." Didi ta bawa Mama abinda ta taho musu dashi Abiy ya ce, "harda wahala? Ku da ku ka yi tafiya mai nisa har sai an yi tsaraba?." Didi murmushi ta ke yi ta ce, "Babu komai Abiy." Abiy ya ce, "mun gode sosai, Allah ya bar zumunci."

Didi ta amsa da amin tana murmushi, ta ji daWin yadda Abiy ya karSe su wallahi, ta kuma fuskanci gadon kirki Nayla tayi daga wajansa. Mama ta kalli Nayla da ta kwantar da kanta a kafaWar Didi tana kallon Omar ta gefen idanu ta ce, "Nayla ki je ki saka a haWa musu abinci su ci ko?." Nayla ta Wago a sanyaye ta ce, "To Mama." Abiy ya ce, "Mamana jikin ne?." Ta girgiza kai ta ce, "A'a Abiy, murnar ganin Didi ce kawai."
"To maza ki je a haWa musu abinci, sun yi doguwar tafiya."

Bata mi?e ba gani take in ta tafi bazata cigaba da kallon Omar ba, shi kam ko kallon inda take ma bai yi ba balle ya yi magana. Abiy ya ce, "amma dai sai gobe zaku koma?." Didi ta wara idanuta ce, "A'a, anjima kaWan zamu koma in sha Allah." Abiy ya ce, "Toh, ai na Wauka zaku kwana ku huta gajiya ai. Shikenan ni daga nan zance ya kiyaye hanya, zan shiga Zaria bazan dawo na zame ku ba gaskiya. Allah ya kiyaye hanya na gode da girmamawa." Omar ne ya buWe baki kamar mai koyan magana ya ce, "Amin. Mun gode sosai, Allah ya ?ara girma."

Lumshe ido Nayla tayi jin kalaman Omaar idanunta suna cika da hawaye saboda tsantsar bugawar da zuciyarta take yi. Salma na lura da ita haka Mama duk motsin ta akan idanunta take yi. Abiy ya ce, "amin Omar, Na gode sosai. Mamana ki raka su falo su huta." Nayla ta amsa ta mi?e ta ce, "Didi ku zo mu je" ta faWa a sanyaye. Didi ta mi?e Salma ma ta mi?e Abiy ya ce, "Omar ku je tare, Jawad raka shi zai fi sakewa." Jawad ya amsa yana mi?ewa shima suka shiga ciki.

?aramin falon ba?i aka shigar dasu mai kyau madaidaici. Nayla ta kunna a.c bayan ta kunna hasken falon ta fita daga falon ita da Salma. A kitchen Salma take ce mata, "Nayla don Allah ki nutsu, sai rawar jiki ki ke yi kina bayyana feeling Winki a fili." Sai kawai ta rungume Salma ta fashe da kuka tana cewa, "Salma Omar ne a gidan mu, Omar ne a zaune shaida Abina suna magana. Salma na kasa tantance adadin farin cikin da nake ji, ji nake kamar zuciyata zata buga saboda murna Salma. Omar Wina yana nan lafiya, Allah na gode maka, Allah na gode maka" ta faWa cikin kuka sosai.

Salma ta ce, "to ki yi ha?uri ki bar kuka mu kai musu abincin in ya so sai mu yi magana." Nayla ta Wago daga jikin Salma tana share hawaye ta ce, "Salma ki yi addu'a Allah kar ya Wora miki soyayya irin wacce ya Wora min, akwai azaba ba kaWan ba Salma. Na kasa yin lafiya cikin kwanakin nan kuma duk saboda tunaninsa." Tausayi ta bawa Salma matu?a, idon Salma ya kawo ruwa amma bata yi kuka ba ta daure ta yi mata shiru bata tanka mata ba.

A haka suka zuba abincin a flaks, doya ce da ?wai da sauce sai dankalin turawa soyayaye da kuma soyayyen ?wai. Ga farfesun naman rago da aka yi shi mai ruwa, sai shayi da manyan slice bread da gwangwanin madara da na milo da sugar.

A kan table suka ajjiye sannan Salma ta koma ta kawo ruwa da lemo masu shegen sanyi ta ajjiye. Didi ta kalli Nayla da take tsaye kana ganin ta ka san tayi kuka ta ce, "Nayla jikin ne?." Nayla ta kalli Didi ta ce, "A'a Didi, kaina ne yake ciwo shiyasa."
"Sannu, Allah ya ?ara lafiya. Ki je asibiti a duba ki." Kai kawai ta Waga dan ?irjinta ya yi mata mugun nauyi, ga Omar dai tana kallonsa amma kewarsa take ji kamar ta je ta rungume shi haka take ji.

Shi kuwa Omar yana jin su amma baya Wagowa waya yake dubawa ba tare da yana yin wani abun a wayar ba. Fitar Salma da Nayla ya saka Didi ta ce, "kai kuwa Omar ko sannu ai ka ce mata ko? Itace silar fitowar ka daga hannun Sen na faWa maka. Ko ya jiki ai ya kamata ka ce mata zata ji daWi." Shiru ya yi bai ce komai ba, gabaWaya a takure yake jin kansa cikin jin nauyi wanda bai san dalilin faWuwar hakan ba.
Salma da Nayla sun jima basu dawo ba har kusan mintina talatin kafin su dawo, Didi ce kawai ta sha tea amma shi ruwa kaWai ya sha bayan nan bai sake Waukar komai ba.

Nayla ta kalli Didi ta ce, "Didi har kin ci?." Didi ta ce, "na sha tea Nayla, in zan yi tafiya bana son cin abinci wallahi." Nayla tayi murmushi tana satar kallon Omar da ya ajjiye ruwan da ya sha a lokacin.
"Yaushe zaki zo mana Kano?." Nayla ta kalli Didi ta ce, "ai sai bikinki, aiki ya saka ni a gaba ya hana ni zuwa ko ina. Ni dana sanin ma fara aikin nake yi wallahi."

Didi tayi dariya ta ce, "Allah ya kaimu, ya taimaka miki." Ta amsa da amin wajan ya yi shiru babu mai magana. Didi ce ta sake cewa, "Salma an kaiwa driver abincin?." Salma ta ce, "na tabbatar ma ya cinye yanzu." Didi ta yi murmushi suka sake yin shiru. ?arar wayar Nayla ce ta katse shiru ta kalla ta ga Abbas ne ta kalli Salma ta ce, "Yayanki ne." Salma tayi dariya ta ce, "yayan mu dai, kema ai yayanki ne. Baza ki Wauka ba?." Nayla ta ce, "ana babbakar giwa waye zai je ?aure zomo?."

Salma ta murmusa cikin tausayin ?ar uwarta ta ce, "Gaskiya ne." Didi ta kalli Nayla ta ce, "Nayla zan shiga banWaki." Salma ta ce, "mu je na raka ki." Didi ta mi?e ta fita ita da Salma aka bar Omar kawai da Nayla a zaune. Wani irin yarrr Nayla take ji a jikinta, gashi dai kamar bai san tana zaune ba amma wani irin suka zuciyar take yi ga farin ciki da yake mamaye zuciyarta. Ganin ba ita yake kallo ba kawai sai ta zuba masa ido tana kallon sa cikin shau?i ko ?ifta ido bata yi.

Waya ta Wauka kamar tana dubawa tana yi masa video ta yadda bazai fahimta ba. Omar kuwa shi kansa wani iri yake ji, ya na kallon su har fitar su Didi ya kuma san tana zaune ita a falon. Wani iri yake ji a jikinsa kamar taSa zama da mace shi da ita kawai ba. Duk da dai akan Narma kawai ya faru amma sai yake jin wannan daban kamar bai taSa shiga irin yanayin da yake ji ba.

Hannunsa ta kalla ta kuwa yi farin gani, domin azurfar da ta bashi tana sanye a Wan yatsansa na biyun ?arshe a hannun haggu. "Wayyo Allah!." Ta furta bata san ta ce ba saboda farin cikin da ya sake mamayeta. Jin abinda ta furta sai ya Wago ido yana kallonta a lokacin ta rufe ido ita kuma saboda tsananin farin ciki. ?auke kai ya yi ita kuma ta buWe ido, gabaWaya ta kasa sarrafa kanta ?iris take jira ta fita daga hankalinta

Didi da Salma ne suka dawo Didi ta kalle ta ganin sai murmushi take yi ita kaWai sai ta kalle shi taga babu alamun ma sun yi magana da ta san hali. Mamakin murmushin Nayla take yi saboda ta san tsoron Omar take ji, amma yanzu gashi an bar su su biyu tana ta murmushi mai kyau.

Nayla ta kalle ta ta ce, "Didi mu je Wakina ki kwanta ki huta." Didi tayi dariya ta ce, "Sallar azahar kawai zamu yi mu juya, kwanciyar me zanyi gashi har sha biyu da rabi tayi?." Nayla ta ce, "kai Didi, ni na Wauka sai yamma."
"Gwara mu shiga Kano kafin duhu ya yi Nayla." Nayla ta girgiza kai tana ta murmushi abin ta kamar sabon kamu. Omar dai baya magana Didi sai girmama hali irin na sa take yi, yazo har gidan su yarinya amma ya kasa ce mata ya jiki bayan a gabansa aka ce bata da lafiya.

Salma ta ce, "Didi mu je Wakin Nayla ki yi alwala ki yi sallah." Didi ta amsa da to Nayla dai bata son tafita amma haka ta mi?e a lokac??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????in Jawad ya shigo ya zauna yana Wan jan Omar da hira duk da bai sake ba. Nayla bata so barin wajan ba, haka suka shiga babban falon suka hau sama har Wakin Nayla.

Didi girmama gata irin na Nayla take yi, musamman yadda Abiy ya ruWe akan ciwon ta ga kuma girman Waki kamar baza tayi aure ba. A nan suka yi sallar azahar suna ta hira da Didi, duk da ta lura Nayla bata cikin walwala dawowar su Wakin amma bata tambaya ba.

Bayan an idar da sallama suka sakko suka haWu sa Mama ta bawa Didi kaya a leda sannan ta bata kuWi ta ce in ji Abiy ya ce su yi kuWin mai. Ta dinga yi mata godiya sosai, Nayla ta ri?e mata kayan ita da Salma suka fito har bakin motar.

A tsaye suka tarar da Omar shida driver da alama su suke jira. Didi ta buWe motar sannan ta kalli Nayla ta ce, "Nayla ba?o zai yi halin sa, Mun gode da karrmawa Allah ya bar zumunci." Nayla ido ya ciki da hawaye ta ce, "Amin Didi. Allah ya kiyaye hanya." Salma ta ri?e hannunta tace, "Nayla meye na kukan?." Sai ga hawaye shar ya sakko mata, ta juya da sauri ta rungume Didi ta ce, "bana so ku tafi Didi, don Allah ku kwana." Omar da yake jin me cewa ya kalle ta yana mamaita su kwana, Lallai ma yarinyar bata da hankali.

Didi ta ce, "Nayla banda abin ki meye na kuka kuma? Ki yi ha?uri wata ran ai zan dawo in sha Allah." Nayla ta Wago daga jikinta ta ce, "to Didi. Wallahi bana so ku tafi, ji nake kamar na bi ku."
"Ki yi ha?uri kin ji? Ai zaki zo Kano Win ko?." Ta Waga kai kamar yarinyar ?arama Didi ta ce, "to kin gani, ki yi ha?uri kar ki saka ni kuka nima." Nayla ta goge ido ta ce, "Allah ya sauke ku lafiya."
"Amin Nayla. Allah ya baki lafiya, ji ke ki ga likita gabaWaya kin canja kin rame kamar ba ke ba."

Nayla ta ce, "to Didi zan je in sha Allah." Didi ta shiga mota Salma ta ri?e Nayla ta ce, "ki yi ha?uri ki ta addu'a, canji zai zo daga wajan Allah."
"Ina yi Salma, kema ki dinga yi min."
"Ina yi miki kullum Nayla, Allah ya sassauta miki. Ba dan ban cewa Daddy zan kwana ba ai da nayi zamana na Webe miki kewa. Amma zan dawo." Ta Waga kai kawai tana kallo Salma ta shiga motar.

Kallon inda Omar yake tayi suka haWa ido dan kallon ta ya ke yi yana tunanin meyasa yake yawan ganinta tana kuka, shagwaSa ce ko sangarta ko rashin hankali?. Ganin sun haWa ido sai tayi murmushi idonta duk hawaye ta ce, "Allah ya kiyaye hanya& .Yaya Omar!.." Wani iri yaji a zuciyarsa, mace ta farko da ta taSa ce masa Yaya kenan a rayuwarsa. Sai yaji wani irin rauni da bugun zuciya, har lokacin kallon ta yake yi hawaye suna sakko mata daga idonta.

Samun kansa ya yi da yin murmushi ya Waga kai ya ce, "Amin, Mun gode" daga haka ya buWe motar ya shiga. Ai Nayla suman tsaye tayi a wajan saboda gigicewa. Na farko murmushin da ya yi mata, na biyu maganar da ya yi, na uku godiyar da ya yi mata sai take ji kamar an yi mata babban albishir.


Horn Win motar ne ya saka ta dawo hankalinta, ta share hawaye tana dariya tana kuka ta Waga musu hannu suka fita daga gidan ita kuma ta juya a sanyaye ta koma cikin gida.
KRB2P012
Arewabooks@nanahaleema11.


Sai la'asar suka shiga Kano, Didi sai da ta shiga wajan Hajja ta bata labarin duk abinda ya faru har kayan da Mama ta bata da kuma kuWin da Abiy ya bayar ta nuna mata. Hajja ta dinga murmushi dan ta san daman baza ta ji kunya ba dan Didi ta je gidan su Nayla ba, saboda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login