Showing 81001 words to 84000 words out of 85380 words

Chapter 28 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3831

irin raping kuma? Mijita ne fa."
"Mijin ta fa, ta ya zai dinga zuwa wajanta ba tare da izini ba? Ai dan yana mijinta ba hakan yana nufin ya dinga amfani da ita duk sanda ya so ba, akwai lokacin da zata ji bata ra'ayi ko da yana ra'ayi sai ya ?yale ta tunda bata so. Kuma a wannan yanayin da take ciki ni ban Wauka ma Ashraf zai kai wannan waje ba, na Wauka zai bata time ya rarrashe ta har ta dawo nutsuwarta sannan sai su yi honeymoon Winsu. Amma yanzu ga damuwa, ga wannan tsinannen yaro, ga damuwarsa da me zata ji?."

Dad ya yi murmushi ya ce, "in dai wannan ne babu abin damuwa a nan, na tabbatar faWar Narma ce babu wani rape, ki manta kawai."
"Na gani da idona ka ce babu wani rape? Ni gabaWaya aurenta dashi ya fara fitar min daga rai wallahi, bata samun farin cikin da muka so ta samu a gidan."

Dad ya ce, "zan kira Ashraf Win naji abinda yake faruwa." Mum ta ce, "ya dai kamata gaskiya, zuwan mu baka ga yadda ta sake ana yawo ba. Amma lokacin da mu je tana Waki a kwance shi kuma yana falo. Meye hakan yake nufi? Ni kar ya Worawa yarinyata ciwo fa."

Dad ya ce, "gaskiya akwai damuwa, amma ki bari zamu bi komai a hankali mu gani. Zan kira shi na ji in da matsala sai ya dawo da ita nan ayi bikin kawai a huta, sai ta zauna a nan Abuja yadda zamu dinga ganinta ko yaushe." Mum ta ce, "da dai ya fi gaskiya" ta faWa tana kawar da kai gefe dan gabaWaya zaman Narma da Ashraf ya fita daga zuciyarta.

" " " " " " "

Kafin sallar juma'a suka shiga Kano, kai tsaye gidan Hajja aka wuce kamar yadda aka ce za a yi. Ana ajjiye motar suka fita zuwa cikin gidan Mama na ri?e da hannun Nayla, fuskarta a buWe dan mayafin ma ya dawo kafaWa dan bata da nutsuwa. Gidan cike da mutane suka tarar dashi, matan su da Daddy da ?an uwa duk dai dangin mahaifiyar Nayla suna gidan.

Nayla na shiga ta ?arasa wajan Hajja ta zube a kan guiwarta ta Wora kanta a jikin Hajja bata ce komai ba. Hajja ta dafa kanta ta ce, "Sannun ku da ?arasowa Hauwa'u." Ta kalli Mama ta ce, "Zeenatu barka da hanya." Da fara'a Mama ta gaishe da kowa na wajan suka amsa mata da murmushi dan tana burge su bata da matsala ko kaWan.

Mama ta ce, "To Hajja ga Nayla nan dai Abiy ya saka mun kawo ta, sai ha?uri da yadda abin yazo gabaWayam mu bamu yi tunanin hakan zai faru ba." Hajja ta murmusa ta ce, "?addarar kenan ai, baka sanin ta inda zata zo ba balle ka yi ?o?arin kiyayewa kafin zuwanta. Babu komai, in sha Allah alkhairi ne."

Mama Sa'adatu ta dafa Nayla ta ce, "Nayla sannu, jikinki akwai zafi, kanki na ciwo?." Nayla ta Waga kai alamun eh, Salma ta ce, "Mama ba dole tayi rashin lafiya ba, kullum cikin damuwa da kuka take. Yanzu ma tunda muka taho ko ?ala bata ce ba, sai dai tayi hawaye ta gaji ta daina." Mama Sa'adatu ta ce, "ki yi ha?uri Nayla, duk Wan adam baya tsallake ?addararsa kin ji ko?."

Bata ce komai ba ko motsawa ma bata yi ba, tana jikin Hajja da take shafa kanta a hankali cikin shigar rarrashi. Lokacin sallah da ya yi ne ya tashe su gabaWaya, akayi alwala aka yi sallah sannan aka ci abinci. A lokacin Jawad da Ahmad suka shigo suka gaisa da mutanen gidan kafin su shiga mota su tafi.

Nayla na zaune a Wakin da take kwana tayi tagumi, Mama Sa'adatu ce ta shiga ta cire mata tagumin ta zauna kusa da ita ta ri?e hannunta ta ce, "Ki daina tagumi kin ji ko?." Nayla ta Waga mata kai kafin ta ce, "yanzu me ki ke so?."
"Babu komai Mama."
"Ki faWa min in akwai abinda ki ke so na kawo miki."
"Babu Mama."
"Kin sha maganin ciwon kan?." Ta Waga Kai alamun eh ta ce, "to ki kwanta ki yi bacci zaki ji daWi."

Nayla ta ce, "bazan iya baccin ba." Mama ta ce, "to me za ki yi?."
"Nima ban sani ba" ta faWa murya na rawa alamun zata cigaba da kuka. Mama ta ce, "kar ki yi kuka mana, ni kukan ne bana so na gani." Nayla ta ce, "Abiy yana fushi dani Mama."
"Kar ki damu komai zai wuce. Ba dai kina son mijin na ki ba?." Nayla ta sunkuyar da kai ta ?asa bata amsa ba. Mama ta ce, "Nayla ni ?anwar mahaifiyarki ce, baki da wata uwa kamar ni. Ki faWa min abinda yake ranki kar ki ji kunya, kina son mijin ko?."

Nayla ta ce, "Mama da dai nasan ina sonsa, amma yanzu tunda ake kiransa da mijina na kasa tantancewa." Mama ta ce, "zaki tantance sai a hankali, yanzu ma ruWani da yadda abin yazo bazata shine ya saka ki ke jin hakan. Amma kar ki damu komai zai zo ya wuce ya zama tarihi. Abiy ba ya fushi dake, ki kwantar da hankalinki."

"Fushi yake yi Mama, tunda na furta Ina son sahikenan ya canja. Mama Abiy ne yake cewa kar na je gida sai ya ce na je, in ba fushi ya yi dani ba meye?. Mama daga zuwana Kano na koma na ji labarin wai ya aura min shi."

Mama ta ce, "to ke waye ya ce ki zo Kano baki tambaye shi ba?." Nayla ta ce, "Mama ce. Mama ce tazo zan fi samun nutsuwa a nan, itace ta saka aka kawo ni amma ni ban yi niya ba." Shiru tayi tana kallon Nayla kafin ta ce, "ita ta san kina son Omar Win ne?." Gaban Nayla ya faWi, indai aka ambaci sunansa sai gabanta ya faWi matuka. A hankali ta ce, "ta sani, itace ta ke bani goyan baya akan shi. Dan koda Abiy ya ce na manta dashi tana cemin kar na damu zata san ya zata yi."

Mama Sa'adatu ta yi ajiyar zuciya ta ce, "shikenan dai ki kwantar da hankalinki, komai zai wuce. Kuma mahaifinki baice kar ki je gida saboda yana fushi ba, yana so ki nutsu ki yi zaman aure, kar wannan ya dame ki kin ji?." Kai ta Waga almaun to. Mama ta tashi ta bar Wakin zuciyarta cike da zargin wani abu akan Mamansu Jidda.

Bayan an idar da sallar juma'a mutane suka Wan ragu a gari sai ga Mama Zaliha ?anwar Abiy itama rarrashinta dai ta dinga yi. Gidan Hajja ya zama gidan biki domin kuwa an cika shi dam da ?an uwa ana hira ana kuma cin abinci. Nayla da aminanta kuwa suna Waki tana kwance akan gado su kuma suna gefen suna aikin rarrashinta da kalamai masu daWi.

Didi kuwa tana gida ta kasa shiga gidan Hajja, gabaWaya kunyarsu Hajja take ji, sai ta ga kamar tana da laifi akan abinda aka yiwa Nayla. Tana zaune ya dawo daga masallacin juma'a ta ce, "Yauwa Omar, don Allah zuwa sallar magriba ka dawo saboda akwai abu mai mahimmaci da za a yi." Ya bita da kallo yana taSe baki ya ce, "to zan duba na gani."
"Ba dubawa zaka yi ba, yi zaka yi don Allah."
"To" ya furta dan shima ta saka shi a tunanin abinda zai farun nan.

Fita ya yi ita kuma ta zauna tana hasaso abinda zai faru, idanunta kallo mata Omar suke yi yana tijara da rashin mutunci a gaban mutane. A bayyane ta ce, "in sha Allah bazai yi ba, zai nutsu ya saurare abinda za a ce masa in sha Allah."

Da yamma Mama Zaliha ta tafi gida sauran matan su Daddy ma sun tafi ya rage Mama Sa'adatu ce kawai su Jidda da Jalila da kuma Mamansu Jidda.

Mama Sa'adatu ta ce, "Ina Aisha ne? Ya kamata ta shigo ta bamu key mu je mu ga inda Nayla zata zauna ko Maman Jidda?" Ta faWa tana kallon Mama. Mama ta ce, "gaskiya ne, nima a waya na dinga ganin gidan da ana shiryawa, ya kamata muje kam." Mama Sa'adatu ta ce, "bara a kirata, sai mu je mu dawo tunda an ce babu nisa."

Salma aka tura aka ce taje ta karSo key Win, ta shiga ta samu Didin duk tayi tsuru-tsuru kamar mara gaskiya. Salma ta ce, "Hajiya Didi lafiya ki ke kuwa?." Ta yi murmushin ya?e ta ce, "Lafiya lau Salma, Ya taro?."
"Alhamdu lillah. Su Mama ne suka turo ni akan ki bada key na gidan za a je a gani." Didi ta amsa a sanyaye ta Wauko ta mi?awa Salma tare da yi mata kwance sa sannan ta ce, "Ya Nayla kuwa?."

Salma ta ce, "Tana nan a kwance."
"Bata da lafiya ko?."
"Kusan hakan gaskiya." Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "Allah ya bata Lafiya, ki gaishe ta zan shigo zuwa anjima in sha Allah." Salma ta ce, "Amin. Ni na Wauka a gidan ma zamu zo mu same ki." Didi ta ce, "hmm Salma baza ki gane ba, ki je kawai sai na zo." Salma ta amsa mata ta fita ta kai musu key Win ta koma inda take zaune.

Bayan sallar magriba Omar ya dawo kamar yadda ta ce, tana ganin shigowarsa ta mi?e ta ce, "Yauwa sannu da zuwa. Ka taimaka min yadda Allah ya taimake ka kayi wanka ka canja kaya, kar kace ?ananun kaya zaka saka, don Allah ka saka manyan kaya."

Ya bita da kallo bai ce komai ba ya zauna sannan ya ce, "ni yunwa nake ji." Didi ta wuce kitchen ta kawo masa abinci ta ce, "ga abinci ka ci." KarSa ya yi ya fara ci yana kallonta ganin gabaWaya bata cikin nutsuwarta.

Ajjiye abincin ya yi ya kalle ta ya ce, "Didi wai me ya mayar dake haka ne? GabaWaya kin firgice bakya tare da nutsuwa sam. Da kin bani haushi na ce bazan sake tambayarki ba amma na kasa, meye ne don Allah?." Didi ta ce, "samun nutsuwata ka kammala mu je inda zamu je."
"Indai na je na shirya mu ka tafi zaki nutsu?." Kai ta Waga alamun eh ya ture abincin ya ce, "shikenan bara a yi sallar i'sha sai na shirya Win, bana son wannan yanayin na ki wallahi, gabaWaya bana jin daWi in na ganki a haka." Didi ta ce, "ka ci abincin tukunna."

"Ya fita a raina" ya faWa yana tashi ya fita ta bishi da kallo. Hawaye taji suna sakko mata, tunaninta kawai ta ya Omar zai karSi auren Nayla? Tuna hakan kawai faWuwar gab yake sakata, balle ta san bakinsa da bashi da control komai ya zo bakinsa faWa yake yi ko a gaban waye.

Tana nan zaune taji kiran sallar i'sha ta tashi a sanyaye tayi sallah ko shafa'i da wutir bata yi ba tana zaune tana jiransa. Wayar Didi ce tayi ?ara ta ga sunan Salma ta Wauka da sallama, Salma ta amsa ta ce, "Didi su Daddy ne suka ce na faWa miki suna hanya, ku shigo gidan Hajja yanzu zasu ?araso." Da?yar ta iya amsawa sannan ta kashe wayar cike da tsoro.

Babu jimawa taji an dafa kafaWarta, ta Wago kai ta kalle shi kamar yadda yake binta da kallo cikin son gano damuwarta. Kamar ta bu?ata ya yi wanka ya canja kaya zuwa manyan kaya riga da wando na shadda ash colour. Ya yi mata kyau sosai a idanunta, ta zuba amsa ido tana kallo kafin ta mi?e tsaye ta ce, "ka yi kyau." Kallon fuskarta ya yi ya ce, "kuka ki ka yi?." Kai ta girgiza alamun a'a ya ce, "gashi nan na gani a idanunki, kuka ki ka yi Didi? Ban san wanne abu ne wannan da ki ka kasa sanar dani ba, kodan kin yi aure ne yanzu kina ganim ban kai na san damuwarki ba ban sani ba."

Didi ta ce, "yanzu zaka ji."
"Mu je to, na shirya ko?." Ta kalle shi ta ce, "shiyasa na ce ka yi kyau, dama zaka saka babbar riga."
"TaS bazan iya ba, ni bani da babbar riga ma a duniya. Ban sani ba ko sai nan gaba." Didi ta yi murmsushi kawai bata ce komai ba sai ya kalle ta ya ce, "wata?ila sai aurena zan Winka." Gabanta ya faWi sosai a haka ta yafa mayafi ta Wauki jakarta da wayarta ta ce, "ka kashe hasken gidan sai mu je."

Ya kalle ta da mamaki ya ce, "Kashe hasken na meye kuma? Abinda dai zan dawo." Ta kalle shi ta ce, "Don Allah ka kashe, in ka kashe ka kulle gidan." Zai yi magana ta ce, "Allah na ce." Bai ce komai ba ya yi abinda ta ce suka fito ?ofar gidan ya kulle sannan ya kalleta ya ce, "Sai ina....?."
KRB2P028
Arewabooks@nanahaleema11.

Kallon ?ofar gidan Hajja tayi ta ga manyan motoci da alama su Daddy Win sun iso. Ta kalli Omar dsa yake kallonta yana jira yaji inda zasu jw ta ce, "Zo mu je." Gaba tayi yana binta a baya har ?ofar gidan Hajja. Da mamaki yake kallon ta ganin ta tura gate Win ta shiga sai ya ce, "na jira ki?."

"Ka shigo dai."
"A'a ban yi niya ba gaskiya, ko na shiga babu lada, kedai ki je ki gaishe ta."
"Ka shigo Omar, don girman Allah." Mamakin wannan magiyar da take yawan yi masa yake yi ta san kuma baya so, babu yadda iya haka ya shiga kamar yadda ta ce.

Sallamarta da shigar falon ya saka suka mutanen falon suka san sun iso aka amsa mata tana bin kowa da kallo. Gaisawa suka yi da kowa da yake zaune, Omar da yake bayanta ya gaishe su cikin gaisuwarsa ta ko yaushe ta?aitacciya. Kallon Didi yayi ya ce, "ina jiranki a waje." Hannunsa ta ri?e ta ce, "ka shigo ka zauna." Kallon mutanen falon ya yi da suke kallonsa ya kalle ta ya ce, "na zauna nayi me kenan? Zan dai jira ki." Didi ta ce, "ka zauna don Allah."

Juya idanu ya yi cikin gajiya ya ce, "wai magiyar nan ta meye? Kin fara isata wallahi." Didi ta yi ?asa da murya ta ce, "Mutane suna jinka, don darajar annabin Allah ka zauna." Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba ya ?araso ya zauna akan carpet kamar yadda ta zauna.

Daddy ya kalli Abba da yake kallonsa shima suka Wauke kai a tare. Nayla tun da ya shigo da maganarsa ?irjinta yake bugawa, tana jin gardama da yake yi akan ya zauna, a nan ta tabbatar da har lokacin bai san abinda yake faruwa ba. Hawaye ta ji na sakko mata cikin tausayin kanta.

Daddy ne ya fara magana bayan an buWe taro da addu'a ya ce, "kowa ya san abinda ya tara mu a nan,magana ce akan abinda ya faru da kuma wanda zai faru yanzu. Nayla dai an Waura mata aure a wani bahagon yanayi wanda mahaifinta ne kaWai ya san dalilinsa na yin hakan. Amma ya ba mu ragamar kula da komai a yanzu, ya ce mu gyara inda aka Sata shiyasa mu ka zo aka zauna gabaWaya domin a tattauna a kai."

Omar jin kalaman Daddy ya saka shi ya kalli Didi zai yi magana ta yi masa alamun don Allah ya yi shiru. Dole ya yi shiru amma shi bai ga amfanin zamansa ba, har ita Didin bai ga amfanin zamanta ba tunda taro ne na familynsu to su me zai kawo su ciki?.

"Omar!." Daddy ya katse masa tunani hakan ya saka ya Wago yana kallonsa ba tare da ya amsa ba. Daddy ya ce, "ka san wannan?." Ya faWa yana nuna masa Nayla da take zaune kai a ?asa. Kallon inda aka nuna masa ya yi ya sake kallon Daddy ya girgiza kai alamun bai santa ba.

Daddy ya yi murmushi shi kuma Omar ya mayar da kai ?asa dan baya jure magana da manyan mutane irin su Daddy, Daddy ne mutum na biyu bayan Abiy da ya yi amsa kwarjini a duniya. Daddy ya ce, "Omar ranar juma'a da ta gabata sati Waya kenan yau, ?addara ta gifta a tsakani har aka yanke hukunci ba tare da ka sani ba. Domin kuwa a wannan ranar aka Waura aurenka da ita wacce take zaune yanzu." Omar bai motsa ba dan bai Wauka shi Omar Win ake nufi ba, ya yi tunanin akwai wani Omar Win a wajan bayan shi.

Ganin bai nuna firgici ba sai Didi ta Wan ji sanyi tana cigaba da kallonsa. Daddy ya ce, "Mahaifin Nayla ya yanke hukunci cikin wani yanayi na fushi da wani dalili na sa, ya aurawa ?arsa kai kamar yadda ake Waura ko wanne aure. Wakilanka sun shaida dan sune suka karSi auren, sannan Yayarka ma ta shaida anyi hakan. To mun zauna a nan ne dan mu ji ta bakinka akan auren, dan yanzu ga amarya ma an kawo ta daga Kaduna zuwa nan. Kana ganin zaka iya zama da ita a matsayin mata?. In baza ka iya ba kar kayi mana kara, ka faWi abinda yake zuciyarka domin muna so komai ya ?are a nan wajan."

Shiru kowa ya yi ana jiran amsar Omar, shi kuma bai ce komai ba dan har ga Allah bai Wauka dashi ake magana ba. Ganin shirun ya yi yawa Hajja ta ce, "Ummaru!." ?ago kai ya yi ya kalle ta ta ce, "baka ji abinda aka ce ba ne?." Omar ya ce, "na ji mana."
"Baka ce komai ba." Ya kalli Hajja ya ce, "Hajja a ganina kamar maganar ai bata shafe ni ba ko? Zamana a wajan nan ma bashi da amfani tunda maganar da ta shafeku ku ke yi. Ba batun aure naji ana yi ba?."

Hajja ta ce, "shi ake yi mana, kuma in bai shafe ka ba ai ba za a ce kazo ka zauna ba Omar." Ya ce, "nima shine nayi mamaki ai. Yanzu me ya shigo da ni cikin maganar?." Didi ta ce, "Saboda kaine mijin! Kaine Omar Win da ake zancen Waurawa aure da Nayla jikar Hajja!."

Kallon Didi ya yi ya Wauke kai dan gani yake ba dashi take ba, sake kallon ta ya yi yaga dai shi take kallo ya ce, "Didi!." Ta ce, "Omar!."
"dawa ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login