Showing 24001 words to 27000 words out of 85380 words

Chapter 9 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3837

Tsaki Mum ta yi ta ce, "wannan ba shawara ba ce, ka ?yale ni da kaina zan Wauki matakin da kai ka kasa Wauka, zan yi masa abinda zai karya asirin koda ba ya so, na san abinda zan yi" ta faWa tana fita daga Wakin da yake ya bita da kallo yana ajiyar zuciya cikin ?unar zuciya.

" " " " " " "

Haka Omar ya yini a gida babu inda yaje saboda baya jin daWi ko kaWan. Didi ce take ta hidima dashi har dare a lokacin AbdilHamid yazo. Ya yi farin cikin dawowar Omar ko babu komai Didi zata nutsu su fuskanci abinda ya ke gaban su.

Washe gari ya tashi babu laifi ya Wan ji ?arfin jikinsa, da ya shiga falon ya same ta tana karatun alkur'ani, da sallama ya ?arasa ya zauna sai kuma ya tashi ya shiga kitchen ya zuba tea ya dawo ya zauna yana sha a hankali. Sai da ta kai ?arshen aya sannan ta rufe ta kalle shi ta ce, "ya jikin?."
"na ji sau?i. Ya ku ka yi da AbdulHamid jiya?."
"Maganar gida ce. Ni wallahi ban san ma ya za a yi ba, ya ce zai zo da makullin gidan a je a gani dan asan abinda za a zuba. Sai kuma batun kawo lefe, shi na ce kawai maza su kai gidan Kawu."

Kai ya girgiza kafin ya ce, "Allah ya kaimu."
"Amin" ta amsa a ta?aice dan baza ta yi masa maganar hidimar biki da kayan Waki ba a yanzu saboda yanayin da yake ciki. Kira ne yake shigowa wayarsa ya kalla yaga Narma ce ya Wauke kai ba tare da ya Wauka ba yana kulle ido.

Didi ta ce, "ana yi maka waya." Bai buWe ido ba balle ya amsa mata, a lokacin wayar ta sake shigowa nan ma bai Wauka ba kuma bai katse ba. Didi ta kalle shi a sanyaye ta ce, "Narma ce take yi maka waya?." BuWe ido ya yi ya kalle ta ya ce, "tun jiya take kira na, ni ban san me zance ba." Didi ta ce, "gwara kar ka Wauka Win ya fi alkhairi. Ka cigaba da addu'a Allah ya cire maka ita daga zuciyar ka, ita kuma sonka da Allah ya Wora mata ya canja mata da mafi alkhairi."

Bai amsa ba ya sake mayar da ido ya rufe, baya jin daWi gabaWaya a zuciyarsa sai yaji kamar bai kyauta mata ba. Ko babu komai ai tana sonsa kuma mai sonka yafi wanda ya ce baya sonka. Gashi abinda yake ji a kanta a baya duk ya sire masa, ya kasa gane dalilin da ya saka baya jin abinda ya ji dah a kanta. Duk da ya ala?anta hakan da abinda ya faru amma bai kamata ace ya daina ji gabaWaya ba, ya Wauka wani abun zai rage ko ya ya yake amma babu ba. Ya ajjiye batunta a gefe, ya tsallake ta ya wuce gaba dan shi giwa ce baya waiwaye, in dai har ya wuce to ya wuce kenan har abada.

"Didi!." Jin yadda ya kira sunanta sai ta kalle shi a nutse ta ce, "Na'am." Zuba mata idanu ya yi ya ce, "dama hiv ta kashe mahaifiyar mu?." Didi ta runtse ido a sanyaye ta ce, "?arya ne wallahi, ?arya ce kawai aka faWa mana dan mu ji zafi a zuciyar mu amma ba haka abin yake ba. In da ace haka ne kaima ka san da labarin bai kai yanzu bamu sani ba. Da lokacin da muke gidan su Kawu mun san labarin, tunda har basu faWa mana ba wallahi ba haka bane Omar."

Ajiyar zuciya ya yi yana tuna irin kalaman da Senator ya yi amfani dasu masu zafin gaske a gare shi, in ya tuna kalamansa akan iyayensa sai yaji kamar duniyar tana juya masa. Yafi jin zafin zagin iyayensa da ya yi fiye da komai, ya ji raWaWi da ?unar zuci wacce bai taSa ji ba a rayuwarsa. BuWe ido ya yi ya kalli Didi ya ajjiye kofin hannun sa ya ce, "Didi daman ashe kece ki ke ciyar dani a gidan nan? Na kasa yarda da gaske kece ki ke Waukar Wawainiyata. Daman kallon da ake yi min kenan?."

Didi ta ce, "ba gaskiya ba ne Omar, ka tuna kana bani kuWi a siyo abinda babu a gidan nan. Kaine ?arfin yin abubuwa na gidan nan Omar bani ba, kar wannan maganar ta dame."
"Amma kafin na baki kuWi a siya ke kin siya, saboda haka ki ke sana'a mai wahala domin ciyar dani. Tabbas abinda aka ce gaskiya ne, ban iya Waukar Wawainiyar Yayata ba ta ya zan iya Waukar ta wata mace?."

Didi a sanyaye ta ce, "Wallahi ?arya ne, in ma Senator ne ya faWa maka haka ya faWa dan ranka ya Saci kawai. Omar meye baka yi min? Duk kuWin da ka samu a kaina yake ?arewa, kana Winka min suttura ka hana kanka, ka bani kuWi ka hana kanka amfani dasu. Don Allah kar wannan ya dame ka, ?arya ce kawai da son Sata maka rai."

Ajiyar zuciya ya sake yi idanunsa sun yi ja sosai ya ce, "ba a taSa faWa min kalaman da naji zafin su a duniya ba kamar abubuwan da ya faWa a kanki da iyayen na, ba a taSa yi min abinda naji zuciyata na rawa kamar abinda ya yi min ba. Ya kira ni jahili ya fi a irga, tabbas kuma na san bani da ilimi boko amma na addini ina da daidai nawa, ina da karatun addinin da bana tunanin shi yana dashi. Amma daman sai mai ilimi ne akwai yake zama wani a duniya?" Ya faWa yana tsareta da idanunsa da suka koma jajaye.

Didi t ce, "A'a, Allah yana Waukaka duk wanda ya so a lokacin da ya so. Baka ji hausawa suna cewa dare Waya Allah kan yi bature ba? Wanda ba baturen ba ma dare Waya Allah yake yin sa. Haka arzu?i, mutuwa, aure duk lokaci ne dasu, Omar in yanzu rabon ka ya kira ka rufe ido da buWewa ya fi wahala akan Waukakar da zaka samu a lokacin da ka amsa KIRAN RABON ka. Shiyasa Allah ya ce tashi in taimaka maka, baza ka je kan titi babar mota taho ka kwanta ka ce Allah kare ni ba, baza ka ?i karanta komai a yayin rubuta jarabawa ba ka shiga Wakin jarabawa ka ce Allah zai yi min ba. Dole sai ka tashi sannan Allah zai taimaka maka."

Sunkuyar da kai ya yi kafin ya Wago ya kalle ta ya ce, "Didi!." Ta kalle shi bata amsa ba ya ce, "Daga yau zan koma irin yadda ki ke so na zama, duk abinda nake yi wanda ba mai kyau ba ki faWa min ni kuma daga yanzu zan daina." Didi ta yi murmushin cikin farin ciki ta ce, "Da za kayi haka da ka nunawa masu son ganin ka ?as?anta cewa da Allah ka dogara, da zaka bawa ma?iya mamaki Omar."

"Ina jin ki."
"Omar gabaWaya harkar daban nan zaka ajjiye ta a gefe, ka daina Waukar wu?a kwata-kwata, sannan ka nutsu ka kama sana'a ka zama mutum kamar kowa. Daman ba shiga harkar mutane ka ke yi ba, ka cigaba da rayuwarka ka sake ?arfafa addininka. Sallah, azumin nafila, sadaka, taimako ka ?ara akan yadda ka ke yi, aikin alkhairin ka ya danne na sharrinka Omar."

Ya kalle ta bayan ta gama ya ce, "iya abinda zan yi kenan?." Ta Waga kai ta ce, "shine kawai. Sai kuma ka koma makaranta, sannan ka shirya da dangin mu, ka bar komai ya wuce a cigaba da zumunci."

Hannu ya Waga ya girgiza yatsansa ya ce, "har abada na gama yin karatu, bazan sake yin makaranta ba, Har gwara ma karatun addini akwai makarantar da na gani ana yi online zan shiga kodan sake gyara lahirata. Sannan batun dangi ma ki cire shi ya koma gefe, har gwara makarantar akan dai batun waWancan matsiyatan. Ki cire batun karatun boko dana dangi, amma abinda kika ce da farko zan yi."

Didi ta yi dariyar farin ciki ta ce, "Allah ya baka iko Omar, Allah ya taimake ka ya yi ri?o da hannunka, Allah ya kai ka matakin da baka yi tunanin zuwa ba, Allah ya sa ka taka matsayin da baka yi tunanin takawa ba, Allah ya kawo maka alkhairin da baka yi zaton samunsa ba a rayuwarka. Naji daWin wannan canjin Omar, naji daWi, Allah ya sa ka yi abinda ka ce."

Kallon ta yayi yana girgiza kai ya ce, "zan yi, tunda na ce ai kin san zan yi" ya faWa yana Wauke ido daga kanta yana wani tunani daban. Didi ta ce, "Har makarantar da kayi magana zaka yi?."
"Da ban faWa ba kin san da ita ne?."
"A'a ban sani ba."
"To tunda ki ka ji na faWa zan yi."
"Ka yi mana register nima zan shiga."
"To."

Didi sai murmushi take tana kallon sa shi kuma ba ita yake kallo ba, Mi?ewa ya yi ya fita ta bishi da kallo kafin ta faWi a wajan ta yi sujjada ta godiya ga Allah da ya nuna mata ranar da ta faWi kuskurensa ya amsa har ya ce zai gyara. Duk da bai amince da batun gyara zumunci ba, amma tunda ya fara karSar gyara ta san a hankali zai bar komai ya zama labari. Tabbas soyayyar Narma a wajansa tamkar kiran rabo ce.
KRB2P010
Arewabooks@nanahaleema11.

Da wannan farin cikin Didi ta yini tana ta aikin ta cikin zafin nama da karsashi. Wajan Hajja ma take so ta shiga ta bata labarin abinda ya faru amma so take yi ta gama sai ta shiga. Bayan sallar la'asar ya shigo da sallama ta amsa tana fitowa daga kitchen tana cewa, "Ina ka shiga? Ga abinci ka zo kaci." Omar ya zauna tare da Wan kashingiWa ya kalle ta ya ce, "na je unguwa ne."

Fitowa tayi ta zauna ta ce, "unguwar bata da suna?." Mi?ewa zaune ya yi a kan kujerar ya ce, "zan faWa miki."
"To abincin fa?."
"A'a bana jin yunwa yanzu." Didi ta ce, "zuwa jibi nake so mu je Kaduna gidan su Nayla mu yiwa mahaifinta godiya." Kallon Didin ya yi ya ce, "to" ya furta dan bai san me zai ce ba. Ya san dai bazata taSa amincewa ba in ya ce bazai je ba shiyasa ya ce to.

Wayar ta ce take ?ara ta duba ta ce, "A'a wacce irin number ce wannan? Tun Wazu ake kirana." ?auka tayi ta saka a speaker daga can Sangaren aka ce, "Didi barka, Narma ce." Didi jin muryarta da suna ta sai gabanta ya faWi ta kalli Omaar da ba ita yake kallo ba ta ce, "A'a Narma, barkan ki. Ina ta ganin kiran ashe kece ni Wauka nake company ne duba da yanayin number." Narma ta ce, "ni ce. Ina kiran ki da layin ?asar England ne shiyasa."
"Allah sarki, ya ki ke?."
"To gani dai kamar mai lafiya amma ba lafiya nake ba Didi."

Didi ta ce, "me ya faru kuma?." Narma ta ce, "Didi rabuwa da Faruk ba abu bane mai sau?i a rayuwata ba, ban taSa son wata halitta kamar yadda nake sonsa ba Didi. Har yanzu ban cire rai da samunsa ba."

Didi t???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ayi ajiyar zuciya ta sake kallon Omar da ba ita yake kallo ba har lokacin amma ta tabbatar yana jin duk abinda ake faWa, ta ce, "Narma addu'a zaki dinga yi itace maganar damuwarki, Allah ya kawo mafita ya yaye miki abinda yake damunki. Kin san duk abinda ya faru ba sai na faWa miki ba, auren ki da Omar bazai yu ba, kafin ma aje ga maganar aure tarayyar ku ma baza taSa yuwa ba. Tun farko na faWa miki amma baki fahimta ba, yanzu gashi komai ya lalace. Kar ki sare ki ta addu'a, in kina da rabon auren sarabon zai kira ki a lokacin da zaki amsa bama ki san kin amsa ba."

Narma tayi murmushi ta ce, "haka nake ji a jikina Didi, jikina yana bani zan zama matarsa in sha Allah" sai muryarta ta fara rawa ta ce, "basu san wahalar da na sha kafin na samu ya saurare ni ba, na samu kansa da?yar amma Dad ya lalata komai bayan ya yi min alqawarin bani duk abinda nake so."

"Ki yi hakuri" Didi ta faWa a sanyaye cikin tausayinta. Narma tayi murmushin ya?e ta ce, "babu komai Didi. Ya Faruk ya dawo gida? Ina fatan Lafiya?. Na Kira shi yafi a irga baya Waukar wayata, Ina so naji lafiya ya dawo amma laifin su Dad ya shafe ni. Ni me nayi masa Didi? Ban cancanci ya saurare ni ba?."

Jin ta fara kuka sai Didi ta tausasa murya ta ce, "Ba haka bane ba Narma, yana ?o?arin kiyaye abinda iyayenki suka ce ne shiyasa, amma ba wai dan yana ganin laifinki ba."
"To ko sau Waya ya Wauki wayata ya yi min magana, na kira shi sau babu adadi amma baya Wauka kuma san ya san ni ce. In ba laifina yake gani ba meyasa bazai Wauka ba? Meyasa bazai saurare ni ba?."

Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "ha?uri dai zan ce ki yi Narma, ki ta addu'a." Narma tayi ajiyar zuciya ta ce, "shikenan Didi zan yi. Ya dawo lafiya?." Sai ta sake bata tausayi matu?a a sanyaye ta ta ce, "ya dawo lafiya lau Narma."
"Don Allah ki gaishe min da shi in yazo, sannan ki ro?ar min shi ko sau Waya ne ya amsa kiran wayata, Ina cikin tsananin azaba da raWaWin zuciya, ni kaWai na san abinda nake ji a zuciyata Didi, ni kaWai na san zafin da zuciayata take min akan rashinsa. Ko sau Waya ne ya Wauki wayata Didi zan ji daWin hakan, koda bazai yi min magana ba saukar numfashinsa ya ishe ni."

Didi gabaWaya jikinta ya gama yin sanyi ta sake kallon Omar har lokacin ba ita yake kallo ba amma shi kansa ta san yaji a jikinsa. Ta ce, "zan faWa masa in sha Allah, ki cigaba da addu'a kin ji?."
"Zan yi in sha Allah. Sai anjima" ta faWa tana yanke wayar Didi ta ajjiye wayar a gefe tana sauke numfashi.

Shiru bai ce komai ba itama bata ce ba, tausayin Narma ya gama mamaye mata zuciya, in ba soyayya ba wai Narma ce take wannan kalamai akan Omar Winta, in banda soyayya ina ruwan biri da gada? In ban da soyayya mai ya kai akuya gaida kura har raminta?. Kallon sa ta yi ta ce, "Omar Narma tana sonka, Allah sarki kaWai ya san azabar da zuciyar take yi mata. Kaima na san kana sonta har yanzu, bamu san abinda Allah ya Soye ba baza mu yanke hukunci ba."

Kulle ido ya yi ya buWe cikin mutuwar jiki amma ya dake bai nunwa Didi ba ya kalle ta? ya ce, "babu wanda ya san abinda Allah ya Soye kam, amma bana tunanin aure ta gaskiya. Ke kin san in na wuce bana dawowa."

"Daman bai kamata ka yi wannan tunanin ba duba da abinda ya faru, amma in Allah ya rubuta ?addara babu wanda ya isa ya canja ta." Ajiyar zuciya ya yi ya kalle ta ya ce, "shagon aikin takalmi nake so zan buWd" ya faWa dan kawar da zancen Narma kar ta saka jikinsa ya yi sanyi saboda tausayinta.

Didi a sanyaye ta ce, "Da gaske?."
"Da gaske nake, Ina tattara kuWin ne saboda hidimar aurenki da kuma buWe shagon. Amma a yanzu haka fitar da nayi akwai wani machine na aikin takalmin dana bayar za a siyo mana shi daga lagos. Bana so abin ya Wauki lokaci ne da wuri nake so a fara in sha Allah." Didi tayi murmushi ta ce, "Allah ya tabbatar da alkhairi, Allah ya sa albarka a neman da za a fara."
"Amin."
"Amma Omar ba da kuWin ?an siyasar nan zaka gina halak Winka ba ko?." Ya kalle ta ya ce, "ban gane ba."

Didi ta ce, "Ina magana akan kuWin da irin su Senator suke baku dan a zubar da jini a wajan zaSe ko a tayar da hayaniya, ba dasu zaka fara sana'ar ba ko?." Ya zuba mata ido yana kallon ta kana ya ce, "Didi daman an taSa biyana na kashe wani ne ko na zubar masa da jini?." Ganin yadda ya kafe ta da ido yana kallo sai ta ji daWi a ranta, hakan da ya yi ya bata tabbacin ba irin kuWin da take tunani bane, kallon da yake mata kuma na rashin jin daWin maganar ta ne.

Didi ta ce, "Ni ban ce an taSa baka ba, kawai ina nusar da kai da ka gina halak Win ka da tsarkakan kuWi, kar ka gina halak da kuWin haram babu abinda zaka Wauka a ciki." Ya ce, "ki daina yi min wannan tunanin bana jin daWi, na san abinda nake yi. Ba a taSa bani kuWi dan na cutar da wani na karSa ba, ko shi Senator ki je ki tambaye shi ban taSa karSar aikin tayar da hayaniya bama balle kisan kai. Tunda na wuce lokacin da nake ji da iskancina? ban yi kisa ba bana tunanin akwai wata halitta da zata iya biyana dan na kashe rai. Ki daina min irin haka ban so."

Didi ta yi murmushi ta ce, "To Allah ya baka ha?uri."
"Da ha?urin ya mutu sadakar nawa ki ka bayar?" Ya faWa yana harararta alamun ya ji haushi. Didi ta yi dariya ta ce, "Tunda dai na bada ha?uri ai sai ya wuce ba sai an faWa min magana ba."

Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "Ya kamata a fara siyayyar kayan aurenki ko?."
"Eh haka ne, lokaci yana ta zuwa kamar wasa. Zan sanar da kai abubuwa da ya kamata." Kai ya Waga kawai bai ce komai ba yana kallon wani wajan daban. Tashi ya yi ya fita ita kuma a gaggauce ta gama abinda zata yi ta fita zuwa gidan Hajja.

Hajja tana ganinta ta fara murmushi ta ce, "Aisha ke ce tafe?."
"Hajja ni ce, Ina tare da labari mai daWi da nake so na faWa miki." Hajja ta ce, "Ina jinki."
"Hajja Omar dai ya fara nutsuwa, Omar ne jiya yake yi min zancen na faWa masa duk abinda yake yi mara kyau zai daina. Na faWa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login