Showing 15001 words to 18000 words out of 85380 words

Chapter 6 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3836

ta kusa aure babu labari. Murmushi tayi kawai bata ce komai ba kafin ta ce,  Yau baki yi abincin sadaka bane?. Didi ta ce,  bani da lafiyar yi ne, da Omar ma yana nan sai ya yi ni bani da wannan ?arfin gabaWaya tana faWar haka sai hawaye ya sakko mata.

Nayla daman zancen Omar Win take so ayi sai ta ce,  Didi meye na kuka?. Didi ta ce,  Nayla baki san an kama Omar ba?. Nayla tayi ajiyar zuciya ta kalli Salma kafin ta kalli Didi ta ce,  Salma ta bani labari.
 To na je har Abuja naga halin da yake ciki Nayla, Omar yana cikin wahala da azabtarwa, dauriya da rashin son sani a damuwa ne ya saka shi ya dake har yake yi min magana kamar ko yaushe. Suna cutar min da Omar kawai dan suna ta?ama da mulki baza a iya ja dasu ba, in ba dan haka ba meye laifin Omar? Me ya yi da za a kama shi a Waure ba tare da ya yi laifin komai ba?. Laifin Omar Waya da yaje gidan, amma da ya je ai ba kisan kai ya je yi ba, ba kuma wani laifi ya aikata musu ba. Kawai saboda bai kai matsayin da suke kai ba, a gare su ?as?anci ne ?arsu ta so Omar. Yanzu zancen asiri suke yi, sun ce asiri ya yi mata take sonsa, ko nazo na karya asirin ko kuma bazan sake ganinsa ba har abada!& ..Kashe Omar suke son yi, kashe shi suke son yi kawai! Ta faWa da rauni tana hawaye mai taSa zuciya.

Nayla kuka take yi sosai wanda ya bawa kowa mamaki, sun santa da tausayi sosai kuma tsaf labarin zai iya saka ta kuka. Amma yadda take kuka da zuciyarta da gangar jikinta zaka tabbatar da ba iya kukan tausayi take yi ba akwai wani abun a cikin zuciyarta. Hajja a sanyaye ta ce,  Aisha na ce ki yi ha?uri komai zai zo ?arshe in sha Allah. Didi ta ce,  Hajja wallahi mahaifiyar Narma so take a kashe Omaar, yanayin kalamanta kashe shi suke son yi kawai. Sun san in sun kashe shi sun kashe banza tunda bashi da gata, bashi da wani gatan da za a neme shi shiyasa.

Hajja ta ce,  su Baba Adamu dasu Kawu duk babu wanda zai samu hanyar magana da Sanata?. Didi ta ce,  Tunda har Daddyn Salma bai samu ba bana tunanin zasu samu. Kuma ni ko faWa musu ma ban yi ba, ban saba kai damuwata gare su ba na saba ni da Omaar mu ke warware ko meye in ya tunkaro mu. Ban sani ba ko sun ji a gari amma ni ban sanar musu da komai ba. Hajja ta ce,  ai ya kamata ace sun sani Aisha, iyayen Omar ne fa, ya kamata a sanar dasu ko da addu a su taya mu.

Didi ta ce,  Hajja yanzu bana cikin wannan nutsuwar, hankalina baya jikina wallahi.

Nayla dai kuka take yi har sautin nata kukan yafi na Didi fita, Didi ta kalle ta cikin rauni tace,  ki bar Kuka Nayla, ni ban faWa miki dan ki yi kuka ba. Ki share hawayenki. Nayla ta kalli Didi cikin muryar kuka ta ce,  Didi ki yi ha?uri in sha Allah zan yi ko meye ganin na dawo dashi, zan yi duk abinda zanyi dan ganin ya bar hannunsu.

Didi ta murmusa cikin tsokana da son kawar da damuwa ta ce,  na Wauka zaki barshi a can kawai, kin manta tsorataki yake yi?. Nayla bata yi murmushi ba sai ma hawayen da ya sake sakkowa daga idonta ta ce,  Didi ba maganar wasa nake yi ba, zan yi ko meye ganin na dawo da shi.

Didi tayi murmushi ta ce,  to Nayla. Na gode sosai Allah ya bar zumunci. Idanu Nayla ta goge ta kulle idanun nata, ita kaWai ta san raWaWin da take ji akan rashin Omar, ita kaWai ta san azabar da zuciyarta take mata akan Omar. Dole ta san abinda zata yi ta fito da Omar, ko meye shi kuwa zata aikata in dai zai dawo. Zata iya sadaukar da komai dan Omar ya dawo, zata iya rasa komai indai Omar zai fito ta amince.

Ganin tayi shiru sai kowa ya yi shiru Salma da Jidda dai kallon Nayla kawai suke yi cikin tuhuma. Nayla sai ta mi?e ta shiga Waki tayi alwala tayi sallar azahar kafin ta dawo falon. Abinci ta tarar suna ci, Hajja ta kalle ta tace,  baza ki ci abincin ba?. Nayla ta ce,  bana jin yunwa, kaina ciwo yake yi. Jidda ta ce,  dole kan ki ya yi ciwo, kin zo daga Kaduna ko hutawa baki yi ba kina taho nan, ga kukan da ki ka yi gashi ko abinci baki ci ba, ai dole ki yi ciwon kai. Hajja ta ce,  Hauwa u me yasa haka?.

Kallon Jidda ta yi tace,  Twiny mu je gida ta faWa tana Waukar mayafinta da yake wajan. Jidda ta ce,  ki ka ce sai anjima zamu tafi.
 Na fasa, mu tafi yanzu. Salma zaki je bikin ko baza ki ba?.
 Zan je mana. Nayla ta ce,  ku zo mu tafi, Hajja sai gobe abinda ta ce kenan ta fita da hanzari bayan ta Wauki key Win motar Jidda ta fita dashi.

A mazaunin driver ta zauna ganin haka sai suka shiga motar ta ja motar da ?arfin gaske suka tafi. Gudu take yi sosai ga yanayin gari na juma a a cushe garin yake da mutane amma haka take gudu kamar zasu bar gari burinta kawai ta je gida. Jidda da take a zaune a gaba ta kalle ta ta ce,  Twiny wai lafiyar ki kuwa? Wannan gudun da ki ke yi na meye?.

Bata yi magana ba Salma da take baya ta ce,  malama magana ake miki ki rage gudu Ina zamu je? Sai gudu ki ke yi kamar zaki tashi sama. Daidai nan suka ?araso gate Win gidan ta dinga danna horn dashi ?arfi, mai gadi ya buWe da gaggawa ta shiga da motar ganin motar Abiy tana nan ko parking daidai bata yi ba ta fita daga motar da sauri.

Jidda ta kalli Salma ta ce,  lafiyar ta kuwa?. Salma tayi tsaki ta ce,  ?iris ya rage bata saka mun ba?unci lahira ba, ko aure ban yi ba zata kashe ni. Jidda tayi dariya suka shiga cikin gidan.

A zaune suka same ta a gaban Abiy da yake waya suma suka zauna saboda ya kammala. Kashe wayar ya yi ya kalli Nayla ya ce, "Mamana lafiya ki ke kuwa? Meye ya same ki haka fuskarki tayi ja haka?." Nayla ta ce, "Abiy ai ka san Didi ko?." Abiy ya ce, "Wacece Didi kuma?."
"Ma?ociyar Hajja Yayar...." Kafin ta ?arasa ya ce, "Oh Yayar Wan daban nan ko? Na gane ta, da Aisha na santa ni ba wani Didi ba. Mutuwa tayi?."

Nayla gaban taya buga dum jin da sunan da Abiy ya kira Omar dashi, amma bata nuna ba ta ce, "da ranta." Abiy ya ce, "to lafiya ki ka shigo a firgice haka?." Jidda ta ce, "Haka ta dinga gudu damu a titi Abiy, gari ya cushe mutane an dawo daga masallacin juma'a amma bata daina ba, ?iris ya rage bamu yi hatsari ba." Abiy ya kalli Jidda ya ce, "Wai daman ba Jawad ne ya shigo da mota a guje ba itace?."
"Wallahi itace" ta bashi amsa tana kallon Nayla.

Ya kalli Nayla a nutse ya ce, "Me ya faru haka?." Nayla ta ce, "Tausayin Didi nake ji Abiy, an kama mata ?aninta sai kuka take yi har da zazzaSi. Don Allah Abiy ka taimaka a fito dashi don Allah." Abiy ya bita da kallo cikim mamaki ya ce, "akan wannan ne kika kusa kashe kanki da ?an uwanki?."

"Na kasa sarrafa kaina ne kawai Abiy, bana jin daWi a zuciyata, Didi tana sona, nima ina son abinda take so." Abiy ya kalle ta a nutse ya ce, "mun yi maganar da Hajja jiya sai dai ba a bani labari duka ba aka kira ni a waya. Waye ya saka aka kama shi Win sannan me ya yi?."

Shiru tayi bata amsa ba ya ce, "ke nake saurare, me ya yi aka kama shi har kike so na fito dashi?. Ko wani ya kashe?." Ta girgiza kai alamun a a ya ce, "to faWi." Nayla ta ce, "Dama ya je gidan Sen Sagir Sani ne, shine ya saka aka kama shi."
"Me ya je yi gidan? Sata ko kuma kisan kai?." Salma ce ta bawa Abiy labarin abinda ya faru kaf har zuwan Didi wajansa. Abiy ya girgiza kai cikin mamakin ?arfin halin Omar ya ce, "Barr Narma ya je yace yana so? Kuma yana da hankali?." Salma ta ce, "gashi nan dai akwai Abiy."

Abiy ya ce, "gaskiya dai gashi nan dai kawai, dan in har yana da hankali to tabbas shaye-shayen su na Sata gari ya taSa masa ?wa?walwa. In ba haka ba ya Wauki ?afa ya je ya ce yana son ?ar Sen Sagir? Ya san waye Sen Sagir kuwa?." Suka yi shiru Abiy ya ce, "To ai ko zauna gari banza wanda bashi da komai ya je ya ce masa yana son ?arsa dole ya Wauki mataki balle Sen. Kuma dole ya ce asiri ya yiwa mata take sonsa. Meye abin so a tare dashi har da zata fita hankalinta haka?." Nayla dai wani irin sanyi jikinta ya yi da jin kalaman Abiy, zuciyarta na bugawa, guiwarta kamar ana dukanta saboda sagewar da tayi.

Abiy ya numfasa ya ce, "well, ya taimaki Nayla a lokacin da take bu?atar taimako, ya kuSutar da ita daga masu sharrin fyaWe. Ya cancanci na taimaka masa a fito dashi tunda ba wani laifi ya aikata ba. Na san Sen Sagir sosai, abokina ne sosai tare muka yi ABU Zaria. Kuma ni ne class captain a lokacin, bara mu ga" ya faWa yana Waukar waya yana dubawa.

A speaker Abiy ya saka kiran daga can Sangaren Sen yana Wauka ya ce, "Class Captain....!." Abiy ya murmusa ya ce,  ni Wauka baka da number ta ai. Sen yayi dariya ya ce,  Haba ni na isa nace bani da number ka?.
 Ka isa mana Sem, ai ka kai matsayin da ba number kowa zaka ajiiye ba.
 Ai kai kana cikin mutane na farko a wayata. Abiy yayi murmushi suka gaisa cikin wasa da dariya na ?an makaranta kafin Abiy ya ce,  kwanaki nazo Abuja na karSi offer ta ?ar wajena Nayla, naso nazo wajan ka sai kuma na sha afa wallahi.

Sanata ya ce,  gaskiya baka kyauta ba, duk da dai nima kwanaki na shiga Zaria naso na kira ka wallahi dare ya yi min. 
 Haka ne, komai sai Allah ya yi.
 A wacce ma aikata ta samu aikin?.
 FIRS.
 Haba Captain, me zata yi da wannan ?aramin aikin da salary sa bai wuce 400k per month ba? Ga aiki a nan Abuja da zata samu kuWi me zata yi da 400k kamar wata almajira?. Abiy ya yi dariya kafin ya yi magana Sen ya ce,  ka turo ta Abuja akwai aikin da zan bata, 900k ne per month banda allowances da suke shigowa. Shima dai tayi manage kawai.

Abiy ya yi dariya ya ce,  Senator! Ai ba dan salary take aiki ba, hakan burinta ne shiyasa kawai na bari tana yi. Sen ya ce,  Sai ta cika burinta da abu mai kyau ba wannan ba, ka rasa aikin da zaka bata sai wannan ?aramin aikin? Me zata yi da kuWin da bai wuce albashin house maids Win gidansu ba?& Ka turo min ita kawai, zan cika mata burinta da aiki mai kyau, in kana tunanin baka so ta zauna ita kaWai a guest house sai ta zauna a gidana wajan Narma da Najwa.

Abiy ya ce,  A a, barta a Kaduna kusa dani ya fi. Nayla me zata yi da kuWi tana yarinya ?arama?. Tana da shop fa. Senator ya yi dariya ya ce,  Najwa ba ma Narma ko Nabil ba, itace take kula da Sangare guda na companyna, kuma tana aiki sannan itama tana da shops. Ai yaran yanzu sai da kuWi Captain, haka duniyar ta zama.

Abiy ya ce,  kana Abuja ne?. Sen ya ce,  A a ina Kano, nazo Waurin aure ?ar sarkin Kano da za a yi gobe. Abiy ya ce,  nima Ina Kano Win, gobe zan kuma shiga Waurin auren in sha Allah. Sen ya ce,  to ya kamata mu haWu gabaWayan mu, dan yawancin ?an class Winmu duk suna nan goben. Abiy ya ce,  Allah ya kaimu goben, sai mu haWu gabaWaya yi zumunci a samu lada. Sen ya amsa yana dariya kafin su yi sallama Abiy ya kashe wayar.

Kallon Nayla ya yi da ta sunkuyar da kai ya ce,  Gobe zan yi masa maganar Omar Win, in sha Allah zai dawo. Nayla farin ciki take ji a zuciyarta har hakan ya bayyana akan fuskarta, ta ce,  to Abiy na gode. Abiy ya kalle ta a nutse ya ce,  ga murmushi nan kina yi, da alama dai shima kina shiri dashi sosai ko? Ya tambaya da niyar bugun cikinta.

Sunkuyar da kai tayi ta ce,  A a Abiy, ko magana bamu taSa yi ba, ni saboda Yayarsa kawai nake so ya fito. Abiy ya girgiza kai ya ce,  ko dan taimaka miki da ya yi a shekarun baya ai ya cancanci ki so ya fito. Kar ki damu komai ya ?are. Nayla ta yi dariya tana kallon Mama da ta zuba mata ido tana kallon ta.

Da sauri ta tashi ta shiga Waki Salma da Jidda suka bita. Murmushi suka samu tana yi a bayyane tana cewa,  zan zama silar fitowar Omar in sha Allah, in sha Allah zai fito. Wayyo daWi, Allah na gode maka. Jidda ta kalli Salma da suke kallon Nayla da mamaki, Jidda ta girgiza kai tana gasgata abinda take zargi a zuciyarta. Jidda ta ce,  Twiny ko dai Omar shine wanda ki ke so?!.
KRB2P006
Arewabooks@nanahaleema11.

Nayla gabanta ya faWi sosai, ta jiyo a firgice tana kallon su dan tambayar tazo mata babu zato babu tsammani. Duk sun tsare ta da ido suna jira su ji abinda zata ce. Kallon kallo ake a tsakanin ta su, suna jiran amsarta ita kuma duk ta firgice. Salma ta ce, "tambayar ki mu ke yi Nayla, Omar ?anin Didi shine wanda ki ke so Win?." Tayi ?o?arin dakewa da son Soye damuwarta ta ce, "Wacce irin magana ce wannnan? Ni ba haka bane ba."

Jidda ta ce, "to meyasa muryarki take cracking? Meyasa ki ka ji tsoron tambayar da muka yi miki?. Sannan meyasa hankalinki ya tashi a kan ance yana cikin wahala?, gudu kika dinga yi da mota sai da kika zo ki ka samu Abiy sannan hankalinki ya kwanta. Ki faWa mana shine wanda ki ke so Win?. Duk alamomin soyayya ya bayyana a yanayin ki, yadda ki ka za?e a kansa ya saka muna zargin shine wanda soyayyarsa take wahalar dake, ki amsa mana Nayla."

"Eh shine!" Ta faWa a sanyaye tana zubewa a kan gado tana sake fashewa da kuka. A tare suka wara idanu Jidda ta ?arasa inda Nayla take dan Salma tayi suman tsaye. Jidda ta zauna kusa ta da ita ta ce, "Twiny da gaske shi ki ke so?." Kai ta Waga tana kuka ta ce, "Shine Twiny. Ban san ya akayi hakan ta faru ba, na san dai tsoronsa nake ji amma ban ya akayi na fara sonsa ba. Nayi kuka, na yi addu'a amma na kasa cire shi daga zuciyata. Bai san ina yi ba, tunda shi Abuja ya je neman aure a gidan su wata bani ba, amma duk da haka bana jin haushinsa Twiny."

A kan kafaWar Jidda ta Wora kanta tana kuka sosai Jidda tana shafa kanta dan bata san ne zata ce mata ba. Salma da?yar ta iya motsawa tazo wajan da suke ta zauna a Waya gefen ya zama sun saka Nayla a tsakiya kenan. Salma ta ce, "Nayla wai Omar Win Didi ki ke so?."

Bata iya bata amsa ba sai numfashi da take saukewa a jikin Jidda. Salma ta ce, "Innalillahi! Mun shiga uku." Nayla ta Wago daga jikin Jidda idanunta sun ji?e da hawaye ta ce, "shiyasa na?i faWa muku saboda faWar babu amfani Salma. Babu ribar da zan samu da soyayyarsa, wahalar da ni kawai take yi wata?ila tayi ajalina. Wallahi duk samarin da Abiy yake basu damar ganina na kasa kallon kowa da fuskar so, shi kaWai nake so, shi kaWai zuciyata take da burin aure, shi kaWai nake ji a raina in ban aura ba kamar bazan iya zaman aure da kowa ba, na kuma san bazan taSa mallakarsa ba har abada."

Jidda a sanyaye ta ce, "Meyasa ki ka ce haka?." Tayi murmushi ta ce, "baki ji me Abiy ya ce bane? Ko zauna gari banza yaje yace yana neman aure a gidansa baza a bashi ba balle gidan Sen. Dame Sen ya fi Abiy Twiny? Mulki kawai ya fi Abiy, amma duk abinda ya mallaka a duniya Abiy ma ya mallaka. Kinga kenan harda gidan mu a cikin gidajen da baza'a bashi aure ba, ni daman na san aurena dashi bazai yu ba shiyasa ban sakawa zuciyata zan aure shi ba. Kuma shi bai ma san ina sonsa ba."

Salma tayi ajiyar zuciya ta ce, "gaskiya ne zancen ki Nayla, auren Omar bana hango yuwarsa a rayuwarki. Gwara mu faWa miki gaskiya kar mu cuce ki mu yaudari zuciyarki da kalamai na ?arya dan mu kwantar miki da hankali. Omar ba irin wanda ya cancanci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login