Showing 39001 words to 42000 words out of 85380 words

Chapter 14 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3846

mata wani ba shi ba. Tuna hakan ne yake sakawa ta ?ara ?arfin kukanta cike da ?unar zuciya. Rarrashinta suka dinga yi amma ta?i ta daina sai kawai Dad ya kira Ashraf ya ce ya hayo saman, yana shigowa saman ya samu tana wannan kukan duk sai jikinsa ya yi sanyi.

Dad ya kalle shi ya ce, "ka rarrasheta" abinda ya ce kenan suka bar musu wajan shi da Mum. Ashraf a hankali ya taka zuwa inda take ya Wagota daga kan kujerar ya haWata da jikinsa ya rungumeta tsamtsam yana shafa fatar bayanta a hankali kasancewar rigar bayanta a buWe yake. A kunne yake raWa mata yana cewa, "Shiii! relax my wife, i'm here for you, stop craying."

Kuka take yi sosai a jikinsa shi kuma ya matse ta ya hanata koda motsin kirki sai kukan da take yi. "Ki bar kuka my wife Ina tare dake a ko yaushe, bana so ki dinga zubar da hawayenki. Ina sonki zan zauna dake a ko wanne yanayi ki ke, don't be nervous about this early marriage. I'll take care of you, i promise i'll always be there for you and make you happy. I love you so much my love, I love you! I love you! you're my heart, you're my life, you're my world. Stop crying, please..." a kunne yake raWa mata cikin salo mai Waukar hankali da son rarrashi yana sake hura mata iska a cikin kunnenta tare da sake matse ta a jikinsa.

Narma duk tana jinsa amma bata daina zubar hawaye ba, imagination take yi wannan kalaman da yake faWa mata ace Faruk Win tane yake faWa mata da bata san farin cikin da zata yi ba, hango kanta take a rungume a jikinsa ya matse ta yana faWa mata wannan kalaman. Nan take tsigar jikinta tashi ta runtse ido zuciyarta na bala'in bugawa har shi Ashraf yana jin bugun zuciyar a jikinsa.

Ido a kulle tana daga jikinsa ta ce, "I love him, I love Faruk. Dashi nake so nayi rayuwa, shi nake so na aura. Bana son zama da kai, dashi nake so na zauna......!" ta furta cikin wata irin murya mai nuni da raunin da yake tare da ita. Maimakon ya ji haushin kalamanta sai ya zaunar da ita akan kujera ya zauna a gefenta ya ri?e hannunta ya ce, "ina jin irin abinda ki ke ji, komai zai wuce na tabbatar da kina sona soyayyata zata dawo a cikin zuciyarki. Ina so kawai ki nutsu ki bani dama zan saka ki manta dashi a cikin rayuwarki gabaWaya."

"Bazan taSa mantawa dashi ba, shi nake so ba kai ba, shi nake so na aura ba kai ba, dan haka ka ?yale ni" ta faWa tana mi?ewa da sauri ta shiga Waki tare da kulle ?ofa ta saka key. Bai yi ?o?arin binta ba sai ma murmushi da yake yi, tunda dai an aura masa ita koma me zata yi daga baya ne.

Narma tana shiga a kan gado ta zube tana sake fashewa da kuka mai tsuma zuciya, lokaci Waya kanta yayi nauyi sosai saboda ciwo idanunta suka tasa saboda kuka. Sai da tayi kukan mai isarta sannan ta tashi zaune tana sauke ajiyar zuciya. A sanyaye ta Wauki waya ta nemo number Omar da tayi saving da my Faruk ta kira. Bata da tabbacin zai Wauka ko bazai Wauka ba, ta yi shiru tana jiran tsammani.

?it taji ta katse alamun bai Wauka ba ta ajjiye wayar a gefe tana kallon sunansa cikin bahagon yanayi. Kamar a mafarki sai ga kiransa na shigowa ta zabura ta Wauki wayar hannu yana rawa ta kai kunnenta. Kafin ya yi magana ta ce, "Hello...hello...my Faruk kaine ka kira ni?......Wayyo Allah! yau ya kira ni, Allah na gode maka. My Faruk Ina kewar ka Ina so na ganka..." abinda take faWa kenan a ruWe kana ji kasan bata cikin yanayi mai daWi.

Omar da yake jinta bai ce komai ba ta sake cewa, "My Faruk su Dad suna son kashe ni, wai sun Waura min aure da wani ba kai ba, mutuwa kawai zan yi....!" Ta faWa cikin kuka mai ban tausayi. Omar ya lumshe idanu jin abinda ta ce, maganar tayi masa daWi kuma bata yi masa daWi ba. ?angare Waya yaji daWin aurenta kodan ta daina takura masa ta daina damun kanta a kansa ta san ita matar aure ce. ?angare Waya kuma bai ji daWi ba saboda tausayinta, ya san tana sonsa, aura mata wani a wannan yanayi bazai mata daWi ba.

Narma ta ce, "ni da kai nake so na rayu, bazan iya rayuwa da kowa ba sai kai. Don Allah ka amince nazo na zauna da kai, ni kai kaWai nake so nayi zaman aure dashi ba wani ba. In na zauna da Ashraf mutuwa zanyi! Bana sonsa, kai nake so da kai zan rayu......!"

"Narma! Ki nutsu" ya furta a hankali cikin murya mai taushi. Numfashi taja kamar ya saka mata pause ta dakata da kukan sai ajiyar zuciya da take yi. Ya sake cewa, "Kin ce an Waura miki aure ko?." Kamar tana gabansa ta Waga kai ta ce, "eh, amma bana sonsa, ni kai...." Dakatar da ita ya yi ta hanyar cewa, "Matar aure ce ke, furta kina son wani ba mijinki ba babban laifi ne. Kina jina?."
"Ina ji" ta faWa murya na rawa sosai.
"Waye ni a wajanki?."
"Wanda nake matu?ar so, wanda nake so na rayu dashi har a aljanna."
"Na isa nace ki yi abu ki yi? Na isa na ce ki bari ki bari?."

Narma ta ce, "har ka yi yawa ma Faruk! Har ka yi yawa wallahi. Zan iya sadaukar maka da raina da rayuwata." Ya Wan yi jimm kafin ya ce, "to ki ri?e aurenki, ki yi abinda iyayenki suke so ki zauna da mijinki..." Katse shi ta yi ta ce, "Amma bana sonsa, bana ?aunarsa ta ya zan iya zama dashi?."

Omar ya ce, "ki koya, ki koyi sonsa zaki iya. Ina faWa miki gaskiya matsayina na Yayanki, in na ce miki Ina kallon ki matsayin wacce nazo gidan ku a matsayin mai sonki a yanzu ?arya nake miki, gwara na faWa miki gaskiya ki ri?e aurenki ki daina tunanina a cikin rayuwarki. Narma Allah bai rubuta ni da ke zamu zauna a inuwa Waya matsayin ma'aurata ba, ki karSi Waddara hannu biyu Allah ne ya tsara ba ni ko ke ba. Iyayenki da kike gani kamar basu kyauta miki ba ba laifin su bane, babu ni a cikin rabon ki Narma, babu ni a cikin ?addararki saboda haka ki kwantar da hankalinki yi fuskanci rayuwa."

Narma hawaye take yi, ta san gaskiya yake faWa mata amma zuciyar baza ta iya Waukar kalamansa ba, zuciyarta bugawa take yi sosai ta runtse ido tana jin kalamansa kamar saukar ruwan zafi a zuciyarta, ta wani Sangaren kamar saukar ruwan sanyi a zuciyarta.

"Wata?ila akwai Omar a ciki rayuwarki ta gaba, wata?la babu. Ni dake babu wanda ya isa ya amsa kiran rabon da ba na shi ba. Dan haka ki nutsu, ki ri?e aurenki ki daina tunawa da kin san mai suna Omar a rayuwarki. Ina yi miki fatan alkhairi da fatan samun rayuwa mai albarka" ya sake faWa cikin taushin murya wacce take ratsa zuciyar Narma.

Kai take girgizawa tana hawaye ta ce, "A'a Faruk, kar kace haka don Allah, bazan iya rayuwa babu kai ba, Ina sonka, ina son rayuwa dakai. Na san kaina kana jin abinda nake ji, ka amince min kawai nazo na rayu dakai ta ko wanne hali."
"Matar aure ce ke, Zancen na amince dake bai tashi ba. Kuma ni babu abinda nake ji a kanki kema ki daina ji a kaina, Ki manta dani ki kalli rayuwar aurenki zai fi miki kwanciyar hankali. Indai da gaske zan saka ki abu ki yi kamar yadda kika ce to ki ri?e aurenki, ki kuma manta dani!."

Jin tana kuka mai sauti ya saka Omar ya ce, "Ina yi miki fatan alkhairi, sai anjima" yana faWa ya yanke wayar ta kifa kai akan wayar tana kuka sosai. Sai da ta gaji da kanta sannan ta dakata, kanta ya ri?e sosai saboda kuka ta koma sauke ajiyar zuciya. Bata san haka soyayya take ba, bata san haka ake ji a soyayya ba, bata san haka azaba da raWaWin soyayya yake ba da bata yi gangancin fara son Omar ba. Numfashi take saukewa a hankali a hankali cikin rashin sanin abinda zata yi.
KRB2P015
Arewabooks@nanahaleema11.

Tana ji ana buga ?ofar bata buWe ba sai daga baya ta tashi ta buWe, Najwa ta gani ta kalleta ta ce, "Ya ki shirya before magrib zaku wuce." Rungume Najwa tayi tana cewa, "Bana so Najwa! Bana son Ashraf, Ni Faruk nake so!. Ya zanyi? Ya ake so nayi da raina?." Najwa hawaye ya cika mata ido amma bata yi ba ta ce, "ki yi ha?uri." Ajiyar zuciya take yi a hankali kukan ma ya daina zuwa idanunta sai kanta da ya yi nauyi sosai.

Idanu a kulle ta ce, "Nayi magana da Faruk, ya ce wai na ri?e aurena na manta dashi. Hmmm ki ji fa Najwa, taya zan iya mantawa dashi? Shi ne wanda naso kuma nake so har yanzu. Ya kasa gane irin yadda nake ji a kansa." Najwa ta ce, "Gaskiya ya faWa miki Ya Narma, mantawa dashi Win shine yafi alkhairi a gare ki da kuma shi kansa. Yanzu kina da aure ya zama dole ki manta dashi, addu'a zaki dinga yi a hankali komai zai wuce." Bata ce komai ba ta bar jikin Najwa ta koma ta zauna a gefen ta dafe kanta.

Najwa da kanta ta jawo trolly bag ya fara haWa mata kaya a ciki. Komai da ta san zata yi amfani dashi ta zuba tayi zipping bag Winta ta ajjiye ta fita. Bayan sallar la'asar Najwa ta sake dawowa ta tarar ta idar da sallah kalle ta ta ce, "Ya Narma ki tashi ki shirya." Kallon Najwa tayi kamar zata yi magana sai bata ce komai ba, kalaman Omar ne suke yi mata yawo a zuciyarta. Mum da Dad suka shigo Wakin a tare, Dad ya kalle Narma a tausashe ya ce, "Daughter ki tashi ki shirya zaku wuce America." Kallon Dad tayi da idanu ta da suke a kumbure ta ce, "Dad ka san bana sonsa ka ce na bishi ko?."

Dad ya ce, "Narma mun gama wanna maganar dake, kar ki sake dawo da ita please. Ni na haife ki fa Narma, bazan taSa yin abinda zai cutar da rayuwarki ba. Duk duniya babu wanda ya kai ni sonki, Ina sonki, Ina son inganta miki rayuwarki. Kar ki dinga kawo tunani mara kyau a zuciyarki na tabbatar da komai zai wuce nan da lokaci kaWan." Narma tayi ajiyar zuciya ta ce, "Yanzu me zanyi?." Mum ta ce, "ki tashi ki shirya zaku wuce." Narma ta mi?e tsaye ta ce, "To zan yi, Tunda kun yi min auren dole zan tafi. Shima haka Faruk Wina ya ce, ya ce kar na sake kiransa, na manta dashi wai ni matar aure ce" ta kalle su ta ce, "tambaya ta yake yi indai Ina sonsa nayi abinda ya ce. Tunda haka yake so kuma haka yake so zan yi" ta faWa a sanyaye.

Tausayi ta bawa Najwa ta kawar da kai bata son yin kuka a gabanta. Duk sun ji me ta ce Mum ta kalli Dad ya Wauke kai Narma ta shiga banWaki.

Mum ta kalle shi ta ce, "bai daina bibiyar min yarinya ba kenan ko?." Najwa ta ce, "Ya Narma itace take bibiyarsa, ko a yanzun ma itace ta kira shi kuma tayi sa'a ya Wauka dan baya Waukar wayarta. Gwara ma da ta kira shi Win ai, ba dan ya ce taje Win ba da baza ta tafi ba" Najwa ta faWa tana fita daga Wakin. Mum ta kalle Dad ta ce, "kaga tabbacin asiri ya yiwa Narma ko? Kana Waukar maganar nan wasa, Ina faWa maka abinda ya kamata a yi kana mayar dashi wasa ko Dear?. Shikenan" ta faWa tana ficewa daga Wakin.

Narma duk tana jinsu tana daga banWaki a haka tayi wanka ta fito ta shirya cikin riga da wando. Rigar tana da tasho har guiwar ta Wauki Jessy veil ta naWa a kanta ta zauna a gefen bata ce komai ba. Najwa ce ta shigo ta kalle ta ta ce, "Ya Narma muje" ta faWa tana Waukar mata jakar. Har Najwa zata wuce sai taga charger Win wayarta zare ta saka a jaka ta fito daga Wakin ita kuma tana bayan ta.

Ashraf yana tsaye a falon ?asa suka sakko ya ri?o hannunta bata kwace hannunta ba dan bata da ?arfi a jikinta. Mum ce ta buWe mata hannu alamun taje jikinta, ta zara hannunta daga na Ashraf ta ?arasa ta shiga jikin Mum ita kuma tana murmushi ta ce, "Fatan samun kwanciyar hankali da nutsuwa my love." Dad ma kallon ta yake yi bayan ta Wago daga jikin Mum ta ?arasa wajan Dad shima ya rungume ta ya ce, "Allah ya yi miki albarka my love, fatan samun lafiya."

?agowa tayi ta kalli Yayan ta Nabil Shima ta shiga jikinsa ta rungume shi ya ce, "Allah ya dawo dake lafiya." Zare jikinta tayi ta koma kusa da Najwa ta tsaya. Dad ya ce, "Ashraf ga Narma nan please ka bita a sannu, kaga dai ba lafiya ce da ita ba sai ka yi ha?uri na Wan lokaci saboda yanayinta. Bani da wani tunani mara kyau a kanka, na san kana sonta zaka iya kula da ita a ko wanne yanayi. Please ka bata farin ciki, ka tabbatar da ta dawo nutsuwarta." Ashraf yana murmushi ya ce, "in sha Allah Dad kamar an yi an gama." Suka amsa gabaWaya suka fito harabar gidan suka shiga mota Najwa ma ta shiga dan zata rakata airport suka tafi.

Motar su na wucewa Mum ta dawo gida ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Sai nake ji kamar na sauke wani abu mai nauyi, Daughter zata sumu kwanciyar hankali ko ya ya ne." Dad bai ce komai ba ya murmusa kawai amma a zuciyarsa ya san basu kyautawa Narma ba, irin wannan aure da suka yi mata ba tare da shiri ba, amma in ya tuna haka shine zai saka ta samu kwanciyar hankali ta manta da Omar sai ya ji daWi har hankalinsa ya kwanta.

" " " " " " " " "

Omar tunda ya yanke wayar wayar Narma ya jingina da kujera ya lumshe ido. Sautin kukan ta yake ji a kunnensa sai ya ji rauni ya mamaye zuciyarsa gabaWaya. Da a ce ya san haka lamarin Narma zai zamar masa da tun farko bai bata fuskar da zata saki jiki dashi har su saba haka ba. Da ya san haka zata dinga shiga damuwa ta dalilinsa da bai tsaya ya saurareta ba, da bai bari yaji abinda yaji a kanta a lokacin baya ba. Tana bashi tausayi sosai, bai san abinda take ji a zuciyarta ba, amma ya tabbatar ko meye yana da zafi da raWaWi mai yawa. Ya sauke ajiyar zuciya ya buWe idanunsa a hankali yana kallon falon cikin kewar Didi.

"Assalamu alaikum, Boss na dawo" aka faWa ana shigowa falon. Ya kalli Tk a kasalance ya ce, "ya ake ciki?."
"An samu shagon akan titi, kuma babba ne yana yana da girma zai yi yadda ka ke so."
"An karSa?."
"E, an karSa. Yanzu kai mu ke jira mu ji ya za a yi." Ajiyar zuciya ya yi ya kalle shi ya ce, "a gyara shi a saka abinda za a bu?ata. Ku yi lissafi duk abinda kuke ganin ya dace ayi, kar dai ku yi min hauka a Sarnatar min da kuWi. Zan fito zuwa anjima sai mu ga yadda abin yake."
"An gama Damisa" ya faWa cike da girmamawa ya fita. Bai bari tunanin Narma ya dawo zuciyarsa ba ya tashi ya shiga kitchen dan samun abinda zai ci.

Kallon kitchen Win yake yi kafin yaja tsaki a bayyane ya ce, "Rashin Didi babbar illa ce a gareni, daman ni maraya ne na rashin iyaye yanzu na sake maraicewa. Ko me zan ci ma oho" ya faWa yana sake kallon kitchen Win. Tea kawai ya haWa ya zuba madara mai shegen yawa tare da sugar, dan shi Allah ya yi masa son madara da sugar, in zai sha shayi to fa sai yayi kauri sugar kuwa sai yayi masa yadda yake so. Da tea Win ya fito ya zauna yana sha yana kallon falon yana tunanin Didi.

" " " " " " "

Nayla tunda ta koma gida gabaWaya ta sake zama shiru babu walwala balle ta sake a zauna a falo ana hira da ita. In ka tambaya ta ce babu abinda yake damunta amma da ka kalle ta ka san tana cikin damuwa. Jin daWin ta ma in ta fita tun safe sai yamma take dawowa, wannan ya saka bata zama gida sosai ba kasafai ake game yanayin ta ba.

Haka Nayla ta cigaba da rayuwa cikin dauriya da juriyar abinda take ji a zuciyarta. Suna waya da Didi suna gaisawa kamar yadda suka saba bata taSa ce mata ga abinda yake damuna ba itama bata tambayarta ba sai dai a yi hira kawai a kashe wayar.

Cikin kwanakin Abiy ya yi fama da rashin lafiya shiyasa maganar masu neman auren Nayla bata tashi ba saboda baya jin daWi. Amma abun yana zuciyarsa so yake ya warware ya kira ta yaji ta bakin ta.

Yau ta kama ranar Asabar Nayla tana gida babu aiki tana kwance a Waki suna waya da Twiny cikin hirar su da bata wuce guda Waya. Mama ce ta shigo Wakin da sallama Nayla ta amsa tana kashe wayar tare da tashi zauna. Mama ta ?araso ta zauna kusa da ita ta ce, "Keda Jidda ne?." Nayla ta ce, "itace Mama." Mama ta girgiza kai ta ce, "Nayla kin san tun kafin kije Kano bikin ma?ociyar Hajja mahaifinki yake maganar ki fitar da miji a cikin samarinki ko?." Gaban Nayla ya faWi ta Waga kai alamun eh Mama ta ce, "ni ce na ce a ?yale ki saboda a lokacin bakya jin daWi kuma bakya tare da nutsuwarki. Kwana biyu kuma kinga bashi da lafiya shiyasa bai tayar da maganar ba. Amma jiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login