Showing 18001 words to 21000 words out of 85380 words

Chapter 7 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3825

a bashi aure bane, sam ba tsarin auren ki bane."

"Na sani Salma. In ba dan Wabi'arsa ba ni zan iya zama dashi, ban damu da bashi da kuWi ko bashi da wani abu ba. To Wabi'a sa baza ta taSa sakawa Abiy ya amince ba, Inda Abiy zai amince ni zan iya zama dashi a haka, koda zai dinga bani tsoro kamar yadda yake yi ko yaushe na shirya Salma...." ta sake faWa a sanyaye hawaye na sakkowa. Jidda ta kalle ta da kulawa ta ce, "kuma kin ce bai ma san kina sonsa ba ko?."

"Bai sani ba, kuma bana fatan ya sani Win. Domin Didi ta faWar min kalar wula?ancin da ya yiwa Narma a lokacin da ta je gidan su ta ce tana sonsa. Da?yar ta iya samun kansa har ya amince mata, jin kunnena naji yana waya yana yi mata faWa kamar ba wacce yake so ba. Wata?ila soyayyarsa kashe ni zata yi, dan wallahil azim ina matu?ar son Omar, Ina matu?ar ?aunarsa, ina yi masa ?aunar da ban taSa yiwa wata halitta a duniya ba sai shi. Matu?ar dauriya nake yi, juriya da ha?uri da jajircewa nake yi nake iya sarrafa zuciyata akansa. Amma ha?uri na ya fara ?arewa, gab nake da karaya..." ta faWa tana kuka sosai.

Salma ta rungume ta tana kuka itama cikin tausayin ?ar uwarta. Jidda a bayan Nayla ta Wora hanunta cikin tausayin Nayla, dan yanda Naylan take yin maganar zai baka tabbacin daga zuciyarta maganar take fitowa. Sun jima a haka ko wacce na kuka kafin Nayla ta tsayar da kukan ta ce, "Abiy ya bani lokaci na fitar da wanda nake so a cikin mutune huWu. Wallahi bana son su duka, bana tunanin zan iya zaman aure da Waya daga cikin su, ko na zauna zuciyata tana ga Omar ba ga wanda na aura ba. Ya zanyi? Ku faWa min abinda zan yi na daina sonsa don Allah!" Ta faWa da rauni wanda ya saka su Jidda sake fashewa da kuka.

Duka kuka suke yi da?yar Salma ta iya dakatawa ta ce, "Addu'a zaki yi Nayla, addu'a zamu dage da yi Allah ya kawo mana mafita." Nayla ta ce, "Ina addu'a Salma, Ina yin addu'a babu dare babu rana. Wallahi zuwan mu umra ban san adadin addu'ar da nayi akan lamarin nan ba, kuka na ke yiwa Allah Ina faWa masa ya cire min son Omar daga zuciyata amma soyayyar ta?i fita. In ina kuka a cikin sujjada ina faWawa Allah damuwata sai na yi awa Waya a haka ban san nayi ba. In aka cigaba da haka zan mutu ne kawai, dan na san bazan same shi a matsayin miji ba mutuwar itace hutu a gare ni."

Jidda ta ce, "kar ki sare, ki cigaba da addu'a Allah zai miki magani Nayla. In kika ro?a yau Allah bai baki ba ki ?ara ro?a gobe, yana ji kuma yana gani, shi ya ?addara miki kuma shi ya nufe ki da fara son Omar. Allah ya san damuwarki amma yace ki ro?e shi zai yaye miki, kar ki sare Nayla, kar guiwarki ta yi sanyi akan addu'a, ki cigaba kar ki tsaya. Ki yi ha?uri." Basu hanata kuka ba dan ya cancanci tayi kukan, zuciyarta ta yaudare ta da ta fara son wanda auren ta dashi bazai taSa yuwa ba. Shiyasa suka barta tayi kukan son ranta ko dan taji daWi a zuciyarta. Ai kam ta kwashe sama da mintina ashirin tana kuka, zuwa lokacin kanta ya yi nauyi zazzaSi ya rufe ta ruf.

Salma ce ta kwantar da ita ta tashi ta samo towel a banWaki ta ji?a shi da ruwan sanyi tana goge mata fuska da wuyanta. Rarrashin ta suka dinga yi har ta daina kukan Salma ta takura mata ta sha magani suna zaune a gefenta. A hankali kuma sai tayi bacci su dai kallon ta suke yi cikin tausayi.

Salma da Jidda fita suka yi zuwa harabar gidan dan su tattauna abinda ya kamata su yi. Salma ta ce, "Zuciyar Nayla bata yi mata adalci ba da ta fara son Omar Jidda, gashi bai ma san tana yi ba, sannan ko ni bazan goyi bayan ta aure shi ba duk da son da take masa."

Jidda ta ce, "yanzu meye abin yi? Wanne abu ki ke ganin zamu yi da zai taimaka mata?. Tana cikin halin azabar so da raWaWi mai ciwo, ya ki ke ganin zamu yi?."
"Addu'a kawai zamu taya ta Jidda, to in ba addu'ar ba me zamu yi mata?. Zamu je mu samu Omar in ya fito mu ce masa Nayla na sonsa ne?. Ko zamu je mu samu Didi mu faWa mata?."

Jidda ta ce, "Amma tana bu?atar Wauki Salma." Salma ta ce, "shiyasa na ce addu'a itace mafita." Jidda ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba Salma ta ce, "ikon Allah, shi kuma farin jinin mata masu hankali da kyau Allah ya bashi. Ki dai duba Nayla da Narma, a cikin babu wacce tayi sa'ar aurensa, amma lokaci Waya duk sun birkice a kansa kamar wani mutumin kirki? Anya ma ba asirin ya yi musu ba kuwa?." Jidda tayi dariya ta ce, "Wanne asiri ana zaune lafiya?."

"Allah Jidda abin da mamaki, ?an mata zu?a-zu?a kamar Nayla da Narma ace sun birkice akan sa? ?an mata masu asali, kyau, ga arzu?i amma su rasa wa zasu fara so sai wani Omar....Omar Win ma na gidan Didi Wan daba wanda ko sana'a bashi da ita?. Allah lamarin nan abin dubawa ne, dan ni zuciyata ta fara amincewa da batun sanata akan asirin nan wallahi. Kuma da alama wanda sunan su fara daga N ne suke faWawa tarkonsa, wata?ila wani malamin ne ya bashi sa a akan Nayla da Narma. Aniyarsa ta bishi, in sha Allah Nayla tafi ?arfinsa." Ita dai Jidda dariya kawai take yi jin kalaman Salma na asiri.

Sai yamma Nayla ta farka a lokacin har sun shirya tafiya bikin Shayida, ta bisu da kallo ta ce, "har kun shirya?." Jidda ta ce, "ya ciwon kan?."
"Ya yi sau?i sosai."
"To ki tashi ki yi sallah da wanka mu tafi."
"Anya zan iya zuwa Twiny? Ku je kawai basai naje ba." Salma ta ce, "A'a tashi ki shirya sai kin je, ganin mutane zai iya rage miki damuwa." Ta dole suka saka ta wanka ta shirya suka fita zuwa wajan bikin gabaWaya.
KRB2007
Arewabooks@nanahaleema11

Washe gari bayan sallar azahar Abiy da Senator da wasu manyan mutane su shida gabaWaya suna zaune a wani babban falo na alfarma suna hira da nishaWi ana tuna rayuwar makaranta. Su huWu a ciki duk ?an siyasa ne, Abiy da wani ne kawai ba sa harkar siyasa.

Ana cikin hira Abiy ya kalli Senator ya ce, "Senator daman akwai maganar da zamu yi da kai." Sen ya ce, "Ina ji." Abiy ya ce, "Akwai wani yaro Omar da ka kama ya je Abuja gidan ka haka ne?."

Sen ya Waure fuska yanayin sa ya canja lokaci guda ya ce, "Haka ne." Abiy ya ce, "Ina neman alfarma ka taimaka ka bani shi." Sen ya kalli Abiy ya ce, "ka san abinda ya aikata min kuwa? Narma fa ya je har gida ya ce yana so yana kallo na ina kallon sa." Abiy ya ce, "na sani, naji labarin komai. Ya yi tsaurin ido sosai bai kuma kyauta ba, amma kaima matsayin ka na babban Wan siyasa ajjiye a wani waje ana azabtar dashi hakan bai kamace ka ba."

Sen ya ce, "Babu yadda na iya ne, ina so a koya masa hankali shiyasa na aikata hakan. Na so na tura shi prison kawai na ?yale shi ne."
"Amma abinda kayi a yanzu zai iya taSa maka siyasarka, da zarar maganar ta fita shikenan za a dinga yaWawa ana faWar ?arya da gaskiya. Ka fini sanin meye siyasa, ka san yadda ?aramin abu yake zama babba, ka san yadda ?aramar magana take zama babba a gare ku."

Sen ya yi ajiyar zuciya ya kalli sauran ya basu labarin Omar kaf har zuwan Narma Kano da komai ya faWa musu, kana ya ce, "in ban saka an killace shi an wula?anta shi ba ta ya zai fahimci ya yi kuskure?."

Mai girma gwamnan jahar Katsina kuma mahaifi ga Ashraf ya ce, "hakan ya yi, amma da ka sani baka saka ana wahalar da shi b??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a gaskiya, kai ka faWa mana tasiri da ya yi maka a lokacin zaSe, baka ganin zai zama tasiri nan gaba wajan lalata komai?." Senator ya yi shiru yana tunani kafin ya ce, "shiyasa zan san abinda zan yi a kai shi kotu a yanke masa hukuncin da bazai fito ba har abada."
"Wannan ba shawara ce mai kyau ba, kafi kowa sanin meye siyasa da yadda harkokinta suke gudana" Abiy ya faWa yana kallon sa.

Senator ya ce, "asiri ya yi mata, in ba haka ba tana matu?ar son Ashraf, rana tsaka ta daina wai shi take so." Abiy ya yi dariya ya ce, "babu wani zancen asiri ni a ganina gaskiya, kawai tasirin soyayyar ne ba komai ba. Kuma yanzu ai komai ya wuce tunda ka tura ta london, a shawarata kawai ka aura mata Ashraf Win ya bita can su zauna a hankali zata manta dasahi."

Mahaifin Ashraf ya ce, "Abinda zan ce kenan, tunda ka ce ka tura ta Londan ayi auren au sai Ashraf Win ya bita can. Su samu good one year basa ?asar nan, in suka dawo sai ayi biki tunda babu wanda ya san ma sun yi aure. Amma barin sa a kulle ana wahalar dashi zai iya taSa ka nan gaba wallahi. In ?an uwansa suka shiga gidajen yaWa labarai suna cewa dan ya ce yana ?arka ka yi masa haka ka yi tunanin maganar da zaka jawo." Wajan ya rabu biyu, Abiy da mahaifin Ashraf suna ganin ri?e omar bai kamata, ba sauran suna ganin hakan shine daidai.

Senator ya kalli Abiy ya ce, "A ina ka san shi?." Abiy ya ce, "Unguwar su a nan kakar Nayla take mahaifiyar Bilkisu matata da ta rasu. Shekaru kusan goma baya an taSa yun?urin yiwa Nayla fyaWe, shine ya kuSutar da ita har aka yi ?o?arin kai shi prison saboda ya zubarwa da yaron jini aka ce ya Wauki doka a hannunsa, ni na san yadda akayi dai bai je prison ba. Yayarsa sun saba da Nayla sosai, halin da take ciki shine ya tashi hankalin Nayla tazo tana yi min kuka, kuma ko bata zo ba nayi niyar bin maganar saboda na rama alkhairin da ya yi min da alkhairi. Ina neman alfarma ayi masa afuwa bazai sake wannan gangancin ba."

Sen ya yi ajiyar zuciya ya kalli Abiy ya ce, "kuma ka tabbatar itama ba asirin ya yi mata ba?." Abiy? ya yi dariya mai sauti ya ce, "babu asirin da ya yiwa Narma ma balle Nayla ta shigo ciki, Babu abinda ya yi musu. Kuma ni dan ina bibiyar good background da good manners a aure ne, da ace yana dasu tsaf zan ce ka bawa Narma shi Win. Ai kana da arzu?in da zaka iya sakawa ya tashi daga nobody to somebody."

Sen ya taSe fuska ya ce, "Allah ya kiyaye, Jahili ne fa ko secondary school bai gama ba. Ina zai iya kaiwa a rayuwa babu ilimi?." Abiy ya ce , "ni dai ayi min alfarma a bani shi." Sen ya yi shiru yana tunani, bazai iya ?in yiwa Abiy alfarma ba saboda mutuncin da yake tsakanin su. Amma in ya tuna wula?ancin da Omar ya yi masa sai yaji bazai iya bada shi ba.

Senator ya ce, "Shikenan, za a ?yale shi gobe. Amma saboda kai ne kawai babu yadda zan yi maka, amma wallahi da sai ya ?are rayuwarsa haka." Abiy ya yi dariya ya ce, "godiya nake mai girma Senator kuma sirikin Gov, future Kano state gov in sha Allah." Dariya suka yi aka share zancen suka cigaba da hira har bayan sallar la'asar kafin kowa ya watse.

Kasancewar ranar ne dinner Win Shayida su Nayla suna gida su ukun a falo suna ta jan Nayla da hira amma ta kasa sakewa. Abiy ne ya shigo falon duk suka mi?e tsaye ya kalle su da murmushi suka gaishe shi ya amsa kafin ya kalli Nayla ya ce, "Mamana kina lafiya kuwa?." Nayla ta ce, "lafiya lau Abiy, ciwon kai ne tun na jiya har yanzu."
"Kwana biyu ciwon kai yana damunki sosai, ki je asibiti mana."
"Wallahi stress ne aiki na kawai Abiy, da nayi bacci na tashi sai na dawo daidai."

Abiy ya yi dariya ya ce, "kaga sabuwar ma'aikaciya." Tayi dariya Abiy ya zauna yana cewa, "?arfe nawa zaku tafi Kaduna gobe? Ni sai jibi monday zan dawo in sha Allah ." Nayla ta ce, "Duk lokacin ka ce Abiy."
"Saboda aikinki dole a koma gobe gaskiya, zamu gani zuwa azahar sai ku tafi in Allah ya kaimu."

Bata yi magana ba ya kalle ta ya ce, "Maganar Wan daban yaron nan." Ai da sauri ta Wago tana kallonsa a lokacin Mama tazo ta zauna a wajan. Abiy ya ce, "Mun yi magana da Senator..." ya faWa yana duba waya wacce sa?on text ya shigo. Shiru ya yi bai yi magana ba yana duba wayar. Nayla ji take kamar ta ?wace wayar daga hannunsa saboda ya kai ga faWa mata abinda zai ce.

Abiy ya ajjiye wayar ya ce, "mun yi magana ya kuma amince zai ?yale shi, gobe ma ya ce zai sake shi ya dawo gida in sha Allah." Wata irin ajiyar doguwar zuciya Nayla tayi, ta lumshe idanu tana jin wani irin daWi na ratsa zuciyarta. Abiy ya bita da kallon mamaki ganin yadda farin ciki ya bayyana a tare da ita kamar itace Yayar ta sa. A hankali ta buWe ido suka haWa ido da Abiy da yake kallonta, da sauri ta sunkuyar da kai amma murmushi take yi. Abiy ya ce, "ko dai kema ?anwarsa ce ne Nayla? Wannan ajiyar zuciya haka kamar Jawad aka kama za a saki?."

Murmushin ya?e tayi ta ce, "Abiy kawai Ina murna ne in na tuna yadda Didi zata yi murna." Abiy ya zuba mata ido yana binta da kallon tuhuma kafin ya ce, "kin tabbata?." Sai taji tsoro ya shige ta da tunanin Allah yasa bai gane wani abun ba. Ta sake sunkuyar da kai tace, "Eh Abiy."

"To ya yi. Ki sanar mata gobe zai dawo in sha Allah." Da farin ciki ta amsa shi kuma ya tashi ya shiga ciki Mama ma tabi bayansa. Nayla na shiga Waki sai gata ta fito da key Win motar Mama, Salma da Jidda suka kalle ta kafin su magana ta ce, "Gidan Hajja zan je, in zaku je kuzo mu tafi." Salma ta karSi key Win hannunta tace, "bani baza ki sake ?o?arin kashe mu ba." Bata ma ji ba tayi gaba burinta kawai taje ta faWawa Didi. Salma ce ta ja motar suka tafi gidan Hajja.

Nayla na shiga ta tarar da Didi ita da AbdulHamid suna tsaye da alama sallama yake yi mata. A guje ta faWa jikin Didi ta ce, "Didi Abiy ya yi magana da Senator ya tabbatar masa da gobe zai dawo, gobe zai dawo Didi" ta faWa da murna sosai. Didi cikin farin ciki ta ce, "da gaske ki ke? Da gaske ki ke Nayla?."
"Da gaske nake Didi." Didi ta ce, "Alhamdulillah! Allah na gode maka, Allah na gode maka" ta faWa tana sake rungume Nayla da take dara saboda murna.

"Na gode Nayla, na gode Allah ya saka miki da alkhairi Allah ya baki miji na gari." Ciki suka shiga dan Didi ta manta da AbdulHamid da yake wajan. Sai da suka shiga falon Hajja Salma ta ce, "Amin Didi. Dan wallahi itace jiya ta samu Abiy tana kuka kamar zata mutu saboda a fito da Omar, yadda muka bar gidan nan jiya baki ga gudun da ta dinga yi damu a mota ba saboda kawai take ta samu Abiy. Cikin ikon Allah tana faWawa masa ya kira shi a waya ya Wauka, yau suka haWu ya yi masa maganar ya kuma amince" Salma ta faWa tana kallon Didin da ta san aikin Nayla ne yadda ko Omar Win ya fito ya san ita tayi masa hanya ya fito.

Didi ta sake ri?e Nayla tana godiya tana hawaye tana cewa, "na gode Nayla, Allah ya bani abinda zan saka miki Nayla. Na gode sosai." Hajja ta ce, "itama ai ta saka alkhairin da ya yi mata ne Aisha, kin manta abinda ya yi mata?." Didi ta ce, "ban manta ba Hajja, amma wannan taimakon da tayi min ai baza ki haWa shi da wancan ba. Ta ceci rayuwata ta ceci ta Omar, bani da abinda zan saka mata saka addu'a."

Hajja tayi dariya dan ko ita ta ji daWin labarin dawowar Omar. Didi ta ce, "Nayla mu je na yiwa Abiy godiya, mu je yanzu in yana gida." Hajja ta ce, "A'a Aisha, ki bari ya dawo sai ku je ku same shi tare." Didi ta ce, "Amma ya kamata na je yanzu kafin ya dawo ko?." Nayla ta ce, "to sai mu je in anjima, ko kuma ki yi masa waya."

A nan suka baje ana ta hira da nishaWi Didi ji take kamar ta mayar da Nayla ciki saboda son da take yi mata. Sai bayan i'sha suka tafi saboda dinner da zasu je, tare da Didi aka je ta yiwa Abiy godiya ya ce babu komai. Drivern Hajja ne ya dawo da Didi su kuma suka fara shirin dinner. Ko a wajan dinner kowa ya lura da walwalar da Nayla take yi, su dai su Salma fatan samun sasssuci akan abinda yake damunta suke yi mata.

Washe gari ranar lahadi ?arfe goma na safe ta fita daga gida zuwa gidan Hajja. Ta samu Didi ma bata nan ta shiga gida tana aikace-aikace Saboda dawowar Omaar. Salma ce ta shigo tana cewa, "shine ko ki jira ni kika taho bayan kin san Jidda tana gidan ta." Nayla ta ce, "to ba gashi kin zo ba. Matsa min naje gidan Didi." Salma ta ce, "ba da wuri Abiy ya ce zaku koma ba ne? Yana ta faWa ya ce kin san zaku tafi Kaduna ki ka fito

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login