Showing 60001 words to 63000 words out of 85380 words

Chapter 21 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3848

zauna a gidan ba kinga an fasa auren, ki lallaSa Omar ki san dabarar da zaki yi masa sai ya zauna a ciki. Kar sunana ko sunan wani ya fito a kyautar gidan nan, ki san yadda zaki yi dashi amma kar ki ce daga hannuna ya fito. Kuma wallahil azim na bar masa kyauta, yadda na siya da sunan Wana auren bai yu ba na barwa Wana na wajen marigayi ?anina Usman gidan halak malak."

Didi a sanyaye ta ce, "To Kawu, an gode Allah...." Dakatar da ita ya yi ya ce, "Aisha kar ki gode min, muje magana ta gaba." Didi ta ce, "To Kawu. Ni yanzu so nake a san yadda za ayi a tunkare shi tukunna." Kawu Yusuf? ya ce, "Aisha wannan ai aikin ki ne, mu a cikin mu akwai wanda ya isa ya tari Omar da wannan maganar ne?."

Sai taji jikinta ya yi sanyi a sanyaye ta ce, "kun isa mana Kawu."
"Ba mu isa ba wallahi, kema kin san bamu isa a wajan Omar ba. Tunda hakan ta kasance naji daWi da kina nan, da bakya nan tsaf zai iya zuwa ?ofar gidan nan ya tara mana jama'a. Ki je ki san yadda zaki faWa masa."

Kawu Mamman ya ce, "Aisha ni kuma in za a haWa lefen amarya kizo ki yi min lissafi zan siyi komai in sha Allah." Didi tayi murmushin ya?e zata yi godiya ya dakatar da ita ya ce, "kije ki tattauna da Omar kawai."

Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "To Kawu zan yi. Bara jama'a su Wan ragu a gari sai naje na same shi" ta faWa a sanyaye tana kallon su. Suka amsa mata ta shiga ciki tana tunanin dalilin Abiy da aikata wannan Wanyen aiki.

Su Abiy sai da suka tsaya a hanya suka siyi abinci sannan suka wuce gida. Suna shiga Abiy ya Wauki pack Waya na abincin yana ci ba dan yana jin daWinsa ba sai dan babu yadda zai yi ne. Jawad kam sun kasa ci kallon Abiy kawai suke yi suna jiran ?arin bayani, ?arfin hali Yaya Ahmad ya yi ya ce, "Abiy meyasa ka yanke wannan hukuncin akan Nayla don Allah? Wannan ba yukunci bane, taya zaka Waura auren ta da wannan yaron?."

Abiy bai yi magana ba Jawad ya ce, "Abiy don Allah meyasa aka yi mata haka? Ko me ta aikata ai yarinya ce sai ayi mata uzuri a tsawatar mata, amma Waura mata aure dashi ba hukunci bane ba Abiy." Abiy bai ce musu komai ba ya ajjiye abincin ya tashi ya shiga ciki.

Jawad ya kalli Yaya ya ce, "wannan hukunci ne Yaya? Wannan ai lalata mata rayuwa aka yi ba aure aka yi mata ba. Ko me tayi ai wannan ba hukunci bane, sai a zaunar da ita ayi mata faWa, in auren ya zama dole sai aura mata wani amma ba irin wannan yaron ba." Yaya cike da damuwa ya ce, "ni ban san ma abinda zan ce ba wallahi, ban san abinda ya saka Abiy ya aikata haka ba. Dan ta ce tana sonsa akwai sai a bata shi? Haba gaskiya Abiy bai kyauta mana ba wallahi." Abincin da basu iya ci ba kenan Abiy ya fito ya kalle su ya ce, "abinda ya kawo mu Kano mu yi, ku tashi mu wuce gida."

A sanyaye suka tashi suka bi bayan sa bayan sun Wauko abincin har wanda Abiy ya ajjiye. Yaya ne yanzu ya shiga gaba wajan mai tu?awa Jawad ya shiga kusa da shi Abiy ya shiga baya. Har zai kunna motar Abiy ya tuna ya yi mantuwa ya koma ciki. Jawad kasa ha?uri yayi ya Wauki waya ya kira Nayla yayi sa a ta shiga, tana Wauka kafin tayi magana ya ce, "Malama duk abinda ki ke yi a Kano ki tabbatar kin wuce Kaduna yanzu, ko me ki ke yi ki ajjiye ki wuce gida." Nayla ta ce, "Yaya J rana ta yi yanzu, driver Hajja baya nan waye zai kai ni Kaduna yanzu?."

A tsawace ya ce, "ki san yadda zaki yi ki dawo gida, in ba haka ba wallahi sai ranki ya Saci sosai" ya faWa ya yanke wayar ganin Abiy ya taho. Yana shiga motar Jawad ya ce, "Abiy mu biya gidan Hajja mu tafi da Nayla?." Abiy ya ce, "tare muka zo da ita?." Jin abinda ya ce sai ya yi shiru amma zuciyarsa gabaWaya babu daWi akan abinda Abiy ya yi, to babu yadda zasu yi ne dole su yi shiru kamar yadda ya ce. Fita suka yi daga gidan bayan sun bawa mai gadi abincin suka Wauki hanyar Kaduna.

Nayla kuwa da suka je gidan Didi bata nan sai kawai suka wuce gidan Jidda, suna zaune a Jawad yayi mata waya duk sun ji abinda ya ce. Ta kalli Twiny ta ce, "Yaya J ne yau yake yi min wannan faWan, yanzu waye zai kai ni Kaduna?." Twiny ta ce, "ke share shi, gobe sai ki tafi. Haka kawai sai yaja Abiy ya yi miki faWa daman gashi Abiy na fushi."

Nayla ta ce, "yanayin maganar Ya J da Sacin rai ciki sosai Twiny, ko dai naje na hau motar haya na koma?."
"Ki share shi, gobe da safe sai ki tafi." Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce, "Allah ya sa Abiy bai yi fushi da tahowa ta Kano ba, Allah ya sa ya fahimce ni ya yafe min laifin da nayi masa." Suka amsa mata da amin. Hira suke ta janta da ita amma ta kasa sakin jikin saboda bata da walwala ko kaWan, yamma nayi suka wuce gida a motar gidan Hajja da Salma ta kawo su.
KRB2P021

Su Abiy da suka koma gida bai cewa kowa komai ba sama ya hau ya barsu a wajan a tsaye. Mama ta kalle su ganin fuskar su Wauke da damuwa ta ce, "Wai ne ya faru ne? Me kuka je yi Kano?." Jawad ya kalle ta ya ce, "dangin wannan yaron Omar muka je, abin mamaki Abiy ya bada auren Nayla, dan yanzu haka Nayla matarsa ce." Mama ta wara idanu waje a zahiri, a baWini kuma farin ciki ne ya mamaye mata zuciya ta ce, "Aure kuma? Auren Nayla da Wan daban aka yi?."

Yaya ya ce, "Wallahi shi aka yi Mama, Abiy ya?i faWa mana dalilinsa, sannan kuma ya hana mu tamabaya. Yanzu zancen da nake miki an Waura auren su ita dashi, kuma ko sani Omaar Win bai yi ba, haka Nayla Win ma bata sani ba."

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Meyasa mahaifinku ya yanke wannan hukunci? Me Nayla tayi masa haka?. Ko dan ta tafi Kano ne ya saka ya yanke wannan hukuncin?." Jawad ya ce, "itama bata da mutunci ai Mama, ban da rashin hankali da shirme meye na barin gida a akan wannan maganar? Na rantse da Allah in ta dawo sai na zaSa mata kamanni."

Mama ta ce, "bara naje na samu Abiy Win naku naji dalilin sa na aikata wannan Wanyen aiki." Yaya ya ce, "Yauwa Mama, in da hali a kira yaron kawai ya sake ta tunda daman bai san anyi auren ba. In yaso ni a bani Nayla mu koma Lagos ta koma zama a gidana, nayi alqawari zan kula da ita babu wata damuwa irin wannan da zata sake kunno kai." Mama ta girgiza kai ta hau sama da sauri wajan Abiy. Sallar magriba ta samu yana yi sai ta zauna tana zaman jiran ya idar suyi magana.

Koda ya idar lazimi ya fara ta san kuma baya gamawa sai za a yi i'sha gashi ita ta ?agu tayi magana dashi. Mama ta ce, "Don Allah Abiy ka katse lazumin nan muyi magana. Ta ya za a aurawa Nayla wancan yaron?. Bai kamata a biye mata a aikata abinda take so ba." Ko motsi bai yi ba balle ta saka ran zai bata amsa. Mama ta ce, "Abiy don Allah kace wani abu, ka dakatar da lazumin nan muyi magana don Allah."

Ban ma bai kula ta ba Mama ta zauna tayi tagumi tana kallonsa. Gajiya tayi da zaman ta tashi ta fita shi kam bai ma kalle ta ba. Sai da ya kammala yaji ana kiran sallar i'sha sannan ya tashi ya fito dan zuwa masallaci.

Koda ya dawo a falo ya tarar dasu gabaWaya da alama zaman jiran sa suke yi. Wucewa yayi ba tare da ya zauna ba suka bishi da kallo ganin ya shiga ciki. Jawad ya ce, "Mama don Allah kije kuyi magana ya bar mu cikin tunani." Mama ta ce, "maganar ce baya so shiyasa ya wuce bai kula mu ba, amma bara na sake zuwa naji" ta faWa tana hawa saman ta barsu a ?asa.

Tana zuwa ta same shi ya zauna akan kujera yana kallon tv, ta zauna a kusa dashi ta ce, "abinci fa?." Ya girgiza kai kawai alamun baya ci. Mama ta ce, "maganar dai da baka so ita zanyi Abiy. Meya faru ka yanke wannan hukunci akan Nayla?. Naji bata kyauta ba amma da ka sani baka yi haka ba." Bai ce mata komai ba itama sai tayi shiru bata sake magana ba.

Katse shirun tayi da cewa, "bata kyauta ba abinda tayi na barin g1da, bata kyauta ba maganar da tayi ta ce zata kashe kanta akansa amma Abiy bai kamata ka biye mata ba, Nayla yarinya ce ?arama bata da hankali har yanzu." Abiy ya kulle ido ya buWe ya kalli Mama ya ce, "gobe ku shiga kasuwa, duk abinda ake siyawa amarya ku siya mata. Duk abinda za ayi ayi shi a gama ba sai ance za ayi order daga wata ?asa ba. A siyi komai gobe zuwa ranar Sunday nake so tafi gidan mijinta" yana faWar hakan ya tashi ya bata waje.

Mama ta ce, "meyasa haka...." Katse ta yayi ta hanyar cewa, "kar ki shigo ki dame ni" yana faWa ya wuce Waki. Mama tayi wani mayaudarin murmushi ta ce, "an gama." Canja yanayinta tayi ta sakko ?asa wajan su Yaya da Jawad suka bita da kallo ganin yanayinta ya nuna musu alamun rashin nasara. Ta kalle su ta ce, "yace gobe na shiga kasuwa na siyawa Nayla duk abinda ake siya na aure, wai zuwa jibi zata tare." Yaya ya ce, "Mama sai kika ce masa me?" Ya faWa kamar zai yi kuka.

Mama ta ce, "bai bani damar magana ba, ya kuma kalle ni yace kar na dame shi ya shiga Waki ya bar ni a falo." Jawad ya ce, "wai me yake damun Abiy ne har haka? Me Nayla tayi masa da ya canja lokaci guda don Allah?."
"Bata kyauta ba Jawad, abinda tayi ba tarbiyyar da ya baku bace gabaWaya. Amma shima yayi gagagwar yanke hukunci, Nayla yarinya ce ?ar ?arama ba babba ba."

Yaya ya ce, "kome tayi ai bata cancanci haka ba, irin wannan aure kamar bata da gata kawai an Wauketa an bashi ba tare da yana so ba? Babu kuWin aure, babu komai hatta sadaki biya masa aka yi. Ko da yake bai ma sani ba." Mama ta ce, "ka wuce gida dare yayi, in yaso gobe zai kuzo mu ji in zai yi mana magana." Jawad ya ce, "ai wallahi gobe in bata dawo ba da kaina sai naje na dawo da ita, shashasha mara hankali da tunani" ya faWa yana fita daga falon shima ya bi bayan sa.

Mama shiga Waki ta Wauki waya ta saka a kunne kafin ta ce, "Yauwa, in zaka iya ka sake hacking account Winta na WhatsApp ka sake turawa Abiy sa?o. In zai yu zan turo maka irin abinda da zaka tura masa yanzun nan." Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin ta ce, "karka damu, na tura maka kuWin ka harda na data ka ?ara." Yanke wayar tayi tana kallon wani wajan daban tana Wan dukan wayar da hannunta.

Murmushi tayi ta ce, "kwanciyar hankalina shine auren nan ya tabbata, babu ta yadda za ayi na bari a warware shi tunda an riga da an Waura. Yadda ban ji daWi zaman gidan nan ba, yadda Bilkisu ta wahalar dani a rayuwar gidan nan Nayla ma sai ta WanWana irin abinda na WanWana. Muje dai zuwa" ta faWa tana yanke wayar ta shiga banWaki zuciyarta fes take dan ta san ta zama silar aurawa Nayla wanda baza ta taSa jin daWin zaman aure dashi ba.

" " " " " " "

? ? ? Didi tana barin gidan Kawu gidan su ta wuce ta samu Omar Win a zaune ya dawo daga masallaci yana zaune akan kujera ya Wan zame kansa na bayan kujerar ya Wora ?afa kan Waya kamar yadda ya saba. Kallon sa take yi ganin yayi mata kyau gashin kansa ya kwanta kamar na jariri, idanunsa a rufe gashin idanunsa sun kwanta a ?asan idanun.

"Omar Lafiya?" Ta faWa tana zama daga gefen sa. BuWe ido yayi ya ce, "Didi! Saukar yaushe?."
"Yanzu na shigo, baka da lafiya ne?."
"Ciwon kai ne yake damuna tun safe."
"Amma ka sha magani?."
"Na sha" ya faWa yana sake lumshe idanunsa bai ce mata komai ba.

Didi kallonsa take yi tana haWa kalaman da zatayi amfani dasu wajan sanar dashi abinda ya faru amma ta kasa, ta rasa ta ina zata kamo zaren, ta rasa da wacce kalma zata yi amfani wajan sanar dashi abinda yake zuciyarta akansa. Ajiyar zuciya tayi hakan ya saka ya buWe ido ya kalleta ya ce "Lafiya dai?." Didi ta kalle shi sai taga idanunsa sun yi ja alamun yana jin ciwon kan sosai ta ce, "ciwon kan ne dai?." Ya Waga kai alamun eh.

Lumshe ido tayi ta sake buWewa tana kallonsa ganin ita yake kallo, ya sauke ?afa Waya ?asa ya kalleta sosai ya ce, "kar ki damu da kaina na ciwo, ki faWa min abinda yake faruwa. Naga kin canja alamun damuwa, meye?." Kai ta girgiza ta ce, "Babu komai Omar, Tambayar ka nake so nayi kawai."

"Akan son tambayata kawai kika koma haka?." Kallon sa tayi sai bata amsa ba ya ce, "Ina jinki."
"Omar na isa da kai? Na isa na zaSa maka abu ka karSa hannu biyu?." Wani irin kallo yake yi mata na me ya kawo wannan tambayar kafin ya ce, "me ya kawo wannan tambayar? Wani abun ya faru ne?."

"Babu abinda ya faru, ka amsa min tambayata."
"Akwai abinda ya faru, kawai bakya so ki faWa min ne. Ni kuma Ina so na san meye abinda ya faru kafin na amsa miki."
"Kawai ka amsa min Omar."
"Me zan amsa?" Ya tambaya yana kallonta. Didi ta rausayar da kai ta ce, "na isa da kai? Na isa na zaSa maka abu ka karSa?."

Omar ya bita da kallo yana so ya gano dalilin tambayar amma bai gane ba, ya Wan Wauke ido yana kallon wani wajan daban kafin ya ce, "kin isa."


Didi ta ce, "Koda matar aure ce? Koda Wauko mace nayi a yanzu nace maka na saka an Waura maka aure da ita zaka karSa ta?." Omaar ya bita da kallon mamaki ganin ba da wasa take yi kamar yadda ta saba ba, sannan ya ga damuwa a kwance a fuskarta, sannan ya tabbatar da akwai abinda take so ta faWa masa kafin wannan. Didi ta ce, "ka yi shiru kana kallona." Omar yayi ajiyar zuciya ya ce, "dalilin wannan tambayar nake so naji."

"Ni dai ka amsa min kawai" ta faWa tana kallon sa. Shiru yayi na wani lokaci yana kallonta kafin ya ce, "eh to, kin isa ki zaSa min Win tunda kece zai karSa babu yadda zanyi. Amma kin san kin bani ita ne ba dan Inaso ba, kuma zama da wacce bana so bazata taSa jin daWin zama dani ba har abada. Kin fi kowa sanin halina, bana son ganin abinda ban saba gani a tare dani ba." Didi gabanta ya yanke ya faWi tsoro ya mamaye mata zuciya ta ce, "amma zaka iya zama da ita a matsayin matarka dai ko? Babu tsawa, babu tsoratarwa, babu razani, babu harara ko?."

Gyara zama yayi ya shafa kansa zuwa gashin fuskarsa, ya Wan sosa girar sa da yatsa Waya kana ya ce, "gaskiya bazan iya zama da ita matsayin mata ba, zan dai zauna da ita a gida Waya matsayin zaSinki, amma gaskiya ba dai a matata ba."

Kallon sa take yi ta kasa magana dan ya kashe mata baki, ya katse shirun ya ce, "me ya kawo wannan maganar wai? Aure zaki yi min ne?." Jin yana ?o?arin gano ta sai ta girgiza kai ta ce, "Kusa hakan, bana son zaman ka kai kaWai a gidan nan shine nake tunanin zaSar maka mata na aura maka."

"Kar ki wahalar da kanki bana bu?ata, bana so in kika yi ma zaki Sata lokacin ki ne, ko wacece ita zaki Sata mata lokaci da rayuwarta ne dan ni ban shirya aure ba. Gwara ki bari taje ta auri wani daban da dai ace ta aure ni, zaman aure da wacce babu ita a rayuwara tun farko babbar matsala ce. Na hutar dake, bance ina so ba, dan haka ki bar maganar nan."

"Baza ka iya kallonta a matsayin matarka ba saboda ni?".
"Haba Didi! Na faWa miki ban so a bar maganar nan, in ma kina niyar yi ne kar ki yi na hutar dake bana bu?ata, zama ni kaWai baya damuna kinfi kowa sanin haka. Wacce mace zaki Wauko ki kawota cikin rayuwata ba tare da sanina ba? Don Allah ki adana wannan tunanin, kar kuma kiyi wannan gangancin in ba haka ba zan ta Sata miki rai, ki ?yale ni!" Ya faWa a kausashe yana kallonta dan ta katse batun shi ya gaji da wannan kalaman nata.

Ajiyar zuciya tayi ta rasa da wacce hanya zata yi masa magana ya fahimta, me zata ce masa ne wai? Ta ce masa mahaifin Nayla ya zo ya baka auren ta? To Akan wanne dalili ya aura masa ita? Meyasa yayi hakan?. Ganin ta tafi duniyar tunani sai taji ya murza yatsunsa a kusa da fuskarta sun bada sauti, ta kalle shi ya ce, "Ki faWa min damuwar ki Didi!" Ya faWa cikin kakkausar murya yana kallonta. Didi ta buWe ido tana kallonsa ta ce, "babu komai na faWa maka, zaman ka haka ne bana so, ya zama dole na nema maka matar aure koda baka so."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login