Showing 33001 words to 36000 words out of 85380 words

Chapter 12 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3840

kirkin Abiy da matar gidan. Dubu hamsin ta lissafa a dubu Wari biyun da Abiy ya bayar?ta bawa Salma ta ce, "Salma ga na saka data." Salma tayi dariya ta ce, "Haba Didi, wallahi bazan karSa ba, na gode sosai."

Didi da mamaki ta ce, "Meyasa baza ki karSa ba?."
"Haba Didi, dan na raka ki sai kin bani kuWi? Wallahi bazan karSa ba." Didi ta ce, "to ki bawa Sayyadi driver Hajja ya saka kati." Salma ta karSa ta ce, "zan bashi in sha Allah." Didi ta dinga godiya sannan ta tashi ta shiga gidan su.

Sallar la'asar tayi tare da yin wanka sannan ta dawo falo ta zauna. Yunwa take ji amma bata tunanin zata iya girki a gajiye take sosai. Baccin gajiya ne ya Wauketa sai kiran sallar magriba ne ya tashe ta. Mi?ewa tayi tana salati ta yi alwala ta dawo ta tayar da sallah, bayan ta idar ne ta iya tashi ta dafa musu indomie ta zuba a plate kenan ta fito falon ya shigo da sallama.

Amsawa tayi sai ta bashi plate Win hannunta ta ce, "tun Wazu na so nayi mana girki sai nayi baccin gajiya." KarSa ya yi ya zauna ta koma ta Wauko ragowar da ta ajjiye masa ta dawo ta zauna ta fara ci kamar yadda yake ci shima. Sai da ta kusa cinyewa sannan ta tura masa ragowar kuWin da Abiy ya bayar ta ce, "Mahaifin Nayla ya bada dubu Wari biyu ya ce mu zauna mai a mota, na bawa Salman Hajja dubu hamsin ta?i karSa, amma na ce ta bawa driver da ya kaimu shima ya siyi kati. Ga ragowar nan, ga kuma kayan da Mamanta ta bani. Lace ne da atampa sababbi da turaren wuta, humra da mayafi" ta faWa tana nuna masa kayan akan kujera.

Bai ce komai ba sai da ya kusa cinye indomie Win sannan ya ajjiye plate Win ya kalle ta ya ce, "Didi baki kyauta min ba, abinda kin ka yi min sam ban ji daWi ba." Didi da mamaki ta ce, "me nayi maka?."
"Meyasa baki faWa min in za a ce waje irin wannan ana siyan abu a kai ba? Sai gani nayi kawai kin bada tsaraba ba tare kin faWa min ba. Shiyasa ake cewa ke ce kike Waukar Wawainiya ta bana yi miki komai." Didi da mamaki ta ce, "Omar da girman ka da komai sai na faWa maka? Baka san ya kamata ba dai?."

"Didi ban sani ba, ban sani ba. Bani da mahaifiyar da zata faWa min abinda ya kamata da wanda bai kamata ba. Ban ji a raina ya kamata ace na siyi wani abu na kai ba saboda ban saba zuwa ba, ban taSa yiwa wani godiya a duniya ba daga shi sai Hajja. Da nake zaune a gabansa ji nake kamar ana Waure ni, ban taSa jin nauyi da girman mutum a idanuna kamar yadda na ji na shi ba. Na ji na kasa haWa ido dashi balle na yi magana, a karo na farko a rayuwata da naji girma da nauyin wani mutum, duk na Wauki hakan a rashin sabo saboda ban taSa zuwa wajan wani da sunan godiya ba. Meyesa kafin mu tafi baki faWa min ana siyan abu a kai ba?."

Didi kallon sa take yi har ya kai ?arshe ganin da gaske yake maganar sannan ta ce, "shikenan naji laifina ne ban faWa maka ba, nan gaba sai ka aikata ba tare da an faWa maka ba. Kuma in na siya kamar ka siya ne ai." Omar ya ce, "ni dai ban ji daWi ba, da kin faWa min da ko wani abun an siya an haWa an ka. Da kin faWa min da ni zan bada kuWin abinda zaki yi." Didi ta ce, "shikenan ai ya wuce."

Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "Nawa ki ka kashe?."
"Gurasa ce fa ta dubu goma ba wani abun ba." Hannu ya saka a aljihu ya Wauko dubu bakwai ya ajjiye mata ya ce, "ga kuWin da ki ka kashe. Sannan ki haWa da wannan ma ki ri?e hidima ce a gabanki" ya faWa yana nuna mata wanda ta turo masa kusa dashi. Didi tayi murmushi ta ce, "to na gode."

Wayar Didi ce ta katse masa maganar da ta yi niyar yi, ta duba taga Nayla ce sai ta saka a speaker daga can Sangaren Nayla ta ce, "Didi ina fatan kin sauka lafiya, Ina ta kiran ki Wazu baki Wauka ba." Didi ta ce, "mun sauka lafiya lau Nayla. Bacci nayi shiyasa baki same ni ba. Ya jikin naki?."
"Jiki da sau?i Didi."
"Kin daina kukan?." Nayla ta Wan murmushi ta ce, "Didi na daina" ta faWa a sanyaye. Didi ta ce, "ai gwara da ki ka daina, gabaWaya duk na damu wallahi:"

?ar dariya tayi ta ce, "An gode Didi, na ji daWin zuwan ku sosai." Didi ta ce, "mu ne da godiya Nayla. Yadda aka karSe mu a gidan ku wallahi ya fi min komai daWi."
"Babu komai Didi. A gaishe da.....Yaya Omar" ta faWa a rabe muryarta har rawa take yi. Didi tayi murmushi ta kalli Omar da yake suraren su ta ce, "Yaya?Omar yana jinki." Nayla tayi murmushi ta ce, "na san bazai yi magana ba, amma ki ce ina? yi masa bangajiya mun gode sosai."

Didi ta ce, "to Nayla, mun gode da tarba mai kyau Allah ya ?arawa Abiy tsahon rai." Nayla ta amsa da amin tayi shiru ko Omar zai yi magana amma bai ce komai ba dole ta yanke wayar. Murmushi Didi tayi bayan ta kashe wayar ta ce, "Wai Yaya Omar, Nayla akwai ta da bin dariya. Ko yaushe ya zama Yaya Win oho mata."

"Ban cancanci ace min Yayan bane shiyasa har sunan ya baki dariya?." Da mamaki ta kalle shi dan bata Wauka zai yi magana ba, sanin halin sa ba tankawa zai yi ba musamman Nayla da yake yawan faWar haushinta yake ji.

Didi ta sake yin dariya ta ce, "A'a ni ban ce ba Malam Omar, meye nawa na cewa baka cancanta ba? Kawai na san haushinta ka ke ji ne." Bai yi magana ba ya share ta Didi ta ce, "anyi kiran sallar i'sha, sallah zan yi" ta faWa tana tashi ta shiga ciki ya bita da kallo.

Yaya Omar Win da Nayla ta faWa a lokacin da zasu bar gidan su da yadda hawaye yake zuba a idonta kawai ya tuna, ajiyar zuciya ya yi ya rufe ido sai kuma Narma ta faWo zuciyarsa itama lokacin da take kuka lokacin da ta je wajansa. Tashi ya yi ya bar falon zuciyarsa cike da tunani kala-kala.

Bayan Kwana biyu.

Bikin Didi ya matso sosai an kai lefe gidan Kawu akwatina goma sha huWu kaya masu yawa sosai. Baba Adamu kamar yadda ya ce an gama zuba komai na gidan Didi, hatta kayan kitchen ya zuba sai abinda Didi ta siya ta ajjiye aka kai can. Gida ne babba da falo biyu da bedroom uku, sai dai unguwar babu jama'a sosai amma gida kan ya yi kyau sosai.

Didi ana ta yi mata gyaran jiki duk da ita kaWai take yi komai, sai Hajja da Salma da suke taimaka mata dan bata da wani dangi da yake taimakon ta tunda ba sabawa suka yi sosai ba. Har gwara Umma Sarood ?anwar mahaifiyarta ta kawo mata turaren wuta irin nasu na mutanen Chad, har kayan gyaran jiki ta haWo ta kawo mata. Mama Zainab Yayar mahaifiyarta ita kuma ta Wau?i nauyin zuba turaren wutar gidan, ta ce duk wani abu indai na ?hamshi ne ita zata yi amma bata so Omar ya sani. Didi ta ji daWi sosai har ta nuna musu, kuma suna yawan kiranta su ji shirin biki, zuwa ne dai basa yi saboda haWuwa da Omar baya zama alkhairi. Duk wani shiri ita da Hajja ake yi sai Salma da ta kasance tana tare da Hajja ko yaushe.

?angaren Omar ya watsar da duk wani abu da yake yi a baya, duk da daman ya jima da watsarwa amma yanzu yana ?o?arin ganin ko cikin ?an uwansa ?an daba na baya ya daina shiga. Ya tattara kayan sana'ar da yake so ya fara kawai yake yi, shida yaran sa su uku gabaWaya sun bashi haWin kai wajan yin sana'ar da suke fatan zata kai su inda basu yi tunani ba. Duk abinda ake saka shi a ciki a Sangaren daba yanzu an daina, ko an zo masa da maganar zai ce babu ruwansa a kai maganar gaban hukuma. Duk da hakan dai ba a kawo masa wargi saboda lasar yaji baya hana gyaWa yin garWi, duk da haka akwai sauran tsoro da kwarjinin da yake dashi a wajan mutanen gari. Halayyarsa baby abinda ya canja, baya shiga harkar kowa kuma baya sauraren kowa, fuskarsa kullum a haWe magana ma ba ya yi.

Lamarin Narma ya ajjiye a gefe, duk da yana tunawa musmaman yadda abubuwa suka faru a gidan su, kuma yana matu?ar tausayinta in yaga tarin messages da kiran da take yi masa baya Wauka. Wani messages Win ya karanta kamar ya yi mata kuka haka yake ji dalilin da ya saka ya daina buWewa gabaWaya, dan in yana buWewa zata iya karya masa zuciya wata ran ya saurareta, shi kuma in yayi gaba baya komawa baya, in tsallake baya sake tsallakawa.

" " " " " "

Nayla kuwa duk yadda ta kai ga dauriya Soye abinda yake ranta ta kasa, gashi Abiy ya matsa mata da tambaya abinda yake damunta, da ya gaji ya haWa ta da Jawad suka je asibiti, da ta faWawa likita abinda yake damunta ya tabbatarwa da Jawad tana tare da damuwa a tambaye ta aji abinda yake damunta. Duk ta tsorata saboda kar Abiy ya tambaye ta dan gaskiya bazata iya cewa ga abinda yake damunta ba dan ta san ba abu bane mai yuwa.

Bayan sun dawo daga asibitin suna zaune wajan Abiy Jawad yana yi masa bayanin abinda likitan yace. Jawad ya ce, "Zancen gaskiya Abiy likita ya ce tana tare da damuwa sosai. Dalilin damuwar shi ne yake haifar mata da zazzaSi da kuma ciwon ?irjin da ta ce tana yi. Na tambayeta abinda yake damunta amma ta ce babu komai, na tambayeta ko akwai wani mai takura mata a wajan aiki ko barazana nan ma ta ce babu komai."

Abiy ya kalli Nayla da take zaune a gefen sa a tausashe ya ce, "Mamana me yake damunki?." Nayla ta sunkuyar da kai ta ce, "Abiy babu komai."
"?arya ki ke yi, likita ai bazai miki ?arya ba sannan yanayinki ya gwada kina tare da damuwa mai tarin yawa. Me ya ke damunki? Ki faWa min ko meye zan miki maganinsa." Nayla ta yi ajiyar zuciya tayi shiru bata ce komai ba.

Abiy a tausashe ya ce, "ban kai na ji damuwarki bane?." Ta girgiza kai alamun A'a ya ce, "ni mahaifinki ne, Jawad yayan ki ne, Maman ku kuma babarki ce. Babu abinda zaki Soye mana na rayuwarki saboda mu ne ahlinki, ki faWa min abinda yake damunki nayi miki al?awarin zan yi miki maganin ko meye."

Nayla ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba. Ganin haka sai Mama ta ce, "Abiy ka bar ni da ita zamu yi magana." Abiy ya kalli Mama ta Waga masa kai ta ce, "zan yi magana da ita, zata faWa min in sha Allah. Nayla tashi ki je ki shirya, ko ba zaki je Kano bikin Didi ba?."

Nayla a sanyaye ta ce, "Zan je Mama."
Mama ta ce, "to tashi ki je ki shirya." A sanyaye ta tashi ta fita. Mama ta kalli Abiy ta ce, "kar ka damu, ka bari ta je Kano ta dawo zan tambayeta a nutse na tabbatar zata faWa min. Sai ta kasa faWa maka damuwarta amma ni ta faWa min, na san ta yadda zan bi da ita har naji abinda yake zuciyarta."

Abiy ya ce, "meyasa zaki ce ta ce ta tafi Kano bayan yanayin da take cikin na rashin lafiya?." Mama ta ce, "zuwa Kano zai Webe mata kewa sosai, ko babu komai zasu haWu da Jidda da Salma." Ambatar Jidda da tayi sai wani abu ya shiga zuciyar Abiy amma bai nuna ba ya ce, "shikenan ai, Allah ya dawo da ita lafiya. Ki tambayeta har batun samarinta."

Mama ta ce, "in sha Allah." Bata sake cewa komai ba shima haka, amma a zuciyarta tana ji lokacin da take jira ne yake gab da zuwa, da wannan damar zata yi amfani wajan cika burinta a akan Nayla.
KRB2P013
ArewaBooks@nanahaleema11

Bayan sallar juma'a Nayla suka tafi Kano, kamar ko yaushe a gidan Hajja ta sauka a lokacin Didi ma tana gidan ana ta shirye-shirye ana walima gashi washe gari ne Waurin aure. GabaWaya bata da walwala bata sakewa ayi komai da ita, tana daga gefe tana tunani ko Omar Win bata son gani saboda kar ya taso mata da abinda take son binnewa a zuciyarta.

Washe gari da safe aka Waura auren Aisha da AbdulHamid, Didi ta sha kukan farin ciki, tayi kuka kamar babu gobe Hajja ce ke aikin rarrashi tana sake tuna mata sai yanzu lokacin auren ta ya yi. Omar ma tunda aka Waura auren yake ciki da matu?ar farin ciki, duk da yana daga gefe aka yi komai, Kawu ne ya bada aurenta bai hana hakan ba saboda burinsa a Waura auren kuma an Waura. Yana sanye da manyan kaya riga da wando na farar shadda sai hula da ya saka, ya kame kansa a waje Waya ko magana ma ba yayi sai masu yi masa Allah ya sanya alkhairi.

A gidan Hajja ake taron ?an uwan su Didi na Sangaren uwa da uba duk sun zo,musamman su Umma Saroot da suka kasance iyaye a gareta duk suna nan aka Waura auren.? Su Jidda dasu Salma har da iyayen su Salma Win ma duk sun zo saboda kowa ya san Didi.

Ana ta hidima, ko wanne dangi yana so ya nuna ?auna ga Aisha da ?aninta. Wannan ya ciko cooler da abinci, wannan ya bada kuWi a siyo abinda ake bu?ata duk burin su su wanke laifin da suka yi a baya. A Sangaren Didi zata iya cewa ya wuce ta karSe su hannu biyu matsayin iyaye, babu kamar dangin Maman su in tana kallon su sai ta ga kamar mahaifiyar su take kallo. ?angaren Omar ko kallon kirki ma basa samu, in ya gansu bazai nuna ya gansu bama balle ya yi magana. Su kuma tsoron dizgi da wula?ancin da ya saba yi ne ya saka basa kula shi.

Bayan Waurin auren ne Didi ta nemi Nayla ta raka ta gidan su suka fito ita da Nayla da Salma zuwa cikin gidan. Tana shiga takar gidan taga babu kowa sai Omar da yake ya jingina da bango ya harWe hannayen sa a ?irji yayi shiru kamar mai cike da damuwa.

"Omar!." Didi ta furta murya na rawa, Omar sai ya kalle ta ya mi?e tsaye sosai ya yi murmushi ya ce, "to meye na kukan Didi?." Da sauri ta ?arasa wajansa ta rungume shi har lokacin murmushi yake yi ya Wora hannunsa a bayan ta kafin ya Wagota daga jikinsa ya ri?e kafaWarta ya ce, "meye na kuka kuma? Yau ranar farin ciki ce a gare mu gabaWaya, me ya saka ki kuka?."

"Sai naga kamar baka murna" ta faWa murya tana rawa. ?an ?aramin tsaki yayi yana murmushi ya ce, "KiWa ki ke so kiga na saka? Ko tsalle-tsalle ki ke so ki ga ina yi sannan zaki tabbatar ina murna?." Ta yi dariya kaWan ta ce, "kusan hakan." Ya kalle ta ya ce, "ban san meyasa ba amma har na fara kewarki, gabaWaya bana jin daWi."

Didi ta ce, "Omar nima ina jin hakan a zuciyata, ina ta tunanin wacece zata dinga kula min da kai?." ?ar ?aramar dariya ya yi ya kalle ta bayan ya Wage gira sama ya ce, "yaro ne ni da za a kula dani? Allah Didi kin raina ni" ya faWa yana share mata hawaye da hannunsa.

Didi ta ce, "Omar rayuwarka kai kaWai ce bana so, don Allah kawai ka yi aure." Idanu ya wara waje sosai sai kuma ya sake yin dariya mai sauti ya ce, "kawai dan kin yi aure sai nima nayi kamar ?an wahalar matan su Kawu? Su ne duk abinda Waya ta yi sai sun yi." Zata sake magana ya ce, "Didi don Allah ki yi shiru, a bar maganar nan tukunna dai."

"Ka ci abinci yau kuwa?." Ya kalle ta cike da tsonaka ya ce, "waye zai bani abinci? Bani da kowa fa" ya faWa cike da tsokana yana kallon ta. Sai zuciyar ta sake karyewa ido ya ciko da hawaye ya ce, "Wasa nake miki fa, na ci abinci tun Wazu. Kar ki yi kuka, Allah bana so." Idanunta goge tana murmushi ta ce, "ni na san cin abincin ka kuma sai yadda hali ya yi tunda babu mai ce maka gashi, daman ya lafiyar kura balle ta yi zawo."

Murmushi ya sake yi ya ce, "Yaushe za a tafi kai ki? Bana son taron mata nan da kaina zan kai ki gidanki" ya faWa bayan ya Waure fuska. Kallon sa tayi ganin ya ci magani alamun da gaske yake sai tayi dariya ta ce, "to babban yaya."
"Da gaske nake, na faWawa mijin na ki bana son taron hayaniya. Baza a je gida ai ta kallo babu mai addu'a ba."

Murmushi tayi ta ce, "Ai daman kai kullum da gaske ka ke, wannan kalma kamar a bakin ka aka yi ta. Komai ka ce da gaske nake."
"To da ?arya nake?."
"A'a, indai ka ce to da gasken ne." Share ta ya yi bai sake magana ba, tayi sosai tana mamakin ?arfin hali irin nasa kafin ta juya ga Nayla da Salma da suke tsaye har lokacin.

Didi ta ce, "Nayla ku shiga ciki na bar ku a tsaye." Kai tsaye inda ta kalla ya kalla ya haWa ido da Nayla da take murmushi tana hawaye. Salma ya kalla ya ga murmushin itama ta ke yi amma ita babu kuka. Ya Wan taSe baki kaWan ya ce, "ita wannan kullum cikin kuka?" Ya tambayi Salma yana nuna mata Nayla da girarsa.

Ba Nayla da Salma kaWai ba, har Didi sai da tayi mamakin abinda ya ce, kuma har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login