Showing 6001 words to 9000 words out of 85380 words

Chapter 3 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3827

amma bazan iya furta masa ba, kuma bazan iya faWa muku sunansa ba koda zan mutu. ?ar?ari in na mutu ku ce soyayya ce ta kashe ni keda Jidda. Tabbas in na bar duniya a yanzu da tasirin soyayyarsa a yin ajalina."

Salma ta sake karya murya zata yi magana Nayla ta katse ta ta ce, "Ya Didi? Tana lafiya?." Salma jin ta kawar da maganar sai ta ce, "Allah ya kawo miki mafita, in alkhairi ne a gare ki Allah ya zaSa miki shi ?ar uwa."

Ta amsa da amin kafin Salma ta ce, "Didi tana gida, Wazu dai ta fita daga nan, da yake a nan ta kwana." Nayla ta ce, "ta kwana a gidan Hajja? Lafiya dai ko?."
"Ba ?alau ba dai. Ta?adirin ?aninta ne mana, Wan kuka mai jawa uwarsa jifa." Gaban Nayla ya faWi matu?a ta ce, "Me ya faru?."

Salma ta ce, "Wai ?ar Senator Sagir yake so dan tsabar bashi da hankali, to ko ni zauna gari banza babana ba Senator ba yazo ya ce yana sona ba sai na saka an yi masa abinda har ya mutu bazai manta dashi ba?. Ke ko ban??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i ba, ko wacce bata kai ni rufin asiri ba ya ce yana so sai mun haWu mun hana ta sonsa saboda ba mijin da za a so bane. Wai ?afa ya Wauka yaje har Abuja gidan Kano centaral Senator wai yana son ?arsa Narma. Ki ji fa Nayla, Barr Nass fa wacce ki ke gani a social media yaje neman aure dan tsabar ?arfin hali irin nasa. Tsabar wiwin da yake sha ta taSa masa ?wa?walwa harda kwasar gajojin ?an daban yaransa suka tafi wai neman aure. Ai kam Sen ya yi ram dashi, ya saka an Waure shi yana neman hanyar da zai kai shi prison, kuma ya ce? sai ya yi life in prison."

Dum dum dum dum! Haka ?irjin Nayla yake bugawa, ta zazzaro idanu waje kamar Salma Win tana ganinta. Duk da a.c da take Wakin gumi ya gama wanke mata jiki saboda tashin hankali. An kama Omar? Omar Win ta da ake zancen zai yi life in prison? Omar fa masoyinta.

Salma ta katse mata tunaninta hanyar cewa, "Shine fa hankalin baiwar Allah ya tashi, ta shigo tana kuka abin tausayi. Allah ya haWa ka da Wan uwa irin Omar ma ko ?addara, haka kawai ya saka hankalin baiwar Allah ya tashi. Hajja har Daddy ta yiwa magana ya ce zai san yadda za ayi, za a yiwa Sen Win magana ko zai fito dashi. Gashi an ce bashi da kirki ko kusa, baya Waga ?afa akan komai da?yar ya amince ya bada Omar. Ke ni fa a wajena Omar ya cancanci fiye da haka, tsabar raini da tsaurin ido ya Wauki ?afa ya je har gida wai ?arsa yake so? Ni ban ga laifinsa ba."

Nayla bata iya cewa komai ba domin ?wa?walwarta tafi hutun rabin lokaci. Salma bata damu da shirun ba ta kuma cewa, "jiya da daddare Hajja ta saka ta dawo nan ta kwana saboda gidan babu kowa, kuma kin san ?an daba ?an uwasa masu jin haushinsa zasu iya shigowa su cutar da Didi. Inda mutumin kirki ne ma sai ka tauyasa masa, gwara ma haka."

Nayla hawaye ya gama wanke mata fuska, hawaye na tausayin masoyinta, hawaye na tausayin abin ?aunarta, hawaye na tausayin halin da yake ciki a wannan lokaci. Hango fuskarsa take yi tana tunanin yadda ya koma a yanzu. GabaWaya nutsuwarta ta bar gangar jikinta.

Da?yar ta iya buWe baki ta ce, "Allah ya kyauta" daga haka ta yanke wayar ta toshe bakinta da hannunta fashe da kuka mai sauti. Mama tana tsaye daga bakin ?ofar duk hirarta da Salma taji, girgiza kai take yi domin wannan soyayyar da Nayla ta fara babban makami ne a gareta, tunda gashi har taji tana cewa mahaifinta bazai amince ba, lallai tsuntsu ya faWo daga sama gashashshe.

Shigowa Wakin tayi tana kallon Nayla, Nayla tana ganin ta manta halin da take ciki ta mi?e a guje ta faWa jikinta tana kuka. Mama tana shafa bayanta a hankali cikin rarrashi ta ce, "yi shiru kar ki damu, kwantar da hankalinki."

Kuka Nayla take sosai na tausayi Omar da Didi, jikinta har rawa yake yi saboda tashin hankali da tsananin bugawar zuciya. Mama ta Wago ta daga jikinta ta kalle ta ta ce, "Nayla ko baki faWa min ba idanunki sun faWa min soyayya ce ta saka ki a wannan yanayi, kar ki damu kar kuma ki tsorata ni uwa ce a gare ki, zan shige miki gaba wajan samun duk abinda ki ke so a wajan mahaifinki. Haka ne hasashena?."

Nayla ta yi shiru ta sunkuyar da kai sai hawaye da yake zarya a kan fuskarta. Mama ta sake janta jikinta ta ce, "kar ki damu ki nutsu, Ina tare dake a ko yaushe. Na kuma yi miki alqawari zaki auri wanda ki ke so ko waye shi, kar ki damu da faWa min waye shi a yanzu, ki bari sai lokacin da zuciyarki ta aminta da ki faWa min. Ni kuma a lokacin zan jajirce kamar ko wacce uwa na samar miki da farin ciki. Zan sadaukar da komai wajan ganin mallaki wanda ki ke so, zan iya yin komai dan tabbatar da cikar burin ki Nayla."

Nayla kwanciya tayi a jikin Mama tana kuka tana ji wani Sangare na zuciyarta na tabbatar mata da abinda Maman ta faWa. Ido ta a kulle cikin tausayi da soyayyar Omar..
KRB2P003
Arewabooks@nanahaleema11.


Mama sai da ta bar Nayla tayi kukan ta sosai sannan ta Wago ta daga jikinta ta ?arasa da ita kan gado ta zaunar da ita, ta tashi ta kawo mata ruwa a glass cup ta sha ta zauna a gefenta tare da ri?e hannunta tana kallon ta. Nayla sai sauke ajiyar zuciya take yi irin ta wacce ta sha kuka ta gaji. A tausashe Mama ta ce, "ki nutsu, Ina tare da ke a akan duk abinda ki ke so. Mahaifiyarki ni ta barwa amanarki, bazan taSa bari wani abun ya cutar dake ba."

Nayla ?arfin guiwa maganar Mama take ?ara mata hakan ya saka ta Waga kai Mama ta ce, "Sanar dani yaushe kika fara sonsa? Sannan a Ina yake?." Nayla ta rausayar da kai ta ce, "Mama don Allah bana so Abiy ya sani."
"Bazan sanar dashi ba Nayla, ai wannan sirrin uwa da ?arta ne." Nayla ta sauke numfashi ta ce, "A Kano yake da zama Mama, kuma ni ma ban san lokacin da na fara sonsa ba."

Mama ta ce, "ya sunansa?." Nayla ta kalli Mama sai bata ce komai ba. Mama ta ce, "shikenan ba sai kin faWa min waye ba, amma meyasa ki ke cewa Abiy bazai amince ki auren shi ba? Yana da wani hali mara kyau ne ko kuwa ba musulmi bane ba?." Nayla a sanyaye ta ce, "Musulmi ne Mama, kawai dai...." Sai tayi shiru bata ce komai ba. Mama ta ce, "Ina jinki, kawai dai me?."

Nayla ta kalli Mama ta ce, "don Allah Mama mu bar maganar nan kawai." Mama tayi murmushi ta ce, "shikenan Nayla. Ki daina saka damuwarsa a zuciyarki komai zai zama labari kin ji ko?." Nayla ta Waga kai Mama ta ce, "Dama nazo na sanar dake Abiy ya ce zaki yi ba?o yau, sai ki shirya tarbar zuwansa."

Nayla ta amsa a sanyaye Mama ta dafata ta ce, "kar ki damu, zaki auri wanda ki ke so in sha Allah." Murmushin ya?e kawai tayi dan ko amin din ma bata ce ba. To in ta ce amin ta wacce hanya auren zai zo? Na farko dai Omar bai ma san tana sonsa ba, na biyu yanzu haka Omar yana kulle babu ranar fitowarsa, na uku koda yana nan ita dai baza ta ce tana sonsa ba, na huWu Abiy bazai amince ta auren shi ba. Duk da Abiy baya damuwa da lallai sai mai kuWi za a aura, amma yana son good background da kuma good manners wanda ta tabbatar da Omar ya rasa. To akan me zata ce amin? Gwara tayi shiru kawai kar ta faWa da bakin mala'iku.

Mama ta ce, "ki yi ?o?ari ki dinga sakewa in ba haka ba Abiy zai takura ki akan rashin da sakewar nan taki." Kai ta Waga kawai Mama ta fita ita kuma ta koma da baya tana ajiyar zuciya. _Ko ya Omar yake yanzu? Wanne hali yake ciki?. Allah sarki Omar ya haWu da sharrin so, son maso wani kenan, ni ina nan ina haukan sonsa shi yana can ya sadaukar da ?uruciyarsa akan wata. Ko da yake abinda nake ji shima shi yake ji a zuciyarsa akan wata, amma ni bazan iya furta Ina sonsa ba, gwara na mutu....eh gwara na mutu kawai na huta. Bayan a gabana yake yiwa wacce take son sa faWa a waya...? Hmmm ga wula?ancin da Didi ta faWa min ya yi mata a gabanta, me ya kaini cewa ina son Omar?. Gwara nayi shiru kawai na auri wanda suke sona._ tunanin da take yi kawai a zuciyarta kenan ita kaWai cikin yanayi na damuwa da bugawar zuciya.

Sai bayan sallar i'sha sannan aka turo tazo ba?on ta yazo. Da?yar ta samu ?arfin guiwar motsawa daga inda take ta mi?e ta canja kaya zuwa doguwar riga ta slik mai kyau da santsi. ?inkin bubu ne, amma wacce ake yayi, wacce ake Wan Waureta daga ciki. Tayi mata kyau sosai ta saka hular kayan sannan ta yaga mayafi ta fito zuwa falon.

Yau ma dai ba?uwar fuska ta gamu da ita, daman Abiy ya ce mata mutum huWe ne har Abbas, ta zauna da mutum biyu ga na ukun, na huWun kuma Abbas ne daman ta sani. Kamar sauran bata haWe rai kuma bata kore shi ba, sun gaisa da girmamawa ya gabatar da kansa itama ta gabatar da kanta, sun Wan tattauna kafin ya yi mata sallama ya tafi.

Kamar ko yaushe yau ma dai Abiy na zaune a falo ta dawo, shi da Yaya J ne da kuma Mama. Da sallama ta shigo kamar baza ta zauna ba sai kuma Abiy ya kira ta dole ta dawo ta zauna gabanta na faWuwa matu?a. Abiy ya kalle ta ya ce, "Mamana kun gaisa da Lamin Win?." Nayla ta Waga kai ta ce, "Eh Abiy, ya tafi ma."

Abiy ya ce, "To daga kansa zan dakatar da duk mai zuwa neman aurenki. A cikin Omar, Lamin, Abbas da Hashim ki Wauki guda Waya a cikin su. Dukkan su na amince da iyayen su, aikin su, ilimin su, halayen su da sauran su. Sannan ko wanne Wan babban gida ne sun fito daga gidan mutunci da tarbiyya. Babu Waya a cikin su da yake shan koda taba balle a kai ga batun maye ko wani abun. Babu wanda na bawa damar zuwa wajanki a cikin su har sai da nayi bincike a kansu sannan na bari suka zauna dake. Kun tattauna da ko wanne a cikin su, to ki zaSi guda Waya da ki ke jin zaki iya zaman aure dashi. A cikin guda huWu ai na san baza ki rasa wanda ya kwanta miki a rai ba, In kuma Wan uwanki Abbas kika Wauka duk Waya ne."

Nayla gabaWaya kalaman Abiy tarwatsa mata zuciya suke yi, dan gabaWaya abinda yake lissafowa samarinta suna da shi ita kuma hange ta ke yi Omar bashi da ko Waya. Gashi Abiy ya jefa ta a tsaka mai wuya, ta ya ake tunanin zata iya Waukar mutum Waya a cikin su da sunan tana so? To wa take son Win a cikin su...?ita ko kamannin su ma bata tunanin zata iya hange a idanunta balle tayi batun so, ko waya suka kirata bata jimawa take sallama dasu ta kwanta. So Waya take yiwa mutum Waya tak a duniya kuma shine Omar Tiger, ta kuma tabbatar son bashi da wani amfani tunda ba auren sa zata yi ba.

Abiy ya katse ta ya ce, "kina ji ko?." Nayla ta girgiza kai ta ce, "in sha Allah Abiy. Ka taya ni da addu'ar neman zaSin Allah." Abiy ya murmusa ya ce, "Allah ya tabbatar da alkhairi a rayuwar ku baki Waya." Aka amsa da amin ta tashi ta shiga ciki.

Abbas ta gani yana yi mata waya ta taSe baki dan baza ta Wauka ba, ita a cikin samarin nata ma zata iya auren kowa amma ban da Abbas, sam tsarin Abbas bai mata ba, ita maza masu gym Win nan ba burge ta suke yi ba. Omar ne kawai mai irin wannan jikin da taji ya burgeta amma shi kam Abbas ko kaWan bata son halittar jikinsa. A cikin samarin na ta ma gwara Omar, zata iya Waukarsa ba dan ya cancanta a wajanta ba, sai dan saboda sunan masoyinta da yake dashi kuma yana da sanyi bashi da yanayi saSanin nata Omar Win. Da wannan tunane-tunanen ta shirya ta kwanta tana tunanin halin da masoyin ta yake ciki a Abuja.

Bayan Kwana biyu.

*Abuja.*


Yadda Narma take kuka sai ka Wauka mutuwa aka yi mata, ta rame sosai ta yi wani iri da ita kamar ba ita ce Narma ?ar gayu mai ji da ?walisa ba. Soyayya ta sakata birkicewa, ta koma kamar wata mai taSin hankali saboda surutan da take yi ita kaWi. Wannan dalilin ya saka iyayenta suka sake gasgata asiri Omar ya yi mata.

"Mum ni bana son barin Nigeria, in naje England me zan yi a can?. Ni ku barni na zauna a nan babu inda zan je" ta faWa tana kuka tana ri?e da Mom da take ri?e da ita itama. Mum a tausashe ta ce, "zaki je can ne ki samu hutu Narma, ba zama zaki yi a can gabaWaya ba, zaki huta ne na Wan lokaci sannan ki dawo kin gane?."
"A'a Mum, ni a barni na zauna a nan bana so na tafi na bar Faruk a gidan da Dad ya kai shi, ban yi masa adalci ba in na tafi tunda ni ce na gayyato shi. Don Allah ku bani dama na fitar dashi sai na tafi."

Dad ya ce, "Narma! Ki yi abinda aka ce kawai." Narma ta ce, "Dad bashi da laifi fa, ni ce nace Ina sonsa har ya amince dani, kuma ni na gayyace shi nan ya amsa gayyata ta yazo. Sai da ya maimaita min babu matsala na ce masa babu saboda na yarda da alqawarin da kayi min, ban Wauka zaka yi disappointing Wina ba Dad. Na Wauka kana son duk abinda nake so, na Wauka zaka bani abinda nake so ko meye shi, amma ka kasa....ka kasa bani farin ciki Dad...ka kasa cika min burina..." ta faWa tana kuka sosai. Dad cikin tsawa ya ce, "Narma ya isa! Kar na sake ji kin ce nayi disappointing Win ki

Narma ta ce, "inda falon sama zai yi magana zai bada shaida, kai ka ce ko waye kana maraba dashi, kai kace kana maraba da shi matsayin sirikinka, da yazo dan ya gaishe ka ga abinda ka yi masa. Ina sonsa, ku barni na zauna a nan in ba haka ko na je can bazan ji daWin zaman ba."

Dad a fusace ya ce, "sai kin tafi! sai kin je England in ki yi duk abinda zaki yi. Last warning zan miki yanzu, kar na sake ji kin furta na karya miki alqawari, kar na sake ji kin ce kina sonsa kin gane!?." Kallon Dad Win take yi dan bata saba jin tsawa daga wajan iyayenta ba hakan ya bata mamaki ta ce, "Dad you shouted me?."

Mum ta katse Sen ta ce, "Dear stop please, ka daina sake tsorata ta don Allah. Ka bari mu ji da yanayin da take ciki mana." Shiru ya yi bai ce komai ba ta kalli Mum ta ce, "Mum zaki saka a fito dashi? Dad ya saka ana ta wahalar dashi. Zaki bari na aure shi?."

"Babu maganar aure tsakaninki dashi, in akwai a zuciyarki ya kamata ki goge dan ba abu ne da zai yu ba" Dad ya faWa yana nuna ta da yatsa dan ta fara fusata shi. Zata yi magana ya katse ta ya ce, "kar ki ce min komai, zaku yi missing flight ku wuce ku tafi" ya faWa yana hawa sama. Narma tana kuka Mum ta ri?e ta har bakin mota, ta shiga itama sai da ta kai su airport tana jajjadawa Najwa kula da ita, sai da taga tashin jirginsu sannan ta dawo.

Kai tsaye Wakin Dad ta shiga ta same shi ta ce, "ya zama dole a saka Tiger ya karya asirin da ya yiwa Narma, sannan ya zama dole a samu abinda zai Wauke mata hankali a London." Dad ya kalle ta ya ce, "na san abinda zan yi akan maganar Tiger. Maganar Narma a London kuma Ina tunanin nan da kwanaki biyu na tura mata Ashraf."

Mum da mamaki ta ce, "Ka tura mata Ashraf for what?." Dad ya ce, "Auren masa ita zan yi." Mum ta wara idanu waje ta ce, "aure fa? Auren Narma ne zai kasnace a haka?." Dad ya ce, "kina da wata hanyar ne bayan wannan? Ashraf shine boyfriend Winta, shi ta so kafin asirin Tiger ya kamata, in aka Waura auren su ya bita London zai Wauke mata kewar Omar har ta manta dashi. Ki daina tunanin a yadda auren zai zo, ki duba yanayin da ?arki take ciki. Ba lallai sai duniya ta san anyi auren ba, in aka Waura auren daga baya in ta dawo daidai sai ayi biki mai girma. Amma a yanzu ba maganar biki ake yi ba, magana ake ta ceto Narma."

Mum tayi ajiyar zuciya ta ce, "Dear Don Allah ka tabbatar da Tiger baya numfashi a duniya, ka tabbatar da ?asa ta rufe idanunsa. Duk ta silarsa wannan abubuwa suke faruwa, don Allah a Satar dashi a daina jin labarinsa, hakan shine kawai zai saka na huce daga raWaWin abinda ya yiwa Narma." Sen ya taso ya rungume ta ya ce, "kar ki damu Dear, na san abinda zan yi akansa. Labari da tarihin Omar zai shafe a duniya gabaWaya, don't worry."

"Saboda shi Narma ta tafi London

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login