Showing 51001 words to 54000 words out of 85380 words

Chapter 18 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3828

Nayla ya ce,  Hauwa!.

Nayla murya na rawa ta ce,  Na am Abiy.
 Tunda ta nan ki ka Sullo zan yiwa tufkar hanci, zan sake baki dama ki fitar da mijin aure a karo na uku, in kika sake aikata irin abinda kika aikata yanzu bazan sake baki dama ba har abada. Sannan ki cire batun wannan yaron daga zuciyarki, ba mijin aure bane, in ma bakya cikin hankalinki to ina mai baki shawara da ki dawo cikin nutsuwarki ki san waye a gaban ki! Ya ?arasa faWar maganar da tsawa yana nuna ta da yatsa.

 In da ace ya dace ya kuma cancanci ya zama mijinki zan iya amince miki, amma yanzu ki adana kalamanki bana son sake jin magana irin wannan daga cikin gidan nan, ki Wauka baki san shi ba, ki kuma manta dashi a cikin zuciyarki. Kin ji abinda na ce ko?. Nayla ta Waga kai kafin ta ce,  Naji abiy, zan yi in sha Allah.
 Yafi miki yana gama faWar hakan ya fita daga Wakin ya barta a ita da Mama.

Mama ce ta ri?eta ta mi?ar da ita tsaye ta ce,  ki kwantar da hankalinki komai zai zama daidai nayi miki alqawarin hakan, kar ki damu da kalaman mahaifinki zan san yadda zan yi ya sakko ya fahimce ki. Nayla ta ce,  Mama kawai ki ?yale shi, ni daman sai da nace tsoro nake ji kar a faWa masa kika ce a faWa masa, kinga ransa ya Saci yanzu ni kuma bana son hakan. Don Allah ki ?yale shi kawai Mama ni na ha?ura, zan Wauki mutum Waya a cikin waWancan kawai na huta. Mam ta ce,  kar ki cuci kan ki, kar ki cutar da zuciyarki saboda faWan mahaifinki na yanzu. Zai sakko na yi miki wannan alqawarin, zai amince da auren ki da Omaar kar ki damu.

Nayla dai hawaye take gogewa tana ji zafi a zuciyarta da ta fara son wanda soyayyar sa bata da wani amfani a gareta da cikin rayuwarta baki daya.

Mama fita tayi zuwa wajan Abiy ta same shi a zaune da alama har lokacin ransa a Sace yake sosai ta zauna ta ce,  Lamarin Nayla ya fara bani tsoro wallahi, da gaske sonsa take yi fa. Ka ji irin kalaman fitar hankali da take faWa bayan fitar ka? Ita sai ta aure shi, shine farin cikinta, kalamai dai barkatai. Allah ya kawo mana mafita a wannan lamari kawai.

Sake tunzura zuciyar Abiy Mama tayi ya yi ?wafa ya ce,  Ashe da gaskiyar Senator Sagir da ya ce na bincika anya nima bai yiwa Nayla asiri ba, a lokacin sai nake ganin ba haka bane ashe da gaske dai asirin yake yi, tunda ga Nayla ma tana neman fita daga hankalinta saboda shi.

Mama ta ce,  ni wallahi gani nake ba wani asiri da yake yi, kawai zuciyarsu ce bata yi musu adalci da take fara son wanda bai kamata ma ace ta so ba. ?an shaye-shaye, Wan daba, karen ?an siyasa, wanda ya yi zaman prison, abubuwa da yawa marasa daWi akan mutum meye abin so a wajan?. Allah yasa kar ya shirya ya Wauko ?afa yazo yace yana son Nayla.

Abiy ya yi shiru kawai amma gabaWaya zuciyarsa bata yi masa daWi, sam bai ji daWin kalaman Nayla akan tana son Omaar ba. Meye abin so a Omar don Allah? Me yake dashi da har Nayla ?ar cikin sa zata ji tana so duk wannan tarin abubuwa marasa kyaun da suke dabaibaiye shi?. Tsaki Abiy yayi ya sauke numfashi ya kulle ido amma bai ce komai ba. Mama ta ce,  Ashe daman yawan zuwa Kanon da take yi duk saboda shi ne, wallahi ?unar abinda nan nake ji har zuciyata. Inda mutum ne na gari ma da sau?i, amma irin wannan Wan iskan garin meye amfanin son sa?.

Abiy nan ma bai ce komai ba amma kalaman Mama tuna masa wasu abubuwan suke yi musamman yawan san zuwa Kano da Nayla take dashi, bai taSa kawo haka a zuciyarsa ba amma yanzu ya kawo hakan ya kuma tabbatar da saboda shi take zuwa Kano a kai a kai tunda ma?ocin Hajja. Girgiza kai ya yi kawai ya tashi ya barwa Mama wajan gabaWaya jikinsa ya yi sanyi.

Mama ta yi murmushi ta ce,  Ai indai Ina nan sai Nayla ta auri yaron nan, a gaban idonka Ina tare da kai, amma a bayan idonka ni ce zan dinga zuga Nayla akan Omar. Haba ai dole ma ta aure shi hakan shine zai saka ni farin ciki da kwnaciyar hankali a zuciyata. Ko babu komai na san zata je inda bazata taSa farin ciki ba a rayuwarta, tunda baya sonta itace take sonsa kuma ga yanayin halayyarsa komai zai iya faruwa ta faWa tana murmushi cikin ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?farin cikin cikar burita.

Nayla haka ta kwana ciwon kai saboda damuwa da kukan da tayi, da safe kasancewar Sunday ce babu aiki ta jima tana bacci sai sha biyu na rana sannan ta fito babban falo ta tarar da Jalil yana game a tv. A sanyaye ta ce,  Auta Abiy yana nan?. Kai ya Waga mata ya cigaba da game ta nufi Sangarensa.

Mama ta gani ta fito daga apartment Win Nayla ta kalleta ta ce,  Mama Ina kwana. Da kallo ta bita kana ta ce,  Lafiya lau Nayla. Lafiya naga fuskarki ta kumbura? Kar ki ce min kwana ki ka yi kina kuka?. Nayla ta sunkuyar da kai kafin ta ce,  Mama Abiy yana nan?. Mama ta ce,  ya kwanta sai dai zuwa anjima. Zo mu je ta faWa tana jan hannun Nayla zuwa Wakin ta.

Mama ta kalleta ta ce,  Nayla faWa min kuka ki ka kwana kina yi?. Nayla a sanyaye ta ce,  na dai yi kuka amma ba kwana nayi Ina kuka ba Mama. Mama ta ce,  mahaifin naki ai ya fara sakkowa, shiyasa nake faWa miki indai ina nan zan san abinda zan yi ya amince da auren ki da Omaar. Tunda yaron yanzu kince ya daina abinda yake yi ya kama sana a hannu biyu, to meye aibu? Ai ba a tuna da abinda ya wuce abinda yake faruwa yanzu ake kallo. Yanzu kafin ya kwanta maganar mu ke yi yana tambayata da gaske kina sonsa, na ce kina sonsa mana shine ya ce yana so ya sake tabbatarwa daga bakinki, in kina sonsa sosai zai iya amincewa ki aure shi tunda kina so. Amma in bakya sonsa zai bari ki samu wanda ki ke so.

Nayla ta kalli da sauri Mama ta ce,  Da gaske mama?.
 Da gaske mana Nayla. Ke kin san Abiy yana matu?ar son farin cikinki, zai iya sadaukar da nasa farin cikin saboda naki farin cikin kawai. Dan haka ki daina damun kanki a hankali zai amince kawai ki bashi lokaci. Sannan in ya sake tambayarki akan Omar ki tabbatar masa da Omar shine rayuwarki, rasa Omar daidai yake da rasa ranki. Na tabbatar yana jin haka zai amince miki Wari bisa Wari.

Nayla ta ce,  Amma Mama sai nake ganin kamar bazai amince ba. Ni na ha?ura wallahi, daman shi ma bai san Ina sonsa ba, bai san ina yi ba gwara na auri wanda suke sona da na auri wanda nake so shi ba sona yake yi ba. Ni kawai ki daina masa maganar,in ya tambaye ni zan faWa masa sunan Waya daga cikin waWanda ya ce na zaSi mutum daya a cikin su.
 Kar ki aikata haka, in kika aikata haka daidai yake da kin saka ?afa kin yi fatali da farin cikin ki ne. Na faWa miki Abiy yana son farin cikinki, zai iya yin komai saboda farin cikin ki meyesa ki ke haka? Ko baki yarda dani ba ne?.

Nayla kamar zata yi kuka ta ce,  Mama in ban yarda dake ba da wa zan yarda?. Mama ta ce,  to ki kwantar da hankalinki na faWa miki zanyi duk abinda uwa take yi dan samarwa da Wanta farin ciki a kan ki, haihuwar ki ce kawai banyi ba, amma ni na raine ki har kika kawo yanzu. Kedai ki bani haWin kai ko me nace miki ki yi shikenan komai zai wuce. Mahaifinki zai daina fushi dake, kema zaki samu abinda kike so ba shikenan ba?.

Nayla ta Waga kai ta ce,  To Mama, na yarda dake zan kuma yi duk abinda ki ka ce. Na gode Mamana, ina sonki. Mama ta shafa fuskarta ta ce,  ai ba ke kika Worawa kanki soyayyar ba, Allah ne ya Wora miki kuma shine zai yaye miki. Tunda har Allah ya saka miki soyayyarsa a zuciyarki wata?ila alkhairi ne ga rayuwarki, kar ki ji komai ki Wauka kamar an yi an gama ne.

Nayla ta rungume Mama itama ta rungume tana shafa bayanta ciki sigar rarrashi. Nayala gabaWaya jinta yake wani iri, wani Sangare na zuciyarta ya amince da maganar Mama wani kuma zuciyarta tana rawa a kai. Ta san Mama bazata cutar da ita ba amma ta rasa dalilin da ya saka zuciyarta take rawa akan kalaman Maman ta.

Nayla bata haWu da Abiy ba sai yamma, ta same shi a falo a zaune dashi da yaye ta da ?anenta. Abin mamakin bai nuna mata komai ba sun gaisa kamar ko yaushe, sai taji kalaman Mama sun samu gurbi sosai a zuciyarta, kamar yadda ta ce Abiy ya sakko kenan ya sakko Win tunda gashi sun gaisa hankali kwance bai yi mata faWa ba bai kuma Waure fuska ba. Duk da dai walwalarta ta ragu sosai amma hakan yayi mata daWi yana lura da yadda yake ta murmsmushi amma bai ce mata komai ba.

Abiy bai sake yi mata maganar ba sai ranar talata da daddare tana zaune a falo ita da Mama da Abiy tana cin abinci kasnacewar su Auta sun kwanta saboda akwai makaranta washe gari. Abiy ya kalle ta yana lura da ita cikin kwanakin gabaWaya komai a sanyaye take yi, sannan bata da lafiya kawai dauriya take yi saboda shi.

 Nayla!. Abiy ya kira ta yana kallon ta. Gaban ta ya faWi ta Wago ta kalle shi ta ce,  Na am Abiy.
Ya kalle ta sosai ya ce,  Ya maganar da mu kayi akan wanda zaki aura Win?. Ta kalli Mama da take kallonta ta sake kallon Abiy ta ce,  Abiy duk abinda kace.

 A a abinda kika ce dai, faWa min waye zaSin ki?. Nayla tayi ajiyar zuciya tayi shiru bata yi magana ba. Abiy ya bita da kallo kafin ya Wauke kai ya ce,  ke nake jira. Ta yi shiru ta kasa furta komai gabWaya kwarjinin Abiy ya dabaibaiyeta.

Mama ta ce,  Nayla kar ki ji tsoro mahaifinki ne, ki faWa masa abinda yake zuciyarki. Nayla ta kalli Mama ta sake kallon Abiy ta sunkuyar da kai tana ajiyar zuciya. A kasalance ta ce,  Abiy&  Sai ta kasa ?arasawa ta sunkuyar da kai. Abiy ya sauke numfashi ya ce,  faWi ina jinki. Mama ta kalle shi ta ce,  tana jin nauyin ka sosai, ka bari na tambaye ta zata fi sakewa ta faWa min. Abiy ya kalli Mama ya ce,  ni ba?onta ne da take jin nauyina?.
 Amma ka san maganar aure ce, dole zata ji nauyi sosai. Abiy ya ce,  to ki tambaye ta sannan ku dawo tare. Mama ta mi?e ta ri?e hannun Nayla suka shiga Waki.

Suna shiga dakin Mama ta kalli Nayla ta ce,  Meyasa kike jin tsoron faWar abinda yake zuciyarki ne? Na faWa miki kar ki ji tsoro Ina tare da ke amma kin ?i ji ko?. Nayla ta ce,  nauyin Abiy nake ji, kuma sai nake ganin kamar bazai ji daWi ba.
 Baki yarda dani ba ne?.
 Na yarda Mama.
 To ki faWa masa ke Omar kike so, shine wanda ki ke burin aure.
 To Mama, Allah ya sa na iya.
 Zaki iya. Indai da gaske kina sonsa zaki iya, ki rufe ido kar ki kalli idon mahaifinki, ki saurare zuciyarki duk abinda yazo zuciyarki kawai ki furta.

Nayla cikin gamsuwa da ?arfin guiwa ta ce,  To Mama zan yi. Mama ta ce,  nutsu ki biyo ni ta faWa. tana fita ta bar Nayla. Nayla addu a ta fara yi a zuciyarta sannan ta fito ta samu Mama a zaune inda ta tashi itama taje ta zauna inda ta tashi. Abiy ya kallli Mama ya ce,  me ta yanke?. Mama ta kalle shi ta ce,  Omar Win dai.

Abiy ya kalli Nayla bayan ya Wan Waure fuskq ya ce,  Nayla bani amsa. Nayla ta rufe ido kamar yadda Mama tace, ta yi shiru tana sauraron bugun zuciyarta sannan ta ce,  Eh Abiy. Shi nake so kuma shi nake so na aura. Shiru tayi kuma bata buWe idon ba. Jin shiru yayi yawa ya saka ta buWe ido taga yadda Abiy ya kafa mata ido yana kallo ko kiftawa baya yi. Ajiyar zuciya yayi ya tashi zaune sosai ya haWe hannayensa waje Waya ya ce,  Omar Win Kano kike so ko?. Ta sunkuyar da kai tare da Waga kai alamun eh.

 FaWa min meye sana arsa?. Nayla tayi shiru bata ce komai ba. Abiy a kausashe ya ce,  kar na sake tambayar ki kiyi min shiru!. Nayla ta gyara zama cikin rauni da sanyin murya ta ce,  ance yana sana a yanzu.
 Okay, da fa?. Nayla ta diririce sosai a raunane take magana ta ce,  ban sani ba Abiy.

Abiy ya ce,  FaWa min aikin da ke kika san yana yi. Nayla saboda tsoro har zufa take yi duk da sanyin a.c da yake tashi a falon, ta ce,  ban san yana ko wanne aiki ba. Abiy ya ce,  yanzu in kika je neman sa unguwar su Hajja wanne suna za a faWa da za a gane shi?. Nayla ta ce,  Tiger.
 Meyasa ake ce masa Tiger?.
 Saboda Wan daba ne.
 Meye aikin ?an daba?. Tayi shiru bata amsa ba, cikin tsawa Abiy ya ce,  ba magan nake miki ba!?. Nayla ta tsorata ta ce,  Waukar wu?a?e.

 Su yi me da wu?ar in sun Wauka?. Nayla hawaye ya sakko mata cikin muryar kuka ta ce,  su yanki mutane.
 Ko su kashe su ko? Ya tambaya yana tsare ta da idanu. Ta Waga kai alamun eh. Numfashi ya sauke ya kalle ta yayi shiru zuwa wani lokaci kafin ya ce,  duk da tarin abubuwan nan da kika faWa a kansa kike iya kallona kina cewa kina sonsa Nayla?. Ta sunkuyar da kai tana goge hawaye cikin karayar zuciya.

Abiy ya canja murya zuwa tausasawa ya ce,  Akwai abinda na rage ki dashi a gidan nan?.
 Babu komai Abiy.
 Meyasa kika sake maimaita min kina son Wan daba Nayla?. Muryarta fara rawa sai ta kasa magana ta fara kuka sosai. Abiy ya ce,  Nayla! Daga yau, daga yanzu, daga wannan lokaci kar na sake jin kin furta wannan maganar, in har na isa dake kar na sake ji kince ke shi kike so in ba haka ba wallahi zaki dana sani a cikin rayuwarki. Sannan ki yi gaggawar mantawa dashi kafin na saSa miki. Zan iya Waukar ko wanne shirme amma banda wannan, zan iya baki aure mai gadin gidan nan amma banda shi.

Kuka take yi bata iya cewa komai ba. Abiy ya fusata matu?a ya ce,  akan sa ki ke kuka!? A kansa kike zubar da hawaye!?. Nayla ta girgiza kai alamun a a tana kuka.
 To kiyi shiru ki goge wannan hawayen. Da sauri ta goge idanunta jikinta har rawa yake yi dan bata da tsawar abiy ba.

Abiy ya ce,  inda ace mutum ne gari na sai na amince miki ki aure shi, inda mutum ne kamar kowa sai amince miki, inda mutum ne mai hankali da Wabi a mai kyau sai na amince miki. Amma bazan aurar dake ga namiji irin sa ba, in ma kina wannan mafarkin ki daina, dan baza ki aure shi ba sai dai in bani da rai!!.

Abiy ya sake cewa,  Dan haka ki goge labarinsa a zuciyarki shine kwanciyar hankalinki kin ji ko?. Ta Waga kai alamun to tana share hawaye. Abiy ya kausasa murya ya nuna ta da yatsa ya ce,  gargaWi na ?arshe Hauwa, wallahi kar na sake Jin wannan maganar a bakinki, in dai na isa dake ki ajjiye batun nan, in kuma ban isa dake ba na sake jin wannan maganar Nayla!.

Nayla tana kuka ta ce,  bazan sake ba Abiy, bazan sake ba. Ka yi ha?uri. Nima ban san na fara sonsa ba, ban san ina sonsa ba. Wallahi Abiy da zan iya mantawa dashi da tuni na manta, na kasa Abiy, na kasa mantawa! Ta faWa cikin fitar hankali ta manta ma abinda take cewa.

Zuba mata ido yayi jin abinda take cewa kafin ya ce,  kina faWa min kin kasa mantawa dashi ni kuma nace ki manta dashi Hauwa! Dole ki manta dashi, ko kina so ko bakya so. Ba sa an aurenki bane, ba daidai yake yake ba, rayuwarsa da taki ba iri Waya ba ce!. Sai da ta firgita jin tsawar da Abiy yayi mata ta sake fashewa da kuka cikin ?unar zuciya da tsoro.

Abiy ya tausasa murya ya ce,  ki daina kuka, ki tashi ki bani waje, kije ki cigaba da addu a Allah ya cire miki shi daga zuciyarki. Sannan ki tabbatar da kin fitar da wanda kike so in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login