Showing 9001 words to 12000 words out of 85380 words

Chapter 4 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3826

ba dan tana so ba, saboda shi ana ?o?arin yi mata irin wannan auren. Ji nake kamar na kamo shi na harbe." Bayan ta yake shafawa cikin rarrashi amma shi kansa abin ya tsaya masa a zuciya, zai kuma zan abinda zai yi.

*Kano.*

Didi tun tana jiran tsammani daga Hajja har ta gaji, ba labarin ceto mata ?aninta gashi har an yi kwanaki goma da kama Omar. Duk ta damu ta koma wani iri ?an unguwa kaf an fahimci Omar baya nan, duk da haka babu wanda ya yi gigin yiwa Didi wani abun a san duk inda ya je tabbas ai dawo.

A ranar Bashir ya ce mata zai je Abuja ya duba prison ko an kai Omar Win can. Sai dai ya je Win ya faWi sunan Omar matsayin wanda yazo yiwa ziyara, kaf sunayaen mutanen da suke ciki babu mai suna irin na Omar. GabaWaya ya damu shima a haka ya dawo Kano a ranar duk ya galabaita.

A gidan Hajja ya same ta da daddare ko abinci ta kasa ci tana jiran dawowarsa. Tana jin sallamar da ta mi?e tana kallon sa har ya shigo yana kallon ta shima. Hajja ta ce, "Bashir ka ga Omar Win?." Bash ya girgiza kai ya ce, "Ban gan shi ba, ko mai irin sunan sa an tabbatar da baya cikin prison Win."
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Shikenan sun kashe min Omar, Hajja sun kashe min shi" ta faWa cikin kuka sosai. Hajja ta ri?eta cikin tausayi ta ce, "Haba Aisha! bai kamata ki yi wannan tunanin ba, in sha Allah Omar yana nan da ransa kuma zai dawo gare ki in sha Allah."

Didi tana kuka ta ce, "Hajja in ba basu kashe shi ba yana ina? Meyasa ba a same shi a can ba?" Ta faWa tana sake fashewa da kuka cikin rashin mafita. Sai kuma ta kalli Bashir a firgice ta ce, "Zaka iya raka ni Abujan gobe? Ina so naje gaban Senator da kaina na bashi ha?uri akan abinda Omar ya yi masa. Zaka raka ni mu je tare?."

Hajja ta kalle ta tana jinjina girman ?aunar da take yiwa Omar tace, "wa kika sani a Abujan da zakije? Sannan kema in ya yi miki wani abun fa?." Didi ta ce, "Hajja gwara na je, gwara naje Hajja bazan iya zama babu Omar ba. Ban san halin da yake ciki ba, ko zai yanka ni gwara naje na bashi ha?uri."

Tausayi ta bawa Hajja ta dinga rarrashinta amma ta kafe akan ita fa sai ta je Abuja. Hajja ganin ta kafe ya saka ta ce, "Shikenan Allah ya kaimu goben, zan saka a kai ki da motata sannan ku tafi Bashir Win." Didi ta ce, "Na gode Hajja." Hajja ta ce, "ya isa, ki daina wannan kukan shine bana so."

Hajja ta kalli Salma ta ce, "Ko zaki raka ta Abuja gobe?." Salma ganin Didi ba ita take kallo ba sai ta wara ido ta ce, "Zan je wajan Daddy gobe." Hajja ta kalle ta kawai dan daman ta san baza ta je ba, dama dai Nayla ce. Ita kuwa Salma ?un?uni take yi tana cewa, "Haka kawai na je nima ayi ram dani, wallahi bazan je ba ita dai taje tunda Wan uwanta ne. Haka kawai babu dangin iya babu na Baba ga rashin mutuncin da yake yiwa mutane, naje na bada ha?urin a karSo shi ?arshe ya dawo yana yi min wula?anci. Bazan je ba wallahi."

Ranar da?yar Didi ta iya yin bacci,asubar fari suka buga sammako suka Wauki hanyar Abuja da fatan dacewa da kuma nasara a kan abinda zai kai su Abujan.

*Kaduna.*

Nayla ta damu sosai akan Omar, tana ?o?arin dannewa ne kawai saboda Mama tace ta dinga daurewa saboda Abiy, amma Allah kaWai ta san meye a zuciyarta da kuma abinda take ji akan Omar da rashinsa da aka ce ba a yi ba. Ta fara neman hanyar da zata bi wajan ganin ta dawo da Omar, ta rasa inda zaje ta samu damar da za a iya yiwa Sen magana ya sakar mata masoyinta. Tana nan tana shiri akan tunkarar Ogan su na wajan aiki da maganar Sen ko Allah zai saka a dace.

Video call Nayla da Salma suke yi suna hira, hirar dai rabi rarrashin Nayla take yi akan abinda yake zuciyarta. Nayla ta ce, "Salma ya batun Didi kuwa? Omar Win ya dawo?." Salma ta yi ?aramin ta ce, "ke wai kullum sai kin tambaye ni batun wani Omar? Ina ruwanki da dawowarsa ne?." Nayla ta daure ta ce, "Ina damuwa ne saboda Didi kawai malama."

Salma ta yi tsaki ta ce, "Har yau dai babu labari, Daddy bai san kowa da yake da alqala mai kyau da Senator ba. Allah sarki kin san me?." Nayla da ta ke ta shirin tafiya aiki ta ce, "Sai kin faWa."
"Didi ta Wauki hanyar zuwa Abuja dan ta bawa Sen ha?uri. Wallahi ni itace take bani tausayi ba shi ba. Ban Wauka haka take tsananin ?aunar Omar ba sai yanzu, gabaWaya ta firgice in kika ganta sai ta baki tausayi. Tana son ?anin nan nata, gashi Allah ya haWata da ?addara, dan Wan uwa irinsa ai ?addara ce." A sanyaye Nayla ta ce, "ita da wa ta tafi?."
"Ita da yaron sa Bashir sai Hajja da ta saka Sayyadi ya kai su."

"Allah sarki, Allah ya sa tayi nasarar zuwa, Allah yasa su dawo tare."
"Amin. Ke ni bana so ma ya fito wallahi, haka kawai yake bani haushi." Nayla sai taji ranta ya Saci sosai da kalaman Salma akan Omar, ta harare ta tare da yin tsaki ta ce, "Sai ki ta ji ai, bani da lokacinki" ta faWa tana datse kiran tana jin zuciyar ta bugawa sosai. Tabbas ya kamata tayi wani abun akan Omar.

A haka ta gama shiri ta fito zuwa falo ta tarar Abiy ma bai fita ba. Ganin sa a falo sai suka gaisa ya ke cewa, "ya zaki yi da bikin yayarki Shayida ta Kano?." Nayla ta ce, "Zan je."
"Aikin fa?." Nayla ta kalli Abiy jin abinda ya ce sai ta ce, "Abiy ai na lokaci Waya ne, zan Wauki excuse ." Abiy ya ce, "har yaushe kika fara aikin da zaki fara Waukar excuse? fara Waukar excuse ya yi wuri Mamana."

"To Abiy haka za ayi bikin Yaya Shayida babu ni?" Ta faWa tana hawaye daman a wuya take, kukan take son yi. Abiy ganin tana kuka aya yi tsaki ya ce, "to meye abin kukan? Kwana biyu kin zama shagwaSaSSiya, da anyi magana sai kuka."

Ta share ido dan a zahiri ne kawai take kukan son zuwa bikin Shayida Kano, amma a baWini Omar ne a zuciyarta. Abiy ya ce, "akwai abinda zai kai ni Kano ni zan riga su Maman ku yin gaba, babarki ma ta ce ranar laraba zata tafi, in sun tafi ranar laraba Win ai Jawad yana nan, sai ku zauna tare in ya so ranar Friday sai ki tafi kema."

Nayla ji tayi kamar an sakata aljanna saboda farin ciki, ta kasa Soyewa ta ce, "To Abiy Allah ya kaimu, na gode sosai."
"To maza tafi aiki." Hanyar fita tayi tana murna ya ce, "kin yi breakfast?." Nayla ta ce, "nayi takeaway sai naje can."
"Okay, Allah ya kiyaye" ta amsa da amin ta fita tana murya. Ko babu komai zata je Kano, duk da dai Omar Win baya nan amma zata je ko gidan su ne ta kalla ta ji daWi, kuma tayi al?awarin zata yi duk yadda zata yi wajan ganin Omar ya dawo.

Fan's Waye zai ci wasan ne? Nayla ce ko kuma Narma?. Waye zai yi silar dawowar Omar? Nayla ce ko kuma Narma ko kuma Didi ce?.
KRB2P004
Arewabooks@nanahaleema11

Su Didi sun isa Abuja sha biyu na rana, Bashir yana yiwa driver Hajja kwatancen estate Win da zasu shiga wancan lokacin. Suna zuwa gate na estate Win suka ganshi a kulle ga manyan jami'an tsaro a wajan da alama ba a shiga. Didi ta kalli Bashir ta ce, "ba a shiga ne?." Bashir ya ce, "Gaskiya mu ma saboda Damisa ne a lokacin mu ka shiga, amma yanzu ban san ta ya zamu shiga ba." Tk ya ce, "muje muyi magana dasu mana."

Didi ta ce, "A'a karku je su yi mu ku wani abun fa." Tk ya ce, "kar ki damu babbar Yaya, Bash mu je" suka faWa suna fita zuwa wajan su. Sun jima suna magana kafin su dawo su kalli Didi Bashir ya ce, "sun ce ba a shiga dole sai da izini." Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "kawai dai munyi wahalar banza za su ce." Kallon gidan da aka nuna mata na Sen ta ke yi don shine na biyu layin, jinjina girma da kyaun da take yi a zuciyarta.

Didi ta ce, "Bashir ku shigo mu san abinda zamu yi, gashi mu ba wani muka sani a garin nan ba balle mu je mu huta." Driver Hajja ya ce, "Akwai gidan da Hajja ta ce na kai ku ku huta a can, ku zo mu je in yaso in anjima sai mu sake dawowa nan Win." Shiga motar suka yi ya bar unguwar dasu zuwa gidan da Hajja ta ce su je.

Gida ne babba mai apartment guda biyar, ya faka motar ya fito suka shiga ciki yana cewa, "Gidan Hajja ne da take bayarwa haya, Waya daga cikin gidajen da mahaifiyar Nayla ta rasu ta bari Hajja ta gada, shine take karSar kuWin haya. Wannan Sangaren babu kowa ta ce na kawo ku nan a huta in yaso gobe sai mu koma Kano."

Didi murmushi take yi a bayyane ta ce, "Allah ya sakawa Hajja da alkhairi, ya biya ta da aljanna. In ba ita ba waye zai yi min haka?." Suka amsa da amin suna shiga ciki. ?ofar farko ya nunawa Bashir da Tk ya ce, "ga Waki a nan sai mu zauna a ciki, ita sai ta shiga ciki." Da to suka amsa suka shiga ciki itama ta shiga.

Falon harda kujeru sai dai ya Wan yi ?ura, bata damu ba ta zauna sai ga wuta haske gauwaye ina. Sayyadi ne ya shigo da sallama ya shigo ya kunna mata a.c sannan ya kalle ta ya ce, "yanzu za a kawo abinci." Ita dai Didi murmushi take kawai cikin jin daWi. ?aunar Hajja da iyalanta take ji a zuciyarta, girma da darajar na sake mamaye mata zuciya. A nan suka ci abinci suka Wan huta, ita dai tana kwance ne kawai amma burinta kawai ta ga Sen ta nemi alfarma ko zai amince.

Sai dare sannan suka koma wajan suka tarar an canja masu tsaron wajan ba na Wazu bane, suka sake yi musu magana amma basu bada dama ba Didi ta ja ta tsaya a wajan ta ce babu inda zata je sai ta ga Senator. Sun hana su tsayawa a wajan gate Win, sai can baya suka koma kamar almajirai.

Motar Sen ce take fitowa daga gidan ba tare da jiniya ko jami'an tsaro ba, ya hangi su Didi a tsaye tunda a baya yake zaune amma bai san su waye ba, suka wuce su dan ya Wauka almajirai ne. Bashir ya kalle ta ya ce, "shine ya wuce a cikin motar nan." Didi ta ce, "mu jira dawowarsa to."

Haka suka ta zaman jiransa sama da awa uku sannan motar ta dawo ta sake wuce su ta tsaya a wajan masu gadin wajan Sen ya sauke glass daga baya da yake zaune ya ce, "su waye waWancan can a tsaye? Meyasa ku ke barin mutane a tsaye a bakin gate Win nan?." ?aya daga ciki ya ce, "Sorry Sir! Sir kai suke nema, tun da rana suka zo. Na gansu a lokacin da nazo wajan Jibson."
"Ni suke nema kuma? Ina sadaka ne a gidana?."
"Haka dai suka ce kai suke nema." Sen ya juya ya kalli bayan sa ya hango Didi a tsaye tana kallon motar.

Kallon su ya yi ya ce, "kira Waya daga cikin su." Cikin Waga murya ya yafito Tk, da hanzari Tk ya ?araso Sen ya kalle shi ya ce, "su waye ku?." Tk ya ce, "mu ?an uwan Damisa ne, mun zo muna son ganin ka, tare da yayar sa muke." Sen ya ce, "waye haka?." Da mamaki Tk yake kallon sa amma sai ya ce, "Tiger na Kano."

Wani irin kallo Sen ya yi masa na baku da hankali ya ce, "gani na Win me ku ka zo yi?." Zai yi magana ya kalli masu tsoron wajan ya ce, "a tabbatar duk bar wajan nan yanzun nan, in na le?o naga Waya a cikin su ranku ne zai Saci" yana faWa ya Waga glass Win motar aka ja motar zuwa ciki.

Nan da nan aka fara yi musu tsawa su bar wajan babu shiri suka bar wajan zuwa inda suka ajjiye motar. Jingina Didi tayi da motar ta rufe ido kawai bata ce komai ba. Kallon gidan ta sake yi ta yi ajiyar zuciya cikin damuwa mai yawa. Ga gidan tana kallo amma babu yadda zata yi, bata da damar shiga balle ta yi magana da Senator ko zai taimaka mata.

Senator da Sacin rai ya fita daga motar ya shiga ciki, a sama ya samu Mum a zaune ya kalle ta ya ce, "kin san su waye a wajan estate Win nan?." Mum ta ce, "su waye?."
"Wai ?an uwan Tiger ne suka zo son ganina." Mum ta ce, "?an uwansa? Kenan daman da sanin su yazo nan neman aure?."

Dad ya ce, "bara na yi waya gabaWaya a kama su." Mum ta ce, "A'a Dear, kar ka saka a kama su."
"Meyasa?" Ya tambaya yana kallon ta. Mum ta ce, "ka shigo dasu, ka shigo dasu mu yi musu warning, sannan mu saka su je su karya asiri da Tiger ya yiwa ?armu." Dad ya kalle ta da mamaki ya ce, "hakan ya yi?."
"Hakan ya yi mana, ki shigo dasu muyi amfani dasu a karya asirin da ya yi mata. Babbar dama muka samu da zamu tura su gida su je su karya asirin ko dan hankalin Narma ya dawo jikinta."Waya Dad ya Wauka ya kira masu gadin ya yi musu magana yana kashewa.

Su Didi suna tsaye aka ?araso inda suke, su sun Wauka ma laifi suka yi. Bashir ya ce, "ya dai? Nan ma korar mu za a yi ne? Na ga nan kan titi ne ko?." Kallon su ya yi ya ce, "ku ku zauna a nan, ke mu je Sen yana kiran ki." Bashir ya kalli Didi da ta zabura zata bisu ya ce, "Didi bai kamata ki je ke kaWai ba." Didi ta ce, "kar ku damu, bara naje na dawo." Tare suka tafi zuwa gidan aka raka ta har bakin falon gidan sannan ya dawo wanda ya rakata.

Da sallama Didi ta shiga amma bata ga kowa ba, falon shiru sai sanyi da ?hamshi da yake tashi a cikin sa. Didi bata tsaya ?are masa kallo ba dan ba abinda tazo yi ba kenan. Tana tsaye a falon aka turo aka shiga da ita ciki, a wani falon ta same su a zaune su biyu suna kallon mai shigowa. A sanyaye Didi take shiga, ganin su kawai ya sanyaya mata jiki,
ba kamar kallon wula?ancin da suke binta dashi duk sai ta sare guiwar ta tayi sanyi sosai.

A kan carpet ta zauna a sanyaye ta ce, "Ina yini." Mum ta ce, "ba gaisuwarki muka kira ki mu ji ba, ke ce Yayar ta sa?." Didi ta Waga kai alamun Dad ya ce, "Ina iyayen ku?." Didi ta ce, "sun jima da rasuwa."
"Na sani, na san hiv ce ta kashe babar ku, sannan baban ku ya mutu ta sanadin shan taba har huhunsa ya lalace."

Didi ta sunkuyar da kai idonta yana cikowa da hawaye. Dad ya yi tsaki ya ce, "Wan uwanki ya yiwa ?ata asiri mai ?arfi kin san da hakan?." Didi ta girgiza kai ta ce, "Ban sani ba." Dad ya ce, "to na faWa miki yanzu, ya yi mata asirin da ta kusa fita daga hankalinta. Dalilin da ya saka nace ki zo shine, ki je duk inda ki ka san ya binne asirin nan ki tona shi a karya, in ba haka baza ki sake ganin sa ba har abada."

Hawaye ya sakko daga idanun Didi, ta yi sauri ta share a sanyaye ta ce, "don Allah ku yi ha?uri ku barshi ya dawo gida, nayi al?awarin bazai sake kallon koda hoton ?arku ba balle har wata magana ta shiga tsakanin su. Omar yana jin maganta sosai, in na ce ya yi zai yi, haka in nace ya bari zai bari. don Allah, don Annabi ka yi ha?uri ka sassautawa Omar. Maraya ne bashi da uwa bashi da uba, nima shi kaWai ne dani, don Allah ka taimaka min."

Mum ta ce, "ya san shi marayan ne ya yiwa ?ar mu asirin da shiga wani hali mara daWi? Ya san da bashi da kowa ya kawo kansa gidan nan cikin gadara da nuna iko?. A wajan mu bai wuce sauro ba, yadda zamu kashe sauro mu kwana lafiya haka zamu kashe shi ba tare da kowa ya sani ba. Matu?ar kina son sake ganinsa a duniya dole ki san yadda zaki yi a karya asirin nan, in ba haka ba wallahi sai mun Satar da shi a duniya, sai ya bar rayuwa a duniya, ke dashi sai dai a lahira wallahi!."

Didi murya na rawa ta ce, "wallahi bai yi mata komai ba, wallahi bai yi mata asiri ba. Itace ta fara cewa tana sonsa, ita ce tazo har gida ta......." Cikin tsawa mai ?arfi Dad ya ce, "ki mana shiru! Jahila mara hankali. Mu za ki kalla kina cewa ba asiri ya yi mata ba? To me ya yi mata? Ko kina so ki ce soyayyarsa ce zata iya shiga zuciyar ?armu?. Waye shi da ?ar mu zata so shi? Na ce waye shi!?."

Didi ta sunkuyar da kai tana hawayen ba?in ciki da damuwa. Mum ta ce, "wai har tana ?o?arin faWa mana ita taje har gida ta ce tana sonsa, to in ba asiri ya yi mata ba taya haka zai faru?. Dear ka san abinda zaka yi wannan matar ta bar falon nan kafin raina ya Saci na saka a yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login