Showing 63001 words to 66000 words out of 85380 words

Chapter 22 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3835



"Didi ki daina ?o?arin raina min hankali mana, na sanki na san halin ki kar ki manta da wannan. Wallahil azim akwai wani abu a zuciyarki, ki sanar dani damuwarki in kuma baza ki faWa min ba kice baza ki faWa ba." Didi ta kulle ido ta buWe sai ta tashi tsaye ta ce, "Akwai abinda zan Wauka a kitchen, na san ba amfani kake yi dashi ba ni kuma ina so. Gwara na haWa kayan na ajjiye kar na manta" ta faWa tana shiga cikin kitchen ta barshi a wajan yana kallon ta cikin tunanin abinda yake damunta.

Da ta fito ya fita bata sake ganin sa ba, dan Waki ya shiga ya kwanta saboda ciwon kan da yake damun sa. Sai da magriba sannan ya fito yayi alwala ya same ta a tsaye a tsakar gida ta kalle shi ta ce, "zan shiga wajan Hajja." Kai ya Waga kawai tazo ta wuce shi.

? ? ? ? Da sallama ta shiga gidan Hajja aka amsa mata, abinda ya bata mamaki bai wuce Nayla da ta gani a zaune ba tana yi mata oyoyo. Murmushi tayi ta zauna ta ce, "mutanen Kaduna, saukar yaushe?." Nayla ta ce, "saukar jiya, kuma gobe zan koma. Har gidan ki muka je Wazu bakya nan." Jin hakan sai Didi ta bita da kallo da alama itama bata san da auren ba. To me hakan yake nufi wai? Meye dalilin Abiy na aurawa Nayla Omar ba tare da ta sani ba?.

Hajja ce ta katse mata tunani suka gaisa kafin ta kalli su Nayla ta ce, "naje gidan Kawu a can na yini sai yamma nazo nan, Meyasa baku yi min waya ba?."
"Muna ta kiran ki ta?i ta shiga shiyasa."
"Ayya, amma kun kyauta na so kun same ni." Nayla tayi murmushi ta ce, "zamu dawo wani lokacin."

Hira suka cigaba da yi da Hajja da kuma Salma dan ita dai Nayla tayi shiru bata magana. Didi ta taSata ta ce, "Nayla ya dai?." Nayla tayi murmushi ta ce, "babu komai, anyi kiran sallah bara naje nayi sallah" ta faWa tana shiga ciki duk suka bita da kallo.

Didi tausayi ma take bata wallahi, ko meyasa mahaifinta yanke hukuncin aura mata Omar oho, gashi da alama itama bata sani ba, meye amfanin yin hakan da yayi Allah ne ya sani. Duk tashi sukayi akayi sallah kafin Didi tayi musu sallama ta ce zata tafi, Nayla da Salma suka raka ta bar ?ofar g1da a nan suka ga motar AbdulHamid da alama ita yake jira.

Didi ta ce, "Don Allah kuzo ku taya ni Wauko kayan a ciki, kayan kitchen ne wanda na san ba amfani dasu zai yi ba na tattaro kayana." Salma tayi dariya ta ce, "wallahi gwara da kika Wauko" ta faWa suna bin bayanta zuwa gida. ?irjin Nayla bugawa yake yi sosai ba kamar da suka shiga tsakar gidan, Nayla ta Wauki leda Waya Didi ta Wauki biyu Salma ma ta Wauki Waya.

Daga falon Omar ya fito sanye da ?aramar riga mai gajeren hannu mara nauyi, sai wando three quarter. Kallon sa tayi ta ce, "Omar sai da safe."
"Ki kwana Lafiya" ya bata amsa yana niyar wucewa ba tare da ya kalleta ba.
"Ya ciwon kan?" Ta tamabaya tana kallon sa. Juyowa yayi ya kalleta ya ce, "naji sau?i."
"Baka ga su Nayla da Salma ba? Baka yi musu magana ba."

Kallon su yayi, Nayla dai kanta yana ?asa Salma ce ma take iya kallonsa kamar zai yi magana sai ya fasa, ya Waga ?afa da niyar barin wajan sai ya juyo ya kalli Didi ya ce, "na rasa meyasa kike son saka ni a abinda bai shafe ni ba" yana gama faWa ya wuce ya barta a wajan.

Wani iri taji a zuciyarta, dan ita ta san yanzu Nayla matarsa ce shida ita ne basu sani ba, hakan da yayi ya tabbatar mata da karSar Nayla zai yi masa matu?ar wahala, duk ganin da yake mata gashi bai saba da ita ba. Ita ta Wauka ya saba da ita har zai iya yi mata magana, tunda shi magana da wanda bai saba ba babban tashin hankali ne a wajan sa.

Didi ta kalli Nayla bata ce komai ba sai Salma da tayi dariya ta ce, "Kema Didi ban da abin ki ina Omar inayi mana magana? Mu je" ta faWa tana yin gaba duk suka bi bayanta Nayla dai kanzil bata ce ba.

Har motar suka saka mata kayan tayi musu godiya suka gaisa da mijinta sannan suka wuce gidan Hajja. Tunda ta shiga motar shima ya lura tana cikin damuwa mai yawa, ya kalle ta cike da kulawa ya ce, "Ya dai? Akwai abinda ya faru ne?." Didi ta ce, "Akwai wallahi. Kaga yarinyar nan da kuka gaisa mai blue Win mayafi?."
"Eh na ganta."
"Itace Nayla, itace wacce ta yi silar da aka fito da Omar daga wajan Senator. ?azu mahaifinta yaje har gidan Kawu ya saka aka Waura aurenta da Omar."

AbdulHamid ya ce, "Iyee! aure da Omar? kuma!?." Didi ta Waga kai ta ce, "wallahi, yanzu maganar da nake maka ita matar Omar ce wallahi."

"Ikon Allah, to garin ya haka ta faru?. Daman suna soyayya da Omar Win ne?." Didi ta ce, "ita dai tana son Omar, na ji da kunnena suna tattauanwa a ranar Waurin aurena da kai. Ta bani matu?ar tausayi, domin soyayya bata yi mata adalci ba da ta saka ta fara son Omar. Ita ba tsararsa bace, ta wuce ajinsa nesa ba kusa ba, ko masu gadin gidansu sun fi Omar matsayi wallahi. Abinda ya bani mamaki ya kuma Waure min kai shine; mata guda biyu kyawawa, masu asali da iyaye masu kuWi da faWa a ji a ?asar nan, mata masu ilimi, aji da wayewa sune suke yiwa Oamar irin wannan soyayayar? Anya ta baki Senator ba asiri Omar yake yi musu ba kuwa?."

Abdul yayi dariya ya ce, "Wanne irin asiri ana zaune Lafiya? Kawai haWuwar jini ce. Kin san mata suna son farin namiji kyakykyawa mai saje kamar Omar Win."
"Amma haWuwar jinin su rasa da wasu haWa jini sai Omar? Mata kamar su ace sune suke sonsa ba shine yake sonsu ba?. Har gwara Narma ita ya furta min yana so, to Nayla fa da take matsayin matarsa yanzu?."
"Ni maganar auren ce ta Waure min kai, haka kawai mahaifinta ya aura masa ita kamar auren ?ar tsana?."
"Wallahi nima ya Waure min kai, abin mamakin kuma a yanayin yarinyar na tabbatar da bata san da auren ba kamar yadda Omar bai sani ba. Meyasa mahaifinta ya aura masa ita?."

"Ko ya gano tana sonsa ne?."
"Dan ya gane tana sonsa kuma sai ya Waura mata aure dashi yau kwatsam? Gaskiya akwai lauje a cikin naWi a lamarin nan." AbdulHamid ya ce, "yanzu shi Omar Win ya sani?."
"Waye zai faWa masa? Kaf duniya ni kaWai ce zan iya tunkararsa da wannan maganar, to nima Win na rasa ta wacce hanya zan faWa masa. Jurwaye mai kamar wanka nayi masa, nace masa na kai matsayin na bashi mata ya zauna da ita, ka san me ya ce?."

Ya girgiza kai alamun a'a Didi ta ce, "cewa yayi zai iya karSa tunda ni ce babu yadda zai yi, amma bazai iya kallonta matsayin mata ba, zai dai zauna da ita gida Waya matsayin wacce na ajjiye masa amma ba matarsa ba." Abdulhamid yayi dariya ya ce, "Wallahi Omar yana burge ni, yanayin ?arfin guiwarsa da gaskiyarsa tana matu?ar burge ni a halayensa. Yanzu ya zaki yi?."
Cike da damuwa ta ce, "Dole dai ni zan faWa masa, amma nima ban san ta wacce hanya ba."

"Zaki samo hanya, ki nutsu kawai, ai yana jin maganarki zai yi duk abinda kika ce masa." Didi ta ce, "hmm baka san Omar ba ne, a dai yi shiru kawai" ta faWa tana kawar da kai zuciyarta cike da tunanin dalilin auren Nayla da Omar lokaci guda haka.
KRB2P022

Narma tana tsaye a tsakiyar bedroom ta idar da sallah tana ninke sallaya Ashraf shiga yana binta da kallo. In ba da sexy dress ya ganta ba bata burge shi gabaWaya, yana so ya ganta da kayan da suka bayyanar da surar ta, in ya same ta da hijjabi ko riga mai girma sai yaji haushi ya tokare masa ?irji lokaci Waya sai yaji tana bashi haushi, amma da zarar ya ganta a yadda yake so sai yaji babu abinda yake so sama da kasancewarsa da ita.

Jin motsinsa sai ta kalle shi tana zare hijjabin daga jikinta, ajiyar zuciya ya yi ganin rigar jikinta wacce tayi daidai da yadda yake so ya ganta. Iyakar rigar guiwa tana da hannu mai Wan girma kaWan amma bata da kauri sannan tana bin jiki. Zama tayi a gefen gado tana kawar da kai dan tun lokacin da ya same ta sau Waya bata sake bari hakan ya faru ba.

Murmushi yayi ya ce,  My Love zamu iya fita?. Kallonsa tayi ta girgiza kai alamun a a ya ce,  Haba my love, ki amince muje ba jimawa zamu yi ba dawo. Kullum kina g1da, tunda muka zo bakya fita. Bata ce masa komai ba yazo kusa da ita ya zauna yana ?are mata kallo, halittarta na burge shi sosai, amma yanzu abinda yake ji a kanta ya ragu da kaso mai yawa, kawai ya san yana son kasancewa da ita bayan wannan babu wani abu a zuciyarsa a kanta.

A hankali ya kai hannu ya fara shafata ya ce,  My love muje mu dawo. Ko kina so mu taje miami mu kalli ball Win messi?.
 Pls Ashraf ka ?yaleni, babu inda zanje in kai zaka je kaje amma ka daina saka ni ciki ta faWa tana kawar da kanta gefe.
 Come on my love ya faWa yana yajowata jikinsa lokaci Waya yana ?o?arin zare rigar jikinta. Da hanzari ta fincike jikinta ta mi?e tsaye ta ce,  kar ka sake wannan kuskuren, wancan ka damu dama a banza a yanzu baza ka samu ba. Ka tashi ka fita ka bani waje bana son ganinka, wallahi na tsaneka, ka fahimi bana so ganin koda fuskar ka ne.

Kallon ta yake yi jin wai ta tsane shi ya Wan buWe idanu tare da taSe baki ya mi?e shima yana kallonta ya ce,  kin tsane ni kika ce?.
 Eh natsane ka, bana son ganinka ko kaWan.
 Wannan mahaukacin yaron kike so?. Ba tare da shakka ba tace,  eh shi nake so, ganganar jikina kawai kake tare da ita a nan amma zuciyata tashi ce. In ka sake kuskuren zuwa kusa dani zanyi maka illa babba a jikinka.

 Wow! Daman ni ai ganganar jikin naki nake da bu?ata ba zuciyarki ba Nar???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ma. Jikinki nake so kuma na riga na mallaka, ko yanzu nace Ina son wani abu a tare dake baki isa ki hana ni ba. Dan yana ri?e da zuciyarki Ina ri?e da jikinki hakan yayi min daidai. Da ki soni, da kar ki soni ni dai ina son jikinki. Narma ta bishi da kallo kamar zata yi magana sai ta fasa ta koma gefe ta harWe hannaye a ?irji bata ce komai ba.

Ashraf ya ce,  this is the last time da zaki sake yi min maganar sa a nan, ni mijinki ne ko bakya so, in kika sake ambatar wancan shashashan mara hankalin a gabana ranki zai Saci matu?a. Harararsa tayi ta ce,  Sai na faWa baka isa ka hana ni ba, kuma kaine shashasha mara hankali amma ba shi ba. I love Faruk! I love him!i love him!! I love him!. In kaga dama ka kashe ni kar ka barni da rai ta faWa tana harararsa cike da jin haushi da tsana.

A firgice ya tako inda take ya na zare mata idanu ya ce,  ni kike kira da mara hankali Narma?.
 Eh na faWa, baka da hankali& .. bata ?arasa ba ya Wauketa da mari mai zafi yana huci. Sai da ta gigice jin zafin marin da yayi mata, in tace tunda take Dad ne kawai ya taSa dukanta lokacin da Omar yaje gidan su bata yi ?arya ba, amma kafin nan iyayenta basu taSa marin ta ba tunda tazo duniya, zata iya cewa babu wanda ya taSa marinta a duniya bayan Dad sai shi. Nan da nan idanunta suka yi ja ta kalle shi ta ce,  ni ka mara Ashraf?.

 Na mare ki, in ki ka sake furta maganar da kika furta wallahi sai na yi miki dukan tsiya a wajan nan.
 Ni Narma ni ka mara? Ta amsa faWa tana kallon sa. Ta Waga hannu zata rama ya ri?e hannun tare da murWa shi baya, tayi ?ara mai sauti tana runtse ido.

Ashraf ya ce,  lallai baki da hankali, ni zaki daka?. Narma ta ce,  to ka sake ni, bana son aurenka, ka sake ni na koma gida bana sonka.
 Nima bana sonki amma bazan sake ki ba, zama dake nake so yi ko dan na mallaki jikinki a duk lokacin da nake so ya faWa yana jawowa jikinsa da ?arfi ya fara kissing Winta da zafi-zafi cike da mugunta. Da faWa da dambe da Asharaf ya samu yaje inda yake so yaje a jikin Narma, tun tana fizge-fizge har ta daina ta koma zubar da hawaye cikin ?unar rai da kuma ?unar zuciya.

Shi kam Ashraf ko a jikinsa, abinda yake so a tare da ita ya samu yana barin wajan yaji gabaWaya haushinta yake ji, abinda yake ji a zuciyarsa gabaWaya ya kau, indai yana jin shau?i akanta to tabbatar akwai abinda yake bu?ata a tare da ita, da zarar wannan bu?ata ta gushe shikenan sai yaji ta fita daga ransa gabaWaya komai tayi baya burge shi. Kallonta ya yi tana kuka yaja tsaki ya fita ya barta a wajan bai ko sake kallon ta ba.

Narma da?yar ta iya mi?ewa ta shiga banWaki tayi wanka ta fito da zazaaSi da ciwon kai. Hannu na rawa tasha shan pracetamol sannan ta Wauki waya hannunta na karkarwa tana neman ticket na Nigeria dan baza ta sake kwana a America ba, gida zata koma duk abinda zai faru sai dai ya faru amma ta gaji.

" " " " " " " " "

Nayla ta shirya tana jiran Baba Salisu yazo su tafi tana zaune a falon Hajja, gabaWaya jikinta babu daWi ji take kamar tayi ihu bata san dalilin faruwar hakan ba. Hajja ta kalleta ta ce,  gashi ba a siyawa Abban naki gurasa ba, ko zaki jira?.
 Hajja ki ?yale shi kawai, ai duk zuwa kina siya masa wannan dan ba a siya ai ba komai.

Hajja tayi shiru bata ce komai ba amma zuciyar ta bata yi mata daWi in taga Nayla a wannan yanayi na damuwa. Babu abinda zata iya, ta tambayeta tace babu komai amma ba dan ta amince ba. Tana zaune ba jimawa Baba Salisu ya ?araso kamar ko yaushe ta kai masa ruwa ya sha yace ba sai ya huta ba tazo kawai su wuce. Sallama ta yiwa Hajja da Salma ta shiga motar suka tafi gabanta yan faWuwa bata san dalilin hakan ba.

Tafiyar awa uku ta kai su garin Kaduna har cikin gidan su Nayla. Yana faka motar ta fito tare da jakar kayanta zuwa cikin gidan. FaWuwa gabanta yake yi abinda bata taSa ji ba in ta dawo daga Kano, ta saba tana jin zumuWin ganin ?an gidan amma yau ta rasa meyasa take ji haka.

Da sallama ta shiga babban falon Mama ce kawai sai Jalila suka amsa mata ta ?araso ta ce,  Mama na dawo. Mama ta bita da kallo ta ce,  sannu da zuwa, na Wauka sai gobe.
 Yaya J ne ya kira ni yana ta faWa ya ce lallai na dawo yau.

Gaisawa suka yi da Mama Jalila ta kalle ta ta ce,  Ashe Abiy bai san kin tafi Kano ba? Bayan kin tafi ya dinga faWa. Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce,  na dawo na bashi ha?uri abinda tace kenan ta mi?e ta wuce zuwa ciki. Sai da tayi wanka tare da yin sallar azahar, tana idar da sallar Jawad ya shigo Wakin nata abinda bai saba ba. Da kallo ta bishi ta mi?e tsaye ta ce,  Yaya J Ina yini.

Harara ya sakar mata ya ce,  Nayla ashe baki da hankali ban sani ba? Ashe ilimin ki bashi da amfani?. Nayla ta sunkuyar da kai duk a tunanin ta akan son da ta ce tana yiwa Omar yake wannan maganar.
 Yanzu Nayla sai ki saka ?afa ki bar Kaduna ba tare da sanin Abiy ba? Guduwa kike son yi saboda an hana ki auren Wan daba ko?.

Ta girgiza kai ta ce,  ba guduwa nayi ba Yaya J, kuma Mama&  dakatar da ita yayi ya ce,  Mama me? Me maman tayi?. Kin bani mamaki wallahi, kin kuma cuci kanki, kin cuci rayuwarki, in kai kanki inda zaki sha wahala. Ba dai kin zaSi Wan daba akan mahaifinki ba? Kin zaSi Wan daba akan mu, kin zaSi Wan daba akan iyalan gidan nan gabaWaya ko?. Shikenan gaki gashi nan sai ki je ki kwaWa soyayya ki cinye, banza mara hankali! ya faWa yana harararta cike da Sacim rai.

Gaban Nayla ta faWi tana tunanin yaushe ta zaSi Omar akan su kuma?. Bata damu da faWan da yake mata ba duk da karo na farko kenan a rayuwarta, ta kalle shi ta ce,  Wallahi Yaya J ni ban zaSe shi na barku ba, taya zan zaSe shi na bar ku?. Ni na ha?ura ma fa, na ha?ura bazan sake maganar ba in sha Allah.
 Ko kiyi min shiru ko na buge miki baki, ha?urar taki me zata hana faruwarsa yanzu kuma? Ai aikin gama ya riga da ya gama. Tunda haka ki ka zaSa gaki ga shi nan ai ya faWa yana fita daga Wakin nata.

Jikin ta gabaWaya ya gama yin sanyi, dana sanin tafiya Kano ya mamaye mata zuciya. Amma Mama ce tace ta tafi ta Wauka zata yiwa Abiy bayani in ya tambaya. Da wannan sanyi jikin ta fito falo.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login