Showing 69001 words to 72000 words out of 85380 words

Chapter 24 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3841

ya faWi, ta Wan yi shiru kafin ta ce, "Wallahi Mama bana ce ba, ni gabaWaya a rikice nake da wannan lamari na rasa abinda zanyi."

Mama ta ce, "mu ma nan duk a haka muke, amma ya zama dole na tambaya saboda ya saka a siyi kayan Waki. Ya ce da a yau ma zata taho Kano, to saboda rashin kayan ne zai saka a Waga." Didi ta ce, "To Mama zan tambaya naji."
"Yauwa ki tamabaya, ki faWa min adadin Wakukanan, in Waya ne to, in biyu ne ma dai duk daya. Bana so ya sake tambayata nace ban yi ba."
"In sha Allah Mama zaki ji ni."
"Yauwa na gode" ta faWa tana yanke wayar. Sai kuma tayi dariya ta ce, "to kayan Wakin ma suka wuce Waki daya ko biyu? Ina yake da wajan da za a ajjiye kaya na alfarma? Me ya ke dashi me ya tara?. Tunda dai an Waura auren ni burina ya gama cika wallahi" ta faWa tana ajjiye wayar tare da shiga toilet.

? ? ? " " " "

Didi lokacin da ta yanke wayar ajiyar zuciya tayi mai ?arfi cikin rashin sanin abinda zata yi. AbdulHamid da yake bayanta ya ce, "Lafiya dai?." Didi ta kalle shi ta ce, "Maman Nayla ce." Ya kalle ta cikin rashin fahimta ya ce, "wacece Nayla?."
"Yarinyar da aka aurawa Omar ita mana."
"To meye ya faru?."

? ? ? ? "Tana magana akan gidan da za a ajjiye Nayla, dan suna siyan kayan Waki ne. Ni wallahi ban san me zance, ban san me zan aikata ba gabaWaya kaina ya gama kullewa" ta faWa tana zama akan kujera tare da dafe kai. Ya ce, "da Omar Win ya kamata ki fara magana, ko kuma ki san gidan da zata zauna Win ki faWa musu dan su naga da gaske suke yi."

Didi ta ce, "Na faWa maka akwai gidan a ?asa, amma babban tashin hankalina Omar wallahi. Tijarar da zai yi akan auren nan shine bana so, ran kowa sai ya Saci wallahi, ya Sata nasa ran ya Sata na mutane." AbdulHamid ya ce, "to ya za ayi? Haka Allah ya ?addara aurensa
haka zai zo. Ni kuma sai nake ganin kamar zai karSi auren."

Didi ta kalle shi tana girgiza kai ta ce, "baka san waye Omar ba ne shiyasa kake faWar haka. Tun asali haushin Nayla yake yi, saboda itace mace ta farko da na taSa yi masa faWa a gabanta. Yayi mata tsawa, ya harareta, ya razanata duk akan na taSa yi masa faWa tana wajan. Babu kalma mai kyau da ta taSa haWa su, kullum a cikin jin haushinta yake. Kwatsam sai naje masa da labarin itace matarsa? Kana ganin zai amince cikin sau?i?."

AbdulHamid ya ce, "Wannan duk ba abin damuwa ba ne, indai zai karSi auren ai shikenan. Ni yarinyar ma nake jin tausayi wallahi, na farko baya sonta, na biyu ga yanayin halinsa, na uku bai ma san da auren ba, na huWu bazata ta taSa jin daWin zama dashi ba. Kiyi ha?uri, amma wallahi wahala zata sha a zama tare da Omar, ban san meye dalilin mahaifinta na aura mata shi ba amma ya dakusar da rayuwarta, ba dan Omar bai cancanta ba sai dan yadda auren yazo."

Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "meye na bani hakuri? Gaskiya ka faWa, ni kaina na san da haka. Ni kaina tausayin Nayla nake ji, yarinya ?ar gata, yarinya kyakykyawa, yarinya mai ilimi da wayewa ta ?are a auren Omaar. In ba ?addara ba meye zai kawo haka?."

AbdulHamid ya murmusa ya ce, "ilimi, wayewa, kyau, gata ko kuWi duk ba shi bashi ne damuwar ba. Inda ace zai karSi auren hannu biyu duk abinda ki ka lissafa baza suyi tasiri ba, rashin karSar da bazai yi ba ya fi komai illa a rayuwarta. Koda ya karSa baza taji daWi ba, kinga an dakusar da rayuwarta an lalata mata ?uruciya."

Didi ta kulle ido ta buWe ta ce, "bara na kira Kawu naji batun gidan sannan na san abinda zanyi akan batun Omar." Tashi yayi ya ce, "zan je na gaishe da Hajiya, in zaki fita wajan Omar Win kije sai ki yi min waya." Amsa masa tayi ya fita ita kuma ta kira Kawu akan maganar gidan kamar yadda ya ce.

? ? ?? A gidan Hajja suna zaune kamar Kullum ita da Salma Daddy yayi sallama ya shigo bayansa ?anensa ne guda biyu Abba da Baba. Suka amsa Salma ta gaishe su suka amsa mata kafin su zauna su gaishe da mahaifiyarsu. Hajja ta amsa ta ce, "yau ku ne tare gabaWaya?." Daddy ya ce, "eh Hajja, mu ne a tafe."

Hajja ta ce, "Allah ya sa dai Lafiya, dan nasan baku cika zuwa tare ba sai wani abun ya tashi." Abba ya ce, "Gaskiya Hajja ba lafiya ba." Hajja ta ce, "to me ya faru?." Daddy ya ce, "Alhaji Abdullah ne ya kirani, mahaifin Nayla kenan. Shine yayi min waya yana sanar dani yayi mana laifi, Nace laifin meye ya ce ya aurar da Nayla a shekaran jiya juma'a." Hajja cikin mamaki ta ce, "Ya aurar da Nayla kuma? Wanne irin ya aurar da ita ban gane ba?."

Baba ya ce, "mu ma bamu gane ba Hajja,
Mamaki muke yi wanne irin aure ne haka lokaci Waya?." Daddy ya ce, "Na tambaye shi na ce wanne irin ka aurar da ita kuma, ya ce min eh da gaske ya aurar da ita yanzu haka matar aure ce. Na ce lafiya wani abu ya faru ne? Ya ce ya faru, shiyasa ya yanke hukuncin aura mata shi." Hajja ta tafa hannu tana salati ta ce, "Waye shi to? Meye dalilin auren kuma?."
"Hajja bai faWa min dalili ba, amma a yanayin maganarsa na tabbatar da bata daWin rai ya aurar da ita ba, duk yadda aka yi Sacin rai ne."


Hajja ta ce, "to Sacin rai sai ya saka ya aurar da yarinya budurwa lokaci Waya haka?. Waye wanda ya aurawa Win?." Daddy ya sauke numfashi ya ce, "yaron nan ma?ocin ku, ban san asalin sunansa ba amma Tiger ake ce masa." Salma da take ji tana faga tsaye ta wara ido tare da dafe ?irji ta ce, "Tiger Daddy!?." Babu wanda amsa mata Hajja tayi shiru kafin ta ce, "Wai Omar ?anin Aisha ta nan kusa damu?." Daddy ya ce, "Shi fa."

Hajja ta ce, "Omar ya aura mata? Abdullahi ya aurawa Hauwa Omar?. To akan me? Omar Win ne yaje neman aurenta ko me?."

Daddy ya ce, "Wallahi ban sani ba Hajja, iya abinda na sani kenan na faWa miki. Shiyasa muka zo gare ki dan ki sani, amma gaskiya bai yi kyauta mata ba, duk da ban sani ba ko da sanin Nayla Win." Abba ya ce, "Koda sanin nata aure haka lokaci Waya haka kamar auren ya?i? Kuma a rasa dawa za a Waura mata auren sai wannan taqadarin yaron?. Haba ai matsayin sa na mahaifin bai zaSa mata miji na gari ba wallahi, bai sauke ha??in da Allah ya Wora masa ba."

Hajja ta girgiza kai take yi cike da mamakin wannan lamari mai Waure kai ta ce, "A yadda Abdullahi yake matu?ar son Nayla bana tunanin haka kawai zai bata auren Omar, akwai dalilin da yasa ya aikata hakan, amma meye dalilin? Meyasa bai yi shawara da kowa ba ya yanke hukunci haka?."

Abba ya ce, "Hajja ni banga dalilin da zai saka ya Wauki ?ar cikin sa ya aurawa wannan yaro ba, duk laifin da tayi ai shi ya haifeta, yana da ikon da ita, yana da ikon da zaiyi mata hukunci amma ba ta wannan hanyar ba. Me ye ma ya kawo Omar cikin rayuwarta? Wanne laifi zata yi masa kawai yaji a ransa shi zai aura mata?. Sai dai in akwai wani abun a ?asa, tabbas Omar Win ya shiga rayuwarta ne shiyasa ya yi haka. In ba haka ba haka kawai bazai aura mata shi ba ba tare da dalili ba."

Hajja ta kalli Salma ta ce, "Salma na san kin san komai, FaWa mana me ya faru?." Salma ganin iyayenta maza sun tsare ta da ido sai ta ruWe ta ce, "Hajja ni ban san komai ba, yanzu naji labarin auren."
"Ai ba labarin aure na tambayeki ba, meye alaqar Omar da Hauwa?." Tayi shiru bata amsa ba ?irjinta na bugawa. Baba ya ce, "ba magana akeyi miki ba ne?."

Salma ta ce, "Daman gaskiya Nayla ta jima tana son Omar, duk wannan damuwar da take shiga ana tambayarta meye ta?i faWa duk akan sonsa ne. Amma babu wanda ya sani daga ni sai ita sai kuma Jidda." Hajja ta sauke numfashi bata ce komai ba cikin ruWani. Abba ya ce, "iya son da take masa bai isa ace shine ya jawo ya aura mata shi ba, kodai akwai wata alaqa da ta taSa haWa shi da Nayla Salma?. Nayla ta bashi kanta ne?."

Salma ta wara idanu tana girgiza kai ta ce, "Wallahi Abba bata taSa ba, ko magana ma basa yi wallahi, kuma bai ma san tana sonsa ba." Abba ya kafawa Salma ido yana kallo kafin ya Wauke ido daga kanta. Hajja ta ce, "Bana wannan tunanin akan Nayla Ali, na san bazata taSa watsar da kanta a waje ba, akwai dalilin mahaifinta na yanke wannan hukuncin ba iya dan tana sonsa bane."

Abba ya ce, "ni fa Hajja banga laifin da zata yi har ya saka shi ya yanke wannan hukunci akanta ba, dan tana sonsa ba hakan yana nufin zai aura masa ita bane, kawai yayi aiki da zuciya ne shiyasa hakan ya faru. Yazo a zauna gabaWaya, dan gaskiya in akwai damuwa akan auren a saka yaron ya sake ta, bazai yu a cutar da ita dan mahaifiyarta bata raye ba."

Hajja ta ce, "yanzu ya ake ciki?."
"Ya ce zai zo har nan, wai kunyarki yake ji akan abinda ya aikata." Hajja ta ce, "to sai yazo, zan ji dalilinsa na yanke wannan hukunci. Dan Nayla na son Omar ba hakan yana nufin a aure mata shi gabagaWi ba. Itama sanin akwai tazara tsakaninsu? dashi ne ya saka ta Soye son da take masa. Ina da tabbacin babu wata mummunar alaqa da ta haWa shi da Nayla, kamar yadda Salma tace ko magana na san basa yi. Inda ace wani abun ya faru tsakaninsa da ita sai ace shine dalilin Abdullahi, to ni na tabbatar da babu komai."

Salma ta kalli Hajja cikin rauni ta ce, "Hajja don Allah zan je Kaduna yau, Ina so naje naga halin da Nayla take ciki." Hajja ta ce, "kije ki shirya, sai a kai ki ai lokaci bai ?ure ba." Daddy ya ce, "in ta tafi ta barki da wa? Hajja?."
Hajja ta ce, "ni kaWai zan iya zama."
"A'a gaskiya, sai dai in zamu tafi gida tare dake, in yaso duk lokacin ta dawo sai ki dawo."

Hajja ta ce, "to me zai ci ni dan na zauna ni kaWai? Naga Salma nan gaba kaWan aure zata yi ko?. Kuma ko bata yi aure ba takardun makarantarta na fitowa aiki zata fara, gwara na fara sabo da zama ni kaWai Win." Abba ya ce, "duk tarin ?an matan da muke dasu? Ai sai wacce ki ka ce kina so tazo ta zauna da ke Hajja. Amma yanzu indai har zata je Kaduna to sai dai ki bar gidan nan gaskiya." Hajja ta yi shiru kawai bata ce komai ba tana tunanin wanne irin hukunci Abiy ya yanke haka?.

Salma dai kaya ta haWa har na kwanaki ta Wauki duk abinda ta san zata Wauka ta fito. Tana fitowa aka kira mata drivern Hajja ya tabbatar da motar
lafiyar lau ta yi musu sallama ta fita dan gabaWaya hankalinta yayi kan Nayla, so take taji abinda ya faru ta kuma ga halin da yake ciki.
KRB2P024
ArewaBooks@nanahaleema11.

Tafiyar Salma ba jimawa Didi tayi sallama ta shigo falon Hajja. Hajja ta amsa da murmushi ta ce, "Aisha sannu da zuwa." Didi ta ?araso ta dur?usa ta gaishe ta amsa ta ce, "ya mai gidan naki?."
"Lafiya lau Hajja. Ina Salma?." Didi ta ce, "Salma ta tafi Kaduna wajan Nayla Wazu. Kin san ta koma jiya." Didi ta ce, "Allah sarki, Allah ya kiyaye hanya."

Hajja ta ce, "Amin. Kin yi sa a AbdulHamid baya yi miki kulle yana barin ki fita, in ba haka ba ranar juma'a ma fa kinzo." Didi tayi dariya ta ce, "dole ce ta saka ni na fito yau Win ma Hajja." Hajja ta ce, "Amma dai lafiya ko?." Didi ta ce, "eh lafiya zance, nazo wajan Omar ne na tarar baya nan, gidan ma a kulle yake shiyasa zan zauna a nan na jira shi." Hajja tayi murmushi ta ce, "Malam Omar kenan, carbin ?wai janka sai mai nutsuwa."

Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "Hajja ban sani ba ko kin ji labarin abinda ya faru, amma jiya yanayin ki ya nuna min kamar baki sani ba." Hajja ta murmusa ta ce, "eh ban sani ba, Wazu ake sanar dani abinda ya faru."
"Hajja meyasa Abiy ya yiwa Nayla haka?."
"Babu wanda ya san dalilinsa, dan yanzu haka ma ya saka ana ta siyan kayan gida."

Didi ta ce, "?azu Mamanta da kanta ta kirani tana tambayar inda za a kawo kaya da kuma adadin Wakunan gidan, wallahi Hajja ni gabaWaya kaina ya kulle na rasa abinda zanyi, wanne irin aure ne wannan ya yiwa Nayla? Ta sani ko bata sani ba duk bamu da tabbas a kai."
"Wannan dalilin ya saka Salma tace zata je Kaduna gano yanayin Nayla Win. Amma ke kin san daman tana son Omar?."

Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "na sani Hajja. A ranar Waurin aurena kin san yarinyar nan Narma ta Abuja tazo, to a ranar bayan ta tafi na taho nan na bar su a can suke hirar su uku, ita da Jidda da Salma. A lokacin naji komai na kuma tausay??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a mata domin soyayya bata yi mata adalci ba, Ina ita Ina Omar? Ba sa'ar auren Omar ba ce ita kanta ta sani, sannan Omar ba mutum ne kamar kowa ba, ko wanne uba ne zai bashi auren ?arsa ba."

Hajja ta ce, "ni babban abinda yake bani mamaki dalilin yin auren da gaggawa haka, meye ra'ayinsa akan wannan auren har ya aikata haka?." Didi ta ce, "wallahi ban sani ba, nima shine abinda yake damuna."

Hajja ta ce, "yanzu Omaar Win ya san batun auren?." Kamar zata yi kuka ta ce, "Wallahi Hajja bai sani ba, babban tashin hankalina ma bai wuce tunkararsa da maganar nan ba. Kin san halinsa Hajja, kin san abinda zai yi da wanda bazai yi ba, yadda zan tunkare shi da maganar nan shine abinda yake Waga min hankali."

Hajja ta ce, "tabbas zaiyi, zai yi abinda ba ki tunani ba ma dan Omat ya wuce tunanin mu gabaWaya.." Didi ta ce, "To Hajja wannan ai kin ga akwai rashin kyautawa ita Nayla Win, sannan akwai zubar da mutuncinta na ?a mace. Ace an Waura mata aure da wanda ake tunanin zai karSi auren ko bazai karSa ba, kinga kamar ba'a kyauta mata ba."

Hajja ta ce, "babu wanda ya san dalilin mahaifinta na aikata haka, ban sani ba ko ita Nayla Win ta san zai Waura mata aure dashi oho? Amma yanzu me ki ka yanke?."
"Wallahi ban sani ba, ga dai gida Kawu ya bayar kyauta, ya kuma ce min don girman Allah kar na bari Omar ya san shine ya ba da gidan. ni ko zuwa ban yi na duba gidan ba."

Hajja ta ce, "nima a shawarata kar ki faWa masa yanzu, ki bari komai ya daidaita tukunna sai ya sani."
"Hajja kar yazo yana Satawa mutane rai fa."
"Ki ?yale shi, ki bari sai nan gaba. Ko da ace ma Nayla ta tare a gidansa ki bari sai zaman yayi nisa sannan ki faWa masa." Dogon numfashi Didi taja ta ce, "Hajja anya haka baganganci bane? Omar fa?." Hajja tayi dariya ta ce, "kar ki damu, komai zaizo da sau?i in sha Allah. Ni a jikina nake jin shine mijin Nayla, wannan auren nasu aure ne na har abada. Karki damu mu cigaba da yin addu'a kawai." Didi ta ce, "To Hajja, Allah ya sa haka shine mafi alkhairi" ta faWa kawai ba dan har zuciya ba. Hajja ta amsa da Amin.

" " " " " " "

? ? ?? Ashraf yana tsaye a falo yaji an danna door bell daga ?ofar falon, ya ?arasa ya buWe da mamaki yake kallon wanda suka zo. Mum ce sai kuma Najwa ya basu hanya tare da murmushi ya ce, "Mum sannu da zuwa." Murmushi tayi ta ce, "Yauwa Ashraf, mun zo babu notice ko?." Ashraf ya murmusa ya ce, "Haba Mum babu komai, have a seat." Mum ta zauna Najwa ma ta zauna.

Mum ta kalle shi bayan ya zauna ya ce, "Good morning Mum."
"Morning Ashraf, ya kake?."
"Am fine Mum. Ya hanya?."
"Alhamdu lillah. I hope komai yana lafiya tsakaninka da matarka?."
"Yes Mum, Alhamdu lillah."
"Glad" Mum ta faWa da murmushi.

Najwa ta kalle shi bayan sun gaisa ta ce, "where is she?." Ashraf ya ce, "Tana ciki." Najwa ta mi?e ta shiga cikin bedroom Win wajan Narma.

A kwance ta hangi Narma ta rufe kanta da blanket ta ?arasa ta buWe fuskarta. Ganin yadda fuskarta tayi ja ya bawa Najwa mamaki, ta taSa fuskar ta tana mamakin me ya kawo wannan jan. Narma da ta fara bacci tashi ana shafa fuskarta ta fusata ta bige hannun tare da zabura ta ce, "Ashraf stop it, how dare you to touch me?."

Najwa ta ce, "easy Sis! It's me, Najwa." Narma ta kalli Najwa da take kallonta ta ce, "Najwa!." Najwa ta ce, "yes Sis." Sai ta mi?e zaune ta ri?e hannunta ta ce, "Najwa yaushe kika zo?."
"Yanzu, nida Mum ne, tana falo...." Bata ?arasa ba Mum ta shigo Wakin. Narma ganin Mum ta shigo sai ta mi?e da sauri ta ?arasa ta rungume Mum. Mum ta yi hugging Win itama tana shafa bayanta ta ce, "My daughter, I missed you."
"Likewise Mum." Mum ta Wagota tana kallon fuskarta ta ce, "meya faru naga fuskarki tayi ja haka? Are you okay?."

Narma ta ce, "Mum I'm not okay, bana son zama a nan ko kaWan." Mum ta ce, "stop crying mana, just calm down and let me know what is happening

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login