Showing 78001 words to 81000 words out of 85380 words

Chapter 27 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3843

Jin abinda tace sai ya Sata masa rai ya kalleta ya ce, "ni kuma zan nuna miki jikinki nake aure ba ke ba" ya faWa yana ri?eta da ?arfin gaske ya fizge towel Win jikinta ya jefa ta kan gadon, zata mi?e ya saka ?afa ya taketa ya danne ta yadda baza ta iya koda motsin kirki ba.

Kuka take tana faWin, "bana sonka, bana ?aunarka, na tsane ka." Ya kalleta ya ce, "nima bana sonki, amma Ina son jikinki. Baki isa ki hana ni mallakarsa ba tunda kina amsa sunan matata." Kuka take tana juya kai amma ya ri?eta tamau babu ta yadda zata iya ?watar kanta. Tana ji tana gani ya sake yi mata fyaWe kamar yadda take faWa, bai ?yale taba sai da ya tabbatar bakin cewa bata sonsa ya mutu sannan ya tashi.

Sai numfashi take saukewa na wahala saboda azabar da ya gana mata, shi kansa ya wahala amma saboda ya nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane shiyasa yayi mata haka. Wanka yayi ya fito ya kalleta a baje a kan gado tana sauke ajiyar zuciya. Harararta yayi ya ce, "daga yau irin halin da zaki dinga shiga kenan indai zaki dinga cewa zaki yi min gardama, wallahi na daina binki da rarrashi, Igiya zan siyo na dinga Waureki nayi abinda nake so na tsallake na ?yale ki tunda haka kika zaSa."

Kallon sa tayi murya a sha?e ta ce, "bazan sake kwana a Texas ba, na faWawa Mum zan bita ta?i tafiya dani, amma yanzu bazan sake kwana ba."? Baice mata komai ba sai bayan ya shirya ya ?araso inda take ya Wauke wayarta, ya koma inda kayan su yake ya Wauke passoport Winta ya nuna mata ya ce, "wallahi babu inda zaki je, babu ke babu amfani da waya sai lokacin da na ga dama. Ban gama morarki ba har yanzu balle ki ce zaki koma nigeria" ya faWa yana ficewa ita kuma ta fashe da kuka.

Yana fita ?ofar da zata fitar da kai shi compound na gidan ya canja passoword Win ?ofar saboda kar ma tayi tunani guduwa, dan bai gama fanshe wahalar da ta bashi ba, ta tara masa sha'awarta mai yawa tun kafin ya aureta, baza su haWu su rabu ba sai ya shiga mugun yanayi ba saboba shigar jikinta. Balle in ta kwanta a jikinsa kusan rasa hankalinsa yake yi. Dan haka sai ya gama fashewa son ransa sannan zai ?yaleta.

" " " " " " " " "

Didi har dare tana gida, Omar tunda ya fita ya bar gidan bai dawo ba, ji take ina ma zata iya hana zuwan gobe da tabbas ta hana zuwanta saboda abinda zata tarar a wajan Omar. GabaWaya a sanyaye take yin komai har ta yi masa girki ta ajjiye masa.

Bayan sallar magriba ya dawo gidan yayi mamaki da ya ga gidan a buWe dan bai Wauka Didi tana ciki ba. Har ya shigo falon bata sani ba ta shiga duniyar tunani, ya zauna ya ce, "Didi tunanin me kike yi?." Kallon inda taji maganarsa tayi ta ganshi a zaune ya zuba mata idanu ta ce, "yaushe ka shigo?."
"Na shigo kina aikin tunani.Wai me yake faruwa ne don Allah?." Tayi ajiyar zuciya, "Sai gobe zaka ji. Ni dai burina kar ka bani kunya Omaar."

"Ko dai AbdulHamid Win yake yi miki wani abun da bakya so?." Ta kalle shi ganin yadda ya kafa mata idanu yana kallonta yana jiran amsar ta ce, "Ko Waya."
"To meye?" Ya tambaya cike da damuwa da kuma gajiya da maganar.

Didi ta ce, "na faWa maka zaka ji gobe, amma don Allah....." dakatar da ita ya ce, "zan baki kunya kuwa indai aka yi min abinda bai min ba, bazan yi miki alqawari akan abinda ban sani ba dan haka ki daina ro?ona. Wallahi bazan yi alqawari ba kin ji na rantse, haka in aka yi min abinda bai kwantan min ba zan baki kunya" ya faWa tana kallonta. Ya yi ?aramin tsaki ya ce, "bazan sake tambayar damuwarki ba, tunda ban kai matsayin na sani ba ki ri?e kayar ki."

Jikin Didi ya sake yin sanyi jin harda rantsuwa, ta san kuma indai ya rantse magana ta ?are, baya taSa karya rantsuwa balle ta saka ran zai yi kaffara. Ta zuba masa ido tana kallo cikin rashin sanin abinda zata yi. To da wa zata haWa Omaar wanda yake jin maganarsa...? Babu kowa a duniyar nan, mutum Waya ne tal kuma baya duniya, baya shi babu wani da Omar yake ganin darajarsa, ita Win ce kawai kuma gashi da alama za a kai ruwa rana dashi.

Tashi yayi ya fita ya barta a wajan yana mamakin abinda zai faru goben wanda shi bai san dashi ba kuma ta kasa faWa masa. Har aka yi sallar i'sha tana nan, ya dawo cikin gidan tana zaune ganinsa sai ta mi?e ta ce, "nayi maka girki, ni zan wuce sai gobe."
"Ke kaWai zaki tafi?."
"A'a, yazo zamu wuce." Kai ya Waga mata kawai ya wuce kitchen ta fita jikina matu?ar sanyaye.

Shi kansa Omar Win da tunani ta barshi, bayan ya gama cin abincin tunanin abinda zai faru goben yake yi, duk yadda ya kai ga son ganowa ya kasa dan gabaWaya tunaninsa ya tattara akan wani abun ne akan danginsu ko kaWan bai yi makamancin tunanin abinda yake faruwa ba. A haka ya gama cin abinci ya Wan zauna yana danne-dannen waya saboda yanayin sana'ar ta su sannan ya tashi ya fita ya kwanta.

? ? ? ? Washe gari.

? ? ? ? Nayla tun asuba yanyinta ya sake canjawa, ko magana bata iya yi sai dai ta bisu da ido, a haka take zaune ko bacci bata iya komawa ba saboda fargabar da take ciki. Gari yayi haske sosai, a lokacin ?arfe tara na safe ta jiyo muryar Abiy a kusa da Wakinta. Mi?ewa tayi da?yar ta kalli Salma da take kallonta tashin ta daga bacci kenan, ta kalli Jidda da take bacci dan a wajena ta suke kwana basa iya barin ta ita kaWai.

Fita tayi tana fitowa falon suka haWa ido da Abiy. ?arasowa inda yake tayi ta zube a ?asa ta ce, "Abiy ina kwana."
"Kin tashi lafiya? Ya jikin?."
"Da sau?i" ta furta a sanyaye ya kalli Mama da tazo wajan ya ce, "kiyi hanzari ki shiryata bana so lokacin sallar azahar ya yi ba ku wuce ba. Nan da sha Waya nake so ku wuce gidan Hajja" Abinda ya ce kenan y bar wajan Nayla ta kasa koda motswa.

Mama ce ta ?araso ta Wagota ta rungume a jikinta ta ce, "mahaifinki baya fushi dake Nayl,? ya kamata ki fahimta ki daina asarar hawayenki haka, baki da lafiya koda dan lafiyarki ki nutsu don Allah." Nayla bata ce komai b, a lokacin Jidda da Salma suka fito falon Mama ta kalle su bayan su gaisa ta ce, "Ku kawo mata abinda zata ci." Jidda ce ta sauka da kanta ta kawo musu abinci suka ci ita dai da?yar ta iya shan tea.

Bayan ta gama Mama ta kalle ta ta ce, "muje ki yi wanka." Hannunta ta ri?e har Waki da kanta ta haWa mata ruwan wanka ta ce tayi. Nayla ta shiga banWakin jiki a sanyaye tayi wanka ta fito, Mama ta fita ba jimawa ta dawo da kaya ta ajjiye mata ta ce, "ki saka wannan" ta faWa? tana bata waje. Salma da Jidda ne suka shigo ta kalle su ta Wauke kai dan bata iya cewa komai, hawayen ma ya gama ?afewa a idanunta.

A haka ta saka kayan a kasalance, atamfa ce mai tsadar gaske Winkin doguwa bubu. Tana gama sakawa Mama ta shigo ta Wauki mayafin ta yafa mata ta Wauki turare akan madubin ta fesa mata ta ce, "mahaifinki yana jiranki, zo mu je" ta kalli Jidda da Salma ta ce, "Ku haWa mata kayan da zata yi amfani dasu kafin a haWa mata duka." Amsawa suka yi a sanyaye ganin da gaske anyi auren Nayla har ana niyar kaita gidan mijinta. Ba jimawa sai ga Jalila da babbar trolly bag ta kawo musu, suka karSa duk kayan da hannun ya kai suke watsawa a ciki.

Abiy yana zaune a falo shida Yaya da Jawad Mama ta shigo da Nayla tana ri?e da hannunta. Tunda Abiy ya ga Nayla a haka sai jikinsa ya yi sanyi matu?a, ya bita da kallo cikin wani irin yanayi wanda bai yi tunanin zai ji shi a lokacin ba.

Nayla ta zauna a akan carpet Mama ta ce, "Abiy ga ta kamar yadda ka ce." Abiy ya kalle ta ya ga kanta yana ?asa, ya yi ajiyar zuciya yana kallonta kafin ya ce, "Hauwa!." Wani irin dum taji a zuciyarta ta runtse, hawayen da ta nema ta rasa suka fara cikowa a idanunta tare da sakkowa kan fuskarta.

"Yau zaki tare a gidan mijinki wanda kika zaSa matsayin wanda kike so ki ke ganin zaki iya rayuwa dashi. Duk da auren yazo a bazata a wani yanayi wanda bai miki daWi ba ina so ki san aure dai sunan sa aure, duk inda akace kalmar miji to mijinki ne biyayya ta zama dole a gareki. Kar ki yi tunanin komai akan auren, kawai ki yi masa biyayya ki nemi aljannaki a gare shi. Ki yi zaman ki a Kano ki yi bautar aure da biyayya ga mijin da ki ka zaSa matsayin abokin rayuwarki. Bana so na ganki a Kaduna har sai lokacin da nace kizo, ba dan bana son ganinki ko dan kin yi min laifi ba, sai dan inaso ki nutsu ki yi zaman aure. Dan haka babu ke babu zuwa gidan nan matu?ar bani na bu?aci hakan ba. Kin san meye aure, kin san me ake nufi da aure, kin san ha??in miji a kanki, kin san naki a kansa. Ki yi biyayya ga mijinki, ban da rashin kunya, ki yi ko yi da halin mahaifiyarki wajan biyayya da kyakykyawan zama. Allah ya bada zaman lafiya. Abinda zan ce miki kenan, Allah ya kiyaye hanya, Allah ya kai ku lafiya, Allah yasa haka shine alkhairi a gareki."

Kuka Nayla take yi sosai jin kalaman Abiy na kar tazo gida, ta ?araso inda yake, ta mi?e akan guiwarta, ta matsa kusa dashi sosai ta ce, "Abiy ban san meyasa ka yanke wannan hukuncin a kaina ba, ban sani me nayi maka ba, ban san meyasa kayi fushi dani har haka ba. Abiy ban san laifin da nayi har kace kar nazo gidan nan sai ka neme ni ba, Abiy gidan da aka haifeni ka yi min iyaka dashi.....!"

Ta kasa ?arasa maganar saboda kukan da yaci ?arfinta. Ta sassauta kukan ta ce, "Abiy nidai burina ka yafe min, ka daina fushi dani, kuma ko meye ya faru har ka yanke wannan hukuncin a kaina wallahi ban sani ba, bani da hannu akai dan ban aikata komai ba." Kuka take yi sosai tana dur?ushe a gabansa.

Ta kuma cewa, "Bani da mahaifiyar da zata fahimce ni, inda Ummana tana da rai ita zata iya fahimtar abinda nake so ka fahimta Abiy. Abiy tunda nake ban taSa jin kewar mahaifiyata kamar wannan lokacin ba, ban taSa jin zafin rashin uwa ba sai a wannan lokacin.....! Ka cike min gurbin uwa da uba, amma a yau ina kewarta, ina tsananin kewarta. Gashi ko fuskarta ban sani ba, a hoto kaWai nake ganinta, amma kewarta nake ji har cikin rai Abiy.....!" Kuka ya ci ?arfinta ta kifa kanta a guiwar Abiy tana kuka sosai.

Dukkan su ta basu tausayi, Jalila da take tsaye kuka take yi haka Jidda da Salma da suka fito. Nayla ta Wago ido yayi kaca-kaca da hawaye ta ce, "Na Wauki wannan auren a matsayin ?addarata kuma jarabawata, jarabawar mahaliccin mu tana zuwa a lokacin da baka yi tunani ba kuma baka yi zato ba. Na Wauki wannan abun a matsayin haka amma ba dan ina so ba Abiy. Na san na furta maka ina sonsa amma tunda akace na bari na ha?ura gabaWaya, ka tambayi Mama itace take bani ?arfin guiwa amma na ce mata tunda baka so na ha?ura. Ka yi ha?uri Abiy, wallahi ko me ka ke zargina dashi ban yi ba, ko tafiyata Kano ban je dan na Sata maka rai ko dan ka kasa bani abinda nake so ba" ta faWa da kuka sosai.

Abiy yayi shiru yana kallon ta, gabadaya kalamanta sun gama sanyaye masa jiki, zuciyarsa tayi rauni tausayin Naylan ya mamaye masa zuciya. Nayla ta kalli su Yaya ta ce, "Yaya da Yaya J wallahi ban yi komai ba, ku daina fushi dani. Kun ji Abiy yace kar nazo gidan nan, ya ce baya so na zo, na zauna a Kano...!" Ta faWa tana ?ara ?arfin kukanta wanda yake nuni da kalaman sun dake ta sosai.

Nayla ta gama raunana zuciyar Jawad, ji yake kamar ya zubar mata da hawaye. Ya ta so da hanzari ya ?araso inda take ya mi?ar da ita sai ta kwanta a jikinsa tana kuka. Shi kansa sai da yayi hawayen tausayinta, ya Wagota daga jikinsa ya zaunar da ita akan kujera ya kawo mata ruwa da kansa ya bata ta sha tana sauke ajiyar zuciya. Jawad ya ce, "ki daina kuka, ni bana fushi da ke Nayla, ina tare da ke a ko yaushe. Duk abinda ki ke so a ko yaushe ki kira ni ki faWa min, kuma ko meye ya faru wanda ki ke neman taimako ki sanar dani zan yi miki."

Kai ta Waga tana kallonsa ta kalli Abiy da yake kallonta. Kafin tayi magana ya rigata dan in ya bari ta cigaba da magana bai san abinda zai yi ba saboda tausayi da rauni da ?aunarta da yake ji a zuciyarsa, hakan ya saka ya katseta? ya ce, "Ku tashi ku wuce lokaci yana tafiya" ya faWa yana mi?ewa tsaye.

Nayla ta ce, "Abiy!." Ya kalle ta ba tare da ya amsa ba, sai ta dawo ?asa ta dur?usa ta ce, "ka yafe min, wata?ila bazan isa Kano da rai ba, wata?ila kuma bazan sake ganinka ba. Ina ji a jikina kamar mutuwa zanyi, don Allah ka yafe min."

Ajiyar zuciya yayi ya kalleta ya ce, "baki yi min laifin komai ba, kuma ni ba fushi nake da ke ba. Zaki je Kano lafiya in sha Allah."? Nayla ta ce, "Abiy in na mutu ka yarda a kawo gawata gidan nan? Kar ka ce za a binne ni a Kano don Allah, ina so a kawo maka ni ka yi min wankan gawa da kanka."

"Ya salam!" Abiy ya furta saboda yadda kalamanta suka daki zuciyarsa, kusan irin kalaman da mahaifiyarta ta dinga amfani dasu ne a lokacin da take gab da barin duniya shiyasa kalaman suka dake shi har cikin jininsa. Hannunsa ta ri?e ta ce, "Abiy ka yafe min, ban yi komai ba wallahi. Ina sonka Abiy, bazan iya Sata maka rai ba, duk abinda ka ce na bari ina barinsa da zuciyata da gangar jikina. Wallahi na bari tunda ka furta baka so, ka daina kallona da wannan laifin don Allah." Abiy da yake kallonta ya yi ajiyar zuciya, ya lura bata cikin hankalinta hakan ya saka ya kalli Yaya da Jawad ya ce, "Ku tashi ku wuce" yana faWa yana zare hannunsa daga cikin nata ya shige ciki ya barsu a wajan.

Mama ta ri?e Nayla suka fito tana kuka zuwa motar Yaya, duk jikinsu ya yi sanyi har Maman zuciyarta tayi rawa sosai musamman kalaman Nayla na mutuwa. Jalila da su Salma kuwa kuka suke yi sosai, Yaya ma ya kasa magana sai kallon Nayla da yake yi cikin rauni da tsananin ?auna da tausayinta. A haka aka saka kayanta a booth Win motar, Jawad ma ya shiga ta sa motar,? Salma da Jidda da Jalila suka shiga mota kuka aka ja mota suka fita daga cikin gidan.
KRB2P027
ArewaBooks@nanahaleema11

Abiy yana tsaye a balcony yana kallon lokacin da motarsu ta fita daga gidan. Wani irin yanayi yake ji a zuciyarsa mai wahalar fassarawa, sai yanzu yake tuhumar kansa akan meyasa ya yiwa gudun jininsa haka? Meyasa bai sake bata lokaci ba? Shin Nayla ta cancanci wannan hukunci daga gare shi kuwa? Anya bai cutar sa marainiyar Allah ba? Ha??inta bazai kama shi ba. Ajiyar zuciya yayi ya kulle ido yana tunani.

_Abiy ni na san wannan ciwo ba na tashi ba ne, ga amanar ?ata Nayla nan na bar maka, ka kula da ita yadda ya kamata. Na san za ka yi koda ban ce ba, amma ina sake maimaitawa ne matsayina na mahaifiyarta. Na san zaka bata tarbiyayya mai kyau, na san Zeenatu zata ri?e min ita hannu biyu ta yi mata tarbiyya tare da su Jidda. Abiy! don Allah kar ka bari Nayla ta yi kukan rashina a tare da ita, kar ka bari ta zubar da hawayen maraici, ka zame mata uwa, ka zamar mata uba, ka zamar mata jigo a rayuwarta._

Ido ya buWe tunawa da wasiyyar mahaifiyar Nayla, ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Allah ya ba ky zaman lafiya Nayla, Allah ya sa wannan auren ya zama alkhairi a gareki." Barin wajan yayi jikin sa a sanyaye ya rufe balcony Win ya dawo falo ya zauna zuciyarsa cike da tunani akan abinda ya faru.

" " " " " " " "

Dad kallon Mum yake yi tunda ta dawo daga America bai ji ta ce masa komai akan batun Narma ba, hakan ya saka shi tambayarta a wannan lokaci ya ce, "My dear Ina jiranki, me yake faruwa da Narma a can? Ina fatan komai lafiya dai ko?." Mum ta kalle shi ta ce, "babu lafiya, Narma ta canja kamar ba ita ba, ta rame sosai kamar bata cikin farin ciki."

Da mamaki Dad ya ce, "rashin Lafiya ta yi ta rame?." Mum ta ce, "lafiyarta qalau, kawai ni na ga alama bata jin daWin zama da Ashraf gabaWaya. Har yanzu da wannan yaron a zuciyarta, babu Ashraf a rayuwarta yanzu gabaWaya." Dad ya ce, "wannan masifa har ina? A can Win ma bata huta ba?." Mum ta ce, "sannan ka san Narma bata son wahala ko kaWan, shi kuma Ashraf ya kasa ha?uri da yanayin da take ciki yana raping Winta ko yaushe."

Dad ya ce, "wanne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login