Showing 36001 words to 39000 words out of 85380 words

Chapter 13 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3833

lokacin idanunsa na wajen fuskarsa a Wan sake. Nayla ta sunkuyar da kai tana murmushi cikin farin ciki, ko babu komai yana kula da yanayin ta, hakan ya yi mata daWi sosai har bata san ta ri?e hannun Salma ba. Salma ganin fuskarsa a sake sai ta ce, "tana kewar Didi ne."

Bai amsa ba ya kalli Didi da ta ce, "Nayla tana kuka ne saboda taga Ina kuka, murmushin ma tana yi saboda Ina yi Omar. Bata da lafiya amma ta taho daga Kaduna tazo kawai saboda aurena, Ina ji da ita sosai kamar yadda nake ji da kai. Kai ?anina ne ita kuma ?anwata ce." Girgiza kai ya yi bai ce komai ba ya Wauke kai yana taSe baki, ya sake kallon gefen da take ya ga kanta a sunkuye amma murmushi take yi.

Didi ta ce, "Nayla mu shiga ciki." Tare suka shiga falon Nayla tana ji kamar kar ta shiga ta tsaya ta dinga kallon Omar tana samun sau?in abinda yake damunta.

Shigar su babu jimawa suka fito harabar gidan da niyar komawa gidan Hajja. Turus suka yi ganin Narma da Najwa sun shigo gidan har lokacin Omar yana tsaye a inda suka bar shi. Narma ta kalle shi ta ce, "Faruk!." ?ago idanu ya yi ya kalle ta sai ta zube a wajan tana kuka sosai. Ido ya kulle ya buWe ba tare da ya kalle ta ba ta ce, "Omar me nayi maka ka ke hukunta ni da laifin da ba nawa ba? Faruk ni meye laifina da ko wayata baka Wauka?. Na yi maka message sau babu adadi amma ka ?i ka saurare ni Faruk, meye laifina a maganar nan?."

Bai motsa ba balle ya yi magana wani wajan daban yake kallo ta sake cewa, "Ina sonka, Ina ?aunar ka, Ina so na rayu da kai. Shikenan kuma sai laifin iyayena ya shafe ni Faruk? Daman laifin wani yana shafar wani ne Faruk?. Ban ?i ka ba, nace a haka Ina sonka, na ce zan bika mu dawo nan a Waura mana aure koda iyayena basa so amma ka ?i ji. Ya kake so nayi da raina ne Faruk? Na mutu kawai?."

?aramin numfashi ya yi ya Wago idanunsa da suka fara komawa jajaye ya kalle ta. Zunbur ta mi?e ta ?arasa kusa dashi tana kallon idanunsa tana kuka ta ce, "kalli yadda na koma, kalli kaga yadda soyayyar ka ta kayar dani, ka tambayi Najwa ko bacci bana iya yi, ko abincin kirki bana iya ci kullum cikin tunanin ka da son ganin ka. Iyayena basu san na baro London ba, kai tsaye daga can Kano nazo saboda kai Faruk, saboda kai kawai na taho tun daga London dan na ganka. Wallahi in na rasa ka zan iya mutuwa" ta ?arasa faWa a sanyaye tana sake zubewa a wajan tana kuka.

Najwa ce tazo ta Waga ta a inda take zube, ta ri?eta a jikinta tana kuka ta kalle shi ta ce, "Yaya Narma tana sonka, a da bana goyan bayan auren ka da ita, amma yanzu Ina goyan baya sosai. Don Allah ka taimaki Yayata ko iya waya da ita ne ka dinga yi kafin komai ya daidaita a wajan iyayen mu. Na tabbatar maka da zasu soka zasu amince da auren ku nan kusa, don Allah ka yi ha?uri ka manta da komai kar Yayata ta rasa tunaninta a dalilin ka" ta faWa tana kallon sa tana hawaye.

Hasbunallahu wani'imal wakil shine abinda yake furtawa kawai a zuciyarsa, zuciyarsa bugawa take rauni ya mamaye masa jikinsa gabaWaya. Tausayin Narma na tasiri sosai a jikinsa amma ya kasa ce mata komai. To me zai ce mata bayan shi ya riga ya ajjiye shafin ta a rayuwarsa?. Hannunsa Narma ta ri?e ta ce, "baza ka ce komai ba?." Zame hannunsa ya yi daga ri?on da tayi masa, domin in ta ri?e shi kamar haWuwar wuta da ruwa haka yake ji a jikinsa. Kallon ta ya yi ido cikin ido kafin ya sauke numfashi ya ce, "Narma!." Luuu tayi ta faWa jikin Najwa ta ri?eta sosai tana kallonsa.

"Ki manta da abinda ya faru, ki manta da abinda ya wuce ki bi umarnin iyayenki. Babu abinda zan iya yi miki a yanzu, na yi iya abinda zan iya yanzu komai ya ?are!."

Narma ta bishi da kallo ta ce, "kenan kana nufin na manta da kai?." Ya Waga mata kai ta ce, "bazan iya ba, wallahi bazan iya ba. Ni kaina da ace na san inda zan ajjiye soyayyarka da na ajjiye na hutawa zuciyata. To ban sani ba Faruk, ban sani ba!"ta ?arasa faWa da ?arfi tana kallon sa.

A kausashe ya ce, "ya kamata ki sani Narma, ya kamata ki sani!. Komai ya ?are, komai ya wuce, bazan yaudare ki da kalaman da na san bazan cika su ba, bazan faWa miki abinda na san bazan yi ba. Shiyasa nake faWa miki gaskiya, kije ki bi umarnin iyayenki, sannan ki tafi!."

Narma murya na rawa ta ce, "na tafi kace fa?." Ya Waga kai ya ce, "eh ki tafi, babu abinda zan iya yi miki a yanzu, ki tafi kawai."
"Na tafi ka ce?" Ta sake maimaita tana kallon sa. A birkice ya ce, "eh ki tafi! Ki je ki yi abinda iyayenki suke so ki ?yale ni!."

Kuka take yi sosai mai sauti na kusan minti biyu bata ce komai ba, Waga kai tayi bayan ta goge idanunta tace, "Farul ka san mutane ?alilan ne suke samun kusanci da zuciyar mace? For examples iyayenta da ?an uwanta, tunda tana tare dasu tana samun soyayya da ?auna daga gare su tun tana yarinya. Kaima haka naji a kanka, na ji a raina kamar na tashi tare da kai tun ina ?aramar yarinya Faruk, ji take soyayyarka ta shiga jinina kamar na jima da sanin ka. Tun daga wannan lokacin naji kawai so nake nayi rayuwata a tare da kai, ko kaso ni ko kar ka soni har abada bazan daina sonka ba Faruk, ko ka so ko ka?i zuciyata saboda kai kaWai take bugawa. Har yanzu ina sonka Faruk!."

Ta sake goge idanu ta ce, "zan tafi Faruk, amma ka sani zan dawo ko ban dawo ba duk abinda ya same ni ka sani soyayyar ka ce sila. Bazan taSa daina sonka ba har a tashi duniya" ta faWa tana fita daga gidan a guje.
KRB2P014
Arewabooks@nanahaleema11.

An kai amarya gidan ta mai kyau ana ta yabon kyaunsa saboda ko ina a gidan yayi kyau sai dai babu mutane sosai a kusa da ita amma kyau kam gida ya yi kyau. Jinkirin auren ta bai tashi a banza ba ya zame mata alkhairi domin kuwa da gidanta da lefen ta komai ma sha Allah.

Su Nayla gida suka dawo suna sauka a ?ofar gidan Hajja suka hangi Omar a zaune a ?ofar gidan Didi akan farar kujera ya Wora ?afa kan Waya yana kaWawa. Nayla murmushi tayi ta Wauke kai ta shiga gidan Hajja bata sake kallon sa ba.

Shi kuwa Omar kewa yake ji sosai a zuciyarsa, ya rasa abinda zai yi ya ji daWi. Ya san Didi kuka zata yi in suka haWu shiyasa ya gudu bai bari sun haWa ba dan baya son ganin kukanta. Gidan yake son shiga amma in ya tuna bata nan sai yaji babu amfanin shigarsa gwara yayi ta zaman a ?ofar gidan in yana ganin mutane zai fi jin daWi. Bai san ya damu da Didi ba sai yanzu, bai san haka Didi take da tasiri a gare shi ba sai yanzu, bai Wauka zai yi kewarta har haka ba sai ya tabbatar da bata nan.

A kan idanunsa su Nayla suka shiga gidan Hajja ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba da zama a wajan. Sai sha biyu na dare sannan ya iya mi?ewa ya shiga gidan, kewarta ta damu zuciyarsa sosai, haka ya zubawa ido yana kallo kamar zai ganta ko ya ji muryarta, ga tausayin Narma zuciyarsa. Tabbas yana jin tausayin Narma amma babu abinda zai mata in ba ya nisanta kansa da ita ba shiyasa ya aikata abinda ya aikata. Da wannan tunanin ya kwanta yana tunanin Didi bacci ya Wauke shi.

Washe gari.

Nayla haka ta tashi da nauyin jiki tayi wanka ta shirya tsaf cikin doguwar riga ta atampa mai kyau. Falo ta fito wajan Hajja ta zauna a kan kujera ta ce, "Hajja Baba Salisu ya taho yazo zamu wuce gida." Hajja ta bita da kallon tuhuma ta ce, "Hauwa me ya ke damunki ne haka?." Hajja ta kalli Salma da ta fito tana shan tea ta ce, "Salma me yake damun ?ar uwarki?."

Salma ta zauna ta mi?awa Nayla cup Win tea Nayla ta karSa ta ce, "na gode." Salma ta kalli Hajja ta ce, "Hajja bana ce ba, ni ma dai haka nake ganinta. Kawai ki ta yi mata addu'a." Hajja ta ce, "Me ya ke damunta? In ba zaku faWa ba zan kira babanta na tambaye shi. Ya ina tambayar? ku kuma ce min babu komai? Ina ganin duk wani motsin ku fa, yadda ku ke yin komai a sanyaye na tabbatar akwai abinda yake damunta." Nayla ta ce, "Hajja babu komai ba wani abun bane, shima Abiy Win haka yake cewa kuma na faWa masa babu komai."

"Mu in baki faWa mana ba ai Salma da Jidda sun sani." Salma ta ce, "Hajiya ni ban san komai ba gaskiya sai dai ko Jidda" ta faWa tana mi?ewa ta bar wajan. Hajja tayi musu banza bata sake magana ba amma tayi kuWurin tambayar Abiy abinda yake damun Nayla.

Lokacin da Baba Salisu yazo sai da ta kai masa abinci kamar ko yaushe, ta dawo daga kai masa abincin idanunta ya sauka akan masoyinta yana tsaye suna magana dasu Bashir suna nuna masa wasu kaya a leda. ?auke ido tayi tana takawa a sanyaye ta shiga gidan Hajja ba tare da ta sake kallon sa ba dan gabaWaya hankalinsa baya kanta. Bata jima da shiga ba ta gama haWa abinda tazo dashi ta kai mota, Baba yana gama cin abincin ya huta tayi musu sallama Salma ta rakata har bakin mota ta shiga suka tafi.

? ? ?? " " " " " "

Amarya Didi ta wayi gari a gidan miji cikin aminci da kwanciyar hankali, ganin abun take kamar a mafarki wai itace tayi aure bayan shekarun da ta kwashe ba tare da auren ba. Tana girmama ikon Allah da kuma lokaci da mutane suke faWa sai yazo komai zai faru. Tabbas ta amince da aure lokaci ne, duk yadda ka kai ga son yinsa in lokacin yin bai yi ba baza ka yi ba. Kamar mutuwa ce, duk yadda ka kai ga yin jinya in lokacin mutuwar bai ba babu inda zaka je, amma da zarar lokaci yayi kamar ?iftawar ido anyi an gama. Ita kam taga tasirin ha?uri, taga tasirin mi?awa Allah lamarinta, taga tasirin ?in sanya damuwar rashin aure a zuciyarta. Gashi fa lokacin yayi har ta wayi gari a gidan mijinta kamar almara.

Tana zaune a falon ta gabaWaya kewar Omar ta cika mata zuciya, AbdulHamid ya shigo falon da sallama ta amsa ya ce, "Omar Win kike tunani ko?." Didi tayi dariya ta ce, "wallahi, ina ta tunanin ko ya ci abinci." Ya yi dariya ya ce, "banda abin ki Omar ai ba yaro bane ba" ya faWa yana zama kusa da ita.

Didi ta ce, "baka san halin Omaar bane, baya son cin abinci sai ance masa gashi, ko ance gashi Win sai yaga dama. Bara ba kira shi" ta faWa tana Waukar wayata kira shi. ?auka taji anyi ta ce, "Assalamu alaikum." Daga can Sangaren Omar ya ce, "Wa'alaiki Salam, Hajiya Didi amarya."
"Alhaji Omar ?anin amarya." Dariya Omar ya yi ya ce, "ya naji maganar ki a dashe? me ya same ki?."
"Babu komai, mura ce kawai." Omar ya ce, "Kin sha ruwan sanyi kenan, shi bai san in kika sha ruwa mai sanyi kina tari ba ya bari ki ka sha?."

AbdulHamid da yake surarensa ya yi murmushi amma bai ce komai ba. Didi ma murmushin tayi ta ce, "jiya shine ka gudu ko?." Omar ya ce, "ni ai bana guduwa, kawai na Suya ne saboda ban son damuwa." Didi ta ce, "HaWuwa dani Win ne damuwa?."
"Kukan da zaki yi min shine damuwa, a haka ma kin barni da tunani inaga kin saka ni gaba da kuka?." Didi tayi dariya ta ce, "To yaushe zaka zo?."

"Zan zo, Zan zo ko dan na yiwa mijin ki huWuba ya san wacce yake aure, akwai gaSar da zan tabbatar masa da Yayar Damisa yake aure." Didi da AbdulHamid suka yi dariya gabaWaya AbdulHamid ya ce, "To Alhaji Omar ina nan jiran ka, Allah ya kawo ka."

Murmushi shima ya yi Didi ta ce, "ka ci abinci? Har sha biyu na rana tayi, Allah ya sa ka karya." Omar ya ce, "ban ci ba, ban jima da tashi ba. Yanzu dai nake tunanin abinda zan ci."
"Ka tashi ka yi girki mana, akwai abinci a kitchen da gas da komai ka dafa ka ci don Allah."
"To Didi zan ci."
"Ka kuma shiga gidan Hajja kayi mata godiyar abubuwan da suka faru."
"Didi nifa bana son godiyar nan kin sani."
"Ta zamar maka dole ne Omar, ta zama dole kaje kayi mata godiya." ?an tsaki ya yi ya ce, "to zan je."

Didi ta ce, "zan kira ka in anjima naji in kaje." Da to ya amsa a ta?aice ya kashe wayar ta kalli AbdulHamid tana murmushi. Shima murmushin yayi ya ce, "Kina ji da Oamar kamar yadda yake ji dake." Didi ta ce, "to mu kaWai Allah ya bawaa iyayen mu, kuma iyayen na mu su ma babu."
"Gaskiya ne. Allah ya ?ara muku zumunci." Ta amsa da amin tana murmushi yana ta tsokanarta da sunan amarya ita kuma tana murmushi cikin jin nauyi.

Bayan Kwana biyu.

*Abuja.*

Najwa tausayin Narma take yi sosai, gashi ana ta batun Waura aurenta a ranar kuma bata sani ba. Duk tayi wani iri kamar ba ita ba kana kallon ta kasan tana tattare da damuwa mai yawa. Najwa ta fita wajan mahaifinsu ta zauna ta ce, "Dad don Allah kar a Waura auren nan, ku ?yaleta taji da abinda yake damunta mana don Allah. In kuka aura mata Ashraf yanzu ba shi take so ba, ku ?yaleta taji da damuwarta."

Mum ta kalle ta cikin harara ta ce, "kin fi mu sanin abinda ya kamata ne?." Najwa ta ce, "A'a Mum, Amma ina guje mana danasani a nan gaba." Dad jikinsa ya yi sanyi, maganar Najwa gaskiya ce amma bashi da zaSi ko mafitar da ta wuce wannan, kuma dole ita zai bi dan samar mata da lafiya da kwanciyar hankali ta kuma manta da batun Omaar gabaWaya a rayuwarta.

Dad ya ce, "Najwa ki bar zancen nan, aure za ayi shi yau in Allah ya kaimu. Sannan bance ki faWa mata ba." Najwa ta tashi ta bar wajan cikin tausayin Narma sosai.
Narma tana zaune tana shan tea a falon sama tayi wanka ta saka ?ananun kaya riga da wando, wando iyakarsa guiwa sai riga mai baya a buWe. Najwa wajanta ta dawo ta zauna bata ce mata komai ba itama bata ce ba tea kawai take sha a hankali.

Sun jima a haka kafin suji ana hayowa sama ba tare da ta kalli wajan ba ya dai jin motsin mutane. Muryar Dad ta ji yana cewa, "gata nan ma a zaune." Kallon wajan tayi sai ta ga gwamna Katsina ne da Ashraf da kuma minister sai Dad da Mum da Nabil. Bata yi ?o?arin mi?ewa tsaye ba Dad ya karaso ya zauna kusa da ita mahaifin Ashraf shima ya zauna ya ce, "Daughter ya jikin na ki?."
Murmushi tayi ta ce, "Da sauki Daddy. Ina yini."
"Lafiya lau. Ina fatan babu abinda yake damun ki?."
"Babu komai Dady" ta faWa tana Wauke kai daga wajan.

Ya ce, "ma sha Allah, Allah ya ?ara lafiya." Ta amsa da amin tana ji suna maganar da ita ba ganewa take yi ba kafin duk su sauka ya rage daga Dad sai Mum sai ita a wajan. Dad ya kalle ta ya ce, "Narma yanayin damuwa da tashin hankalin da kike ciki, yau ciwo gobe lafiya shiyasa muka yanke hukunci a kanki." Da sauri ta kalli Dad ta ce, "ka yarda da Omaar?." Mum ta yi tsaki ta ce, "waye wani Omaar? Daughter ki nutsu mana, ki daina zancen wannan banza."

Shiru tayi bata ce komai ba. Dad ya ce, "Ashraf shine saurayinki wanda zaki aura a baya, kina sonsa shima kuma yana sonki. Wannan dalili ya saka yau Win nan mun Waura auren ku ke dashi, zaku tafi America ku je ku huta in kika nutsu sai a dawo ayi biki gabaWaya." Kofin da take shan tea ne ya suSuce daga hannunta ta kalli Dad murya na rawa ta ce, "au....re...Dad???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~??."
"Yeah Aure, an Waura miki aure keda Ashraf yanzu. Kuma gobe in anjima zaku tafi america ku huta daga baya sai ku dawo."

Narma kallon mahaifin nata take yi ba tare da ta iya cewa komai ba, muryarta rawa take yi haka jikinta ma rawa yake yi cikin tsananin tashin hankali. An aura mata wani ba Omaar ba? Kenan yanzu bata da hope Win aurensa ake so ace ko me?. Ganin yadda jiki ta yake rawa ya saka Mum ta ri?eta calmly ta ce, "Calm down my daughter! Kar ki damu Ashraf yana sonki kuma zai kula dake yadda ya kamata. Mun yi haka ne saboda ki dawo nutsuwarki bama so mu dinga ganin ki cikin damuwa."

Murya na rawa ta ce, "Mum in dai bakwa sona cikin damuwa meyasa baza ku aura min Faruk ba? Meyasa baza ku amince na aure shi ba?. Bana son Ashraf, Faruk nake so dashi nake so nayi rayuwar aure ba Ashraf ba, don Allah ku ce wasa ku ke yi min ba ku yi min aure dashi ba, please Dad you're just kidding me right?" ta faWa tana haWe tafukan hannayenta waje daya alamun ro?o.
Mum ta ce, "Zaki manta dashi a hankali, asirin da yayi miki zai bar jikinki saboda tasirin auren da aka yi miki. Kar ki damu ki nutsu."

Narma kuka take yi sosai zuciyarta nayi mata zafi, shikenan an rabata da Oamar Winta kenan? Shikenan yanzu bata da damar aurensa tunda gashi an aura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login