Showing 54001 words to 57000 words out of 85380 words

Chapter 19 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3832

ba haka ba wallahi zan bayar dake ga wanda na ga dama. Kuka take yi har lokacin cikin wani yanayi da bata san na meye ba. Abiy ganin yadda take kuka kamar ranta zai fita sai ransa ya sosu yaji kamar tausayinta, ya san bai saba yi musu tsawa ba dole ta yi kuka tunda bata saba ba, yayi tsaki ya kalleta ya ce,  tashi ki bani waje. Da sauri ta mi?e ta fita daga falon a guje har tana tuntuSe.
KRB2P019

Da kallo Abiy ya bita har ta fita yaja dogon tsaki cikin Sacin rai ya ce, "wai tana sonsa, kuma bai ma san tana yi ba. Mtsw! da gaskiyar Senator da yace asiri yake yi, nima gashi ya yiwa tawa ?ar. To in ba asiri ba me zai kai Nayla ta ce tana sonsa?. Sai yanzu naji irin abinda Sagir yaji a lokacin da yaje gidansa ya ce yana son Narma. Ashe abun akwai ciwo da ?unar rai, amma a lokacin da ya faWa min Wauka nake rashin ha?urinsa ne kawai." Mama da take gefe ta ce, "ni babban tashin hankalina ma kar ta aikata wani abu wallahi, yanayinta da maganarta kawai zaka ji ka san bata ha?ura dashi ba."

Abiy ya ce, "babu abinda zatayi. Kuma da ace yana da halayya mai kyau da background mai kyau me zai hana a bashi ita tunda tana so? To bashi da shi, ta?adarin Wan daban ne lamba Waya wanda ake jin tsoronsa a ko ina, ko meye abin so a wajansa oho."
"Ai ko yana da hali mai kyau meye amfanin bashi aure? Babu wanda ya san asalin su fa, su biyu kawai suke rayuwa. Ga samarin da suka kasance daidai da ita shi Win banza? Don Allah ka daina wannan maganar raina Saci yake yi."

Abiy ya sauke zuciyar ya ce, "kawai ku fara shirye-shiryen biki, dan bazan sake bata Lokaci ba a wannan karon, zan aurar da ita kawai. Da zarar ta san ta yi aure ai baza ta sake ambatar sunansa ba." Mama tayi ajiyar zuciya itama kafin ta ce, "Allah sarki, amma tana sonsa da gaske." Abiy ya kaawar da kai bai ce komai ba amma zuciyarsa gabaWaya babu daWi. Bai saba yiwa yaransa faWa ba, bai saba saka su kuka ba shiyasa da ya ga Nayla tana kuka sai ya ji zuciyarsa babu daWi gabaWaya.

Mama wajan Nayla ta shiga ta same ta a zaune tayi tagumi amma ta daina kukan. Mama ta zauna a gefenta cikin rarrashi ta ce, "Nayla kar ki damu da faWan da Abiy yayi miki, zai dawo daidai." Nayla a sanyaye ta ce, "ni na ha?ura Mama, zanyi abinda Abiy yake so." Mama ta ce, "baza ki ha?ura ba, na faWa miki sai kin samu cikar burin ki tare da amincewar mahaifinki. Abinda nake so dake kawai ki kwantar da hankalinki, ki? cigaba da harkokin ki zan san abinda zan yi."
"Mama Abiy yayi fushi, kina ganin Abiy dai faWa yake yi min abinda baya yi, ni na ha?ura kawai. don Allah Mama ki bashi ha?uri ki faWa masa da gaske na manta da wannan batun har abada."

Mama ta dafata cikin rarrashi da murya mai sanyi ta ce, "Kar ki damu, shima yanzu yake faWa min da ya sani bai yi miki faWa ba ya san ba yin kanki bane soyayya ce ta kawo hakan. Amma ki nutsu babu abinda zai faru kin ji?." Nayla ta Waga kai alamun to ba dan ta yarda ba. Mama ta dinga rarrashinta cikin kalamai masu daWi har Nayla ta Wan saki jikita kuma yarda da kalaman Mama sosai.

Haka Nayla ta kwana tana ciwon kai, da safe haka ta tashi da?yar ta tafi aiki, da taje can ma sai da suka kai ta asibiti saboda ciwon kai ya takura mata. A asibiti ta yini aka saka mata ruwa bayan an kira g1da an faWawa Mama. Sai yamma suka koma gida Abiy bai ce mata meye dalilin ciwonta ba ya dai yi mata sannu daga nan bai ce komai ba. Sai da daddare suna zaune gabaWaya har su Yaya a falo tana cin abinci kamar bata so saboda har lokacin bata jin daWin jikinta.

Yaya ne ya kalle ta da kulawa ya ce, "Nayla wai ne yake damunki ne? GabaWaya kin canja, bakya walwala, bakya hira, kuma kin rame. Meye a zuciyarki?." Abiy ya kalle ta sannan ya kalle shi ya ce, "Soyayya ce." Yaya ya kalli Abiy da sauri ya ce, "Abiy soyayya kuma? Wa take so?." Abiy ya sha tea ya kalle shi bayan ya ajjiye mug Win yana juya spoon a ciki ya ce, "Ina wani yaro da shekarun baya ya taSa taimakon ta lokacin da za a yi raping Winta a Kano?."
"Wannan Wan daban kenan, na gane shi."

Abiy ya sha tea Win sannan ya ce, "to shi take so. Akansa ta komai haka gabaWaya." Jawad da ya wara idanu ya ce, "Mun shiga uku, Tiger Win take so Abiy?." Abiy ya Waga masa kai alamun eh Yaya ya kalle ta ya ce, "Nayla Tiger ki ke so?." Bata iya magana ba sai sunkuyar da kai da tayi tana juya spoon a cikin abincin ba tare da ta ci ba.

Yaya ya kalli Abiy ya ce, "Abiy kai me ka ce to?." Abiy ya kalle shi ya ce, "kaiSa ai uba ne a wajanta, yanke naka hukuncin naji." Yaya ya ce, "Abiy ai tun wuri ta ajjiye wannan batu a zuciyarta, banda shirme da rashin hankali ta rasa wanda zata ce tana so sai wancan Wan shaye-shayen mai kashe mutane?."

? ? ? ? ?? "Wallahi baya shaye-shaye!."

A tare suka kalli Nayla jin abinda ta ce, itama sai take kallon su dan bata san abinda tayi ba ta ga dai ana kallonta. Gabanta ya yanke ya faWi, kenan a zahiri tayi maganar tunda taga kowa kallonta yake yi har Mama da Abiy. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Ta furta a sanyaye jikinta ya gama yin sanyi. Ta san halin Yayan su akwai saurin fusata yanzu sai ya gaggaura mata mari saboda wannan maganar da tayi.

Abiy yayi dariya ya ce, "to gashi nan ta baka amsa, masoyinta baya shaye-shaye." Yaya ya fusata sosai ya kai hannu kamar zai maketa sai ya fasa ya ce, "ni kike faWawa baya shaye-shaye? Kin fini sanin sa ne!?." Sai data firgita saboda tsawar da yayi mata.

Jawad ya kalli Abiy ya ce, "No wonder ko yaushe tace zata je Kano mana, ashe shi take zuwa gani tunda ma?oncin Hajja. Ka duba ranar da suka zo gidan nan da Yayarsa, gabaWaya Nayla ta rikice ta kasa zama, a lokacin na Wauka murnar ganin Yayarsa ne ashe saboda shi ta fita hankalinta." Yaya ya ce, "baza ta sake zuwa Kano ba, daga yau na soke zuwan ki Kano. In kinga kinje Kano to tabbas babban abu ne da ya kamata ace kin je!" Ya faWa da ?arfi yana nunata da yatsa.

Yaya ya kalli Abiy yace, "Abiy ba shine wanda ka ce Senator Sagir ya kama shi a Abuja ba?."
"Shine Babana, ni tazo ta saka a gaba tana kuka tana cewa tausayin Yayarsa take ji da surutai kala-kala, ashe nima case Win yana nan tafe zuwa gidana."
"Ai in tayi gangancin gayyato shi gidan nan wallahi na saka anyi masa dukan da za a karshi lokaci Waya. Meye abin so a wannan abun don Allah? Hasken fatarsa ne ya Wauke ki ko me?" Ya faWa yana kallon Nayla da bata ce komai ba ko hawayen ma sun ?afe.

Jawad ya ce, "Nayla in soyayyar ce baki wuce zuciyarki ta fara son wani ba, amma ki so wanda ya dace ya cancanta ba wannan ba. Ki ce kina son wannan ki ce kin son me don Allah? ?an daba mai kashe mutane ko karen yan siyasa?. Wai to shi yana sonki?." Abiy ya murmusa ya ce, "bai ma san tana yi ba Jawad." Yaya ya kalle ta cikin jin haushi da takaici ya ce, "wallahi kin bani kunya Nayla, ina Abbas, Ina Hashim, Ina sauran mutane biyun da suke sonki? Duk basu yi miki ba sai wannan mara aikin yin ne ya yi miki?."

Shiru bata tanka ba kanta na ?asa sosai kayan jikinsu kawai take gani ban da fuska. Mama ta ce, "Yayansu ka yi mata a hankali mana, ka daina yi mata faWa haka." Yaya ya kalli Mama ya ce, "Mama Nayla fa ba yarinya bace, tana sane duk abinda yake yi wallahi."

Yaya ya ce, "Abiy ka bani ita mu tafi Lagos, in yaso zan saka ayi mata transfer na aikinta zuwa can. Zan dawo da ita bayan na tabbatar ta bar wannan banzan tunanin."
"A'a, ka barta a nan ana gama azumin Ramadan aure zata yi. Ku fara shirin aurar da ita dan ba za a Wauki lokaci ba."

Jawad ya ce, "shikenan an huta." Sai sake jagalgwala nmaganar suke yi ita dai Nayla bata iya ce komai ba. Ta Wauka ma Ya J zai sassauta mata saboda shine mutuminta sai taga shima sai masifa yake yi kamar tace tana son wani ?aton arne.

Gajiya tayi da zaman kar ta tashi ta sake yin laifi, sai da taji sun yi sanyi da maganar sannan ta mi?e ta hau sama dan ta kwanta. Bacci ya?i zuwa idon Nayla, tana ganin kiran Salma na shigowa amma bazata iya Wagawa ba ta kawar wayar gefe ta rasa abinda zata yi ta ji daWi. Abin mamaki har biyu na dare idanunta biyu, sai kawai ta mi?e tayi alwala ta zo ta tayar da sallah, tana sallah tana kuka. Yadda take kuka a suujjada tana faWawa Allah damuwarta ma abin taSa zuciya ne. Sai gab da asuba ta fara jin bacci, ta hana idanunta bacci sai da tayi sallah sannan ta kwanta.

Sai sha biyu ba rana ta farka, bata fito ba sai da tayi wanka kasancewar alhamis ce azumi take yi baza ta fita ta karya ba. Tana nan zaune Mama ta shigo Wakin ta bita da kallo ganin ta rame daga jiya zuwa yau, ta zauna ta ce, "Nayla kinga yadda ki ka koma kuwa?."
"Mama Ina kwana" ta faWa tana kallon ta.
"Lafiya lau, ya ciwon kan?" Ta faWa tana taSa kanta. Mama ta ce, "har yanzu akwai zafi a kanki Nayla. Meyasa baza ki sassautawa kanki wannan damuwar ba?."

Nayla tayi shiru bata ce komai ba. Mama ta ce, "na san kina son Omar, Allah kaWai ya san me kike ji a zuciyarki. Kar ki damu da maganar Yayanki da mahaifinki zan san abinda zan yi."
"Mama da ace na san inda zan ajjiye son da nake masa da na ajjiye, da ace na san inda zan cire zuciyata da na cire na ajjiye Mama. Amma na kasa, nayi addu'a babu adadi amma ban taSa jin abinda nake ji a kansa ya ragu ba Mama. Ya zan yi? Su Yaya sun kasa gane ba yin kaina bane, sai faWa suke yi min....." ta faWa cikin rauni.

"Ni na fahimce ki shiyasa nace Ina bayan ki a ko yaushe. Abinda nake so dake yanzu ki kwantar da hankali ki nutsu, ki tashi ki shirya kayan ki kala uku zan saka a kai ki Kano." Da sauri Nayla ta kalli Mama da mamaki ta ce, "Kano kuma Mama? Baki ji abinda Abiy da Yaya suka ce ba?."

"Na ji, duk duniya babu wanda ya san waye mahaifinki kamar ni, na san abinda zai Sata masa rai na san abinda zai yi saurin saka shi ya bar fushi. Sannan Yayan ki abinda Abiy ya ce shi zai yi, in Abiy ya bar fushi ya amince da Omaar shikenan. Dan haka Abiy ne abin jin ba Yayanki ba."

"Mama meye amfanin zuwa Kano to?."
"Saboda ki samu nutsuwa, kuma sannan ni zan cewa Abiy saboda kin yi masa laifi ya saka ki ka tafi gidan Twiny dan ya huce. In kinje sai ki yi masa text na ban ha?uri ki turo masa,in kika kwana biyu zuwa ranar Sunday sai ki dawo shikenan." Nayla ta yi shiru tana kallon Mama kafin ta ce, "Mama anya hakan ya yi? Kar Abiy ya yi fushi dani."
"Bazai yi fushi dake ba, kar ki damu. Ki tashi ki shirya ko bakya son zuwa Kano Win?."

Nayla ta ce, "Ina so, amma....."
"Kar kiyi wani tunani, ki tashi ki shirya kawai na saka a kai ki. Amma ki tabbatar kin yi masa text na ban ha?uri tare da addu'a. Kuma kar ki faWawa mutanen Kano ni na ce ki kije, sannan ko Abiy ma kar ki ce masa ni nace ki je. Abinda ya sa na ce haka in kika ce masa ni na ce ki je zai ga kamar ba ke kika yi niyar bashi ha?uri ba ni na saka ki."

Nayla tayi shiru alamun tunani Mama ta dinga rarrashi tana faWa mata kalaman da taji a ranta zata je Kano. Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce, "To Mama" ta faWa tana tashi ta haWa kaya kamar yadda Mama ta ce ta ri?o hannunta har bakin ?ofar Wakin sannan tace taje. Mama tana tsaye a balcony tana kallon Nayla har ta shiga mota suka wuce.

Da hanzari ta koma ciki ta Wauki waya hannuta na rawa ta kira Abiy yana Wauka ta ce, "Abiy Nayla na cikin damuwa, Nayla tana cikin damuwa tana ta maganganun cewa in ba a barta aurensa ba zata iya kashe kanta. Don Allah ka dawo."
"Mtsw ?yaleta, babu abinda zata iya,
In na dawo zamu yi magana" yana faWa ya yanke wayar Mama tayi murmushi ta ce, "Bye bye Nayla" ta faWa tana sauke ajiyar zuciya ta ce, "mu jira dawowar Abiy."

" " " " " " " "

Nayla sai bayan la'asar ta shiga gidan Hajja, Baba Salisu ya sauketa ta shiga cikin gidan da sallama. Salma na ganin ta mi?e ta ?araso ta rungumeta tana cewa, "Oyoyo Nayla, sannu da zuwa." Nayla ta Waga kai ta ce, "Salma bani ruwa na kaiwa Baba ya sha." Amsawa tayi Salma ta fita da kanta ta kaiwa Baba ruwa sannan ta dawo ta zauna.

Nayla ta kalli Salma ta ce, "bara na yi sallar la'asar." ?aki ta shiga tayi wanka tare alwala tayi sallah ta canja kaya zuwa marasa nayi ta fito. Baba Salisu ta tarar yana gaisawa da Hajja sannan ya yi mata sallama ya koma Kaduna.

Nayla ta kalli Hajja ta ce, "Hajja Ina yini."
"lafiya lau Hauwa, ya jikin naki?."
"Da sau?i" ta faWa a sanyaye kai da ka ganta ka san bata cikin nutsuwarta. Salma ta kalleta ta ce, "Me ya faru na ganki katsam haka? Kuma gobe juma'a akwai aiki?." Nayla ta girgiza kai ta ce, "bani da lafiya ne bana zuwa ma aikin Kwana biyu, Nazo nan na huta, in na huta sai na koma."

Salma ta ce, "amma ana ganinki a san akwai damuwa a lamarinki." Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce, "babu komai" ta faWa tana tashi ta shiga Waki. Hajja ta Waga murya ta ce, "baza ki ci abinci ba?." Daga Wakin ta ce, "azumi nake yi."
"Kina azumi ki ka yo tafiya Hauwa?" Hajja ta faWa amma Nayla bata amsa ba. Hajja ta kalli Salma ta ce, "me yake damun Nayla ne haka?:"

Salma ta sauke numfashi ta ce, "bara ta huta yau sai ta faWa min abinda yake damunta, bara na bata lokaci ta samu hutu." Hajja ta Waga kai kawai bata ce komai ba amma zuciyarta na faWa mata akwai wani abun da yake damun Nayla.

A can Kaduna sai bayan sallar i'sha kamar ko yaushe suna zaune an gama cin amma babu Nayla. Abiy ya kalli Jalil ya ce, "jeka ka kira min Yayarka Nayla." Da sauri ya tashi ya hau sama zuwa Wakinta, ba jikawa ya dawo ya ce, "Abiy bata nan." Abiy ya ce, "bata nan kuma?" Ya faWa yana kallon Mama. Mama ganin yana kallonta sai ta ce, "tun Wazu ban shiga Wakinta ba ban san ita take ba, tun lokacin da muka yi waya da kai ban sake shiga wajanta ba gaskiya."

Jalila ?anwar Nayla da ta shigo falon a lokacin ta ce, "A'a Mama ni Wazu naga Anty Naya ta shiga motar Baba Salisu fa, na kuma ganta da jaka a hannunta na Wauka ma kano ta tafi." Mama ta ce, "jaka kuma? Nayla Win?."
"Eh Mama." Abiy bai ce komai ba ya Wauki waya ya kira Baba Salisu nan yake tabbatar masa da ya kai Nayla Kano.

Mama ta ce, "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ba dai maganar da ta faWa Wazu ta aikata ba? Na shiga uku, daman tace zata bar gidan nan in dai ba a yi mata abinda take so ba kuma baza ta sake dawowa ba" ta faWa hannu na rawa tana kiran wayar Nayla. Da yake a speaker ta saka kowa yana jin lokacin da wayarta ce baza ta shiga ba.

Yaya da ya shigo a lokacin yaji abinda ake faWa ya ce, "Wai Nayla ce ta bar gidan nan saboda Wan daba?." Mama ta ce, "ta tafi Kano ba tare da sanin mu ba gabaWaya, Allah ya sa tana lafiya." Abiy dai ya kasa magana ya yi shiru bai ce komai ba dan bai san me zaice ba, zuciyarsa zafi take yi akan abinda Nayla ta aikata wanda bai taSa tunanin zata yi ba. ?arar shigowar message yaji a wayarsa, ya Wauki wayar ya duba yaga ta Whatsapp ne kuma sunan Nayla. Da sauri ya bue yana karanta abinda ta rubuto masa a zuciyarsa.

Abiy ajiyar zuciya yayi bayan ya gama karantawa yayi shiru na wani lokaci. Kallon Jawad da Ahmad yayi ya ce, "Gobe da safe kuzo zaku raka ni wani waje, amma kuzo da wuri ina so mu isa kafin lokacin sallar juma'a" Abinda yace kenan kawai ya mi?e ya shiga Waki zuciyarsa cike da Sacin ran abinda Nayla tayi masa.

Da sauri Mama ta bi bayan sa ta ce, "Abiy me ya faru?."
"Babu komai, ki bani waje zan huta."
"Ka gwada kiran Nayla ko zaka same ta, Ina so na tabbatar da tana lafiya." Cikin tsawa Abiy ya ce, "nace ki bani waje ko!?." Da sauri ta fita daga Wakin ya kulle ?ofar.

Bayan fitar Mama waya ya Wauka ya saka a kunne ya ce, "zan turo maka sunan wani yaro a nan cikin Kano unguwar ?ofar nasarawa, ka tabbatar a daren nan ka nemo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login