Showing 48001 words to 51000 words out of 85380 words

Chapter 17 - KIRAN RABO Book 2 Completed Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

3844

ka dawo kamar Ogan ka."

Bash ya ce, "duk inda Damisa yake a nan muke." Murmushi yayi ya ce, "Gaskiya ne. Gwara hakan, yanzu kowa ya ganku ya ga mutanen kirki. Duk da dai daman Damisar naku bai yi irin kamannin ku ba." Omar mi?ewa yayi suka sake gaisawa da shi sannan ya fita suka wuce shago kai tsaye.

Ana ta aikin takalma shagon ma ya yi kaWan sai da aka sake karSar wani haya aka haWa biyu saboda Waya ya matse. Ya jima a can sai bayan sallar la'asar sannan suka koma gida Bashir yana sauke shi ya tafi shi kuma ya shiga gida.

Kallon gidan ya tsaya yi domin an share shi tass babu ?ura ko kaWan sai ?hamshi yake yi, ya yi murmushi dan ya san aikin Didi ne ya shiga falon da sallama. A zaune ya same ta tana waya yana shigowa ta kashe wayar ta ce, "ina ka shiga tun safe?." Zama ya yi ya ce, "na je shago ne. Ni na Wauka kin tafi."
"Ban tafi ba, sai zuwa magriba zai zo mu tafi." Bai amsa ba ta ce, "da sai na fita na bar gidan a buWe?."
"Yau aka fara?" Ya faWa yana kallonta.

"To kaje dai ka ci abinci."
"To Didi, an gode." Kallon sa dai take yi cikin tausayi dan gabaWaya tausayi yake bata, rashin uwa babban masifa ce a duniya, inda ace mahaifiyarsu tana da rai da Omar bazai yi maraici dan tayi aure ba. Tashi yayi ya shiga kitchen Win sai ga shi ya dawo da abinci a bowl ya zauna yana ci sai aka kira shi a waya ya Wauka yana amsawa duk magana akan sana'ar da ya fara ne kafin ya kashe.

Kallon sa ya ga tana yi ya Wauke kai bai ce komai ba, ya kuma kallonta ya ga dai kallonsa take yi ya ce, "Didi ya dai?."
"Omar ka daure ka yi aure don Allah." Ya Wan yi murmushi kaWan ya ce, "Ikon Allah, wai meye damuwarki akan nayi aure ne?."
"Saboda ina so ka fita daga maraicin nan da ka ke ciki."

"Wa zan aura?."
"Ga mata nan da yawa sai wacce ka zaSa. Ka duba yadda ka koma saboda rashin mai kula dakai." ?an taSe baki ya yi ya ce, "to zan yi."
"Ko ka bani dama na zaSa maka matar?." Kallon ta yayi sai ya Waga mata gira alamun eh ta ce, "da gaske fa nake."
"Nima haka" ya bata amsa yana cigaba da cin abinci dan so yake ya katse zancen auren nan da take yawan yi masa.

Kamar yadda ta ce sai bayan sallar magriba AbdulHamid yazo suka shiga har wajan Hajja suka gaisa sannan suka fito, Omar ta kira a gida suka gaisa yana ta tambayar yaushe zai kawo musu ziyara ya ce zai zo. Sallama suka yi suka tafi shi kuma ya koma gida zuciyarsa babu daWi ko kadan.

" " " " " " " "

Ashraf duk yadda ya kai ga rarrashin Narma abin ya ci tura sai kuka take yi kamar ranta zai fita, hankalinsa ya tashi sosai dan bai Wauka zata yi kuka har haka ba. Ya Wagota jikinsa yaji jikinta akwai zafi alamun zazzaSi ya ce, "Haba my love! ki daina wannan kukan mana, jikinki yayi zafi sosai." Narma ta ture hannunsa daga jikinta ta ce, "ka ?yale ni."

"Ta ya zan ?yale ki bayan baki da lafiya? Ki tashi na kai ki asibiti kinji." Tsaki tayi ta juya ta kwanta tana share hawaywe. Babban ba?in cikinta da Ashraf ya same ta a banza a wofi, ta so tayi tattalin jikinta har ta kai wa Omar masoyinta amma gashi a banza a wofi ya same ta komai ya lalace.

Shi kuwa Ashraf baya ya koma yana kallonta, sai da ta gaji da kukan dan kanta sannan tayi bacci ya tsaya yana kallonta. Murmushi ya yi yana shafa fuskarsa, tarin sha'awarta da yake ji gabaWaya ta kau sai shau?i da ya ke mamaye masa zuciya. LeSensa yake lashewa a hankali in ya tuna irin abinda ya tarar a jikinta sai yaji tsigar jikinsa na tashi har yana mararin sake kai kansa gare ta.

Ta jima tana bacci har akayi sallar i'sha sannan ta farka, tunawa da abinda ya faru da ita sai ba?in ciki ya mamaye zuciyarta, tsanar Ashraf ta yi mata dirrar mikiya a zuciyarta. Da?yar ta iya tashi ta kai kanta banWaki ta jima a ciki sannan ta fito. Doguwar riga kawai ta saka ba tare da ta saka komai ba ta saka hijjabi ta tayar da sallah. Jiri taji yana Waukarta a tsaye sai da ta zauna ta iya ?arasa sallar.

Tana idarwa kiran Mum ya shigo wayarta Wauka murya a dashe ta ce, "Mum!." Daga can Sangaren Mum ta ce, "Subahanallah! Daughter me ya same ki? Kar ki ce min kuka kika yi?." Narma ta ce, "Mum bana son zama a nan ni gida zan dawo, bana son zama da Ashraf baya sona ko kaWan."
"Me ya faru?."
"Mum raping Wina yayi" ta faWa murya na rawa alamun kukan zata sake yi. Mum da mamaki ta ce, "raping! Ashraf Win ne yayi raping Winki?."

Narma ta ce, "Eh Mum." Mum ta ce, "Narma! he's your husband fa, dan hakan ya faru baza ki kira shi da raping ba."
"Amma Mum ai ya faru ne without my consent, ya san bani da lafiya bana cikin nutsuwata amma bai iya ?yale ni ba sai da yayi raping Wina. Ya bari na amince mana, ya bari na samu lafiya mana. Ni na gaji bazan iya zaman nan ba Nigeria zan dawo."

Mum ta tausasa murya ta ce, "i'm sorry, yanzu me kike ji?." Narma a shagwaSe ta ce, "my whole body is in pain, I can't event sit properly. Mum I don't think I can stay here anymore" ta faWa a sanyaye cikin sangarta da shagwaSa. Mum ta ce, "ki daina kuka, kin sha magani?."
"Uhum uhum."
"Ina Ashraf Win?."
"I don't know."
"Okay, let me call him to take you out to hospital" Tana faWar haka ta yanke kiran.

Ba jimawa Ashraf ya shigo ya ?araso ya Wuka a gabanta ya ce, "i'm sorry my love, I'm sorry. Tun Wazu nace mu je asibiti kika ?i, yanzu ga Mum ta kira ni tace na kai ki asibiti. Please saboda Mum ki tashi mu je kin ji?." A tausahe yake maganar amma jin maganarsa take yi kamar ta aljanu saboda haushinsa da take ji.

"Please my love!" Ya sake faWa yana kallonta tare da Wagota ta mi?e tsaye. Zare hijjabin jikinta ya yi ya ajjiye ya kalle ta ya ce, "na saka miki kayan?." Idanunta a kulle yake ya kalli kayan jikinta yaga ana hango komai na jikinta. Wajan kayanta yaje ya duba ya Wauko doguwar riga wacce tafi ta jikin ta kauri sai dai itama roba ce. Bai damu ba ya ?araso ya bata ya ce ta saka.

Zame ta jikinta tayi ta fara saka wacce ya bata yana tsaye yana kallonta, lumshe ido yayi yana sake ?arewa surarta kallo da take a bayyane babu abinda ya rufeta. Ashe duk abinda yake gani a cikin kaya yana Waukar hankalinsa ba komai bane, yanzu ne yake ganin asalilin sura da abinda ya aura, dan shi kam surarta ya aura dan ba ?aramar sha'awarta yake yi ba. Babu abu mai Waukar hankali a jikinta kamar ?ugunta, hips Winta a cike yake sosai ga wrist Win nata Wan ?arami kuma siriri hakan ya bawa shape Winta damar fita sosai, in ta juya baya boobs Winta ma abin kallo ne.

Da?yar ya iya kawar da kai ta saka kayan amma ta?i motsawa ?arshe sai dau?ota ya yi suka fito harabar gidan. Da yake akwai mota a apartment Win da suke yana fita ya ajjiyeta ya buWe garage ya Wauko mota sannan ya sake fitowa ya Wauketa ya sakata ciki suka tafi. Koda suka je can ma duba ta aka yi aka bata magani aka saka mata drip dan jikinta ya saki. Bacci ta sake yi shi kuma yana tsaye yana kallon ta cikin tsantsar shau?i da son sake kasancewa da ita a karo na biyu.

" " " " " " " "

? ? ? ? Da daddare hankalin Nayla sam baya jikinta kasancewar washe gari shine ranar da Abiy ya bata zata faWa masa waye zaSinta. Bata cikin kwanciyar hankali dan bata san abinda zata ce masa ba. Tana zaune a falo tana kallon tv amma ba fahimta take yi ba tunanin ta na ga abinda zata cewa Abiy ya amince da ita. Dan ita dai ta san bata son waWannan mutane, in tace ta Wauki Waya wanda zata iya zaman aure dashi ta cuci kanta ne, kuma kamar yadda Mama ta faWa zata dinga kwasarwa kanta zunubi ne kawai.

Mama ce ta shigo Wakin har ta zauna kusa da ita bata sani ba sai da ta taSata sannan ta kalleta ta ce, "Nayla tunanin me kike yi haka?." Nayla ta sauke numfashi tace, "Mama tunanin gobe nake yi, ban san me zan cewa Abiy akan maganar nan ba."

Mama ta ce, "har yanzu bakya jin zaki iya zama da mutum Waya a cikin su?." Nayla ta Waga kai ta ce, "bana ji Mama, wallahi bana ji gabaWaya." Mama tayi ajiyar zuciya ta ce, "Kawai zan faWa masa akwai wanda ki ke so." Nayla ta wara idanu waje tana kallon Mama da firgici ta ce, "don Allah Mama kar ki faWa masa, in kika faWa masa ya nemi sanin waye shi fa?."
"Sai mu faWa masa waye, in ya kuma kira ki ya tambaye ki ki tabbatar masa da kina sona kuma aurensa kike so ki yi."

Nayla ta fara girgiza kai cikin tsoro ta ce, "bazan iya ba Mama, bazan iya ba wallahi." Mama ta dafata ta ce, "ni zan iya yi miki faWan Nayla, abinda nake so in ya kira ki ya tambaye ki ki tabbatar masa dake shi kike so kuma shi ki ke son aura. Zaki iya ko baza ki iya ba?."

Nayla ta kalli Mama cikin rauni ta ce, "Mama bazan iya ba, bazan iya kallon Abiy na tabbatar masa Ina son Omar ba, bazan iya ba gaskiya." Mama ta ce, "zaki iya, zuciyarki zaki saurara da zarar ya kiraki, kar ki bar harshen ki ya sarrafa kalaman zuciyarki, kai tsaye ki bari su fito daga cikinta ki faWa masa gaskiya, in ba haka ba in ya gano da kansa ransa ne zai Saci sosai."

Nayla ta ce, "Mama gwara ya gano da kansa da ace nice na tabbatar masa." Mama ta dafata cikin rarrashi ta ce, "Nayla bazan taSa bari naga kina son abu ina da damar baki shi ban baki shi ba, sannan bazan taSa bari naga kina shan wahala akan abinda bai fi ?arfin ki ba kuma na zuba miki idanu. Zan iya yin ko meye wajan ganin na samar miki da farin ciki koda ni zai zama silar ba?in cikina. Dan haka ki bani haWin kai Nayla, na tabbatar miki zanyi abinda mahaifinki zai baki abinda kike so ba tare da tashin hankali ba ko wani abun."

Nayla ta kalli Mama cikin gamsuwa da kalamanta ta ce, "Na sani Mama, amma bakya ganin Abiy zai yi fushi dani?."
"Babu fushin da zai yi dake, ki bar komai a hannuna ina tabbatar miki da babu abinda zai faru sai alkhairi." Nayla ta sauke numfashi ta ce, "To Mama" ta faWa a sanyaye tana wasa da hannunta. Mama tayi murmushi ta ce, matar Omar." Kunya ta bata sai ta rufe fuska da hannunta kafin ta buWe ta ce, "Mama shi fa bai san Ina sonsa ba, taya zan aure shi?." Mama ta yi murmushi cikin shigar kwantar da hankali ta ce, "ke dai ki jira mu gama da Abiy zamu koma kansa." Kai ta Waga kawai bata ce komai ba Mama ta fita ta barta a zaune tana tunani.

? ? Washe gari a Warare ta shirya ta tafi aiki, ko a can ma haka take yin komai babu kuzari har lokacin dawowar ta gida yayi ?arfe biyar na yamma. Tana ajjiye motarta taga motar Abiy sai da gabanta ya faWi tayi saurin wucewa ciki ta shige Wakin ta harda kulle ?ofar da makulli.

Bayan sallar i'sha kamar yadda Abiy ya saba yana zaune shida Mama bayan ya gama dinner ya kalli Mama ya ce, "ya kuka yi da Nayla? yau ne kwana biyun da na bata." Mama ta fuskance shi sosai ta ce, "maganar gaskiya Nayla bata son samarin nan guda huWu." Abiy ya kalleta cikin mamaki ya ce, "kamar ya bata sonsu? Duka mutane huWun babu wanda take ji zata iya aure?. Wannan ai shirmen ne da rainin hankali, na bata iya lokacin da zan bata kuma tazo min da wannan iskancin?." Mama ta ce, "hmm wani daban zuciyarta take so ba su ba."

Abiy da mamaki ya ce, "wani daban kuma take so? Waye shi?." Tayi ajiyar zuciya ta ce, "Wani ne daban a Kano, babban abin haushi da tashin hankalin ma data buWe baki ta faWa min waye yafi komai Waga min hankali. Kuma wai bai ma san tana sonsa ba, duk wannan rashin lafiyar da take fama da ita cikin kwanakin nan duk saboda shi ne, wannan ramar da tayi da rashin nutsuwa duk akansa ne. In da ace mutumin kirki ne na gari dan tayi haka a kansa ba laifi bane, amma ni har kunyar faWa maka waye nake yi wallahi" Mama ta faWa cikin zallar nuna takaicinta.

Abiy da yake so Mama ta kai ?arshen maganar a ?agauce ya ce, "wa take so? Waye shi ki faWa min bana son zagaye-zagaye." Mama ta Wan yi shiru kafin ta ce, "wannan Wan daban yaron nan da ka yiwa hanya aka fito dashi har suka zo gidan nan godiya. Shi Nayla take mutuwar so, ta tabbatar min da in baka amince ta aure shi ba zata iya barin gidan nan, ta ce min zata iya barin kowa na gidan nan taje ta tare dashi kaWai. Wannan kalma ta tayar min da hankali, nayi rarrashin na nuna mata hakan kuskure ne amma Nayla sam ta kasa amincewa."

Mutuwar zaune Abiy yayi jin kalaman Mama ya zuba mata ido ya kasa cewa komai, Da?yar ya iya tattaro kalaman bakinsa ya ce, "Omar Wan daban Kano take so? Wai maganar nan gaskiya ce ko wasa kike yi min?."
"Wallahi da gaske nake, ita da kanta ta faWa min. Da farko na Wauka wasa ne amma Jidda ta tabbatar min da gaske shi take mutuwar so. Abin haushin ma ko ta ita baya yi, in da na kirki ne ma da sau?i to na banza ne. Wallahi ji nake kamar na yi kuka."

Abiy ya rasa ma abinda zai ce kawai sai ya mi?e ya shiga zuwa cikin gidan ya hau sama har Wakin Nayla ya same ta a zaune tana ganinsa ta firgita ta mi?e tsaye. Kallonta yake yi kamar yadda take kallon sa dan in ba rashin lafiya ba babu abinda yake kawo Abiy Wakinta sai dai in bata da lafiya.

Abiy kallon ta yayi ya ce, "Nayla da gaske ne abinda Maman ki ta faWa min? Da gaske kina son Omar na Kano?." Gabanta ya yanke ya faWi ta Wago ido ta kalli Mama da take gefen ta tayi mata alama da ta amsa ta sake saukar da ido ?asa tare da zube guiwarta duka biyun a gaban Abiy.

Abiy ya ce, "tambayar ki nake da gaske kina sonsa? Da gaske akan sa kike wannan rashin lafiyar?." Nayla ta sake sunkuyar da kai hawaye na zuba a idonta. Mama ta ce, "Abiy ka yi mata a hankali" ta ?araso kusa da Naylar ta ce, "Nayla ki faWa masa abinda yake ranki. Da gaske kina son Omar?." Nayla zuciyarta bugawa take yi sossai, zuwan Mama kusa da sai ya ?ara mata ?arfim guiwar da ta amsawa Abiy tana so Win.

Dafata Mama tayi hakan ya saka tayi ajiyar zuciya ta sake saukar da ido ?asa ta ce, "Da.....gas....ke....ne......Abiy....."ta faWa a rarraebe cikin tashin hankali da tsoro. Abiy ya ce, "da gaske ne me? Da gaske shi kike so?." Ta Waga kai alamun eh. Abiy ya ce, "'magana zaki yi min!." Tsawar da ya yi mata sai da ta tsorata, a firgice ta ce, "Eh Abiy, da gaske shi nake so..." ta ?arasa faWa cikin muryar tsoro da tashin hankali.
KRB2P018

 Hauwa! Abiy ya faWa cikin tsawa yana kallonta cikin Sacin ran jin kalamanta masu kama da rashin hankali ko wacce bata cikin hankalinta. Dumm ?irjin Nayla ya buga, ta wara idanu waje cikin tsantsar tashin hankali da firgici. Tunda take da Abiy bata taSa ji ya kira asalin sunanta ba, koda wasa bai taSa kiranta da Hauwa ba sai dai ya ce Mamana ko kuma Nayla, amma yau gashi ya kira sunanta da murya mai amo mai nuni da tsantsar Sacin ran da yake ciki.

Kasa Wago kai tayi dan yanayin muryar mahaifin nata da taji bata taSa jinta a kausahe haka ba, hakan ya saka ta kasa Wago kai ta amsa kiran da ya yi mata. Abiy ya ce,  kina cikin hankalinki kuwa?. Nayla ta sake sunkuyar da kai kamar ruwa ya cinyeta ko motsin kirki bata so ta yi.

 Wannan yaron ki ke kallona kina cewa shi kike so Nayla? Me ya shiga kaaki ne?. Wannan dalilin ne ya saka kika tayar da hankalin ki a karSo shi daga hannun Senator?. Yadda yake magana cikin murya mai amo ya saka Nayla yin danasanin furta abinda ta ce dan gabaWayata rasa nutuswarta. Abiy baya taSa yi musu tsawa tunda suka tashi, yadda yake yi mata a yanzu ya sakata take ganin abun ba?o shiyasa ya tsoratata sosai.

Mama ce ta kalle shi ta ce,  ka yi mana a hankali Abiy. A fusace ya ce,  bazan yi mata a hankalin ba, yarinya ce ko kuma bata da hankali? Bata san abinda ya dace da wanda bai dace ba ko me?. Duk mazan duniyar nan, duk mazan da suke Kano da wajan Kano ta rasa wanda zata fara so sai ri?a??en Wan daba wanda aka yi masa shaida mara kyau?. Meye abin so a tare dashi!. Mama ta kalli Nayla da ta kasa motsi ma balle tayi magana, ta kalli Abi zata yi magana ya dakatar da ita ya kalli

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login