Showing 1 words to 3000 words out of 86718 words

Chapter 1 - SAIFUL-ISLAM Book Complete by miss xoxo (2).pdf

06 Jul 2025

2068

[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...*


*NA*


*©NANA HAFSAAT*
*(MISS XOXO)*


*®HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*SADAUKARWA GA:*
*ASY KHALEEL*


*TUKWICI NE GARE KU:*
*YA HAJJAH CE*
*BILLYN ABDUL*



*SHAFI NA D’AYA (1)*


*Daga shafi na d’aya xuwa na biyar na ki ne uwar d’aki na,ni kadai banda Hafsat Rano�.Sis
UMMI AISHA*


مسب الله نمحرلا ميحرلا


*ABUJA*

*A* jiye yaron da ke hannunta tayi akan gadon sa tare da d'ora kansa akan pillow irin na jarirai
dinnan, wanda lokaci d’aya ya keta sharar baccin sa, ta shafe shi da addu'a,sannan ta dauki
macen dake ta faman wangale wawulon bakin ta da babu hakori a ciki.

Kallo d’aya zakai wa yaran kasan cewar 'yan biyu ne.Tashi tayi ta dinga zagaye parlorn da
yarinyar a hannunta, tana d'an jijjiga ta har sai da tayi bacci, sannan ta kwantar da ita a kusa da
tagwai d'in ta.

Komawa tayi gefen su ta rage volume d'in tv da ketayi a tashar Africa magic yoruba. ‘jenifa’s
diary’ ake yi lokaci zuwa lokaci take d'an murmusawa, da alama sosai take jin dad'in drama
series d'in.

Wayar tace ta fara rurin kara ‘Miftahul qalb’ shine sunan dake ta yawo a samab screen d'in
wayarta ta, da azama ta d'auka tare da karawa a kunne had'e da mikewa a hankali tabar wajen
gudun kada ta tashi yaran nata dake ta baccin su.

“Assalamu Alaikum Qalb..”

“Wa’alykm Salam sugar, yanzu na sauka fa” Cewar *SAIFULLAHI* dake janye da akwatin sa
madaidaici a harabar airport d'in Lagos .

“Wayyo! Sannu qalb.. ka sauka lapia?!
Ubangiji Allah yasa albarka a abinda akaje nema, rabbi ya dawo daku lapia, yanzy dai ka samu
abinci kaci banda shan abu mai sanyi dan Allah...kaji?”

Ajiyar zucia ya sauke, Allah ya sani yana matukar son matar sa da yaran sa, dole ce tasa yake
nisa da su saboda yanayin aikin nasu, muryar tace ta sake dawo dashi daga tunanin su daya
tafi ida take cewa.

“Kaji Zawj?”

“Na..Naji Love! Insha Allah bazan sha ba”

“Toh! Bari na kyale ka, ka huta tukunna anjima sai na kiraka muyi video call kaga 'yan biyun ka
dan tuni sunyi bacci babu dadewa”

Shafa kwantaccen sajen sa dake kwance luf-luf a saman fuskarsa yayi, dan ba kad'an ba yana
jin wani shaukin sonta na kuma ratsa shi yana lalata duk wani jini dake shiga jikinsa..

Cikin kasalalliyar murya ya furta,

“Okay love..! Yanzu zamu wuce ikoyi da Abbas anjima kuma zamuje ikeja filling station d'innan
saboda traffic d'in lagos da safe..will call you when I’m done idan dare be yi nisa ba..”

“Okay zawj.. I love and miss you sai anjima..”

Sallama suka yiwa juna, bayan kowannen su ya sakarwa d'an uwansa zazzafan kiss ta wayar,
cike da kadaicin junan su kowannen su ya katse kiran had'e da nannauyar ajiyar zuciya.

Komawa tai parlor wajen 'yan biyun ta dake ta bacci cikin nutsuwa. Tuni har angama shirin

jenifas diary an shiga yin wani kuma, kallon agogo tayi 11 saura.

“Wai..haka dare yayi?..”

A gaggauce ta dau yaran nata ta takai d'aki, bayan ta canza musu kaya izuwa kayan bacci,
band'aki ta fad'a wandake cikin d'akin tayo wanka hade da dauro alwala ta fito. Sai da tai
nafilfilinta sannan ta koma kan gado tai azkhar na bacci hade da addu’oi na kariya ta tofe su
sannan ta dauki wayar ta tana dannawa, ganin har sha biyu tayi bai kira ba, tasan lalle aiki ne
ya rike sa. Gajeren message ta tura masa kamar haka,

_“Every day, I fall in love with you more. I don’t know how that’s even possible when I’m sure
that I couldn’t love you more than I love you now. I guess you just have this thing about you that
makes loving you so easy and natural. I miss you already. Sleep now,honey. Sweet dreams.
Allah ya yi jagora a abinda akaje nema”_
Ajiye wayar tayi a gefen bedside drawer dake gefen ta, ta bud'e ta zaro photo album d'insu na
secondary school, wato BRITISH NIGERIAN ACADEMY(ABUJA)tana kalla..

Memories ne suketa dawo mata kallon 'yan ajin nasu take yi, d’ai-d’ai har tazo kan 'yan gidan da
suke uba d’aya dasu wato Hafsat Khaleel Mai Mota sai ta biyu wadda sunan ta ke rubuce da
Hidaya Khaleel Mai Mota, sai babbar kawarta Haleema Sameer Ameer sai kuma hotan ta dake
k’arshen Page d'in rubuce da Bilkisu Khaleel Mai Mota *(ISLAM)*
Murmushi fadad'e a fuskarta take bin kowan ne hoton 'yan ajin nasu da kallo, tun daga kan
matan har zuwa mazan ajin nasu take kallo abubuwan da suka faru na dad'i dama akasin haka
take ta tunanowa harta gama ta rufe photo album d'in wanda suka kammala makaranta a
shekarar dubu biyu da goma sha hud'u (2014).
“Such is life” (haka rayuwar take) Shine abinda Islam take ta maimaitawa kafin ta kwanta bayan
ta kara yin wata addu’ar.

Kwanciya tai zuciyarta fal da abubuwan da suka faru a baya, idan na kunya ne ta rufe ido, Idan
na dariya ne ta murmusa ita kad’ai.

Haka bacci barawo ya sace ta, zuciyarta cike take da tuna bayan rayuwar ta, tana ta shek'a
baccin ta saifullahi yayo mata reply,

_"Sugar pie.It does not matter how my day was, I always long for the night, to cuddle you all
night as you quench my heart.It was a stressful night,aiki muke tayi yanxu ma muna
construction site na ikeja... A shafa min kan Arya da Aryan...I love you more than life itself.
Goodnight my love.."_
Asubah ta gari masoyan juna.. *SAIFUL_ISLAM*

Da wannan Ni Nana hafsatu nace shin wacece ISLAM?wacce irin rayuwa tayi da har take
tunanin ta haka?!..Ya kamata mu koma shekarun baya don ganewa idanuwan mu abubuwan da
suka shud’e‍♀

***** *ASALIN LABARIN*


*BRITISH NIGERIAN ACADEMY...SS1b*

Zaune kowannen su yake a kujerarsa da yake monday ce duk yawanci ransu a b’ace yake
musamman da yake first period maths ne.

Back sitters babu abunda suke sai ciye-ciye sai kuma 'yan lovey dovey squad dake hirarrakin
soyayya da yake mix school ce (makarantar mata da maxa a hade).. Sai 'yan seat d'in gaba
wato su ISLAM madam serious ita da kawayenta, kowannen su kansa a kasa suna ta karatu
kafin malamar maths din ta shigo..
Shigowa Miss Abigail tayi daga ita sai mini skirt da top d'in riga tasha attachment a kanta,
mikewa class d'in suka yi masu hararta nayi mazan nata faman sakin fito a hankali, da yake
rabin su sun tsani maths, kuma a jin sune sahun gaba a rashin ji, Da karfi 'yan gaba suka fara;

“Good morning ma..! we are happy to see you ma’am, God bless you ma..” Banda 'yan baya
dake cewa,

“We are not happy to see you ma.. God punish you ma” A hankali yadda bazata jisu ba.. Ita
kuma sai washe baki Miss Abigail d'in take yi tana cewa.

“God bless you too..Thank you.. have your seats please”

Juyawa tayi tana rubutu a board, ‘Matrix and Matrices’ shine abunda ta rubuta kafin ta juyo ta
dube su..

“Okay class..Today we are going to discuss and solve Matrix and Matrices’ I’m going to solve
Number one question and one of you will come and solve the other.. I’m I clear?!”

“Yes Ma..” Suka fad’a da karfi.

“Good..”

Ta fad'a tare da juyawa tana solving banda su Islam, babu wanda yake sauraronta sai ma
cigaba da hirar su da suka yi har ta gama tayi musu bayani sannan ta kalli class d'in tana cewa.

''Okay who’s going to solve the next?”

“Maa..” Islam da ta d'aga hannunta alamun zata iya, had'e da gyara zaman medicated glass
d'inta.

“Good..” Cewar Miss Abigail tana mikawa Islam d'in marker..

“Mtcew” Hafsaat da suke uba d’aya sannan tana d'aya daga cikin 'yan back seat taja tsaki a
hankali tana furta,

“Sai dai nacin karatu kawai da san iyawa, banxa mai bakin jini..”





_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...*



*NA*



*©NANA HAFSAAT*
*(MISS XOXO)*



*®HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_



*SHAFI NA BIYU (2)*


Sam Islam bata bi takan ba’ka’ken maganganun da Hafsat da kawayen ta ke gasa mata
ba,Tana jin su suna aiba tata suna mata mugayen fata,haka tai ficewar ta gaban board,babban
burin ta bai wuce tai solving equation dinnan dai-dai ba..

Kaman yadda Miss Abigail da kawayen Islam suka tsamma ta akan Islam, hakan ce kasance,

domin dalla-dallah Islam ta kalkuke maths din, Tafi (round of applause)Miss Abigail tasa yan
class din suyi nan suka fara ji kake.

“Raf raf raf..”

Ajin ya dauka da tafin masoya da kawayen Islam amman banda bangaren su Hafsat wato ‘yan
back sitters da suke jifan Islam din da harara.

10marks sukutum Miss Abigail ta bawa Islam,kan idan exams tazo tanada additional ten
marks,godia Islam tayiwa Miss Abigail tare da ‘yan class sannan takoma seat dinta ta xauna.

“Lam Lam all the way..Go gurl..”

cewar Haleema Sameer Ameer wadda suke kira da Lee, itace babbar kawar Islam kaf BNA sai
sauran kawayen ta su Hafsat Rano,Fatma Bichi,da Hanan, Leesa da kuma namijin cikin su
wato Kamalu,wanda sukewa laqabi da K-boy shine class rep,Islam kuma itace assistant class
rep..
Bayan fitar Miss Abigail,Mr okafor physics teacher dinsu ya shiga class din,sosae su Hafsat
suka shiga nutsojin dan ba kadan ba yake basu punishment idan ya kama wani ko wata suna yi
masa sakarci acikin aji, Saboda makarantar ba’a duka kowa ubansa wani ne a garin kama daga
k’usa a gwamnati ko kuma shahararren dan kasuwa ne a kasar. Duk ‘ya’yan masu farcen susa
ne,shi yasa kowannen su yake baje hanci yana shi ma fa ubansa yana cikin jerin who is
who..wannan kenan!

A cikin BNA ‘ya’yan Dr Khaleel Mai Mota su uku ne Bilkisu (ISLAM), Hafsat,da kuma
Hidaya.Kowanne uba suka hada amman uwa kuma kowa da tasa.Hafsat da Islam sune suke
science, while Hidaya tana Art class, kasancewar hakan yasanya Hidaya hostel dinta daban
ne,Islam da Hafsat kuma hostel dinsu d’aya..
Tsangwama, kyara, ba’a, mugunta, hassada,gulma,tsegumi kai wataran harda rabon duka Islam
ke samu awajen su Hafsat saboda sun tsaneta,tsana mai tsanani wadda takai kololuwar xarce
mizanin mai karatu..

“shin ko me yasa hakan? oho muje zuwa...!”

DR IBRAHIM KHALEEL MAI MOTA: shine mahaifin su Islam,Asalin Ibrahim khaleel dai
haifaffen garin kano ne kauyen y’ar gaya, mahaifin dr khaleel shine marigayi malam tasi’u mai
guga tare da mahaifiyar su inna Bilkisu dake kauyen na y’ar gayan,

Su uku ne wajen mahaifan su, Yaya Bala shine babba sai dr khaleel sai kuma kanwar su
hansa’u..Hakika su dr khaleel sun taso cikin matsananciyar rayuwa, domin tun mahaifin su nada
rai suna kanana guga ce sana’ar sa, tahaka yake ciyar dasu daganan bayan rasuwar sa kuma

mahaifiyar su tafara sana’ar wankau dan rufawa kanta asiri da marayun ta dan takan je tayi
gidah gidah ko kuma a kawo mata tayi,

Da wannan suke samun rufin asirin su,har dai babban wansu Bala ya fara sana’ar shoe shiner,
duk ranar talata kasuwar karkarar yake zuwa yin dako samu yai musu awun hatsi da yan canjin
sa na shoe shiner, har wayo yafara kama Khaleel inda yataso yaro mai kaifin basira yanada
saurin daukar karatu na boko da arabi.
Inna Bilkisu batai kasa a gwiwa ba sosai takeson tacika burin khaleel na zama shahararre a
fagen ilimi tunda yataso da zuciyar yi, itada Bala da dan kudin da Hansa’u ke samu wajen tallar
kayan koli da su akeyi masa amfani .

Allah abun godia kwanci tashi ba wuya wajen Allah, burin inna yacika domin khaleel yagama
sakandire kuma har yasamu fannin karatu na d’aya a sashen karantar halayyar dan adam, da
kuma zaman takewar yadda k’asa take wato (sociology)result d’insa yayi kyau,yafito da first
class take aka bashi scholarship na k’asar Egypt inda ya samu gurbin karatun Msc psychology.
Shekara biyu yayo acan yadawo gidah sunyi sunyi su rikeshi ya xauna acan ya dinga koyar
wa,amma afatau yak’i, domin yana kishin k’asar sa nijeriya Abubuwa da dama sunyi sauk’i,Yaya
Bala yatafi lagos neman kudi,Hansa’u tayi aure sosai yanzu basuda wata sauran matsala sannu
ahankali da yan kudin sa daya dawo dasu yagyara musu gidan su,Ya sai y’ar Mota golf domin
yin haya,da lodin gari gari ga form na PhD ya siya a jam’iyyar bayero ta kano,kasancewar sa
matashin mutum a kauyen daya fara siyan mota yasan ya ‘yan kauyen yi masa laqabi da
‘Khaleel Mai Mota..’ kuma sunan ya bishi!

Sannu ahankali komai na tafiya dai dai da lodin da yakeyi na gari-gari,

sanyayyar safiyar asabar gashi lokacin damuna ne ya ‘dau lodin yan jihar yobe xuwa maiduguri
idanuwansa sukai masa tozali da matashiyar budurwar,da kallo d’aya xakai mata kasan
babarbariya ce kyakkyawa da dan bular hancinta a gefen dama,kwarai matuka tatafi da zuciyar
ibrahima khaleelu,inda yaji duddunia bayan mahaifiyar sa babu abu na biyu daya ke so ya
xamto mallakin sa irin wannan y’ar budurwa,

Sosai tayi nasarar cafke zuciyar khaleel,bayan ya dire su a bornu ya sakko ya nemi samun
number ta,da alama itama yatafi da ita cikin ‘kan’kanin lokaci takaranto number ta harda doriyar
sunan ta.

Arziki aka ce kashi ne,sosai khaleel fa Allah ya dubi talaucin su da maraicin su lokaci d’aya
kofar arziki ta budewa Khaleel da yaya Bala,abun dai sai sam barka kawai cikin wannan
yanayin ne khaleel yai aure da sahibar tasa Aysaa,a kuma wannan yanayi yaya Bala ta biyu ya
kara da yake shi xamansa yama fi yawa a lagos yanzu,domin yaxama babban dan canji a garin
na legas nan dai aka kai masa amaryar sa..

Dare yaxama safiya,safiya taxama yamma,yamma taxama dare,hakik’a Allah mabuwayi ne
gagara misali,a haka dai bayan wasu shidewar shekaru ‘Dr Ibrahim Khaleel Mai Mota’ ya zama
babban mutum mai mata hudu ta hudun ce ma ba’afi shekaru 5 da auren ta ba.

Ya tara iyali,sai dai duk mata ne Allah bai bashi namiji ba,yaso hakan amma Allah be yadda
ba,domin dadin karin auren sama duk dan hakane,sai dai kash amarya na kamuwa da juna biyu
lokacin haihuwarta nayi ta juye masa yan biyu duk mata,to abun dai sai godiar rabbil izzati
domin shidin ma mallakin komai ne.
Hajia Aysaa itace matar sa tafar ko
inji hausawa suka ce ta ladan noma Tanada yara uku,da cikon na hudu a cikin ta.Taso ta cire
cikin,domin aganin ta,ta manyan ta da kara haihuwa,tana yi ya'yanta nayi,Ina xata kai
kunya?!acewar ta.Dr khaleel ya kwararo rantsuwa ya dire,tare da doriyar idan tai kuskuren cire
masa ciki,wallahi tallahi sai ya mugun sab'a mata.Haka ta dauki hak’uri ba wai dan tana so ba,
ba’asan mai zata haifa ba Allah ne kadai yabarwa kansa sani.

Safa da marwa yan biyu ne ta haife su wanda har sunyi aure,safa na lagos tana aure,Marwa
kuma tana Manchester.Sai Bilkisu,wadda taci sunan mahaifiyar sa ake kiran ta da Islam da
kuma dan baba,da ake tsumayin haife shi/ta...!

Sai matar sa ta biyu,wato Hajia Karimatu y’ar kano,ce cikin y’ar unguwar yakasai, tanada yara
uku itama.Khadija,Sajeedah da kuma auta Hafsat data ci sunan kanwar sa hansa’u,

Duk sunyi aure bada jimawa ba suna zaune a Abujan,Hafsat ce kawai batai ba,sa’ar Islam ce,
sai dai Islam ta girme mata da shekara d’aya,amma ajinsu d’aya..

Sai ta ukun Yafendo,ba fulatana ce y’ar yola, tanada yara uku itama... Hissah, Nusrah da kuma
auta Hidaya..Hissah tayi aure Nusrah kuma tana law sch amma an kusa yin auren.

Sai ta hudun amarya ce y’ar kasar chad Helwa nawarma, ya aureta ne ko Allah xai cika masa
burin sa na ‘ya’ya maza, sai dai kash Allah bai yadda ba,domin tana samun ciki akai scanning
yan biyu ne,doki awajen dr khaleel ba’a magana sai dai me?! Yan biyu zankad’a zankad’a mata
ta juye aka sanya musu Afrah da Arfah.Abun dai sai sam barka kawai ga mai hankali.
Rashin wannan buri nashi na samun yara maza yasanya dr khaleel daukar babban mataki na
‘ya’yan sa sai sunyi zurfaffen karatu both arabi da boko domin bature yace ‘what a man can do
a woman can do better’...

Kaf yaran sa banda yan biyu ‘kananan, da su Islam dake babban ajin sakandire na d’aya gaba
d’aya sauran daga doctors, sai lawyers da bankers..
Wannan kenan..!

*****

*B* *N* *A*
(BRITISH NIGERIAN ACADEMY)

*Elizabeth Arden’s hostel*

Zaune Islam take,hannun ta rike da littafin chimamanda mai suna,’purple hibiscus’........!


Ba kullum zan samu yin posting ba pls.Ayimun uzuri naso sai dana gama project da nakeyi,na
fara littafin☹mistakenly hannu na ya danna Page d’aya xuwa grp dinasanadiyyar haka ya
sanya ruguntsumin dole na dinga wantsalo muku shi� Kanwataa Rano kece sila kinci
bashi


_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...*


*NA*


*©NANA HAFSAAT*
*(MISS XOXO)*


*®HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*SHAFI NA HUDU (4) *


*Z*aune Haj Aysaa take a parlorn ta, dake d’aya daga cikin duplex’s apartments dinnan guda
bakwai, cikin nan nata ya k’ara k’asa alamun haihuwa tazo kenan, lokaci xuwa lokaci takan
furta,

“Ya Allah ka sauqaqa mana lamuran mu, Allah ka kare mu da kariyar ka, kayi mana katangar
k’arfe daga sharrin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login