Showing 27001 words to 30000 words out of 94870 words
Chapter 10 - Umarnin Iyaye Book Complete By tyetyelorh.txt
ya shigo
Ya gaidashi ya amsa sannan ya mika mai kayan da yayi mai ordering ya amsa yamai godiya fuskanshi babu yabo ba fassala
Daddy ya lura da haka dan haka seya sama wuri kusa dashi ya zauna ya dafashi yace ya dai lafiya
Adeel yayi murmushin karfin hali yace lafiya Daddy
Idande akwai matsala ka gayan min
Yace babu komai
Toh shikenan ya mike ya ringa sa mai Albarka sannan yace mai ya kamata ya shirya yanxin
Yace toh ya mike shi kuma Daddy ya fita
Ya kalla mirror dinshi dake manne a bango kawai seya daga hannun ya laushe mirror ji kake _tusss_ ya tarwatse
Zuciyanshi wani tafasa yakeyi ya kasa gane dalili dan haka ya kunnan kira'a kawai yahau kan gado
Ko minti goma ba'ayi ba ya dauke da bacci me dadi wanda ya dade beyi irinshi bah
Hankali kwance be tashi ba se wurin 12 shima Mami taji shirun yayi yawa ne shiyasa ta bishi tana shiga ta tarar dashi yana kwance ta mugun jin tausayinshi taga yayi wani mugun rama
Ta tada shi yana tashi ya mike ya zauna tace Adeel zan tambayeka wani abu kuma inason ka fadan min gaskiya
Toh Mimi inajinki
Ka fadan min gaskiya idan bakason auren nan jifa yadda ka rame ka gayan min idan kanaso idan kuma bakaso a fasa duk ka gama lalacewa haka kawai
Yace Mami ba haka bane banda lafiyane jiya da zazzabi na kwana kuma kuda banson auren dole na yarda tunda biyayya zanyi maku kuma yanxin idan nace banso ae be kamata a fasa ba tunda an rigada an tara mutane is already too late
Mami tana kallonshi duk tausayinshi ya rufeshi yadda yake maganan nan bema karasa ba ta mike ta fita tana hawaye
Shi kuma kallonta kawai yayi
Sannan ya kalla agogo ya mike ya shiga toilet dan yayi wanka
💋💋💋
Ameenah ce daga ita se towel ta fito daga wanka tasa Safieyarh a gaba tana rokanta dan taje ta amso mata cake dinta
Ke you are disturbing me ina tunanin prince charming dina
Ameenah tace habah my cute little in-law dan Allah kije tki amso min mana zan amsan maki mota kije dashi
Am still not going meyasa ke bazaki bah and kinsan wani abu yau babu tym din wani celebrating birthday ki
Ji tayi kawai gabanta yayi wani mugun fadi meyasa kikace haka
Safieyarh ta mike zaune tace yau idan an gana daurin aure za'ayi yinin biki sannan ayi dinner ana gamawa kuma a kaiki gidanki sede idan keda mijinki zakiyi celebrating
Tace why not after all his my husband so Dan Allah kije ki amso min
Haka ta ringa lallamata hadda guntun hawayenta sannan ta yarda tace zata
Ameenah ta ruki Auntie Aysha ta ara mata key din motanta
Tace amma fa kuyi sauri dan daddy Meemah yana hanyan banson yaga ana min yawo da mota
Ta amsa key din sannan ta shirya ta fita tana zuwa gun motan seta hango Hakeem ae se jikinta ya fara rawa tana kukarin sa key din amma ta kasa
Shi kuma daya ganta seya tsaya yana kallonta a zuciyanshi kuma cewa yakeyi Allah ka bani daman gayan mata feelings dina ko yayane
Tayi tayi tasa key din ta kasa seya karaso yace may i help
Ko kallonshi batayi bah tace No thanks
Seya kai hannunshi gun key din yana son ya amsa key din seya shafa mata hannun by mistake
A tare suka cire hannun da sauri dan se yayi kaman sun taba abu me shocking
Ya durkusa ya dauko key din ya bude motan sannan yaja kofan motan yace mata bismillah
Ta kasa ko motsawa ne jinta se rawa yakeyi daya gane hakan seya ja hannunta yakaita dayan sit din ya bude mata ta shiga ba musu
Seya zagaya ya shiga ya tada motan suka fita daga layin yace ina zaki
Ji tayi kawai hawaye ya fara zubu mata babu dalili muryanta na rawa tace _lawiza cake store_
Ya juyo da sauri ya kalleta yaga tana hawaye seya yi packing ya kalleta
yace _dan Allah ki dena kuka am so sorry for ignoring you wlh i have my reasons i didnt do it to hurt you_ a hankali yake magana
Tace ban damo da rayuwanka bah Auntie Aysha tace nayi sauri so plx take me to _lawiza cake store_ or get out so dat i can drive myself ita bata ma san sanda ta fada haka bah
Hakeem yace safieyarh i really am so sryyy wlh i missed you so mch-
Why do you keep saying you are sryy w-
Bata karasa bah yayi sauri ya kasteta da cewa
_Because i love you_
Tayi sauri ta dago idonta ta kalleshi
Shi kuma yayi shiru can seya cigaba
_Yes i luv you ban taba sanin ina sonki ba se ranan da naga kina chatting da saurayinki jamal i have never knew i had feelings for se a ranan a ranan ne naji wani abu da ban taba jinshi bah you are d first girl i have ever falling in luv with_ kafin ya karasa maganan da yakeyi tayi sauri ta bude kofan motan seta shiga titi
A guje ya fito ya bi bayanta yana kiran sunanta
kawai seta tara keke napep ta shige kafin ya karaso tace ma me napep din dan Allah malam tafi ba musu ya tada napep din suka fara tafiya
tana ta kuka a cikin napep din batasan dalilin dayasa ta fita daga miotan bah kuma itama tasan tanada feelings akanshi
Da sauri ya kuma cikin motan ya fara binso suna isa gida yaga ta fito daga napep din tayi cikin gida a guje
Shima ya fito da sauri amma seda ya tsaya ya biya mutumin kudinshi ko changin be tsaya amsa ba ya bi bayanta
Tana shiga ta tarar dasu Ameenah suna zaune a parlo suna hira a guje ta shige dakin tasa key dan tasan yana binta
Da sauri suma suka tashi suka bi bayanta dan sunga tana kuka
Ameenah tace Safieyarh meyafaru bude kofan ki gayan min kinji se kawai sukaga Hakeem shima ya shigo yace ina safieyarh
Ameerah tace wai meya faru ne
Tana ina plz
Tana cikin daki meya faru da ita
Seda yayi ajiyan zuciya sannan ya fadan masu abunda ya faru
Fatye ta tuntsure da dariya duk suka ringa masu dariya
Abun ya kular dashi yace toh me haka kun tambayeni abu na gayan maku kuma kuna min dariya mtsewwwww seya fita
Haka suka ringa dariya
Ita kuwa safieeyarh phone dinta ta dauka tayi dialing number Adeel seta shiga closet din dakin
Ta gefan Adeel kowa ya fito daga wanka yasa tv a gaba kawai yana kalla amma a kashe tv yake kawai tunanin duniya yake se phone dinshi tayi ringing beyi niyan dauka bah
Seda ya kusan katewa sannan ya dauka wayan yana ganin _baby sis_ seya daga
Yace baby- be karasa ba yajita tana kuka
A rude yace meyafaru
Tace yaya Adeel
Na'am meya faru
Yaya Hakeem ne seta kara rushewa da kuka
Yace baby sis kiyi hakuri gayan min abunda ya faru
Yaya Hakeem ne wai yana sona
Kawai seya fashe da dariya, dariyan daya dade beyi irinta bah
Seta kara karfin kukan
Yace yahakuri ki dena kuka gayan min abunda yace maki
haka ta kwashe duk abunda ya faru ta gayan
Yace toh ke do you have feelings for him
Tayi shiru batayi magana bah
Yace trust me and tell me
A hankali tace _probably_
Yayi murmuahi yace toh meyasa kika fita daga motan
Ta sake wani kukan tace i don't know
Toh ya isa haka haka ya ringa kwantar mata da hankali har tayi shiru ta dena kuka sannan ta kashe wayan yana mata dariya ita kuma tana kashe call din ta fito daga dakin
Ita kuma Ameenah tayita rokan ummitarh ta amso mata cake din ta mike taje ta amso mata
data dawo sukaga cake din ya hadu ba'a magana
💋💋💋
[20:48, 2/4/2017] Tyetyelorh-❣: Adeel ne a closet dinshi yasa kayan da daddy ya kawo mashi farar shadda ne yana wani sheki yana cikin combing gashinshi Mommy ta shigo da turare a hannuta ta kalleshi tace ango kasha amshi yayi mata murmushi kawai
Ta dauka holanshi tasa mai yayi masifan kyau fararen kayan nan ya haskashi yasa black shoes mommy ta fesa mai turaren se wani kyali yakeyi
Can se Zaid da fai'z suka shigo dakin suka durkusa suka gaida Mommy ta amsa da fara'a sosai sannan ta fita
Suka shiga mai tsiya ango kasha amshi kaga kyan da kayi kowa
Phone dinshi yayi ringing yana dubawa Daddy ne da sauri ya daga yace mai su fito su tun dazin suna gun daurin auren dayake a _sultan bello_ za'a dauka
Yace toh gamunan
Suka fito dukkansu suka shiga wata farar _ford_ fai'z ne ke driving shi kuma Zaid yana dayan sit din dan haka Adeel ne kadai a baya suka kama hanya
Hakeem kowa da kyar Mami ta lallameshi yaje gun daurin auren dan ya gayan mata duk abunda ya faru
Ta ringa kwantar mai da hankali sannan ya shirya cikin blue shadda ta haskashi sosai shida Ahmed suka tafi gun daurin auren
📸
_ TYETYELORH_
[15:42, 5/6/2017] Rrspectable: [19:11, 2/15/2017] Tyetyelorh-❣: 💋💋💋 _UMARNIN IYAYE_💋💋💋
_WRITTEN BY:_
_TYETYELORH_
_EDITED BY:_
_AMEENATOU_
💋💋💋
1⃣0⃣0⃣ ↗ 1⃣0⃣5⃣
Ta cigaba da kukanta ita abunda ke sata kuka shine wai kaman ba yar gata bah za'a kaita gidan mijinta babu kowa daga ita se shi
Seta sake fashewa da kuka
Shi kuma Adeel ta gefe yake kallonta babu daman yayi mata magana
A haka har suka isa Hotel din ya shiga yayi packing ya fita shi kadai ya shiga ciki dan yayi masu booking daki guda biyu ya barta ita daya a cikin motan
Yana shiga gun receptionist suka gaisa sannan yayi mata magana yanason daki biyu
"Am so srry sir but daki daya kawai ya rage babu kowa"
Ya dafe kanshi sannan ya kalla agogan hannunshi yaga 12 hartayi babu yadda ya iya dan haka ya biya kudin ya amsa key din sannan ya fita
Yana zuwa gun motan trunk din ya bude ya ciro kayansu ya kalleta ta waje har yanxin kanta a kasa tana kuka dan haka seya je ya ajeye kayan nasu a dakin ya dawo ya bude sit dinda take still bata dago bah dan haka seya kama hannunta a hankali a lokacin ne ta dago ta kalleshi
Be kalla fuskanta bah ya jawo hannun nata ya fito da ita daga motan haka ta fito ba musu
Yana fito da ita ya kulle motan kana suka shiga ciki hannunshi yana rike da nata.
Su safieyarh kowa sun kasa kwantawa se kuka sukeyi daga bayade Ameerah ta dauka phone dinta ta kira number Auntie Aysha dan tasan ita kadai ce zata magance masu wannan abun
Auntie Ayshevtayi nisa a bacci tana makale da mijinta kaman mafarki se taji phone dinta yana ringing ta bude ido taga yana hanske akan side drawer dan haka seta dauka taga Ameerah
Se gabanta ya fadi Allah sa lafiya tace sannan ta daga"Hello"
Cikin kuka tace "Hello Auntie kinsan meyafaru"
Subhanallah meyafaru meyasa kike kuka
Auntie wai a cikin daren nan se Abbah suka sa Ameenah da Adeel a gaba wai se sun tafi
Ta mike zaune tace yanxin suna ina sun tafi Abujan ne a cikin daren nan
Aa tun dazin suks tafi sunce wai dole se sun kama hotel a kaduna sannan da sassafe su kama hanyan Abujan ta gama tana kuka
Ya isa haka ae kinsan abunda baze taba yuwuwa kenan bah yanxin zan kira number Adeel zan gayan mai karsu tafi da wuri da safe duk zamu tafi hotel din yadda aka saba yima Amarya haka zamuyi ma Ameenah idan a cikinku akwai ne number daya daga cikin abokanshi ku kirasu tare zamu tafi dasu kai amarya kana ku gayan ma Hakeem gobe da safe karfe 8am
A lokacin ne Ameerah ta saukar da wani wawan ajiyan zuciya sannan tace toh shikenan ni inada number zaid zan kirashi da safen
Yawwa toh yanxin ku kwantar da hankalinku kuma karku gayan ma su Mami goben kawai kuyi masu sallama akan zaku tafi gida
To Auntie mungode kana sukayi sallama ta kashe wayan
Ta bama su safieyarh labarin abunda zasuyi a haka duk hankalinsu ya kwanta sannan kowa ya samu ya kwanta
Adeel kowa suna shiga dakin bakin gado ya nuna mata ta zauna har yanxin bata dago bah se wayanshi ya fara ringing yana dubawa yaga Auntie Aysha
Da mamaki ya daga yayi sallama kana ya gaidata
Bayan ta amsa take cemai goben karku tafi zamuzo hotel din dan tare zamu tafi Abujan
Yace toh ba komai
Sannan ta tambayeshi wane hotel ne ya gayan mata kana sukayi sallama
Ya maida wayan aljihu tareda kallon Ameenah ko motsawa batayi bah
Ki kwanta mana
Ba musu ta juya ta kwanta tareda juya mai baya shi kuma ya cire rigan jikinshi dagashi se vest da wandon shaddan nashi ya kashe wutan
Da taji ya kashe wutan koma taji shiru se gabanta ya fara fadi dan gabadaya ta aza gadon ze hau
Shi kuma couch din dakin ya hau ya kwanta yayi addu'a ya tufa
Ita kuma tafi minti goma da kwanciya amma se juyi takeyi ta kasa bacci
Shima idonshi biyu dan yana jinta
Ta sauko daga kan gadon a hankali dan tana son ta dauko phone dinta ne daga jakanta ta shiga tayi alwala se lalube lalube takeyi amma bata tabo bah dan batama san inda ya ajiye bah
Ta mike dan ta kunna wuta se ware hannunta takeyi can seta tabo hannun couch din da Adeel ke kwance akai
Seta shafa ta tabbatar da karshen couch din kenan seta sake ta tafi da karfinta zata kunna wutan
Se ji tayi kafanta ya bugu da couch din seta fada kan Adeel tayi sauri ta rike bakinta
Ashe shima idonshi biyu yanajin duk abunda takeyi
Se taji numfashi a fuskanta hakan ya tabbatar mata da tana gun fuskanahi ne a hankali ta mike ta cigaba da ta wulla wullan hannunta a iska
Shi kuma dayaji ta mike seya saki wata murmushi
Seta kai hannunta gun couch din dan ta aza ta wuce tana shafawa setayi saurin cire hannunta se kuma tayi murmushi dan cikinshi ta shafa
Da sauri ta matsa jefe ta taji babu couch din a gun dan haka seta mikar da hannunta dan ta kunna wuta ae kowa ta tabo se haske ya mamaye dakin Adeel ta fara kalla se kuma ta dauke kanta ta fara waige waigen inda zataga handbag dinta can seta hangosu gefan fridge
Shi Adeel yana cikin murmushin shi se ji yayi ta tabo mashi packs kawai waji zirrrrr yaji a lokaci daya
Ta kama hanyan gun fridge din da sauri ta bude seta hango _Nutella_ a ciki da sauri ta ciro tace thank god ta kalla saman fridge din taga spoon ta dauka shima ta kulle fridge din ta mike a bakin gadon da zauna ta bude ta ringa ci kaman tuwo
Idonshi ya bude guda daya a hankali dan yaga me takeyi yana kallonta seya girgiza kai ya juya mata baya
Taci taci seda tayi rabin choculate din nan sannan ta mike ta maida cikin fridge din ta kalla cikinta daga tumbi be fito bah setayi ajiyan zuciya ta bude handbag dinta ta ciro tablet dinta da phone sannan ta bude akwatin ta ciro night wear dinta riga da wando ta kulleshima kana ta mike ta ajiye tablet din da phone din bakin gado ta wuce toilet ta changa kayan tasa night wear dinta ta dauro da awala ta fito da rigan dake jikinta a hannunta ta ajiye akan akwatin ta yafa veil dinda ke jikinta da ta sama sallaya ta fara salloli ta ringa nafila
Ya juyo ya kalleta se yaji ta burgeshi daman duk haukan yarinyan nan tana sallah
Shima seya mike dan yafi hour a wance ya kasa bacci ya shiga toilet yayi alwala ya hango sallaya ya dauka ya shinfida shima dan gaba da ita ya ringa sallah shima din
Tana ganinshi ya shiga toilet se gabanta ya fadi daman idonshi biyu seta fara tunani kala kala dan haka ta sallame sallaln ta kabbara wani
Se wuraren 3 ta gama sallah shi kuma yanatayi dan shi yanason ya hada hadda asubah ne
Ta mike ta cire veil din ta haye gado tareda kunna wayanta tanata danna danne daga bayade tayi addu'a ta kwanta wani bacci me hauyi ya dauketa
Shi kuma seda akayi asubah yayi nashi kana ya kashe wuta shima ya kwanta a couch shima nan take bacci yayi awun gaba dashi
Basu suka tashi bah se 10 shima Ameenah ce ta fara tashi tayi sallah sannan ta ja akwatinta zuwa toilet tayi wanka a ciki ta shafa mai sannan ta saka duguwan riga baka kana ta fito ta shafa powder da lipstick ta fesa turare ta kuma kan gado seta daga kai ta kalla Adeel fuskanshi yana kallo ta
Kawai kallonshi takeyi tana tunani barkate wanda ita kanta bazatace ga abunda take tunani bah
Can seta ja tsaki "mstewww"
Ta kwanta tareda rufe idonta
Toh tsakinda ya tada Adeel kenan ya bude manyan idonshi a hankali tareda lashe lips dinshi ya mike yayi mike tareda salati ya mike ya shiga toilet yayi wanka ya fito dagashi se towel da kuma kayanda ya cire a hannunshi ya ajiye akan couch din a dauko akwatinshi ya ciro wata bakar kaftan da wandonta ya ajiye seya shafa mai yana cikin combing gashin shi ita kuma ta juyo dan daman ba bacci takeyi bah
Shi kuma tsammaninshi bacci takeyi shiyasa be saka kayanshi bah a toilet din
Tana ganinshi seta kwalla ihu tareda sa hannun a ido ta rufe idonta dasu
Hannunshi yana kan gashinshi ya juyo da sauri yace meyafaru!!!
You!
Me what
Seta mike da sauri still hannunta na fuskanta ta kama hanyan fita daga dakin gabadaya
Yace ina zaki
Bata kulashi bah ta cigaba da tafiya ta tsaya dan ta bude door din dan anyi locking