Showing 93001 words to 94870 words out of 94870 words

Chapter 32 - Umarnin Iyaye Book Complete By tyetyelorh.txt

๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹
[01:59, 4/8/2017] 1D-Tyetyelorh-โฃ: A yanxin anata shirye-shiryen bikin su Safieyarh an gama komai sauran kwana biyu ayi daurin aure su Ameenah suka iso suma anyi biki anyi shagali anyi barin kudi sosai
Su Hakeem an zama ango se gyaran babban riga ake baki har kunne

Yayi gidansu hadadde a Unguwan rimi gida ya hadu harda dakin yara akayi tun kafin ayi daurin auren
Anyi biki lafiya kowa ya kuma gida lafiya An kai Amarya
Ango ya amgwance abinshi

_2weeks later_
Ameenah ta dawo daga school ta shiga gida kenan tayi parking seta tura kofa ta ganshi a bude bata kawo komai ba seta shiga ciki
Tana shiga taji an kamota tareda toshe mata baki aka daura mata wuka a wuya hawaye ta farayi kawai tanata addu'oi a zuciya kala-kala
Sake mata baki yayi yace ina safe yake
Batayi magana ba seta kai hannunta a hanakli gun Alarm din gida ta danna

Adeel yana zaune a office daman Alarm din ya hada da phone dinshi ne ana dannawa ze gani a wayanshi
Mekewa yayi ya fito ya kamo hanyan gida se gudu yake a titi dan yasan bazata danna da wasa ba

Shiru tayi batace komai ba
"Magana nake maki ina safe din yake idan bakiyi magana ba zan yanka maki wuya"
Kuka ta saki "dan Allah kayi hakuri ciki gareni fah"
Shiru yayi can seya daura wukan akan cikin ta kawai seya yanka kan cikin ihu ta saki se kuma tayi salati sakinta yayi ya fita daga gidan da sauri
Jiri ne ya fara daukanta kawai seta sume agun

Adeel yana isowa gidan ya shiga a guje a waje ma yayi parking a bakin kofan ya tarar da ita kama a mace ga jini a jikin riganta jikinshi rawa kawai yakeyi
Kinki manta yayi ya fito da ita a mota ya sakata suka kama hanyan asibiti se gudu yake ji yake kaman ze rasata
Suna isa emergency ward aka shiga da ita shi kuma se zazzaga wa yakeyi ya kasa sukuni tunani yake idan yaga wanda ta mata wannan abun seya kasheshi

Can wata doctor ta fito ta sameshi
"Sir ka kwanta da hankalinka lafiyanta kalaw sannan babu abunda ya sama baby ba wani yankanta yayi sosai amma she's gonna be okey zaka iya shiga ka ganta"
"Okey thank you" seya shige ya tarar da ita yana kwance se hawaye takeyi
Karasawa yayi da sauri ya rike mata hannun
"Meyafaru kike kuka its okey kinji ki dena kuka"
"Me suka ce maka we lost the baby right"
"No stop saying that sunce babu abunda ya sameta yankan be kai gunta ba. Ina ke maki ciwo?"
"Ba ko ina" tana magana tana share hawaye
"Zak iya gane waye ya maki wannan abun?"
"Aa ni kawai ka barshi da Allah kudi yazo nema ba wani abu ba kuma ban gayan mai inda yake ba dan nasan idan na gayan mashi definately seya min wani abu baze barni haka ba"
Share mata hawaye ya farayi
Ta fara basu labarin abunda ya faru shida doctor din
Doctor khadija tace" amma kinyi kukari da kika ce mai kinada ciki da abunda ze maki zefi haka"

Basu kwana ba aka sallamesu suna zuwa gida suka gane hacking kofan yayi se ya bude dan haka a ranan ya kira aka chanja abun ya zama seda thumprint dinka zaka iya shiga gidan and more security.
*****

Mufeedarh kowa wata rana su Castro suka kamata suka mata dan karan duk taci na jaki duk sun fasa mata jiki haka ta dawo gida duk tayi nadaman abunda tayi

Afra kowa yanzin ta hadu da wani saurayi ba laifi yanada kyau sannan doctor ne suna shiri sosai har yake gayan mata shi yana sonta kuma da aure
Kuka ta shigayi take bashi labarin abunda ya faru da ita yace shi babu komai dan Allah yakesonta
Harya kai gaisuwanta an saka rana in 5months time

A gidansu Ameenah kowa an ware daki daya an shirya kayan baby komai da komai tunda na tabbatar masu mace ce

_Some months later_
Yau satin Ameenah daya kenan da dawowa gida dan ta shiga watan haihuwanta shima Adeel ya biyota ya dauka hutu agun aikinsu

Yan biyu yanxin suna koyan rarrafe iftihar itama haka sun zama kaman yan uku

Wani dare Ameenah ta kasa bacci a dakinta se fama shiga toilet take ta shiga yafi so biyar maranta ya wani rike
Wani ihu ta saki Mami dake dakinta tana bacci a furgice ta tashi ta fito ta shiga dakinta a kasa ta tarar da ita tanata juyi
"Ameenah lafiya"
"Mami marana ze cire"

Ina zuwa barin kira Adeel
Daman a dakin Hakeem yake kwana shi beson yayi nisa da matanshi

Knocking daya tayi ya bude kofan ta gayan mai Ameenah haihuwa yazo dan haka ya haura sama daukota yayi cak har cikin mota ita kuma Mami ta dauko akwatinsu bayan ta fadan ma Abbah

Mami tana baya itada Ameenah se nishi take
Mami ta hanata kuka
"Mami dan Allah nayi kuka kadan"
"Aa Ameenah ki daure kinji"
"Ya Adeel tsaya zanyi amai"(my hawwaty๐Ÿ˜‚)
"Aa cigaba da tafiya"
"Mami wlh mutuwa zanyi cikina ze fashi. Mami ki yafe min abunda na maki"
"Ameenah bazaki mutu ba kinji ki daure"
"Wlh mutuwa zanyi. Mami ina ranan da kika nema turarenki kika rasa nace maki Ya Hakeem ne wlh nice dan Allah kiyafemin zan mutu"
Abun dariya ma yaba Mami
Adeel kowa duk a rude yake se tuki yakeyi

Suna isa emergency ward akayi da ita Adeel yana tare dan ita se sambatu take kala-kala gashi ta saka haihuwa har karfe ukun dare ana abu daya
Se doctor ya fito shida Adeel yake cemai bazata iya haihuwa da kanta ba dan west dinta is tiny dan haka Cs za'a mata
Nan da nan ya yarda dan yaga tana wahala sosai aka bashi wasu papers yayi signing sannan aka shiga da ita aka fara aiki kafin su tafi seda ta ruka gafaran Adeel wai tasan bazata fito da rai ba
Shima kuka yakeyi kaman mace Mami kallonsu kawai takeyi tana jin tausayinsu kuka sun bata dariya

Allura aka mata amma kafin ta fara bacci se surutai take kuma ta hadu da dan iskan likita ce mata yake kinga nan aljanna ne(Auntie na๐Ÿ˜‚) se iskanci yake mata itama dayake a bige take se biye mai take

_Some hours later_
Aka fito da ita it was a success an sama baby mace lafiyansu kalaw dukka da aka kawosu daki har a lokacin alluran be saketa ba Adeel yazo ya dauka baby har hawaye yakeji ji yake kaman a mafarki wai shine da babyshi yau addu'a ya ringa mata wani sonta yaji lokaci daya

Ameenah tace "ni wlh bazan saje ciki bah"
"Haba Ameenah ya zakice haka" Mami ce tayi magana tana rike da baby duk dadi ya lullubeta yau itace da jikanta a hannu
"Mami kadan fa ya rage na mutu har aljanna seda aka nuna min"
Dariya Mami ta saki itada Adeel dan sun lura ba cikin hayyacinta take ba
"Mami nifa family planing zanyi Ya Adeel ka yarda koh"
Daga mata kai kawai yayi
Se faman surutu take har bacci ya dauketa

Kwanasu biyar a asibitin tea kawai takesha babu wanda bezo ganin baby ba itama Safieyarh tazo da sabon cikinta
An cika dakin da suke ciki
Ana sallamansu kowa a gidan kullum a cike yake har ranan suna aka yanka raguna manya-manya
Adeel ya bata daman saka suna tunda yaga wahalan datasha
Ta saka mata _Fatyemah_ sunan yarinyan manzon Allah kuma sunan Mommy kenan Mami ce ta tayata zaban sunan amma ana ce mata _Inteesar_
Ba karamin dadi Adeel yaji ba dan shima sunan da yakeson sakawa kenan

Mommy kowa tayi murna itada Daddy mara adadin akwati biyu suka kawo ranan suna
A ranan da sukayi arba'in ba inda basuje yawon arba'in ba hadda gidan Safieyarh da Auntie da Afreen duk anje su Meemah an zama Auntie yanxin
Bayan one week suka koma Abujah
Ana jida yarinyan kaman kwai kullum cikin kara son junansu suke
Yanzin Ameenah itace Manager Adeel komai nashi yana hannunta idan sunada match ita ake kira sesu tafi dukkansu

_Some months later_
A lokacin anyi bikin Ummitarh sannan anyi na Afrah itama kowa yazo hadda dangin baba suma sunzo dan naa Afreen basu sani ba shiyasa basu zo ba
Itama a Abuja ta tare mijinta na matukar sonta
Inteesar kowa yanzin tanada 9months harta fara tafiya yarinyan sak Ameenah da iyayinta da kaudi sanda take yarinya amma ta dauko manyan idon Adeel da kuma rashin son magana duk ta debo nashi

A lokacin itama Safieyarh ta haihu ta haufa danta namiji an sa mashi _Ammar_ se rashinji kaman babanshi kaman copy shi akayi amma yaron kyakkyawa ne sosai ga gashi se farin jini.

_5 years later_

Yarane keta wasa a tsakar gidan
Ga yan biyu sunata wasa ga iftihar sannan ga _siyamarh_(yarinyan Afrah wanda take shekara biyu yanxin) sannan ga Ammar ya zama saurayi
Can gefe kuma Inteesar ce da Meenah suna zaune
Inteesar ta wani harda kafa da wayan papa ta tanata buga game ga karamin shades dinta a idonta sak Ameenah de
Yarinya ce kyakkyawa lips dinta kanana gata fara sol sannan siririya ga gashi kuma baki wuluk ga dan banzan kaudi ita ba komai takeci ba duk abu me hauyi toh bataci haka take

A parlon Abbah ne kowa ke ciki kowa da kowa hadda Alhaji dasu inna anata hira abun sha'awa kowa kanshi a hade
Adeel ne yaja Safieyarh waje ya bata key din mota sabowan mota ya sayan mata dayake yau birthday ta kiran Nissan ihu tayi ta rungumeshi dukda itama tanada motanta dan ranani daurin aurensu Abbah ya bata sabuwa
Murna take sosai shiga tayi tana nuna ma kowa se tayata murna akeyi

Hakeem kowa har yanxin ba'a girma ba yana gefan Ameenah yana tsokana
A yanxin Ameerah,Fatye da Ummitarh kowa ya haihu abinshi

Ameenah ce a dakinta itada Adeel suna kwance se soyayya sukeyi abinsu
"I love you babe"
"I love you my angle i can't wait naga kin kara haihuwa"
"Mee too in haifa twins"
Dariya ya saki bayan kince famliy planing zakiri"
"Aa ni yanxin inason yara inaga sunata yawo a gida suna wasa"
"Nima haka Allah kawo mana nagari"
"Ameen"
Se suka fara kissing juna
Inteesar ta fara knocking da sauri ta janye jokinta
"Come in darling"
Shigowa tayi
"Papa i think am gonna be sick" tana magana tana hawowa kan gadon riketa yayi
"Why darling"
"Cus the house is so noicy and my head is paining me"
"Awwn sorry darling kwanta ki huta kinji"
Ameenah ta fadi tana sakata a tsakiyansu
Suka kwanta suna rungume da juna

_And they live happily ever after_

*ALHAMDULILLAH*

Anan ne na kawo karshen wannan novel nawa me suna UMARININ IYAYE

Godiya ta musamman ga LAWIZAS i love you guys so much you guys are my life so this whole book is dedicated you and olso Ameenah Uthman you are just like a lawiza to me
Love you babe

Ameerah bawa babe i missed you so much can't wait ki dawo kd seta san kin iso love you so much

Tyetyelorh novelx thanks guyx for your support i love you
And Tyetyelorh novels 2 you guyx are very special to me i heart y'all

Allah ina godiya yadda na fara novel dinnana lafiya na gamashi lafiya
Allah idan nayi wani kuskure ka yafe min

This my secound novel amma shine farkon dana gama

Sekun jina a next novel dina idan na gama Zulaihatou amma sena huta tukun nan

Last page din nan har hawaye seda ya sakani aradu nagode ma Allah daya bani ikon gamawa lafiya

Tyetyelorh blogspot.com

IG.Tyetyelorh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login