Showing 39001 words to 42000 words out of 94870 words

Chapter 14 - Umarnin Iyaye Book Complete By tyetyelorh.txt

kular dashi daman yana ciki da ita data watsa mai abu a jiki.....
Tana shiga ta hada da system dinta tayi kallonta hankali kwance
[truncated by WhatsApp]
[15:42, 5/6/2017] Rrspectable: [19:46, 2/25/2017] Tyetyelorh-❣: 💋💋💋 _UMARNIN IYAYE_💋💋💋

_WRITTEN BY:_
_TYETYELORH_

_EDITED BY:_
_AMEENATOU_


_dix page is for you *Abubakar Abdullahi gabiya kawo* May your soul rest in perfect peace Allah ya jikanka Allah kai haske kabarinka Allah ba iyalinka hakurin rashinka we are all gonna miss you most expecially *DITV* we are gonna miss your funny stuff Allah sa ka huta_
_Ameen_

💋💋💋

*112*

_Washe gari_

Tun 7am ta tashi amma tana kan gado se juye juye takeyi dan maranta ke mata wani azaban ciwo se wani nishin azaba takeyi abun tausayi
Adeel tun 9am ya fito a shirye dayaga be ganta a parlo ba seya hada tea yasha
Wuraren 11 ya mike ze shiga daki yana latsa waya se yaji nunfashi sama sama dan haka seya natse ya kasa kunnashi ya tabbatar da abunda yaji dan haka se yayi dakin Ameenah da sauri
Ya tarar da ita se fama juyi takeyi kana gado da hannunta akan maranta ya karasa da sauri ya dagota yana tambayanta meke damunta ta kasa mai magana nuna mai maranta kawai takeyi hawaye na rubuwa daga idonta

Yana dagata yace bari muje hospital
Tace noh ze dena da kanshi tana magana da kyar kaje kawai

Yayi yayi ya kaita hospital amma taki yarda dan haka ya saketa ya kama hanyan fitowa
Ita kuma ta mike tsaye da kyar tana rike da maranta zata shiga toilet kawai ji kake dumm ta zube a kasa kaman mattaciya
A guje ya dawo ya kinki meta yayi waje da ita se kuma ya dawo ya dauka keys dinshi ya sake fita yana sata a mota se ya kara dawowa cikin dakin da sauri ya shiga closet dinta ya duba bega hijab ba dan daga ita se bum short da vist
kawai seya jawo wani jallabiya baka ya fito koh kulle gidan beyiba ya fuzga mota se hospital suna isa emergency akayi da ita shi kuma yana lobby se zirga zirga yakeyi
Can se yayi tsaki ya zauna yace meyasa na dama kaina akan wannan yarinyan se kuma ya sake mikewa ya ciro wayanshi seya fasa ya maida aljihu

Sega doctor ya fito ya mikama Adeel hannu suka gaisa yace kai mijinta ne??
Dan iskanci irin na Adeel se cewa yayi a'a ni elder brother tane whats wrong with her??

Nothing important da zan sama ne inyi magana da mijinta
Ya dake yace tou ae batayi aure bah
Yayi shiru can yace toh muje office
Haka suka tafi office dinshi shi yana gaba while Adeel na biye dashi a baya

Suna shiga ya nuna mai wuri ya zauna se ya fara magana
"Ba wani abu ke damunta bah kawai period dinta ne yazo"
Se Adeel ya yamutse fuska yace idan de akan wannan ne ka rike kayanka ya mike

Doctor ya dawo dashi yace "shawara zan baku tunda kace kai yayanta ne ayi mata aure dan idanba aure aka mata ba duk month haka za'a ringa fama da ita and ever month zena worst ne"

Tou kawai yace ya mike ya shiga dakin da yaga an kaita ya bude kofa a hankali ya ganta akan gado she's still unconsious ya jawo kujera ya zauna a bakin gadon da phone dinshi yana danna-danne har kusan 30mins se ta bude ido a hankali tayi mika tareda salati

Yana jinta amma bema dago bah
Ta mike zaune ji tayi kanta yayi mata nayi tana dafe da kan setaga ana kara mata ruwa tayi tsaki dan ta tsana ta ganta a hospital amma duk wata setayi wannan suman
Ta fuzga alluran dake hannunta ta mike tsaye
a lokacin ne ya dago ya kalleta da mamaki harta mike ta kama hanyan fita se wani wawan jiri ya sake dibanta zata fadi kenan ya rekota ya ajiyeta a kan gadon

Ta amshe jikinta seta dafe kanta dan wani juyawa yakeyi
"Halan kanki ya fara tabuwa ne"
Seya kalla cinyanta ya mike ya dauko mata abayan daya dauko mata ya wulla mata

Wani wawan harara ta galla mai batayi magana bah tasaka
Sega doctor ya shigo ya kalleta yace ya akayi aka cire karin ruwan
Tace doc plx kayi discharging dina na tafi gida

Toh ki bari ruwan ya kara first se muyi discharging dinki dan bazaku kwana bah
Haka ta kuma aka maida mata ruwan seda ya kare doctor yayi discharging nata
Suna shiga mota tace wait taya nazo hospital dinnan daukoni kayi

Yace "God forbid ni zan daukeki janki na ringayi harseda mukazo gun mota
Ita kuma smiling tayi kawai
Suka tsaya a _Zufeey bakery_ suka saya snacks da drinks suka kama hanyan gida
Suna isa ta fito seta kasa bude kofan se cewa takeyi open sasame amma yake budewa ta kalla Adeel setayi guntun tsaki

Yana zuwa yace open sasaeme kawai seya bude
Tace wlh ban yarda bah nima se anyi registering voice dina dan nima ae gidana ne
Yace toh tsaya kiyi da kanki ya wuce ya barta ana

Ta bi bayanshi tace nifa ban yard-
Bata kai aya bah seji tayi amai yazo mata a guje ta shiga dakinta ta shiga toilet ta ringa amai
Adeel ya juya yaga bata bayanshi seya wuce dakinshi

Tana gamawa ta dawo daki ta zauna se wani zazzabi ya riketa lokacin wuraren karfe daya ta lallaba tayi wanka ta fito tasa riga wando ta kashe Ac dakin ta shiga bargo amma se karkarwan sanyi takeyi kaman tana cikin kankara dakyar ta mike ta kunna warmer dakin ta kuma kan gado still tana jin sanyi amma ya rago dakyar bacci ya dauketa tana bacci tana wani nishi kana ganinta kasan ba baccin gin dadi bane

Adeel yana zaune a daki har wuraran karfe biyu seya fito ya a zauna parlo ya dade amma beji motsinta ba kuma yaga ba'a taba snacks dinda ya ajiye bah dan haka seyayi tunanin koh jikinta ne dan haka seya mike yayi knocking kofanta a hankali amma shiru dan haka seya murda ya bude ya ganta akan gado ta nannade cikin bargo jikinta se rawa yakeyi ga wani nishi da takeyi

Da sauri ya karasa gunta yaga idonta a kulle alaman bacci takeyi ya taba tamperature ta jikinta zafi sosai kawai ya tsaya yana kallonta kode na tasheta ne ya tambaya kanshi

Kawai seya shiga toilet dinta ya debo ruwan zafi a karamin roba da karamin towel ya fito dashi se ya dauko kujeran mirror ta ya ajiye a bakin gado ya zauna akai ya shiga tsuma towel din cikin ruwan rabin ya matse kana ya daura mata akan goshi

Seda taja wani nishi yayi sauri ya cire se kuma ya maida haka ya ringa yi mata yanata sawa a goshinta har yaga ta dena rawan sanyi seya tsaya yana kallon lips dinta yanata kalla kawai se yakai hannunshi kai dan ya duba ko tasa lipstick ne dan pink din yayi yawa
Ya kalla hannun babu komai seya sake maidawa dan laushin yayi mai dadi
Seyaji tayi motsi yayi sauri ya cire hannun

Ya mike yaje ya zubar da ruwan ya dawo kan kujeran ya zauna ya dan dade a zaune seya daura kanshi jikin gado se bacci ya daukeshi.

_30 mins later_

Ta bude idonta ahankali seta kulle ta sake budewa setaga alaman mutun a kusa da ita ta sake kullewa da sauri ta bude ta murza idonta ta tabbatar mutun ne seta mike a hankali ta leka fuskan taga Adeel kawai ta tsaya tana kallon fuskanshi tace ba lefi fah ta kai kallonta zuwa lips dinshi se ta kai hannunta kai ta shafa kadan laushi tayi smiling ta kuma ta kwanta dan jikinta ya warware se bacci ya sake daukanta haka suka ringa bacci kaman ana gasan bacci seda aka kira sallan la'asar kaman akansu

Adeel ya fara tashi ya bude idonshi seya fara karo da fuskanta seji yayi yana sha'awan ya taba lips dinta again
No second thougt yakai bakinshi gun nata yayi pecking lips dinta kawai yayi murmushi ya mike ta maida kujeran junshi dan karta gane ya zauna a gun besan ta ganshi bah ya fita yana tunanin wannan shine frist peck dinshi a duniya


💋💋💋
[20:53, 2/25/2017] Tyetyelorh-❣: Yana fita dakinshi ya shiga yayi alwala kana ya tafi masallaci

Ita kowa se kiran sallah na biyu ta tashi tana tashi bata ganshi agun bah kawai batasan dalili ba seta shafa lips dinta ta girgiza kai ta shiga toilet ta gyara jikinta seta fito ta shiga kitchen se taga snacks dinda suka sayo ta dauka donut manya guda biyu tasa tayi warming dinsu ta fito ta zauna a parlo ta kunna tv tana cin donut din tana gama ci seji tayi still tana jin yunwa ta mike ta shiga store dan ta sama abunda zata dafa kawai seta debo shinkafa ta dauka ta gyara kwakwa ta hada coconut rice seta debo soyayan miya ta kara soyawa ta juye a kular ta kawo dining ta deba aya,kwakwa da dabino tayi blanding tasa ice a ciki ta juye a jug ta ajiye akan dining da cups dinshi

Ji tayi kawai she wants to pay him back for taking care of her dukda batasan abunda ya mata bah daya dumama mata jiki
Ta deba nata abincin ta zauna tana ci ta dade rabanda taci abinci me hauyi haka ta deba madaran data hada a cup ta ajiye a jefanta

Can segashi ya dawo ya shigo ya ganta tana cin abinci harze wuce seyace ya jikinki
Da sauki kawai tace

Yace Allah kara sauki a hankali ze shiga daki kenan tace ga launch fah daman yanaji da guntun yunwanshi yace Noh nakushi
Wait ke kikayi abincin

Ta daga kanta alaman yh
Toh meyasa kika hada dani
Tayi murmushi tace kawai
Seya fara tafiya tayi sauri tace thank you
Gabanshi ya fadi yace for what??

For taking care of me
Ya daga kanshi kawai ya gudu daki a zuciyanshi yace Allah sa batasan abunda na mata bah

Tana gama ci takai plate din kitchen taji cikinta ya cika damm
Seta dawo ta cigaba da kallonta
Shi kuma yana daki cikinshi har wani kara yakeyi dan yunwa daga bayade ya yanke hukuncin ya fito yaci ya mike ya fito daga dakin yazo ya dauka cup ya deba abunda ta hada yazo ya zauna a parlon shima yana sha
Ta kalleshi seta dauke kai
Kawai se wayanshi ya fara ringing yana dubawa se yaga Dddyshi ya daga da sallama ya gaidashi
Daddy yace ya iyali
Lafiya klwa yasu Mommy da safieyarh duk lafiyansu lau

Ina Ameenah take
Gatanan in bata ne
A bata mu gaisa
Toh yace ya mikama Ameenah wayan
Ta amsa dan taji yana cewa Daddy
Sallama ta farayi kana ta gaidashi

Ya amsa yace kuna lafiya
Lafiya kalw Daddy yasu safieyarh
Lafiya suke suna gaidake
Ina amsawa
Ba wani matsala koh Mamana
Tayi murmushi tacs babu

Be maki mugunta ??
Da sauri tace yanayi min Daddy
Se Adeel yayi sauri ya juyo
Tayi dariya tace baya min
Suka ringa hira ita kuma se shirme take mai tanata dariya daga baya sukayi sallama ta mikama Adeel

Adeel yace Daddy daman inason na kiraka muyi wata magana dakai
Toh ina jinka
Jiya ne manager na ya kirani wai in two weeks time inada wani game zanyi representing UNITED STATE

Ae Ameenah bata san sanda tayi ihu bah seta tushe bakinta tana dariya
Ya juyo yayi mata wani irin kallo

Toh shi kenan Allah yakaimu amma da iyalinka zaka koh
A toh bansani ba tukun nan

Ban gane baka sani bah da ita zaka
Toh daddy makaranta fa na saman mata addmission fa nxt week zata fara zuwa

Seta karayin wani ihun tana tsalle
Yayi sauri ya mike ya tafi daki
Daddy yace toh shikenan Allah bada sa'a sukayi sallama ya dawo parlo kafin yayi magana tace dagaske ka saman min addmission
Yace Nop dan kar naje dake ne kuma a gidan nan zan barki kide ghost

Ta murguda mai baki tace i don't believe in ghosts so babu wani abu waishi ghost a duniya
Lips dinta kawai yake kalla

Toh shikenan we shall see

Ta matso kusa dashi tace bt plxx ban sama bah da gaske
Yup kawai yace ya mike ta mike tana magana a hankali
Ya dawo ya rikota yace what do you say

Tayi shiru
Wlh idan baki gayan min ba koh Mmmmm
Da sauri tace wlh nima bansan me nace bah kawai magana nakeyi

Ya saketa ta wuce daki tana zuwa bakin kofan tace me halin mugaye kawai ta shige da sauri tareda sa keyy
Shi kuma abinci ya je ya deba ya zauna yana ci

Laptop dinta ta dauko ta hada video chat Ameerah,fatye,Ummitarh da safieyarh sunata hira can fatye tace ya jiki tace wlh da sauki
Tsaya ya akayi kikasan banida lafiya

Duk suka kwashe da dariya
Safieyarh tace ae duk Amarya batada lafiya balle ke ji yadda kika kara haske ji boobs dinki ta kare kirjinta tana dariya tace batason iskanci fah ta mike ta dauko jacket tasa

Ameerah tace ina kika baro mijin naki da daddaren nan
Yana dakin-
Bata karasa bah setaji ana knocking kofanta ta mike da laptop din a hannunta

Ameerah tace toh ya gaji da jiranki yazo amsan hakkinshi
Tayi mata dakuwa tareda ta bude kofan
Ya bude baki zeyi magana seyaji muryan mutane a laptop din dan haka seya amsa daga hannunta tana ja yana ja
Daga karshe ta sake mai yana juyo dashi yaga fuskokinsu su hudu
A tare duk suka toshe bakinsu dan suna ta mata tsiya wai sun kusan zuwa cin ragon suna safieyarh se dariya take masu

Duk suka gaidashi yayi murmushi ya amsa ya wuce da laptop din parlo tana binshi wai ya bata kayanta amma ya shareta
Ya zauna ya kalla safieyarh ta harareshi yayi murmushi yace meya faru kike harara na
Tace bansani bah
Yayi dariya yace am still not missing you
Tace who cares
Haka suka fara hira da kawayanta
Ameenah tanata kallonshi dan abun ya bata mamaki kaman ba Adeel din dabah ga miskilancin tsiya ga kuma girman kai

Yana basu labarin Ameenah bata iya girki bah wai ta dafa nama be dahu bah
Ta matso tace yausha ka taba cin naman dana dafa

Ranan da kikayi maccroni mana
Ta rike baki tace daman kaine ghost dinda ka sace min nama
Murmushi kawai yayi
Ta basu labarin tayi abinci ya sace mata nama suka ringa masu dariya
Ummitarh tace you guyx are so cute

Ta amshe laptop dinta zata shiga daki ya sake kwacewa yace kuje ku kwanta dare yayi ya kashe ya wuce da latop din dakinshi aguje ta bishi[truncated by WhatsApp]
[15:42, 5/6/2017] Rrspectable: [22:56, 2/28/2017] Tyetyelorh-❣: 💋💋💋 _UMARNIN IYAYE_💋💋💋


_WRITTEN BY_

_TYETYELORH_

_In dedication to my newest crush_ *ILY*💋

💋💋💋

*113*

Yana shiga yasa key dan haka ta juya tana kunkuni ta shiga dakinta

Haka rayuwansu ta cigaba da tafiya yau suyi fada gobe suyi magana
Se wata rana tana kwance a dakinta tana kallon tv amma ba kallo takeyi bah dan a kashe yake
Adeel ne ya shigo dan ya bata laptop dinta saboda ya gama binciken da ze mata yana ganinta haka a zuciyanshi yace today is my day seya fita dakinshi ya tafi ya dauko snake din ruba Hakeem ne ya bashi wedding gift ya fito yana wani murmushi me kara fito mai da kyanshi ga kuma wani dimple dinshi nan

Ya shigo dakin still tana kwance inda ya barta a hankali ya karasa gunta ya ajiye snake din a gun kafanta se yayi sauri ya fita.
Tana yin juyi setaji alaman abu ta duba kawai taga maciciji seta dauke nunfashinta ta kasa motsi kwata-kwata dan ta taba ji yadda akace idan maciji yahau jikin mutum tou kar a motsa dan motsin ne zesa ya sareka

Idonta ta damke haryanxin taki nunfashi se wani wawan rawa da jikikinta keyi tunaninta daya taya snake ya shigo mata daki kawai seta bude idon a hankali ta kalla snake din ta sake kalla kawai se tayi tsaki tayi wulli dashi ya fita daga dakin ta mike ta fito daga dakin dan ta gane snake dinta ne wanda ta taba franking yaya Hakeem dashi
Dakin Adeel ta nufa se kuma ta ganshi a parlo dan haka seta yo kanshi kana ganin fuskanta kasan yana tattare da masifa
Ta rike karamin west dinta ta tsaya a gabanshi shi kowa ko dagowa beyi bah
Kawai kuma seta juya ta koma dakinta ta yafa karamin veil dinta ta dauka phone dinta ta fito ta kama hanyan fita tayitayi ta bude kofan amma ta kasa se open sasame take cewa koma gashi bataga remote dinda aka ajiyeshi a gefe bah seta dawo parlon tace mai dan bude min kofa

Kaman baxe dago ba yace where too??
Tace am tired,
Kullum ina waje daya i recently gain 2ponds inason naje strolling ne tunfa dana zo gidan nan so biyu kawai na taba fita kuma dakai ne
Ta gama maganan tana murtike fuska

Ya mike yace toh muje tare
Hell noh,no way kawai in kama fita dakai tahb
Toh shikenan bazan bude bah
And anyway ni na daukeki ne kaman safieyarh sister na wanda na bah five full years

And ni kuma na daukeka kaman yaya Hakeem ne wanda dukda ya ban 5yrs i won't take sh*t frm him ta juya
Ae ko da sauri ya kafkota yace say sh*t one more time

Tayi shiru batayi magana bah ta fuzga hannunta tayi gaba shima ya biyota ya bude kofan ta fara masifa
"Ni wlh ban yarda bah yanzin kace zakayi tafiya and kofan bemasan ni bah haka zanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login