Showing 72001 words to 75000 words out of 94870 words
Chapter 25 - Umarnin Iyaye Book Complete By tyetyelorh.txt
gadonshi da wayanta a hannunta dan tun zuwansu Mama ta bata kayanta
While shi kuma yana kasa a kwance da wani novel a hannunshi _What to expect when you are expecting_
na Ameenah ne tun zuwansu ya sace mata tayi-tayi ya bata kayanta amma yaki shine ya fito dashi yana karantawa dakin shiru
Afreen ce ta shigo ta fuzga wayan Afra "Mama na kiranki kuma wlh naga fuskanta a daure"
"Nashiga uku Allah sa bata gane na saya sabon sim card bane"
"Hehe yau wata yarinya zataci gidansu " Hakeem ya fada yana dariyan mugunta shida Afreen
Punching kafadanshi tayi irin na wasa ta mike ta fita jikinta har rawa yakeyi dan duk rashin jinta Mama na gyara mata zama
Tana shiga dakin Mami ta ganta a zaune akan kujera
Murmushi Mama ta sake mata kafin ta karaso dakin
Wani wawan ajiyam zuciya tayi tunda taga fuska karasawa tayi gunta tace gani Mama
Nuna mata gefanta tayi zauna anan baby girl
Zama tayi
"Yawwa kinsan muna sonku keda sister ki bazamu so abunda ze cutar daku bah koh"
Daga mata kai tayi alaman ehh
"Toh barin tafi kan zancen munga kin girma dan haka muka zaban maki mijin aure a garin nan"
Da sauri ta dago kanta tareda dafa hannunta kan kirjinta "Aure!!!" Ta maimaita
Daga mata kai tayi alaman taji daidai "muna son kibi Umarnin mu dan har Baba ma ya yarda da zancen nan da two week za'ayi bikin
Kuka ta fashe dashi "Mama dan Allah kuyi hakuri ku rufa min asiri idan de salman ne wlh i promise you na rabu dashi daga yau bazan sake kulashi bah am still young dan Allah kuyi hakuri wlh frnds dina zasu ce-"
"Me frnds din naki zasuce since when do you care about what people say about you Afra? yanxin de maganan aure babu ja dole se kin zauna ko kinaso ko baki so"
"Mama Hakeem ne??"
Kallonta tayi da mamaki yadda ta dauke kukan lokaci daya tana tambayan idan Hakeem ne"
"Toh bashi bane Adeel ne"
"Innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un" na shiga uku yau Mama Ya Adeel zaki aura min mijin Ameenah wayyo yau an kasheni ta daura hannu akai tana ihu
Daka mata wani tsawa tayi "bakida hankali koh meye haka toh"
"Mama yanxin fisabilillah Mijin Ameenah zaki aura min" seta fashe da kuka dan Allah ku taimaka min ni wlh na yarda da auren amma dan Allah da Ya Hakeem nakeso
Mikewa tayi ta zare mata ido "Baza'a aura maki Hakeem dinba Adeel zaki aura babu gudu bajada baya dole ki zauna dashi" har zata fita se kuma ta tsaya
"Sauran kuma ki kira Baban ku wlh nida kene"
Seta fita daga dakin
Fashewa tayi da kuka wai ita wlh batason ta aura mijin Ameenah ya zataji idan ta gane ta auran mata mijinta dama dane kafin ya aureta toh da zata iya aurenshi dan yana mata kyau kuka take sosai
Ashe duk wannan zancen a kunnan Afreen da Hakeem dan tana fita suma suka biyota suka labe da Mama zata fito kuma sukuyi sauri suka sauko
Daman shi Hakeem ya gane tun zuwansu tana sonshi so be wani damu da abunda tace bah
Afreen ce ta dawo ta rungume Yar'Uwarta sunata kuka tare
Shima Hakeem beji dadi ba
********
Zance de ya garara gari da dangi cewa za'a hada auren Adeel da yar'uwan marigayiya matanshi wasu na zagi cewa koh wata biyu ba'ayi bah wasu kuma Allah bada zaman lafiya kawai suke cewa
Adeel de har yanxin kaman ana miya dashi se wani kara ramewa yakeyi yasa a ranshi kawai mutuwa zeyi shima dan haka maganan aiki gabadaya ma ya dena tunanin shi
Amma su office din sun gane halinda yake ciki saboda haka basu mai maganan komawa bah sun bashi time dan ya kuma abun tausayi
Rayuwa ta cigaba da tafiya anata shirya-shiryen bikin kullum Afra cikin kuka take ita batason tayi aure yanxin
Har Babanta ya turo makudan kudi wai a sayan mata kayan daki dasu dan Mama tace mashi a kaduna zasu zauna shi yafison ayi auren sesu kuma paris din da zama
Ana sauran One week a lokacin Alhaji ya bada kyautan gida wanda zasu zauna a ciki dakyar Daddy ya yadda ya amsa dan seda yaga Alhajin ya bata rai
Alhaji yace "Ni kamar yaran cikina na daukesu dan haka karku damu"
Godiya yayi mai a gaban Adeel ya bada gidan amma seya dauke kai yayi kaman besan abunda sukeyi bah ji yake kaman ya shake wuyanshi ya mutu ko ze huta
Daddy ya basu Mami key din gida su uku sukaje ganin gidan Mami,Mama da Mommy sunyi santin gidan sosai dan ya hadu ga gun parking babba hadda garden a cikin gidan
Afra dukta rame tana kwance da waya a kunnanta tana waya da Salman "Babe har yanxin fa suna kana bakansu basu chanja ba ni wlh bazan iya aurenshi bah"
"Ya isa dena kuka kinsan wani abu ranan daurin auren idan basu chanja ba kawai ki kamu hanya passport dinki na gunki koh"
"Aa yana gun Mama"
"Toh ae kinsan yadda zakiyi ki dauko zan turo maki kudi kawai seki kamu hanya ni senazo na daukeki a Airport"
"Haba yanxin so kake na gudu daga gun iyayena ni gaskiya bazan iya bah"
"Bazaki iyaba wanda suka nuna basu sanki shine kike cewa bazaki gudu ba toh shi kenan kita zama nasan daman baki sona ae"
Da sauri ta tsayar dashi" Am so soryy zanzo nasan Mama batasona ae Baba ne kawai ke suna shima hadda shi aka hada abun nan gara na gudu kawai "
Haka suka gama plan dinsu akan ranan dauren aure zata taho
Bayan two days hartaji alert ya turo mata kudin
Su Mama anyi ordering kayan dakin Afra online har an kawo masu dan haka aka je mata jere hadda Safieyarh dasu Ameerah suna cikin yi Ameerah ta fashe da kuka tace ita bazata iya ba jakanta ta dauka ta fice sunata bata hakuri ta dawo amma taki gida ta wuce abinta tanata kuka
Gidan Afra yayi kyau sosai ba'a magana komai nata me tsadan gaske an gama shirya komai
Ku ina acan-acan gwanin sha'awa
Kuma an kawo mata wata mata yar muduguri tazo tana mata gyaran jiki itama Afreen tace dole se an hada da ita ba yadda ta iya se ta mata itama
Su Daddy koma sun hada akwatuna duk abunda akeyi dukkansu basusan ya ake ciki bah kowa na daki gara ma Afra dan Afreen takanzo ta gayan mata abubuwa kaman gidanta ya hadu an kawo akwati
Adeel kowa duk wanda ze shigo mashi daki seya hanashi shigowa wani katon drawer ya saka ya tare kofan daki
Daddy yazo yata knocking amma baze bude mai bah haka ze hakura danshi duk haushinsu yakeji ji yake kaman basu damu da happiness dinshi bah shiyasa suka sake hada aurenshi da wata
Ana gobe daurin aure Afra ta lallaba dakin Mamansu taje ta dauko passport dinta ta boye cikin jakanta tareda credit card dinta ta ajiye dan batason ta tafi da komai saboda idan tazo fita daga gida aka ganta da kaya za'a gane
Auntie kowa Mami ta kirata akan tazo harta gaji danta ki zuwa dan tun zanda aka gayan mata za'ayi hadin batayi magana ba de amma bata sake lekowa gidan ba dan taga be kamata ba kaman basu tausaya ma Adeel a yanxin tace bazata sake saka kafanta a gidan bah tunda su basuda tausayi
Abbah ne a kofan dakin Adeel yanata knocking da wani bugeggen shadda a cikin leda irin farar ledan nan
Ya dade yana knocking amma ba'a bude bah idan ya tura seyaji abu ya tare kiran sunanshi ya shiga kira amma be amsa ba dukda yana jinshi sarai
"Adeel taso ka bude min kofan nan tun kafin na bata maka rai"
Shiru ba'a bude bah
"Adeel you know we all love this the best we can do for you please open up"
Lallaman shi ya dade yana yi a bakin kofan kawai se Adeel ya mike ya bude mai seya kuma ya zauna bakin gadonshi
Binshi yayi a baya ya zauna kusa dashi
"Adeel i know exactly how you feel-"
"No you don't" ya kaste shi da sauri
"Noh you have no idea how i feel have you ever lost some one you ever loved have you???
Have you ever lost a girl you loved and never told her you love her??
You don't have any idea how it feels you don't" ya kare maganan yana niyan tashi
Rike mai hannun yayi ya maidashi ya zauna "You are right i don't am so sorry but this the best we can do for you right now ga kayan nan gobene daurin auran wannan kayan shi zaka saka nasan duk wannan abunda kake yi saboda ka faranta mana ne kuma insha Allahu, Allah ze saka maka Allah yayi maka albarka yasa ka gama da dunyi lafiya yajikan matanka"
Da sauri ya amsa da "Ameen "
Murmushi yayi se yace dan Allah ka aske wannan gemu kaji dana
Daga mai kai kawai yayi yana fita yamaida drawer ya kuma ya kwanta
A daren ranan Babansu Afra ya iso fadawa tayi jikinshi tanata faman kuka wai ita yace a fasa auren
Hakuri ya shiga bata dan haka seta mike ta barshi a wurin
πππ
[22:29, 3/26/2017] 1D-Tyetyelorh-β£: _Washe gari_
Ranan ya kama ranan juma'a tou an yanke se an sauko daga sallah juma'a se a daura auren se ayi walima akai amarya anata shirye-shirye
Daddy yasa Adeel a gaba sedaya aske gemun nan gabadaya sannan ya shiga wanka yayi ya fito ya saka bugaggiyan farar shadda yayi kyau sosai duk a ganban Daddy yake shirin saboda yasan idan ya fita baze shiraya bah
Yana gama shiryawa seya fita Mommy ta shigo tana fesa mashi turare seya tuna haka ranan dauren aurensu da Ameenah ta ringa mashi wanka da turare dukda yana hanata
Rungumeta kawai yayi murmushi tayi se tayi huging nashi back tana tapping bayanshi a hankali
Sun dade a haka daga baya ya saketa
Mama ce da atamfa a hannunta super ta bada a dinka ma Afra saboda ta saka
Dakin ta shiga babu kowa seta ajiye kayan kan gado tayi knocking kofan birthroom amma shiru dan haka seta murda ta bude babu kowa a ciki
Tazo fita ne se taga paper akan mirror kai hannu tayi ta dauka ta bude
Karantawa ta farayi seta saki salati
"Afra abunda kika zaban ma kanki kenan toh kije duniya ce"
Fitowa tayi parlo taga Mami da Afreen a zaune duk Afreen ta haye jikinta kaman maje
Hawaye cike a idonta tayi gunsu mikama Mami paper tayi
"Lafiya takaddan meye wannan" tana tambaya tana kukarin buedeqa
"Afra mana"
Afree ita ta leka ta karanta salati itama saki tana tafa hannu
"Yanxin abunda Afra zatayi kenan ta gwammace tabi saurayi akan tayi aure"
"Hmm ki barta kawai duniya ce da kaman ita kadai na haifa se nayi hadiyan zuciya Allah nagode maka"
Tana gama magana se tayi parlon Abbah
Dukka ta tarar dasu acan Abbah da Baba se Hakeem take gayan masu abinda ake ciki
Waya Baba ya dauka ze kirata
"Don't bother tace tabar wayan a gida dan haka ka barta da kafanta zata dawo" inji Mama
Abbah yace "ae sujuji za'a kira a dubata tin kafin tayi nisa
Hanawa Mama tayi tace wlh abarta duk dadan dadewa da kafanta zata dawo
Badan sunsu ba suka hakuri
Baba yace toh ayi auren da Afreen dan yasan ta fita biyayya ita zata yarda
Mama tace toh shikenan seta fita
Acan parlo kowa Mami ta dauka wayanta ta kira Number Mommy tana bata labarin abunda ya faru
Itama salati tayi Adeel dake kusa da ita wanda yaji abunda suke fara seya saki murmushi wanda rabanshi dayin murmushi tun wayansu na karshe da Ameenah randa zata rasu
Abbah shima ya kira Daddy yake gayan mashi amma yace ya kwantar da hankalinshi da Afreen za'a daura
"Amma dukda hakan Alhaji kamata yayi ya bincikata koh"
"A hakane ni na rigada nasa a dubata amma karku damu yadda aka saka lokaci a lokacin za'a daura"
"Toh shikenan Allah sa shiyafi alkairi"
Ameen ya amsa dashi seya kashe call din
Mama ta fito parlo taga Afreen dan haka seta ja hannunta sukayi daki a bakin gado suka zauna
"Afreen kinga abunda yar'uwarki tayi koh nasan ke bazaki yi haka ba dan kinada biyyaya
Afreen am begging you-"
"Mama ki dena rukana nasan abunda zakice min karki damu na amince your wish is my command"
Wani wawan hug Mama takaima Afreen hadda hawayenta
"Afreen kin gama min komai Allah maki albarka saka wannan aure alkairi na"
"Ameen Mama"
Saketa tayi jekiyi wanka kizo na shirayaki dakaina
Murmushi tayi ta mike ta shiga toilet
An gama magana an sanar da kowa cewa da Afreen za'ayi yanxin a take a wajan ta sama motoci guda biyu daya daga gun Daddy while dayan taga gun Abbah dan ba karamin dadi sukaji bah kuma duk masu tsada
Ta gama shirinta ba karamin kyau tayi ba tasha zinare gashi daurin dankwanin nan yayi kyau ba karamin kyau tayi bah
Mami ce ta dauka waya tana kiran Auntie dakyar ta samu ta dauka kafin tayi magana tace
"Aysha wlh idan bakizo a yanzin ba babu ni bake" se tayi hanging up
Badan taso ba ta kama shiryawa dukda yau mijinta ze dawo suka kamo hanya itada Meemah
Adeel ya gama shirinshi suka shigo mota yana baya shida Safieyarh se Mommy da Daddy suna gaba dan gidansu Hakeem zasuje yanxin daga nan se'a tafi masallacin ayi sallah juma'a se'a daura aure
A tare suka iso da Auntie dan tana shigo da mota suma suka shigo da nasu
Tana fitowa suka gaisa dasu Daddy seta kalla Adeel wani mugun tausayinshi taje kawai seta shige gidan dasauri
Babu kowa a parlo dan haka seta leka na Abbah acan ta gansu dukka amma banda Afreen dake daki ita daya
Gaida kowa tayi amma Mami take amsa nata
Matsawa tayi kusa da ita ta ringa lallamata abunka da jini nan da nan ta hakura
Meemah kowa tana makale a jikin Hakeem
Su Adeel suka shigo suka sama waje suka zauna suma
Adeel a kasa ya zauna aka gaigaisa
Shima ya shiga gaida kowa tunda ya shigo gabashi ke fadi sosai
Zama akayi anata hira amma shi tunda ya dukar da kanshi be daga bah
Can Hakeem,Safieyarh da Meemah suka fito tsakar gida suna hira a bakin mota yasha shadda shima ya daura Meemah a saman motan se faman hira sukeyi suna dariya
Se sukaji an shigo a tare suka daga kansu suna ganin wanda ya shigo gabadaya suka saki wani dan banzan ihu a tare kuma suka kasa motsawa
Can Hakeem yayi karfin amma be bar ihun ba yayi parlo a guje itama Safieyarh ta bishi anan suka bar Meemah tana kan mota se ihu takeyi tana kuka
Suna shiga parlon a guje a tare kowa ya tashi a tsorace yana tambayan lafiya sun kasa magana se nuna kofa sukeyi
Auntiee kowa tamabayan yarta takeyi
A tare Auntie da Adeel sukayi waje se kuma suka tsaya a tare sanadin abunda suka gani sun kasa motsi kwata-kwata
Yan parlon gadaya suma suka fito Hakeem da Safieyarh ne a baya dan su kadai suka san abunda sika gani
Suma tsayawa sukayi they were all shocked ko motsi ba meye a gun se Meemah daketa ihu tana kan mota bazata iya saukowa bah
Sun kusan 10mins a tsaye babu wanda yayi kwakwaran motsi se Adeel daya bude bakinshi dakyar yace "Am......."......
IG.Tyetyelorh
[15:43, 5/6/2017] Rrspectable: [10:40, 3/30/2017] 1D-Tyetyelorh-β£: πππUMARNIN IYAYEπππ
WRITTEN BY:
TYETYELORH
πππ
_I dedicate dis page to Lawizas guyx i love you so very much and i will always do_β£
_Yanxin kam na huta aradu Ameenah is back_π
_#12 April is the date am so damn excited can't wait_
*128*
Sun dade a haka dan sun kai 20mins se daga baya Ameenah ta janye jikinta but idonta were still closed
"Meyasa se yanxin kikayi pulling back??"
Ya tambayeta dan yayi tsammanin tuntuni zata kwace
Juyawa mai baya tayi tasa hannu a fuskanta not ready to answer him
Rungumota yayi ta baya hannunshi yana gun cikinta while kanshi yana gun wuyanta ya kulle ido"i still can't believe you are back how i wish this dream never ends
Rike hannun nashi tayi seta budesu but tana rike da hannun seta juyo sannan ta kulle hannun as in ta zagayashi a waist dinta tana ciki kenan "idan mafarki kake za'a maka haka"
Seta mashi light kiss akan lips nashi
"Yah why not. so nawa ina irin wannan mafarkin"
Zata sake magana kenan sukaji muryan Hakeem yana kiran sunanta
Wani burkicewa tayi ta juya zata gudu toilet se yayi sauri ya riko hannunta "Meyasa ina zaki"ya tambayeta
"Ya Hakeem nefa daga dawowa na a ganni dakai" ta gaya tana kukarin kwacewa again
"Toh whats wrong with it niba mijinki bane and since when kika fara tsoran Hakeem"
"Ae ba tsoranshi nake bah be kamata bane sakeni dan Allah na boye idan ya shigo kace kaima nemana kakeyi"
"Bazanfa sakeki ba afterall we are not doing anything wrong" yana magana yana sake jawota jikinshi
Sunajin ya duso bakin kofan ae hadda shi aka boye closet suka shige itace a gaba
Bude kofan yayi yana sake kiranta dayaji shiru harze juya se yaga hijab dinta murmushi yayi "Toh Abbah yace kozo yana nemanku seya kulle kofan"
Har zasu fito se kuma ya dawo "Nima i want to see my sister cus i misses her too" seya sake kullewa
Dariya Adeel keyi a hankali juyowa tayi ta kalleshi ta hada fuska seta buga mai cikinshi "awwchh menayi"
"Ban sani bah" seta wuce mekewa yayi yabita
Harta wuce hijab din zata bude kofa seya mika mata fuzga tayi hannunta ya janyo
"Its only Hakeem fah"
"Toh kasan ko ze gayan masu muna tare" ta gaya tana kukarin amshe hannunta
"Toh tsaya barin fara fita kaman 20mins kema seki fita kinji bazasu ce muna tare bab"
Daga mai kai kawai tayi
Hijab din ta amsa seya fita a parlo ya tsaya ya dauka babban riganshi ya saka seya fito parlon Abbah ya shiga da sallama aka amsa mai inda yake zaune ya kuma ya zauna
Murmushi Mommy keyi yadda taga ya chanja hadda murmushi kwance a fuskanshi its all what she's asking