Showing 36001 words to 39000 words out of 94870 words

Chapter 13 - Umarnin Iyaye Book Complete By tyetyelorh.txt

parlon yana zaune shi se ci yakeyi ta girgiza kai ta shiga daki ta ajiye akan side drawer kana ta shiga closet dinta tayi smiling ta dauka bom short ta saka da vest sannan ta dauka wani riga kaman jallabiya yake amma shi net ne gabadayan shi and bekai kasa bah ya daura kawai akai ta dauka laptop dinta ta hada chagi dan tanason tayi snding hotonan da suka ringa yi da biki da kuma ranan birthday ta.

Shi kuma yana gamawa ya dauka fresh milk din gida biyu da raguwan kazan yakai fridge snacks din koma ya barsu a wurin ya shiga daki.




📸
_ TYETYELORH_
[15:42, 5/6/2017] Rrspectable: [01:52, 2/22/2017] Tyetyelorh-❣: 💋💋💋 _UMARNIN IYAYE_💋💋💋


_WRITTEN BY:_
_TYETYELORH_

_EDITED BY:_
_AMEENATOU_


_Kuyi hakuri na rashin jina yanxin kullum saboda wasu dalilai ne amma yanxin ga two pages for every novel ya zama hudu kenan kuma nayisu da tsayi nasan kuna hakuri ku cigaba plxxx insha Allah idan abu yayi dede zaku ringa jina kullun_
_Ku cigaba da bina i love you all so mch_❣

_This page is for you guyx members of tyetyelorh novelx i love you guyx so mch_❣

💋💋💋

*111*

Suna isa suka ajiye Hakeem da safieyarh suka wuce
Bema shiga ciki ba ya ciro motanshi ya kai safieyarh gida yana dawowa yayi packing ya shigo cikin gidan yana waka hadda rawa se yaci karo da Mami tana zaune a parlo ta nade hannunta ta hada giran sama dana kasa
Yana ganin haka ya juya a wayince ya cigaba da wakanshi

Tace come back!!
Da karfi
Seda ya tsorata dan be taba jin ta daga murya haka bah
Ya dawo ta nuna mai kujera tareda cewa
sit!!
Ba musu ya zauna dan yasan yayi lefi
Can kafin tayi magana yayi sauri yace Mami wlh ba laifina bane Auntie ce tace muzo mukaita shine Ameerah ta bani key din motan Ameenah mu tafi mata dashi

Seta mike da sauri ta leka window aekowa bataga motan Ameenah bah ta dawo ta zauna tace interesting keep going
Haka ya kwashe komai ya gayan mata hadda inda Ameerah ta kusan accident be bar komai bah
Ita dan ta kirashi yaki daukane kuma yayi dare abuda be taba yibah shiyasa ta kirashi ya zauna amma ya gayan mata komai

Murmushi kawai tayi ta mike tace dinner ka yana kan dinning
Ya mike da sauri ya rike hannunta yace Mami are you not mad
Nop kawai tace ta wuce dakinta toh a lokacin ne ta kira Ameenah taki dagawa harta kira Adeel

Shi kowa Hakeem tsalle yayi kaman karamin yaro yaje ya fara cin abinci
Ita Mami haka taso itama taga ankaita da yan uwanta da kawayenta amma dan taga sun yanke wannan ne shiyasa tayi shiru kawai amma setaji dadin abunda Auntie tayi
Abbah yana dawowa bega motan Ameenah bah dan ya fita da wuri ne yau ya tambaya Mami tace Ameenah tace Hakeem ya kaimata harya kai ya dawo ta zuba mai karya
Haka ya yarda ta kawo mai abinci yaci

_Washe gari_

Ameenah ce ke kwance se faman juyi takeyi da alaman baccin yana mata dadi dan tunda aka fara biki bata somu tayi irin wannan baccin bah
Se wuraren karfe 10am ta tashi dan ta tashi da asubah tayi sallah

Tana tashi tayi mika tayi salati tareda addu'an tashi daga bacci seta sauko daga kan gadon ta tafi toilet tayi brush tayi wanka ta fito daga toilet hannu daya ta dafa towel dinda ke jikinta dayan hannun koma tana shafa fuskanta dan tana jin dadin shafa fatanta dan wani laushi da yake dashi saboda haka idonta a kulle yake

Shi kuma Adeel daya tashi yayi wanka ya dade da fitowa yayi warming snacks ya hada tea harze fara sha kenan seya tuna da abunda Mommy tace mai "dan Allah ku ringa cin abinci tare yana kawo shakuwa kuma ita batasan cin abincin dan haka ka ringa sata a gaba"

Dan haka seya mike yayi knocking yaji shiru seyz murda kofan a hankali ya leka
Toh a lokacin ne take fitowa bata ganshi bah shi koma cinyanta ya fara kalla zankala zankala kawai shi kallonta yakeyi
Ita koma tana cire hannunta ta bude ido taga mutum a bakin kofa yana kallonta tayi ihu ta kara rike towel din seta koma toilet din a guje

Shi koma ihun da tayi ne ya dawo dashi duniyan daya tafi na yan mintina yayi sauri ya juya tareda jawo kofan ya fita
Ya zauna akan kujeran dinning amma seya kasa cin komai ita kawai yake gani

Data shiga toilet kuka ta fara kusan mintuna 5 seta mike ta wanke fuska ta fito a guje tasa key a kofan seta fada gado tana tunanin "wai yanxin yaga jikina " se sake sake takeyi a xuciyanta daga bayade ta mike ta shirya cikin wani atamfa dan Auntie tace mata ta ringa sa atamfa harsetayi sati daya seta fara shirin da takeso

Gown ce taga sama zuwa kirginta a matse yake raguwan koma an sakeshi ya wani bude ta daura dankwalinta ta feshe jikinta da turare ta kalla mirror setayi murmushi ta kyafta ma kanta ido ta dauka waya ta ringa mirror pic dan style din ya fito daga baya ta fito daga dakin a hankali dan taji alaman ya shiga daki dan cikinta se wani kugi yake mata

Tana fitowa taje gun dining taga abunda yayi warming ta dauka guda daya ta wuce kitchen ta ciro jug dinda tasa ta leba a glass cup ta ciro cucumber guda biyu ta kama hanyan daki segashi ya fito daga dakin yana kallonta ya dauke kai

Ita ko kallonshi batayi bah dan gabanta se fadi yakeyi ta kara sauri zata shiga dakin kenan yayi sauri yashawo gabanta seta tsaya dan tsokana seya kai hannunshi ya dauka cup din dan akan plate ta ajiye yakai bakinshi ya kurba seya wuce dashi a hannunshi ya hau kan kujera
Kawai kallonshi takeyi "lallai ma wannan dan rainin wayo ne" ta fada a xuciyanta ta wuce dakinta ta ajiye plate din a kan side-drawer ta fito ta ganshi a zaune yana sha yana wani lumshe ido bata kulashi ba ta wuce kitchen
Shi kuma murmushi yayi ya aza ta barshi ne

ta ciro raguwan wanda ya rage ta zuba cup ta ajiye a gefe ta yanka water-melon tayi blanding dinshi ta juye a cup shima ta fito parlo kawai se tayi kanshi dayake yana zaune ne kujeran yana kallon tv toh ya juya mata baya
Kawai ta dauka cup din blanded water-melon ta juye mai akai kuma ga kayan jikinshi fari tana gama juyewa ta tafi dakinta a guje da dayan cup din a hannunta tasama kofan key tana dariya

Shi kuma kofin hannunshi ya ajiye a gefe ya mike da sauri kafin ya juya ta gudu ya kalla jikinshi yayi murmushi kawai yana mata planing mugunta ya wuce dakinshi seda ya kalla kanshi a mirro ya wuce toilet ya sake wanka ya wanke gashinshi dan daga sama ta zuba kana ya fito ya sake wani shirin wannan karon kaftan ne yasa ya kwanta yana tunani kala kala"lallai yarinyan nan ta rainani am gonna teach her a lesson"
Harde bacci ya daukeshi harseda yaji ana kiran azahar ya fita yayi sallah dan basuda nisa da masallaci saboda haka ana kiran sallah kaman akanka ake kira

Yana gama sallah daya dawo ya dauka motanshi ya tafi wani resturant yayi masu take-away su biyu seya ya dawo gida har yanxin bata fito ba murmushi kawai yayi yaci nashi a jiye mata nata ya wuce daki.

Ameenah kowa tana shiga daki tasa key seda ta gama dariyanta dan tayi missing tsokana seta kunna tv dakin tana kallon E! tana cin abinda take kira abinci
Tana gamawa ta ajiye cup din ta hau kan gado ta kwanta tana kallo can aka kira sallah ta mike taje tayi ta dawo ta sake hayewa gadon se bacci yayi gaba da ita

Se wuraran uku ta tashi tayi salati ta kalla agogo taga lokaci seta bude fridge din dakin shi babu wani abun arziki a ciki balle tace bazata sake fitowa daga dakin ba choculate ne kala-kala se drinks da ruwa tayi tsaki tareda dauka ruwan ta kurba can aka kira la'asar tayi ta dauka choculate taci ta shiga closet dinta seta hango akwatin aurenta a sama ba'ama budesu ba ta fito ta dauka kujeran mirronta ta hau ta sauko dasu dukka seta baje a kasa tanata budewa tana murmushi dan kayan ciki sun mata kyau sosai
Kayan kwalliya kowa ba'a magana gasu yan kunne ta bude na inner-wears ta duba size din dede nata seta yamutsa fuska can setace nasan wannan aikin safieyarh ce ita zata gayan masu size din daga baya ta maidasu ta fito lokacin cikinta yana mata wani irin kugi da yana bakadan abu me hauyi ta rasa yadda zatayi wuraran 5 ta yanke shawaran ta fito

Shi koma yana zaune a parlo yana kallon kwallo seyaji fitowanta yayi murmushin mugunta wanda yasa dimple dinshi fitowa

Tana fitowa ya juya ya kalleta yace ga lunch dinki can amma kaman yayi sanyi se kiyi warming dinshi
Ta kalleshi da mamaki da kuma rashin yarda ta je bakin table din ta bude take-away din setaga manya manyan nama ga kuma abinci me lafiya se kuma jikinta yayi sanyi ta juyo ta kalleshi tace na koshi na sani ko ka kamin maganin bera a ciki naci na mutu

Ba tareda ya juyo ba yace ae da nayi niyan kasheki da ijiya kawai zan samo na daure wuyanki harse kin dena nunfashi
A naji still de bazan ci bah ta wuce kitchen

Kanki akeji yace ya cigaba da kallonshi
Ta shiga kitchen ta ringa dubawa babu wani abinci kawai setaga wani kofa ta bude store ne seta shiga



💋💋💋
[23:29, 2/22/2017] Tyetyelorh-❣: Tana shiga abinci ne kala kala se taga wani kula tana budewa se taga suyayan miya tayi murmushi dan Auntie ta gayan mata ta kawo mata miya ta dauka bowl ta leba kadan dede cikinta da yankan nama guda biyu tadan kara suyawa ta dawo store din ta dauka maccroni leda daya ta bude ta daura ruwa ta zuba maccroni din dede cikinta ta kulle seta deba kwanukan da sukayi datti ta wanke tana gamawa ta juye abincinta ta dauka fork tayi blanding cucumber tasa a glass cup ta fito

Adeel yana daga kai ya ganta seyayi wani smiling din mugunta


Ta shige dakinta bata kulle kofa bah seta ajiye akan side drawer ta shiga toilet
Yana jin alaman ta shiga seya mike da sauri ya shiga dakin a hankali gun plate din ya tsaya ya dauka yankan nama daya dan tsokana ya tura cikin baki ya sake dauke dayan ya fita da sauri ya kuma inda yake zaune ya wani dake shi cikinshi a cike yake dan kawai ya bata haushi

Tana fitowa se taje gun tv dakin ta kunna ta dauka remote din ta dawo ta zauna kan gadon takai hannunta ta dauka plate seta kalla taga babu nama a ranta tace kude ban saka bane kuma ga sedan nama ta kalla parlon ta inda take zaune ta hango Adeel yana zaune da remote inda ta barshi seta ajiye plate din ta fito daga dakin aguje tana ihu

Shi kuma seya nuna irin shima ya tsorata ya mike yace meyafaru kike wannan ihun kaman karamar yarinya

Tace wlh akwai ghost a dakin nan na ajiye abinci na da nama amma yanxin babu naman
Ya kuma ya zauna yace halan aljanunki suka satan maki
Ta rike karamin west dinta tace ni banda aljanu
Be sake magana ya cigaba da kallonshi

Tace kallo ma kakeyi
Toh me kikeso nayi so kike naje na amso maki gunsu
Tace why not

Toh yace seya mike ya kama hanyan dakin itama tana binshi a baya yana shiga ita kuma seta tsaya bakin kofan
gun abincin yaje ya dauka cup din cucumber ya kwankwada ya ajiye raguwan a gun ya juyo ya fito
Tanata binshi da kallo dan taga abunda zeyi seya shiga dakinshi ya turo kofa hadda sa key

A guje ta bishi tana buga kofan wai ita akwai ghost a dakinta
Ya shareta harta gaji ta koma parlo ta zauna tana kallon tv daga baya ta mike ta tsaya bakin kofan dakin tayita addu'a duk wanda ya shigo mata kai hadda na shiga gida dana shiga toilet seda tayi tana gamawa ta shiga a hankali ta tura kofan

abincin da bataci ba kenan harta kwanta drink kawai tasha ta kwanta

_Washe gari_

Da karfe takwas ta tashi ko wanka batayi bah ta fito daga ita se night wear zuwa cinya ta daura black rope shima kadan ya wuce kneels dinta ta fito da plate din abincin da tayi ta ajiye a kitchen
Akan fridge taga wani bread ta dauka ta ciro kwai guda shida ta daura guda uku akan wuta ta fasa uku ta soyasu ta ciro cucumber ta yanka sirara ta ajiyeshi shima ta dauko gwan gwani daya na saiden ta bude ta juyeshi a cikin karamin bowl ta sama spoon ta farfasashi ta dauko dafafen kwai ta zubashi shima a cikin bowl ta farfasashi shima din ta hada da _bama_ ta kwabasu kana ta debu bread din ta ajiyeshi akan plate ta guga ketchup ta daura daura soyayan kwai akai ta daura wani bread din ta dauko dafafan kwai ta shafa a jiki ta sake kullewa dawani bread kana ta saka sausage ta kulle ta yankashi ta gefe ta ajiye a gefe

Ta dauka wani bread ta guga saiden ta kulle ta saka ketchup tasa soyayan kwai ta sake kullewa ta saka cucumber da carbage ta kulle tasa bama shima ta yanka ta ajiye ta maida dukka kayan da tayi anfani dasu

Ta dauka sandwitch din ta ajiye akan dining ta hada tea ita da bata shan madara gashi yau ta labta madara a cikin tea yayi kauri sosai ta fara sha ta deba yankan sandwitch din guda biyu ta kulle raguwan biyu ta fara ci sega Adeel ya fito a shirye ko daga kai batayi bah ta cigaba da cin abincin ta

Shi kuma yana kallonta dan ya fito da guntun yunwanshi shima

Ya dauka tea-cup ya zauna akan dining din shima ya hada tea seya mike ya kuma cikin parlon ya zauna
Ko kallonshi batayi bah yaga bata kulashi ba seya dawo ya bude plate din dayaga a kulle se yaga sandwich din kawai ya suntuma yayi parlo dashi dan karfin hali
"A hankali tace ae daman nakane ole kawai"

Ya zauna ya gama ci ya kura da ruwa ya dawo da plate din ya kalleta yace "mutum da iyayi wai da beshan madara-"
Kafin ya karasa seta mike aguje tayi toilet ta ringa kwarara amai kaman kayan cikinta zasu fita

Shi kuma dariyan mugunta yayi ya wuce se kuma ya dawo yabi bayanta yana shiga toilet din ya ganta har yanxin bata dena bah ta durkusa a bakin toilet sit seyi takeyi har reborm dinta ya cire

Se kuma ta bashi tausayi danshi yanada zuciya me saurin karaya dan haka ya je gunta ya durkusa ya kama mata gashi ya tara gu daya harta gama ta ciro abun ruwan toilet din ya amsa yana sa mata ahannun while ita kuma tana kuskure bakinta dashi
Tana gamawa ta mike ta kalleshi shima ya kalleta seya danna abun ruwan se'a fuskanta tayi ihu tayi baya seya ajiye ya fita

Tace bangode ba me halin mugaye kawai
Ya shareta ya fita
Sandwitch dinda bata karasa ci ba kenan tun ranan bata kara marmarin sake shan madara bah dan ta saba duk sanda tasha se tayi amai seyasa ta cireshi a list dinta

_Two week later_

Rayuwansu de se kara tafiya yake ita ta gaji da zama gu daya
Tana parlo tana waya da Mami dansun shirya se shagwaba take mata wai haryanxin ba wanda yazo duba lafiyanta
Haka ta ringa bata hakuri daga baya sukayi sallama
Seta fara downloading film a wayanta dan duk _Wesnesday_ take downloadin sabon episodes na films dinda takebi _Teen wolf_ da _The flash_
Tana gamawa ta ciro memory card din ta sa a flash ta hada da tv ta fara kalla
Adeel ya dawo dan yaje masallaci yana shigowa harze wuce daki se yaga tana kallo tana murmushi dan haka se ya dawo ya zauna shima a two seater
Bata kulashi bah ta cigaba da kallo se kawai ya mike ya dauka remote din tv ya maida gun kwallo
Kawai ta daga kai ta kalleshi seta dauka wayanta tana chatting shi kuma abun ya bashi haushi yana kallo amma hankalinshi yana kanta

Kawai se aka sa wani lokacin da ake final tsakanin UNITED STATE da MAXICO
Yana cikin players din yana representing UNITED STATE
Se kallo akeyi se Ameenah ta dago ta ga Adeel yana cikin players din seta fara kalla dukda ba ganewa takeyi bah tanata kallo United state sanci 2-1
Can seta mike ta dauko ruwa ta dawo tana shan ruwan tana kallo lokacin ball din yana gun Adeel ze buga kenan kawai a cikin players din Mexico sega wani yazo a guje ya buga kafan Adeel se gashi a kasa

Ameenah kawai seta kware dan tana shan ruwan kenan taga abun zatayi dariya seta kware dukda hakan tana tari tana dariya
Kawai seya mike ya barta agun

Ta ringa dariya harta godema Allah
Aka zo aka dauka Adeel aka wuce dashi shi kuma wancan aka bashi red card
Ta sake fashewa da dariya inda aka sashi akan abun daukan wanda sukaji ciwo ya wani kwanta seta sake sakin dariya
Da abun ya isheshi seya dawo ya fuzga remote a hannunta ya maida mata inda take kallo da ya zauna
Seta gintse dariyanta da kyar ta cigaba da kallon se satan kallonshi takeyi da hannun a baki

Ya kalleta yace wlh zan fasa maki baki
Ta daure fuska tace sekace nice na karya maka kafa ta sake sakin wani dariya ta cire flash din tayi shigewanta daki

Ta sake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login