Showing 51001 words to 54000 words out of 94870 words
Chapter 18 - Umarnin Iyaye Book Complete By tyetyelorh.txt
wayan ya dauka seya messege dinta da sauri yayi replying mata wai karta fita ashe iskanci ne ta ganeshi ne
Saloon taje aka gyara mata gashinta sega messege dinshi ya shigo sake replying tayi itama tace "too late dan yanxin ma zan kuma gida"
Shareta yayi ya dauka sport bag dinshi ya fita
Tana gamawa bank taje data saka kudin ta kamo hanyan gida.
Haka rayuwanta ya cigaba da tafiya ita daya kwallin kwal gashi makarantansu an tafi strike kullum tana gida
Adeel kuma yayi match biyu sauran daya yana gama dayan se yaje wani meeting daga nan ya dawo gida kuma tun tafiyanshi kwana uku kenan har yau be zauna yaci abincin kirki bah shima ya kasa gane dalili kawai daga ya yanka wannan yaci yasha coffe se drink haka yakeyi
Ranan da zeyi match dinshi na karshe tana zaune seta dauka remote kawai takai sport channel ae kowa se gashu Adeel sunayi live ajiye wa tayi tana kallo
2-0 akaci su Adeel sune masu 0 dariya tayi tace losers seta mike ta shiga dakinta ta kwanta
Daga baya duka fara ci har 4-2 na karshene Adeel yaci aka ringa ihu yan team dinsu se ihu akeyi.
_Washe gari_
Tunda safe data tashi ta gyara gidan ta goge ko ina gidan yashaturaren wuta se kamshi yakeyi wanka ta shiga bayan ta fito
Bom-shorts tasa da wani half top ansa MSFTSrep a jikinta baka head-phone ta saka a kunnenta ta shiga kitchen tana girki lokacin karfe 2:00pm
Ta gama hadawa kenan ta fito parlo tana tsaye tana kallon tv juyawan da zatayi kawai taga mutum a tsaye yana kallonta shidewa tayi kaman na 3mins daga baya ta saka wani kara seta kuma kitchen din a guje tasa key bata bar ihun bah har lokacin
Fashewa yayi da dariya se ya shige dakinshi ya shiga wanka
Gabadayanta a tsorace take tana manne da kofan ta dade a wurin se taji abincin na kauri kashe gas din tayi seta dauka wuka ta bude kofan a hankali taga babu kowa a gun dakinta ta shige da sauri tasa key zama tayi bakin gado tana maida numfashi se kawai alarm dinda ya fadan mata ya fado mata wukan ta sake dauka ta bude kofan a hankali taje ta danna alarm din a sittin ta dawo dakin
Ya fito daga birthroom din kenan towel ne a waist dinshi da kuma wani a hannunshi yana goge gashin kanshi yaji karan alarm din
Sake towel din dake hannunshi yayi da sauri ya fito daga dakin gun alarm din ya jufa ya kashe seyayi knocking dakinta
A bakin gadon take taji ana buga kofan da karfin gaske wani wawan fitsari taji yazo mata toilet ta nufa tana rike da maranta seda tasa key sannan tayi fitsari
Buga kofan yakeyi da karfi sosai amma bata bude bah kiran sunanta ya farayi bata amsa ba seya cigaba da knocking din
Fitowa tayi closet dinta ta shiga ta rasa me zata dauka seta hango takalminta hill ne daukowa tayi ta fito kofan ta nufa kirjinta na dukan uku-uku tana bude kofan idonta ta kulle tana ihu wajan hill din ts buga mai a kanshi tana kukarin sake bugawa se yayi sauri ya riketa ya kwace hill din
Amma still bata bude idon ba sema wani ihu da take karayi sunanta ya kira da karfin gaske a zuciye
Furgita tayi ta bude idon ta kalleshi sun hada ido goshinshi kuma ga jini yana zuba
Jada baya tayi tace yaushe ka dawo
Ban sani bah yayi wulli da hill din gun kafanta yayi hanyan dakinshi
Da sauri ta bishi tace am really sorry seriously i thought-
Bata karasa ba yace i don't care
Yana shiga dakin ze turo kofan kenan tayi sauri ta shige kallonta yayi
"Dan Allah kayi hakuri wlh bansan kai bane"
Toh naji fita
"Toh ka tsaya nayi treating dinka"
"Banaso ki fita zanyi dakaina"
Shareshi tayi ta nufa inda yake ajiye first aid box din ta dauko bakin gadon ta zauna tana budewa tace kazomana i promise ina gamawa zan fita.
Tsayawa yayi yana kallon shiganta ita tama manta abunda ke jikinta
Bakin gadon yaje ya zaune
Dan matsowa tayi kadan
Tana dagowa takalla wurin fashewa tayi da dariya
"Wlh na samoka sosai"
Kin gani ko tashi ki tafi zan iya gogewa dakaina kuma sena rama in fadan maki kokarin amsan box din ya farayi
Tana kokarin gintse dariyan tace toh tsaya yahakuri
Mikewa yayi nace banso koh ana dole
"Allah tunda nayi niya sena goge koh danneka zanyi sena goge"
Haka kikace koh toh ma gani
Tana mikewa idonta akan abs dinshi suka sauka tsayawa tayi tana kalla so sexy ji take kaman taje tayita shafa har seta gaji
Da yaji tayi shiru seya kalla fuskanta ya gane inda take kallo se yace zo ki fita kona wullaki waje
Se a lokacin ta dawo duniyan data tafi
Kumawa tayi ta zauna "wlh ina gamawa zan fita kalla inda jinika yake zuba"
Dakyar ta lallameshi ya dawo ya zauna gogewa ta farayi tana gamawa ta dauka plasta zata samai ya matsar da fuskan yace bansonshi
"Taya zakace bakasonshi jams fa zasu shiga ka tsaya mana na saka maka"
Jikina ne koh toh banaso bani box din ki fita
Kokarin jan box din ya farayi ita kuma taki sakewa
Wannan karan dukka karfinshi ya hada yaja da karfi seya janyo hadda ita ta fado jikinshi se suka kanta a atare shi kuma first aid box din ya wuntsile gefe ya baje
Tsayawa sukayi suna kallon idon juna fadunwan da tayi se hannunta ya tsaya akan packs dinshi dukka biyun
Sun kai 9mins a haka suna shakar nishin juna se tayi sauri ta mike ta gayara riganta se a lokacin ta tuna dressing dinda tayi kallonshi tayi yana kallonta da sauri ta kare cibiyanta dake a waje ta fita da sauri
Shi kuma yafi 30min yana kwance inda ta barshi kaman statue daga baya ya mike yana jin kanshinta a jikinshi murmushi yayi ya shafa gashinshi seya mike ya shafa mai yayi combing gashinshi yasha turare suman nan dan duk jikinshi daga abs nashi se gashinshi yake kula dashi sosai
Data shiga dakinta tsaki taja seta saka streght shirt ta cire rigan tasaka vest a ciki ta maida kitchen ta shiga warming abincin tayi ta juye a flask akan dining ta ajiye kitchen din ta kuma zubu ta hada wanda tayi blanding pinapple daya a ciki dan haka yayi kauri sosai tasa ice na cube a ciki ta ajiye shime deban nata tayi seta kuma dakinta
πππ
[20:35, 3/14/2017] 1D-Tyetyelorh-β£: Yana fitowa da gajeran wando a jikinshi se shirt zama yayi ya fara cin abincin yaci sosai dan tun tafiyanshi beci abinci bah zoban ya diba ya shiga cikin parlon ya zauna da wayanshi a hannu
Fitowa tayi da plate a hannunta tana ganinshi a zaune seta dauke kanta daga wurin ta shiga kitchen
Tana fitowa gun dining ta nufa tana kwashe plate dinda yayi using seta kalleshi tace wai meyasa ka dawo yanxin bakace one week ba kuma four days kawai kayi
Banza da ita yayi ya cigaba da shan zobanshi da alama yana mai dadi dan hadda wani lumshe ido yakeyi kare mashi kallo tayi
A hankali tace losers kawai
Kallonta yayi yace canceling meeting dina nayi and for your information mu mukaci
Fashewa tayi da dariya hadda shewa
"Kaman ban kalla bah live na kalla fah so don't pretend"
Smiling yayi ya dauka remote yakai channel din cikin sa'a an saka seya mike ze tafi dakinshi
"Ki sama glass kisaka kafin ki kalla"
Ya wuce dakinshi dan yayi alwala dan an fara kiran la'asar
Harara ta galla mai kaika sani kai plate din tayi tana dawowa shi kuma ya wuce masjid dan haka seta sama wuri ta zauna tana sake kallon match din.
_Two days later_
Tana kwance a parlo ne akan three sitter tana rikeda maranta saboda wani radadi da yakeyi mata gashi Adeel ya tafi office
Mikewa tayi dakyar ta debo zam-zam da Mommy ta kawo mata sanda sukazo karamar jarka a cike
zama tayi ta tufa addu'a a ciki tasha seta kuma ta kwanta ba'a dade ba wani wahalallan bacci ya dauketa amma still hannun yana rikeda maranta
KADUNA
Hakeem ne gaban Mami ya sata gaba waishi wlh aure yakeso ita kuma dariya taketa mashi
Daure fuska yayi yace haba Mami ina maki magana amma kina min dariya wlh dagaske nake ni aure nakeson ayimin
Kallonshi tayi tace kanada aiki ne
Girgiza mata kai yayi
"Toh taya zaka rike iyayi?"
Mami ae sena fara aikin
"Daga baya kenan ba yadda bamuyi dakai bah Abbah ya saman maka aiki a Katsina wai kai yayi maki nisa gashin nan ae"
Wlh Mami yanxin zanje koh maiduguri nema zani i promise
Ae kowa akwai wani aiki a maiduguri-
Da sauri ya katseta "Mami ke bakisan wasa bane a neman min na katsinan kawai"
Wai dagaske kake zakayi aure wai ma wazaka aura
"Safieyarh mana Mami"
"And iyayenta zasu baka kayi yaro ae"
Haba Umma Adeel fa mate dina ne amma shi bakuce yayi yaro bane kuka bashi yarku seni
"Saboda shi yasan abunda ya kamata yayi da wanda be kamata bah"
Yace toh nifa Mami yawancin mate dina fa sunyi aure amma ni kice nayi yaro Allah Mami idan bakuyi min aure bah zan shiga duniya seya mike yayi ficewanshi
Dariya ta ringa yi tace ae ga alaman yarintan nan namiji dakai zaka shiga duniya ta ringa mai dariya.
********
Bata dade a baccin bah seta tashi kuma sena kasa kikewa zaune dan rikewan dayayi wani kuka ta saki dan kaman ana suka mata abu me tsini
Tana jin alaman shigowan mutum shiru tayi amma hawaye na zuba a idonta na azaba
Haryazo wucewa dakinshi ya juyo ya kalla parlo se yaganta tana kwance tana hawaye ga hannunta rike da maranta
Karasowa yayi da sauri yana tambayanta mike damunta take hawaye
"Marana ze fashe"
Kawai ta fada ta cigaba da kukan
Dagota yayi yace tashi mu tafi hospital toh
"Noh please idan mukaje karamin ruwa zasuyi ka barni kawai anjima ze dena"
Ae kowa ya tuna abunda doctor ya fadan mashi se yaji tausayinta
Mikewa yayi ya shiga dakinshi wani karamin leda ya dauko ya bude frigde ruwan gora ya dauko ya saka itacen (ararrabi) a ciki ya girgiza yadan ajiye danya jiko
Can seya dauko ya zuba a cikin cup seda ya tufa mata addu'a seya dagota ya bata batayi musu ba ta amsa tasha
Tana sha kaman tsafi yana sauka a hankali
Zama yayi akan kujeran kanta na kan laps nashi tana sha harta gama ta kalleshi meyeshi wai
"Oho nima bansan sunanshi ba Mommy ta bani nima"
Shiru kawai tayi can tace "sometimes you are nice"
Cire kanta yayi daga cinyanshi seya shige daki
Murmushi tayi ta gyara kwanciyanta bacci ya dauketa.
IG.Tyetyelorh
[15:42, 5/6/2017] Rrspectable: [05:55, 3/22/2017] 1D-Tyetyelorh-β£: πππUMARNIN IYAYEπππ
WRITTEN BY:
TYETYELORH
EDITED BY:
AMEENATOU
πππ
_Ina gaisuwa Naja'atou salisu jahun jigawa state dis page is highly dedicated to you Tyetyelorh loves yuh_β£
*121*
Fitowa tayi bayan gidan ta zagaya harcan karashe tana zuwa setaga wani kofa murda handle din tayi danta bude but it's locked tsaki tayi har zata juyo seta tuna da keys dinda ya fadan mata da sauri ta kuma cikin gidan dakinshi ta shiga bunch of keys ta dauko ta kuma gun kofan trying keys din ta shigayi har daga baya tayi dace wani ya shiga daidai bude kofan tayi a hankali seta taja da baya
Da taji shiru seta shiga kunna wutan dakin tayi sake baki tayi kawai setayi wani tsalle na murna shiga ciki tayi sosai tana shafa kayan wani dadi takeji
Dakin Adeel ne na gym so akwai kayan training dinshi kala-kala a ciki
A fili tace ashe nan kake zuwa idan ka dawo daga sallah asubah dan mugunta baka fadan min bah
Ba tareda bata lokaci bah ta fara excising itama ta dade sosai a ciki daga baya ta kulle ta fito duk tayi zufa
Ajiye keys din tayi akan tv stand seta wuce dakinta wanka tayi ta saka riga da wando parlo ta dawo tayi zamanta
A zuciya ta cewa tayi _"Allah yasan am missing you alot the house is so boring without you"_
Dan guntun tsaki ta saki seta kwanta kan kujeran
Shima haka ta gefanshi yana kwance se faman juyi yake ji yake kaman yayi tsalle ya ganshi gabanta he's missing her like crazy wayanshi ya dauka ze kirata har yakai kan number seya maida wayan a ajiye wani mugun yunwa yakeji amma shi baze iya cin wani abinci bah idan ba nata bah tun zuwanshi beci abin arziki bah
Sake daukan wayan yayi kawai yana kallan kan screen din tunani barkate yakeyi a zuciyanshi
Wayanta ta dauka babu second thought tayi dailing numbershi seta saka a kunne
Kallon screen din yakeyi kawai yaga numberta akan wayan alaman kira da sauri ya mike zauna seya dan tsaya wai shi jan aji
Can seya dauka "Hello" yace itama ta amsa seta gaidashi
Mamaki yayi sosai dan bata taba gaisheshi bah
Amsawa yayi a hankali se duk sukayi shiru kuma
Can se tace daman akwai gym a gidan nan baka fadan min bah
Murmushi yayi yace a mana shiyasa na gayan maki inda keys din gidan yake dan nasan wata rana if you get bored zaki zaga
Ae kowa daga nan nake yanxin
Yanxin ma shiru sukayi se tace yaushe zaka dawo ne
Dariya yayi "Someone is missing mee"
"Seriously to be frank i missed you ni kadai a gidan kaman mayya"
Yaji abunda tace kuma yaji dadi sosai seya basar yace toh meyasa baki fita ki dan ringa shiga makuta mana
Da muryan shagwaba tace "ni na gwammace nayita zamana a gida a kan na shiga makuta dan mata sun fiye gulma
"Toh school fah?"
"Ae ba kullum nakeda lectures bah"
Tahb kawai yace
Akwai wani frnd dina zan kirashi ya kawo maki matarshi gobe da safe seta maki yini
Dadi taji sosai "yeey thank you"
"You are welcome"
Toh seda safe ni zan kwanta yanxin
"Sweet dreamx" se yayi hanging up
Wani murmushi ya saki dan har cikin ranshi yaji dadin wayan da sukayi and the best part is da tace she missed him pecking gaban wayan yayi yana murmushi seya mike training ya farayi dan yau basuda wani match se nan da two days
Da daddare ta kasa bacci se famam juyi takeyi mikewa tayi alwala tayi ta ringa gero sallah ta kusan 30mins tanayi tayi addu'anta seta kuma kan gado dukda hakan ta kasa bacci parlo ta dawo ta kunna tv ta ringa kallo but still koh gyan-gyadi ta kasayi kuma gashi dare yayi sosai dan har 1am tayi
Mikewa tayi dakin Adeel ta shige karkade gado tayi ta haye seta kashe lamp din kusa da gadon tana kwance kan pillo amma tana jin kanshin turarenshi sosai koh 10mins batayi bah bacci yayi awon gaba da ita baccin da tun randa ya tafi batayi irinshi bah dan bacci rabi da rabi takeyi kullum batasan dalili bah
Mafarki takeyi wai gatanan tanata shafa packs dinshi tana murmushi ita daya haka ta ringa baccinta
_Washe gari_
Karfe takwas na safiyan ranan tana cikin baccinta se taji bell na gate yana kara a firgice ta mike kallon cameran gate din takeyi tana mika tareda salati
Mota ta gani zooming fuskan tayi se taga mace da namiji ne a cikin motan wanda tanada tabbacin cewa bata taba ganinsu bah
Komawa tayi ta kwanta kawai se abunda Adeel ya gayan mata cewa gobe da safe ze aiko abokinshi ya kawo mata matanshi
Da sauri ta mike fitowa tayi parlo seta bude masu gate din dakinta ta wuce ta zunbula katon hijab na sallanta seta fito a bakin kofan parlo ta tsaya tana kallonsu
Yana gama packing shiya fara fitowa seya zagaya gunta ya bude mata ya mika mata hannu seta fito
Sun burgeta sosai inama itace abunda tace kenan a fili
Dusowa sukayi gunta suna murmushi se a lokacin ta gane shi shine wanda ya taba zuwa yanata danna bell din gate amma bata bude bah
Murmushi ta sakar masu lokacin da suka karaso inda take
"Sannunku da zuwa" tace seta koma cikin parlon suna biye da ita
Seda suka zauna seta fara gaidashi amsawa yayi da fara'a kwance kan fuskanshi itama haka suka gaisa
Mikewa tayi tace bari ta kawo mai ruwa tunda shi yanxin ze koma
Dakatar da ita yayi yace ta barshi kawai jiranshi akeyi idan yazo daukanta yasha
Murmushi tayi seta kuma ta zauna
Mikewa yayi yayi mata sallama akan bayan magrib zezo daukanta se ta fito ta rakashi ita kuma Ameenah tana kallonsu sun mugun bata sha'awa
Muhseen kenan abokin Adeel ne sosai dansun dade tare da matanshi me suna Fauziyya
Yana tafiya Fauziyya ta dawo parlon anan suka sake gaisawa
Shiru sukayi can se Ameenah ta mike kunna tv tayi tace ina zuwa dakinta ta shiga watsa ruwa tayi tana fitowa shafa mai kawai tayi ta taje gashinta seta saka duguwan riga na atamfa ta fito haka gashinta a waje
Kallon fauziyya tayi seta sakar mata murmushi seta zauna can mikewa tayi tace barin hada mana breakfast koh
Itama fauziyya mikewa tayi tana cire gyalen jikinta tace muje na tayaki babu musu suka shiga kitchen din Ameenah na gaba
Dankali ta debo suka shiga barewa tare suna dan hira sama-sama har suka gama
Soyawa suka shigayi dankali da kwai sukayi seda suka gyara kitchen din se suka fito kan dining suka zauna kayan tea Ameenah ta tura mata tace ta hada tea ba musu ta amsa ta fara hadawa
Ita kowa dankalin kawai take ci
Tambayanta tayi ke bazaki sha tea bah
Girgiza kanta tayi tace Aa banshan madara
Murmushi tayi halan munada Baby ne toh Allah saukar lafiya
"Banida komai fah " Ameenah tace
Shiru tayi kawai suka cigaba da cin abincin suna gamawa tare suka shiga da dishes din kitchen
Parlo suka dawo suna dan hira
Wuraren karfe 2pm by now sun dan saba dan ita Fauziyya ta gane cewa ba wani son juna sukeyi ba