Showing 78001 words to 81000 words out of 94870 words

Chapter 27 - Umarnin Iyaye Book Complete By tyetyelorh.txt

jita
"Uhm banji ba" dukda yaji but yanason ya tabbatar da abunda kunnanshi suka jimai
"You heard me"
"Seriously noh just repeat it once"
"I said my baby" ta gaya tana kukarin kulle fuska
Wani dadi yaji se ya manna mata peck akanta se shiru ya ziyarci dakin

He can't believe Ameenahn shice ke wanan magana duk ya gama kusawa su kuma gida cus he wanna shower he his love he want to make her feel very special dukda he knows she's special but he want her to know she has a paticular place in his heart
He want to make her feel like a princess
Shi bawai jikinta yakeso ba ko wani abu Noh ita kanta yakeso shi ze iya zama da ita a haka ba tareda wani abu ya hadasu ba dukda yasan its impossible amma baze taba yi mata abunda bataso bah

Sun dade a haka anyi shiru se sake-saken da kowa keyi a zuciya daga baya Ameenah ta dauke da bacci
Baccin da ta dade batayi irinshi ba
Da yaji shirun yayi yawa seya kira sunanta a hankali amma shiru seya tabbatar tayi bacci shime be dade ba bacci yayi awon gaba dashi

Mami ce ta shiga dakin da Maman da Afreen suke ciki da wani cup a hannunta ta mika ma Afreen "drink up kiban cup din"
Amsa tayi seta kalla Mama ta kalla Mami se kuma ta kalla cup din seda ta yamutse fuska setakai baki ta kwan-kwade tass ta mika mata cup din
"Yawwa yar gari Allah maki Albarka ya bada zaman lafiya"
Ameen suka fadi dukka seta kalla Mama
"Za'a iya bani gu da diyata" tayi magana da alaman zolaya

"Abun hadda yar gori toh shikenan nima ae inada yar" ta mike
"A naji a tafu de"
Dariya sukayi gabadaya se Mama ta fita Mami kuma ta zauna kusa da Afreen ta rike mata hannu
"Afreen Allah maki albarka Allah sa Marwan shine alkairi a tareda ke ya baku yara nagari"
Addu'a take mata sosai tareda shawarwari kala-kala gameda yadda zata rike mijinta

Da ta fara kunya se kuma ta saki jikinta
Tanata fadin mata yadda zata ringa gyara jikinta
*******

Can masallaci kowa an gama gaishe-gaishe aka kamo hanyan gida hadda Hakeem da Ahmed dan tunda Hakeem ya bashi labarin dawowan Ameenah ya fito daga gida zeje ganinta

Mommy ta fito neman Ameenah seta leka dakinta kawai ta gansu suna bacci hankali kwance basuda damuwa ita ta aza ma yana can masallacin ne
Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyanta danta ji dadin ganinsu haka
Finally her son is back ta fadi a zuciyanta seta janyo masu kofa
Tana wani sanyayan murmushi dan a rayuwarta idan yaranta suna cikin damuwa har zuciyanta takeji
Dukka iyaye ma

Suna isowa da mamaki sukaga motan Adeel shiga ciki akayi hadda Alhaji amma Ango bezo ba
Motan Abbah a waje ya barsu dan yanason yanxin su tafi dauko Mallam
Kiran Mami yayi ta kira mashi Inna su tafi
"Dear bazaka ci abunci ba first"
"Aa sena dawo kinga yanxin shi kadai tace yake zaune muje mu taho dashi tukunna kafin a hada masu Passport din"
"Shikenan" seta haye sama ta kirawota nan da nan yace ta fito su tafi
Su biyu suka tafi
Inna tana cikin 30s dinta bata wani tsofa ba kawai wahalan duniya ne ya tsofar da ita while Mallam kuma yana cikin 50s dinshi su duk ba wasu tsofaffi bane amma sun cire hope din haihuwa a rayuwansu.

Su Ameerah ne suka iso su uku Ameerah,Fatye da Ummitarh
Safieyarh na ganinsu ihu suka saki tare
Gaida iyayensu sukayi se suka nufi dakin Ameenah they were all eager to see her
Suna zuwa bakin kofan Safieyarh ta tura suka cusa kai dan duk basuyi expecting ganin Adeel a dakin bah.

"Awwwn" duk suka fadi a tare hadda saka hannu akan kirji kallonsu kawai suke suna murmushi dan sun burgesu
Su kam baccinsu suke tsakani da Allah dan dukkansu sun dade basu sama irin wannan baccin bah hankalinsu kwance Ameenah ta wani lume a jikinshi ta daura kafanta daya akan kafanshi guda daya shi kuma hannunshi daya ya rungumota dayan kuma ya sake rungumota dashi kaman za'a kwace mashi ita

Ameerah ce ta ja hannunsu dukka suka fice ta tura masu kofa
Dariya suka saki a tare suka sauka kasa dakin Hakeem suka shiga suna hira Safieyarh tana basu labarin halinda Adeel ya shiga sanda Ameenah bata nan

_One hour later_

Brand Walima akeyi a gidan an cika rabin mutanen da sukazo dan ganin Ameenah ne
Su Zaid suma sunzo se zuba soyayya akeyi shida Ameerah
Fatye kuma da Ahmed se Ummitarh da Fa'iz kowa yana soyayyanshi gwanin sha'awa
Suma Hakeem suna nan suna nasu
Har a lokacin Ameenah suna baccinsu Mommy ta hana a tashesu dan gadinsu takeyi tana zaune a parlo duk wanda ya nufa dakin take dakatar dashi hadda Mami

Afreen tana can a daki itada Safieyarh da Hakeem suna hira ta sake jikinta abunta
Marwan kuma suna tareda frnds dinshi a babban parlon kasa anata zulayanshi shi kuma bakinshi har kunne sakashi a gaba sukayi wai seya kira amaryanshi
Ya dauka wayanshi daman tun-tuni yanada number ta ya shiga kiranta amma ya matsa gefe
Yanata ringing harya katse bata dauka ba dukda tana gani ita bata dauka number ne
Ya sake kira Hakeem ne yace ta dauka mana taki kawai se ya daga call din ya sa mata a kunne dan dole ta amsa
"Assalamu alaikum" taji muryan Marwan me dadi masifa dan seda tayi ajiyan zuciya
"Waalaikumus salam" ta amsa a hankali

Lumshe ido yayi "Amarya kinsha amshi"
Murmushi kawai tayi batayi magana ba dan tanada masifan kamun kai
"Angonki ne " taji wani ya fadi daga gefe
"Banson iskanci fa Mu'azzam" ya fadi yana mikewa parlon ya bari gabadaya
Ita batayi magana ba tana jinshi kawai

"Afreen" ya kira sunanta wani murmushi ta saki dan bata taba jin wanda ta iya kiran sunanta ba kaman haka
"Na'am" she answerd with her sweet voice
Hira suka danyi kaman wanda suka saba ita kawai
"Uhmm ko Aa" take fadi
Har daga baya sukayi sallalama
Tana kashewa kwanciya tayi kan gado tana wani murmushi
Dariya su Hakeem suke mata dansun gane dawa take waya.


💋💋💋
[14:01, 4/1/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: Walima sosai akeyi se ciye-ciye akeyi kuma kowa se tambayan Ameenah ake
Yan uwansu dake kusa harsunzo anata murnan dawowanta wasu kuma jahilan cewa sukeyi
"Waya sani ma ko aljani ne yayu suffanta yace itace"
Hakade kananan maganganu
Su Ameerah harsun gaji da jiran tashinsu Zaid kowa cewa yayi shi tashi zeyi ya tafi Ameerah ta hanashi
Hakeem ne a kofan dakin yana son ya tasheshe amma ya rasa ya zeyi dan ya gaji kowa idan yazo shi ake tambaya Ameenah
Kujeran dakin Mami na mirror ya jawo yazo daidai kofan dakin kawai seya daga ya buga a kasa da sauri ya dauka ya maida seya sauka kasa yasan dole su tashi
A tare suka furgita suka bude ido
Ameenah taga inda ta shege jikinshi kaman mage se abun ya bata kunya cire kafanta tayi tana mika tareda salati shima haka
Agogan hannunshi ya kalla yaga 4:32pm zare ido yayi yana kallonta
Hannunshi taja gun agogan itama ta kalla ae seta diro daga kan gadon ta shiga toilet dan tayi alwala tasan an nemeta
Tana fitowa shima ya shiga yayi zama tayi tana jiranshi dan yaja masu
Fitowa yayi yana gyara hannun rigan seya kalleta mikewa tayi ta dawo kan dadduman kaman yasan abunda take nufi seya shiga gaba ya tada suka fara sallahn
Suna gamawa tayi addu'anta seta mike ta cire hijab din gaban mirro taje ta gyara fuskanta ta dauka dan-kwalinta ta shiga daurawa ya gama shima amma yana zaune yana kallonta shi be gajiya da kallonta kwata-kwata.

Tana gamawa ta juyo" How many hours muna bacci ze kai 3 fah"
Murmushi yayi mata kawai seya mike "Can we go no"
"Tare" ta fada tana zare ido
"Yah Why not se kace ba matana bah"
Taso tayi magana se kuma ta mike bude mata kofan yayi ta fara fita shima ya fito ya janyo kofan dafa hannunshi a bayanta yayi suka jero
Ba suyi nisa ba sega wata mata irin family frnd dinsu ce kawai seta rungume Ameenah
Itama tayi huging nata back tana murmushi
"Wlh se yanxin na yarda kin dawo am so glad"
Can bayan yan surutai suka sauko tare har a lokacin yana dafe da ita
Duk inda ta wuce daga me rungumeta seme rike mata hannu hadda masu kuka

Dakin Hakeem suka shiga suka tararda kowa a ciki (frnds) hadda Afreen se hira akeyi su Ameerah suna ganin shigowanta a tare suka saki ihu sukayo kanta se kuma aka fashe da kuka rungume juna akayi sosai dukka su hudun sun dade a haka aka sake juna
Su Zaid sannu da zuwa suka mata ita kuma ta gaidasu da fara'arta
"Matarshi ta dawo yaki barin kowa ya ganta"
Abunda Zaid ya fadi kenan yana ma Adeel wani kallo
"Daman yaza'ayi na barta yanxin ma sa'a kukaci ta fito kana bata min rai sena maidata dakin"dariya kowa ya saki

"Ayi mana hakuri" Ameerah ta fadi
Ita kowa Ameenah murmusawa kawai takeyi

waje suka sama aka zauna anata hira Ameerah tana rike da hannunta har a lokacin hawaye takeyi
She can't believe her best frnd is really alife

Ahmed ne ya shigo yana ganinta kanta yayo da sauri ze rungumeta dan zumudi seyaja burki ya kalla Adeel daya zare ido yana kallonshi
"Ya Adeel zan dan iya rike kanwata kadai kawai" da zulaya yake magana
"Uhmmmm Noh!!!" Shima ya fadi
"Toh shikenan tunda an min ruwanki" yana magana yana kallon Ameenah
Mikewa tayi tayo gunshi tana dariya kawai seta rungumeshi "Am so glad you are here"
"And am so glad you are alife"

"1....2... idan na kai 3 baka sake ba i will punch you" Adeel ya fadi yana dosan gun
Ahmed kokarin ganyewa yakeyi amma Ameenah dan mugunta seta ki sakeshi
"Ameenah ki rufamin asiri ki sakeni" dariya takeyi sosai
Adeel yana zuwa gun seta sakeshi ajiyan zuciya ya saki "Amma wlh ke muguwa ce har yanxin baki bar mugutanki bah"
Fashewa akayi da dariya kowa Adeel kuwa murmushi yayi ya riko matanshi
Hakeem yace "Nifa tun zuwanki Adeel ya hanani rikeki" yana magana kaman karamin yaro yanson yin kuka
"And meyasa zan barka"
"Because nima i missed my sister"
"Awwn really you do?" Ta fadi tana zuwa gunshi ta rungumeshi
"And i missed you too big bro"

Kallon dakin tayi taga babu mirror shi dukka biyu
"Ina mirror ka suke wai dakin yayi wani iri haka"
"Hmm ba mijinki bane ya fasa min dukka ae ina jiran randa zaku kuma ne na biko na dakinki zan ciro"
Kallon Adeel din tayi "How comes?" Tana dusan inda yake
Shiru yayi ya wani hada hannunshi gu daya yana kallon gefe kaman badashi take magaba bah

Safieyarh tace ni zan gayan maki abunda ya faru
"Wlh idan kikayi magana Motan da nayi maki alkawari on your 18th birthday zan baki is done"
Ae komawa tayi ta zauna bata sake magana ba
"Ni barin baki labari" Hakeem ya fadi wani kallo Adeel yayi ma
"Ae sefa na fada sede idan zamu sa labule zanyi shiru"
"Zamu saka"ya fadi da sauri

"Haba mana dan Allah ku gayan min"
Auntiee ce ta shigo ni zan gayan maki
Ita tun dazin ta kuma gida tana ma Daddyn Meemah girki dan yau ze dawo se yanxin ta dawo tareda shi
"Haba Auntie karki fadan mata mana" Adeel ya fadi

"Why?? You don't want her to know you love her, tou sena gaya"
Ta kwashe dukka event daya faru ta gayan mata hadda maganganun da yakeyi dukda itama Mami ce ta fadan mata

Ameenah ji tayi ita ta gama sa'a a rayuwa she have nothing else to ask for sede godiya dan ta gama samun komai ga iyaye masu sonta kuma nagari ga kuma mijinta
"Allah nagode maka" ta fadi a zuciyanta
Tana wannan tunanin amma idonta na kan mijinta shi kuma wani basarwa yakeyi
Su Muhseen suma sunxo amma basu wani dade ba suka kuma sunyi murnar ganinta sosai
*****

Abbah sun isa an dauko Mallam amma dakyar ya yarda har seda matanshi abun kaunanshi tayi hawaye seya yarda a taho dashi kulle gidan sukayi aka kamo hanya a lokacin an gama masu komai isowarsu kawai ake jira daga nan ma baze tafi gida ba Airport din Kaduna ze kaisu sesu tafi su uku da PA dinshi ne

Suna isa Airport din Abbah ya bama PA din makudan kudi wanda zasuyi amfani dashi kaman gun sayan kaya dan basu dauka komai ba da kuma gun zama amma komai da komai an gama biya jiranshi kawai akeyi
Godiya suka ringa ma da Addu'oi kala-kala suna kuka dakyar ya lallasesu akan abunda suka mai yafi abunda ze masu
Suna gamawa ya taho gida abunshi sati biyu zasu acan su dawo.

Misalin karfe 7pm
Ameenah da Afreen se Safieyarh suka zaune a dakin Ameenah suna hira abunsu dansu Ameerah duk sun tafi gida dan su shirya saboda kai Amarya da za'ayi se'a tafi Dinner daga nan dan a gidan Amaryan zasu kwana dukka
Dan ita Afreen batada kawaye kwata-kwata anan so sune zasu mata kara
Kaya Mami ta kawo ma Afreen dakin kala biyu
Da wani less da zata saka yanxin idan za'a kaita da kuma na Dinner
Ameenah ce ta amsa wai ita Afreen kunya takeji
Bayan Mami ta fita suka sakata tayi wanka dan sune manyan yayyu saboda Auntiee ta tafi ita tana fitowa aka shiga shiryata cikin less din yayi mata kyau sosai daukwalin ya zauna kwalliya aka shiga mata suna gamawa gyale aka yafa mata Mommy tazo ta fita da ita dan kaita gun iyayenta suyi mata fadi

Su kuma a lokacin suka shiga nasu shirin
Safieyarh daman ta dinka sabon kaya saboda bikin Adeel da Afra ita kuma Ameenah daman tanada kayan da bata taba sakasu ba daman
Cikin atanfa suka shirya sunyi masifan kyau
Jaka Ameenah ta samo ta dauka kayan da zata saka da Dinner da kuma kayan baccinta se duguwan riga kuma
Itama haka Safieyarh ta saka nata a jaka

Number su Fatye aka shiga kira sukace gasunan a hanya sunma iso

Fada ake ma Afreen sosai se kuka takeyi duk ta bata kwalliyan Mama ma ita kukan takeyi kaman ba gobe suna gama mata seta rungume Mama wai ita batasan a rabata da Mamanta dakyar aka rabasu aka fito da ita
A lokacin an kawo motocin daukan Amarya se aka fito da ita waje se kuka takeyi a motan dake tsakiya aka ajiyeta Safieyarh taje ta zauna kusa da ita Ameenah na shirin shiga taji an jawota kawai taga Adeel
"Wlh ka ban tsoro"
"Ina zaki da kayan nan"
"Kai Amarya ofcourse"
"Ki fasa zuwa mana kawai"
Murmushi ta saki "ae kasan baze yuwuba dagani ni se Safieyarh manya kaga dole muje"
"Tou Auntie fah ita bazata bane"
"Zatazo Dinner amma baza'a kai Amarya da itaba dan mijinta ya dawo"

Da kyar ya samu ta yarda akan ta jirashi ya shirya seya kaita daga nan sesu tafi Dinner tare
Cema Safieyarh tayi su tafi ita zata zo anjima
Kumawa ciki sukayi dakin Hakeem suka shiga wanka ya wuce kawai ya wanke gashin kanshi ya fito dagashi se towel ita kuma tana zaune bakin gado da wayanshi a hannunta tana kallon hotona
Hotonanta ne baja-baja a ciki hadda wanda batasan ya dauka bah
Daga kan da zatayi se ganshi da towel kawai idonta akan 6 packs nashi suka sauka tayi 3mins tana kalla shi bema san tanayi ba dan ya rufe fuskanshi da wani towel yana guge gashinshi
Dauke kanta tayi da sauri gabanta na dukan uku-uku kawai se taga ya duso gunta ae wayan dake hannunta hannunta kallonshi kawai takeyi amma hankalinta be gun jikinta har wani rawa yakeyi
Gabanta ya tsaya dai-dai ita seta dago yana kallonta hannunta tayi sauri ta kare idonta "Ya Adeel meye haka babu kayafa a jikinka"
"Wannan towel din meye toh"
Kawai se taga dukuwa gunta baya-baya takeyi amma a zaunan shi kuma se binta yakeyi fadawa tayi kan gadon ta kwanta har a lokacin idonta na rufe
Cigaba da binta yayi
"Ya Adeel please stop it"

Hannunshi yakai seya dauka kayanshi a bayanta seya sakar da murmushi danya ga ta tsorata juyawa yayi ya nufa closet din Hakeem
Da taji shiru seta bude ido taga babu kowa a gun ajiyan zuciya ta saki dan ta aza tabata zeyi se kuma ta saki murmushi

Can seya fito a shirye gaban mirror ya shafa ya gyara gashinshi ya feshe jikinshi da turare
Da sauri ta mike "Nima bani na fesa"
Be bata ba seya shiga fesa mata seda tayi atishawa ya barta
Buttile din riganshi ta gyara mai seya riko waist dinta tana gamawa zata juya se taji be sake ba kallonshi tayi seya ce
"Just a kiss"
"Ammm Nop Akwai lipstick a bakina"
"So zema fi dadi please just one"
"Kasan fa ana jirana kilan ma yanxin sun isa dan Allah kazo mu tafi"
"Seriously bazan sake-"
Ba karasa ba takai mai hannunta na kan packs dinshi shi kuma a waist dinta seda taga yayi nisa se tayi pulling back ta kwace gabadaya tana murmushi
Kallonta yayi "Anya dagaske Ameenah ce wannan" yana magana yana kokarin sake kamota
Tuni ta kama hanyan fita tana dariya biyota yayi suka fito yana rikeda jakanta
Kawai se sukaci karo da Mamai "Daman baku tafi bah "
Kunya ne ya lullubeta seta kasa magana dan taga Adeel ya fito
Shima susa keya yakeyi can yace wayan Afreen muka dawo dauka ta manta dashi ne
"Ohh tou sekun dawo" seta wuce

Can kowa an kai Amarya yar'uwan Mami ce ta sakata tayi addu'a kafin ta shiga haka tayi dukda tana kuka da kafar dama ta shiga ciki basu tsaya ko ina ba se dakinta fuskanta a lullube se kuka takeyi Safieyarh ce keta faman bata hakuri

Suna zuwa gun motan seda ya bude mata ta shiga ya ajiye jakan seya zagaya ta gefanshi shima ya zauna tada motan yayi suka kama hanyan gidan
Suna isa ba tareda bata lokaci ba suka fito ya rakota har bakin kofan dan akwai mutane ne amma yayi niyan shiga har ciki
Mika mata jakan yayi "karfe tara fa zanzo mu tafi tare" daga mai kai tayi seta shiga ciki seda ya ganta ta shige har ciki seya juya ya shiga motanshi
Tana shiga dakyar ta iya shiga cikin dakin dan mutane sunyi yawa a cikin parlon a bakin gado ta samesu Safieyarh nata bata baki amma kaman tana kara zugata ne
Zama tayi itama ta shiga lallashinta dakyar tayi shiru su Ameerah suka iso

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login