Showing 54001 words to 57000 words out of 94870 words
Chapter 19 - Umarnin Iyaye Book Complete By tyetyelorh.txt
dan haka tace zata koya mata rike miji da kuma girki daban-daban
Kallonta kawai takeyi
Shiga kitchen sukayi dan fara koyan girkin
yanxin abinci kala biyu sukayi na yan gayu
Ameenah taji dadin zuwan Fauziyya dan ta koya mata abu kala-kala banda ma girki hadda yadda zata gyara jikinta yadda zatayi tattalin kanta a matsayin ya mace da kuma rike mijinda
Da yamma Muhseen yazo ya dauka matanshi seda suka sashi ya zauna yaci abincin da suka hada
Ameenah tayi mata godiya sannan ta tambayashi akan dan Allah gobe ya kawota
Murmushi yayi yace insha Allah
**********
Wayanta ne ke ringing tana dubawa taga Adeel ba tareda bata lokaci bah ta daga
Gaisawa sukayi se yake tambayanta Muhseen ya kawo matan nashi kowa
"Ya kawota tunda safe harse yamma yazo ya dauketa tanada kirki wlh ta koya min abubuwa kala-kala hadda girki"
"Allah sarki, girki dame ta koya maki?"
"Abu mana"
"Abun nakeson naji ae"
Wai ina ruwanka tsakanin mata ne.
"Kide fadi gaskiya hadda rime miji ta koya maki koh"
Katse wayan tayi da sauri dan wani kunyanshi ne yazo mata
Da yaji ta kashe wayan dariya yayi yana kallon kan wayan dan ya gane kunya taji
Ya rasa gane dalili tun barinshi garin idan yana waya da ita yana samun nishadi sosai ku meyasa ohu
Ta gefanta kowa itama dariya takeyi hadda rufe fuska wane tana gabanshi ne
"She's really crushing on him cus she admit it he's handsome his lips are killing her he have this big brown sexy eyes that duk lokacin da take kalla she's feeling like thousanda butterflies in her stomach and he have this romantic voice wanda tasan ko shi besan yanadashi bah ga wani tafiya da yakeyi kaman yana cat walking ga wasu jijiya a hannunshi wanda tun suna school itada Ameerah da fatye idan kaman class-mate dinsu masu jijiya a hannu ne suna burgesu and the best part is his packs thats her weak point dan lokacin kafin tayi aure wayanta hotonan shirtless maza ne dayawa ga account dinta na instagram packs ne baja-baja Mami ce ta sata a gaba gabadaya ta goge su dukka
A kwance take wannan tunanin a dakin Adeel
Har bacci gwanin sata ya sace ta
Ta gefan Adeel shima haka yaketa tunanin nan yasan he have already falling for her dukda besan ya *so* yake bah
Saboda idan tana magana abu biyu kawai yake sakashi tsayawa kallonta na farko lips dinta suna kasheshi dan idan za'a bashi dama ace yata shafa lips dinta harseya gaji ze iya kuma yasan ba gajiyan zeyi bah na biyu kuma voice dinta dan akwai wasu lokaci da take cewa yana banza da ita shi beman san abunda take cewa ba lokacin dan idan tana magana ji yake tana mashi waka a kunne
"He knows it he have feelings for her but he have no idea taya ze fara gayan mata dan a rayuwanshi be taba tunanin ze fada tarkon soyayya ba balle harya gayan ma ya mace yana sonta but Ameenah deserve it she deserve more"
Tunani barkate kawai yakeyi shima har bacci ya daukeshi
*************
Tun daga ranan idan Muhseen zeje office ze kawo Fauziyya gun Ameenah ta yini mata dansu basuda yara har tsahon kwana biyar haka yake kawota
Rana na biyar ya kama ranan saturday kenan shiyasa be kawota bah
Ranan Monday kowa
A lokacin Ameenah tasan komai gameda zaman aure da kuma gyaran jiki( bawai da bata sni bane Noh amma yanxin ta kara ganewa)
Ameenah ta cigaba da zuwa makaranta abunta idan kuma batada class toh zatayi zamanta a gida ta ringa koyan girki da littafin koyan girkin da Fauziyya ta bata
πππ
[06:28, 3/22/2017] 1D-Tyetyelorh-β£: . KADUNA
Mami ce ke zaune ita kadai da glass a idonta tana danna wayanta se Hakeem ya shigo dakinshi ya shige ba'ayi koh minti 10 bah sega Abah ya shigo mikewa tayi da sauri ta amsa jakanshi tana tambayanshi lafiya ya dawo ba lokacin daya saba dawowa bah
Samun waje yayi ya zauna yana mikar da kafa se yace wlh dan zazzabi ne ke damuna shiyasa
"Subhanallah toh ka tasu muje doctor ya dubaka mana"
"Aa lafiyana kalawa fah hutawa zanyi kawai zan dawo daidai"
"Habah Allah ya zaka ce haka toh barin kirashi yazo kawai" tayi magana tana niyan dauko wayanta
Hannunta ya rike "calm down nace maki lafiya na kalaw fah ki barshi kawai"
Badan taso ba ta hakura seta dauko mashi maganin zazzabi ta mika mashi da ruwa a cikin glass cup ba musu ya amsa yasha
Zama tayi a kusa dashi
_30 minutes later_
Mikewa yayi yace barin dan watsa ruwa sena-
Maganan dabe karasa ba kenan ya zube a kasa sumamme
Salati Mami ta farayi tana hada hannunta waje daya tayo kanshi jijjigashi ta farayi tana cewa Alhaji!! Alhaji!!!
Amma shiru
Kwallama Hakeem suna ta shigayi Allah ya taimaketa yana nan dukda weekdays ne
Kiran sunan Hakeem take sosai tana hawaye
A guje ya fito daga dakinshi a durkushe ya sameta ga Abbah a gabanta kaman mamaci kansu yayo shima ya shiga tadashi yana cewa Abbah!! Abbah!!!
Amma shiru mikewa yayi aguje yayi waje gate-man ya kira danya tayashi sa Abbah a mota suje asibiti
Shigowa yayi shima da sauri a kafada kowa ya saka hannun Abbah suka sauko dashi a hankali
Mami na binsu a baya tana salati da kuka dukka
A sit din baya suka sakashi
Mayafi ta ganyo ta shiga itama bude masu gate megadi yayi a guje suka fita
IG.Tyetyelorh
[15:42, 5/6/2017] Rrspectable: [16:47, 3/16/2017] 1D-Tyetyelorh-β£: πππUMARNIN IYAYEπππ
WRITTEN BY:
TYETYELORH
EDITED BY:
AMEENATOU
πππ
*118*
Abbah daya dawo daga office yana zaune shida Mami da Hakeem tace "Yawwa danka yace aure yakeso kuma idan ba'ayi mashi bah ze shiga duniya"
Dariya ya saki "toh gaskiya ya fito da mata tun kafin yaja mana abun kunya"
Ya fada yana dariya
Hakeem yace Allah Abbah dagaske nake aure nakeso
Dafa mashi kai yayi yace toh an gama wace tayi sa'an samunka
Murmushi yayi yace safieyarh
"Safieyarh dana sani"
Daga kanshi yayi
Toh ae daka fada tun wuri da mun hada dana Ameenah kawai
Wani dadi yaji yace amma yanzin za'ayi din koh
"Da zaran ka fara sana'a naga kuma kana kukari sosai za'a daura"
Mikewa yayi ya rungumeshi yana jin dadi
Mommy tace kaga irinta koh a haka za'a maka aure
Kumawa yayi ya dake ya gyara wuyan riganshi yace "Toh yaushe zan fara zuwa office din"
Dariya Abbah ya saki yace haka akeso ranka ya dade
Yanzin ran monday zamu je na kaika
Dadi yaji sosai ya mike dakinshi ya shiga yana murna
_Two weeks later_
Adeel yayi wata sabowan mota shima kia ce but wannan glass din motan is bulletproof ta ku wannan window kuma is black yasha tint
Sunata shirye shiryen zuwa kaduna zasu kwana biyu acan Ameenah se duki takeyi randa ya gayan mata bata san sanda ta rungumeshi bah
Suna gama shiryawa da sassafe bayan sun karya suka fito kuma ya hanata gayan masu
Tunda suka shiga suketa faman fada kaman kishiyoyi data gaji baya ta kuma seya tsayar da motan yace kaman wani driver ki ae wlh baki isa bah fito ko kuma fito dake
Shareshi tayi ta kulla idonta
Bude kofanshi yayi ya fito zagayawa yayi da karfi da yaji ya kinkimota tana ihu yasata a gaba suka cigaba da tafiya
Se surutai takeyi ita daya
Tsayawa yayi a wani store ya sayan masu tsaraba kala-kala se suka cigab da tafiya
Suna isa gidansu Ameenah suka fara zuwa dan shine a kusa tayi hauka data shiga gidan se ihu takeyi kwanansu daya amma basu gayan ma su safieyarh bah Mami se ji da ita ake duk abunda tace zataci shi ake bata danta ganta tayi wani kiba ga haske
Ameenah bata gane abunda take nufi bah se wani kwanciya take a jikinta kaman mage
Washe gari suka wuce gidansu Adeel sukaje lokacin safieyarh bata gida dan ta fara zuwa school daddy ya hanata zuwa Abujan Mommy jiki na rawa take tambayan Ameenah me zataci Adeel yace ni baza'a tambayeni bah
"Gafara can ae ita tanada nalura ne"
A tare suka hada ido seya fashe da dariya mikewa tayi a guje ta shige dakin safieyarh
Duka takai mai toh mena dariyan gashi kasata ta gudu
"Wai Mommy kunyi tsammanin tanada ciki ne batada komai fah"
Ban gane batada komai ka sani bansan hauka fah
Shiru yayi kawai yana murmushi
Da safieyarh ta dawo rungume Adeel tayi seta tambayeshi Ameenah dakinta ya nuna mata wucewa dakin tayi tana ihu
Rungume juna sukayi suna ihu take ce mata wai kinsan wani abu
Mommy fa da Mami sun aza inada ciki ne
"Toh bakida shine"
Ke wlh banza ce yaza'ayi kice inada ciki
"Ya ko za'ayi bazan ce bah ji yadda kika kara wani haske gashi kin danyi kiba abunki"
Seta kai hannunta gun cikinta tace kuma fa ya fara girma
Bege mata hannu tayi ta mike tace ke kika sani
Washe gari wuraren karfe 3pm sukayi sallama dasu Mommy
Gidansu Ameenah sukaje suma sukayi sallama dasu akan zasu koma kuka ta fara dakyar aka rabata da Mami danta riketa wai ita bazata koma bah
Suna hanya se shan majina takeyi tana kuka a hankali
branch din office dinsu yaje dan zekai ayi mai signing wasu documents toh basu tashi barin kaduna bah se ana kiran magrib tace mai kawai su koma se gobe da safe su kama hanya amma ya shareshi ta ya cigaba da tukin
Sunyi nisa sosai dan har sun shiga Abujan lokacin har anyi isha an gama
Suna cikin tafiya se sukaga motoci sunata juyowa wasu suna masu nuni da hannu suma su juya ga yan-fashi a gaba
Zare ido Ameenah tayi tace mai su juya mana
Yaki kawai se sukaji harbin bindiga wani ne ya gudu shine suke harbin motanshi har seda suka samoshi
Ihu Ameenah keyi ta tushe kunnanta gabadaya ta burkice se kuka
Sit belt dinta ya cire mata ya dafa mata kafada yace kalleni
Ta dago jajayen idanunta still ta tushe kunnanta da hannunta
_"its okey babu abunda ze faru window motan nan is bullet-proof babu abunda ze faru kinji"_
Still ae zasu iya harbin tires din please kawai mu juya
Saketa yayi ya bude wani abu a cikin motan bindiga ya ciro a ciki
Tana gani ihu ta sake yi ta juyarda kanta tana kallon jefe
"Saka sit belt dinki"
Yace mata nan take ta juyo tace me zakayi
Wucewa mana
Rike mashi hannu tayi tace "i beg of you kawai mu juya kowa juyawa yakeyi"
Murmushi yayi dan duk tabi ta tsorata
Juyarda motan zeyi amma motoci sun cika a bayansu kowa nasan guduwa amma an kasa saboda wannan ya shiga gaban wancan
Daga kanda zatayi kawai barayin sukayo kansu da bindigoji a hanunsu koma motansu shine na biyu
Kawai harbin bindiga suka karaji se sukaji ihun mace aka kara harbawa se shiru koma
Yana jin haka ya maida gun din sit belt dinshi ya cire itama ya cire mata nata dan shock dinda ta sama
Fita yayi daga motan ya zagaya ta gefanta ya fito da ita security yasa a motan kawai yajata suka shige daji
Gudu kawai sukeyi se kuma harbin bindiga se duhu da sukeji sosai
Barayin da sukaje gun motan kokarin budewa suka fara amma sun kasa kuma sun haska duhu kawai suke gani dan haka suka shiga harbin windows din amma be fashe ba se bullet dinda ke manne a jiki
Daga baya duka hakura
Cigaba da gudu sukeyi yana rike da hannunta se bayan sunyi nisa sosai seta tsaya tana maida numfashi tace ta gaji dakyar take magana
Shafa aljihunshi yayi seya ji waya da sauri ya fito dashi ya kunna haske daga ita se dankwali dan atanfane a jikinta toh tabar gyalen ma a cikin motan
Tausayinta yaji sosai network din wayan ya duba yaga babo ku daya
Haska gefansu yayi se kuma ya dawo da hasken gunta zaunar da ita yayi shime seya zauna
Kuka ta farayi tace toh yaza'ayi mu kuma gida yanxin gashi dare yayi
Shiru yayi
Can bayan tadan huta se suka cigaba da tafiya koh zasu sama gida su kwana a ciki se da safe su kama hanya
Sunyi nisa seta rikeshi suka tsaya kawai yankan jiki tayi ta zube
Kamota yayi da sauri kiran sunata ya shiga yi amma shiru
Daukanta yayi kaman baby ya cigaba da tafiyan
Wani dan runfa ya gani seya karasa wurin da dabara ya ciro wayanshi ya haska zama yayi seya kwantar da ita akan laps nashi
Fuskanta kawai yake haskawa
Inda yaga dare haka yaga safe dan kwata kwata beyi bacci bah koh rufe ido ya kasa fuskan Ameenah ya kwana yana kalla she looks very innocent
Da gari ya fara haske har yakaiga yana shafa fuskanta bude ido ta farayi a hankali seya cire hannunshi da sauri
Da fuskanshi ta fara sallama da sauri ta mike zaune gefe ta fara kalla ta tabbatar da ba mafarki takeyi bah
Hawaye ta fara seta kalleshi mikewa yayi yana karkade kayanshi yace toh tashi mu kuma
Babu musu ta mike suka fara tafiya seta zo ta rike hannunshi
Tana rike mai hannun wani abu yaji jirrrr ya tsireshi dakewa kawai yayi suka cigaba da tafiyan
Sunyi nisa se kuma ya tsaya danya manta hanyan da sukabi saboda jiya hanya daya kawai ya gani amma yanzin seyaga biyu
Kallonshi tayi tace meyafaru
"Babu" kawai yace mata
Hanya daya kawai yabi tafiya kawai suke amma shide besan inda suka nufa bah
Sunyi nisa sosai kawai se sukaga katon rafi a gabansu shi kuma ya tabbata jiya bega wannan rafin bah
Kalloshi ta sakeyi tace hala mun bata
Daga mata kai yayi alaman hakane
"Toh wayanka fah ka duba map nama"
Cirowa yayi yana unlocking nashi seya mutu tsaki yayi ya maidashi
Juyawa yayi yace mu kuma semu bi ta dayan hanyan haka akayi sun koma amma basuga hanyan bah sun kara bata haka suka ringa yawo a dajin nan har kusan karfe 3pm
Waje ta sama ta zauna wai ita wlh ta gaji gashi kuma tanajin yunwa
Toh hala namana zan yankan maki na baki
"Its not a bad idea zaka iya yanka ae wlh duk laifinkane daka bari mun sake kwana da duk haka be faru bah"
"Haka kikace koh ae seki kuma gidan da kanki"
Seya juya ya fara tafiya mikewa tayi ta bishi da sauri
Tafiya sukeyi idan sunyi nisa sesu huta se kuma a cigaba duk ta gaji se dingishi takeyi har muryanta ya dashe dan kuka
Juyawa yayi seya ganta tana tafita a hankali tana dingishi tsayawa yayi harta iso gun da yake
Kawai daukanta yayi kaman baby gashi daman batada nauyi batayi musu ba dantasan ta gaji haka ya ringa tafiya da ita tafiya suke amma basu san inda suka nufa ba dan they are totally lost
Ya gaji sosai shima seya sauketa suka zauna
Har gari ya fara duhu basu bar dajin nan bah kuma through out basu ci abinci ba talkless of sallah
Suna tafiya ne akwai dan haske kadan kawai suka fito titi wani ihu tayi danjin dadi
Tafiya sukeyi a titin duk motan dayazo wucewa seya saka hannu yana tsayar wa amma dan tsoro ana zuwa kusa dasu se kaga an kara gudu shi abun har dariya yake bashi.
πππ
[18:57, 3/16/2017] 1D-Tyetyelorh-β£: Can sega wata mota tazo wucewa seta fara tafiya kaman zombie danta tsoratar dasu suna isowa kusa dasu wata mace ce a ciki tana ganinta kuwa seta kara gudu sosai
Dariya ta saki
Shima dariya yakeyi yace idan kika ba kowa tsoro ae se muga inda zamu koma gida.
"Toh yan rainin hankalin sunki tsayawa"
Hannu ya kara sawa amma ba'a tsaya bah
Wani haddan mota ya kara zuwa kallonshi tayi tace karka sa hannu "watch and learn"
Kallonta ya tsaya yi
Wani dan iskan tsayuwa tayi hadda harde kafanta wuri daya seta saka hannu
Ae kowa ba tareda bata lokaci bah ya tsayar da motanshi
Kallon Adeel tayi ta sakar mashi da murmushi
Shi ya kasa motsi ma mamakin abunda tayi kawai yakeyi
Gun motan ta nufa ta gaidashi saurayin ya amsa da fara'a shi yaga yan mata
"Daman lift muke so dan Allah motan mu yana gaba yan fashine suka taremu jiya da daddare shine muka bar motan a dajin nan muka kwana so please ka taimaka mana nida brother nane"
Tana magana tana wani fari da ido inda tasan ze yarda kuma tace yayanta ne saboda ta tabbata idan tace mijinta ne baze yarda bah
Murmushi yayi yace Allah sarki babu komai ko shigo
Godiya tayi mai seta kira Adeel wanda ya sankare yana kallonta kawai
Jawo hannunshi tayi ya shiga gaba saurayin ya bashi hannu suka gaisa ita kuma ta shiga baya suka fara tafiya
Chager ya gani a cikin motan seya fito da wayanshi ya hada 5% yana shiga ya kunna seya kunna GPS dinshi yana anfani dashi wurin neman direction din motan
Sunata tafiya babu me magana a cikin motan Adeel se duban motan yakeyi
Ba'a dade ba sega motoci dayawa a wajan anyi fata fata dasu amma an matsar dasu gefe da alama sujoji sunzo wurin
Cigaba da tafiya sukayi se suka hango motansu da sauri Ameenah tace gashi nan tsayar da motan yayi suka fito glass din motan yadan tsage kadan kadan alaman bullet din bude security na motan yayi
Ameenah godiya tayi ma saurayin yace ze iya samin number ta murmushi tayi charap a kunnan Adeel juyowa yayi yace Mallam da aurenta saboda haka ka wuce kawai
Beyi magana bah yaja motan ya wuce
Shiga motan sukayi wayanta ta fara dauka tayi unlocking missed calls ne baja-baja a ciki
Hadda naso Mami
Kunna motan yayi ya fara tafiya gudu kawai yakeyi dan kar su sake haduwa dasu
Basufi 30mins ba suka shiga gari a wani bakery ya tsaya dan cikinshi har wani kara yakeyi,shi ya shiga ya sayo masu burger da lemo se ruwa
Yana dawowa a tsakinyansu ya ajiye kafin ya tada motan