Showing 63001 words to 66000 words out of 94870 words

Chapter 22 - Umarnin Iyaye Book Complete By tyetyelorh.txt

tana magana kaman zatayi kuka
Beyi magana bah yabita suka shiga dakin Hakeem har a lokacin cewa yake "Ameenah ki dawo dan Allah nasan baki mutu bah Ameenah i love you so much come back and i will take you place "
Da sauri Abbah ya karaso gunshi ya dafashi yana cewa "Adeel!!!! Adeel !!!! Ka bude idonka"
A hankali ya bude manyan idonshi yayi jajir kaman garwashi Safieyarh ya fara kalla fuskan Ameenah kawai yake gani dan haka seya mike da sauri ya sake kallonta still fuskan Ameenah was there dan haka seya kai hannunshi da sauri ya rungumota "Nasan dama baki mutu bah amma duk babu wanda ya yarda matseta yayi sosai"
Sake ihu tayi tace "Ya Adeel it's not Ameenah nice fa Safieyarh" ko sauraranta beyi bah ya cigaba da surutanshi
Tsoro abun ya fara ba Abbah seya mike yayi waje da sauri

Yaki sakinta ita kuma bata fasa cemai ba Ameenah bace
Riketan da ya sakeyi sosai yasa tayi kara da karfi tace "let go of me you are hurting me"
Fuzgan kanta tayi da karfi seya saketa yana kallonta a rude

Rike mashi hannu tayi " Ya Adeel kayi hakuri Ameenah is in a better place kuma nasan aljanna ce makumanta insha Allah saboda batada matsala tana bin UMARININ IYAYENnta and am pretty sure kaima tana bin naka dan haka Ya Adeel kayi hakuri please ka dena wannan abun"

Huging dinta yayi yace "Safieyarh i already misses her i did't had a chance to even say goodbye it's all my fault da tun farko ban yarda ta fita ba da duk wannan abun be faru bah" ya gama maganan yana sake sakin wani kuka itama haka Safieyarh tausayinshi takeji sosai dan bata taba gaininshi a irin wannan halin bah


πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
[10:23, 3/25/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: _30 minutes later_

A lokacin Aunty tana zaune kusada Mami hawaye kawai sukeyi
Adeel kowa haryanzin yana kwance shi kadai a dakin dan Safieyarh ta tafi wani numfashi yake sama-sama yana kallon celin din dakin
Ameenah kawai yake tunani yana hango murmushinta ita kawai take mai yawo a kanshi

A waje kowa duk wanda yazo gaisuwa kaman abokan Daddy da Abbah se sun tambaya ina Adeel yake sumai gaisuwa se ace masu bayida lafiya

Alhaji Lawal shine me company da Daddy ke aiki dan haka shima yazo gaisuwa zama yayi yace "A karanta falaki da Nas kafa uku-uku Allah yasa Ajanna ce makumanta Allah ya jikanta da rahma ya haskaka kabarinta kuma Allah ba iyayenta da mijinta hakuri da juriyan rashinta nasan Ameenah yarinyace me hankali kuma me hakuri da biyaya tunda kowa iyayenta suka zaban mata miji wanda bata sonshi amma tayi hakuri tabi Umarninsu Allah ya saka mata da alkairi "
Ameen kowa ya amsa ya dan kara wasu addu'oi kowa ya shafa ya mike yana sake ma Abbah gaisuwa se can ya tambayeshi ina Mijinta yake yamai gaisuwa

Shiru Abbah yayi can kaman zeyi kuka yace Wlh yana daki baida lafiya
Se hawaye ya fara zubumai "Ya isa rakani dakin namai gaisuwa"

Haka suka tafi Abbah na gaba Alhaji Lawal yana biye dashi a baya
Suna shiga tun daga nesa suka hango numfashin shi was worst yi yake kaman ana zare mai rai

Karasawa Alhaji yayi da sauri yace "Subhanallah" taba temperature shi sukayi jikinki zafi sosai
Tapping dinshi yakeyi amma ya kasa bude idon sosai seya bude kuma ya maida ya kasa tsayawa waje daya
Alhaji ya kalla Abbah yace tayani dagashi mu kaishi Hospital da sauri Adeel yace "aa ku barni nima na mutu nabita Allah ka dauka raina nima wlh na gammace na mutu nima akan rayuwa babu Ameenah nace ku barmin ita zan iya zama da ita a haka but you never listen gara na mutu nima maybe i will have peace but idan na cigaba da zama her death will be hurting me cus it was all my fault da ban barta ta tafi bah....... " se kuka yaci karfinshi

Alhaji yace "ya isa haka mike muje asibiti" yana magana yana kukarin dagoshi shida Abbah amma kwace wa yakeyi kaman karamin yaro daga karshe fuzgan kanshi yayi da karfi dukda yadda yakeji gun mirror yaje kawai seya buga hannunshi a jiki yace "I love you Ameenah" kawai se mirror gabadaya ya tarwatse amma ko a jikinshi
Da sauri su Abbah sukayo kanshi amma kafin su karasu ya zubu da turarukan kai sun zubu a kasa duk sun tarwatse "Ameenah i can't live without you" Alhaji ya kira sunanshi da karfi dan ya dusa inda glass din mirror suka zubu kuma babu takalmi a kafanshi

Ko jinshi beyi bah ya taka su amma ko irin motsin nan alaman ya taka abu beyi bah ya cigaba da tafiya yana cire kafanshi jini ne kawai a wajan

Kanshi sukayo kafin su karasu yayi gun wardrope dayake irin me mudubin nan ne a jiki
"Ameenah am so sorry its all my fault i love you so very much and i will do anything just to be with you"

Gabadaya hannunshi ya daga a tare ya bugasu akan mudubin duk suka fashe hannunshi jini kawai ke zuba
Kallonshi sukayi lokaci daya suka tsaya they were shocked
Daddy,Mami,Mommy,Hakeem da Safieyarh suka shigo a guje dan sunji karan glass din a tare suka tsaya yadda sukaganshi cikin jini dan kafanshi akan glass din yake
Hannu Mommy ta saka akan bakinta yadda taga halinda danta ke ciki

Durkusawa yayi da dauka glass guda daya akan hannunahi ya saka wajan vein (jijiya) dinshi seya maida kallonshi kansu
_"Ni gara na mutu nasan nima ban raye akan na zauna a duniya babu Ameenah, my life is completely useless without her she's my first love and she will be my last love whats the meaning of life without you, You left without saying goodbye Ya Allah menayi maka to deserve this meyasa zaka rabani da matata i love her so much why!!! But its all over now nima zan bita can"_

Glass din ya daura ready to cut his vein
Abbah yace "tsaya Adeel karkayi i beg of you se kace ba musulmi bah kasan makuman wanda yayi commuting suicide kowa"

"I don't care anymore Abbah i seriously don't all i want is to be with Ameenah even for a single secoud" duk cikin kuka yake magana

Cikin kuka Mami tace "Ameenah would not want that am begging you dan Allah karkayi lets not loss you too please"
Girgiza kai yakeyi kawai ya kasa magana
"Ya Adeel dan Allah karkayi she's in a better place kuma Allah ya fika sonta shiyasa ya dauka abunshi dan Allah karkayi"

Mommy da Daddy sun kasa cewa komai da Hakeem se hawaye da sukeyi
Kafin kowa ya ankara harya yanka sakin piece of glass din yayi se jiri ya fara kwasanshi

Kurma wani uban kara Mommy tayi sukayi kanshi dukka amma kafin su karaso harya zube kaman matattace
Durkusawa Mommy tayi akan glass din ta daura kanshi akan cinyanta tana wani irin kuka
Da taimakon Alhaji suka kinkimeshi masu zaman makoki se leki sukeyi

Waje aka fito dashi a cikin Motan Alhaji dayake drivershi yana ciki a baya aka saka shi Mommy itama ta shiga tana kuka sosai cus she can't help it
Gaban Alhaji ya shiga dayan gefan
Driver ya tada motan da sauri sukayi asibiti dashi jini ne kawai ke zuba a hannunshi
Babban rigan dake jikin Alhaji ya barkeshi ya juya daure mashi hannun yayi

Suma kuka sukeyi sosai Abbah ya shiga motanshi shida Hakeem suma suka bisu a baya while Daddy,Mami da safieyarh suna gidan dan masu zuwa gaisuwa kuka kawai safieyarh da Mami keyi

Dayake Auntie da mijinta suna waje basusan abunda ke faruwa bah suna ganin an fito da Adeel cikin jini kaman gawa
Kuka Meemah ta saki wai meya faru da Uncle Adeel dinta rungumeta Daddynta yayi
Auntie kuka ta saki itama tayi ciki wajan Mami tana tambayanta abunda ya faru anan ta kwashe komai ta gayan mata tana kuka



IG.Tyetyelorh
[15:43, 5/6/2017] Rrspectable: [18:28, 3/23/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹UMARNIN IYAYEπŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

WRITTEN BY:
TYETYELORH

EDITED BY:
AMEENATOU

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

*123*

Su Daddy gida suka wuce (gidansu Ameenah) da Ambulance din har a lokacin Hakeem yana dafe da yar uwarshi yana kuka yan cikin motan harsun gaji da bashi hakuri duk sunyi shiru
Gawan aka fito da ita me gadi yana ganin an shigo da gawa ga kuma Hakeem na faman kuka ga Daddy shima yana hawaye seya fashe da kuka yana " Innalillahi wainna'ilaihirraji'un Alhaji lokaci daya zaka tafi ka barmu"
Babu wanda yabi ta kanshi shiga da ita cikin dakin Abbah akayi a lullubeta
Fitowa sukayi Hakeem ya sama waje ya zauna kusa da yar'uwar shi kuka yakeyi sosai har a yanxin yana dafe da ita yana kuka while a zuciyanshi yana hada mata da addu'a kuma yana blaming kanshi wai duk lefinshi ne

Police din shiga Amblance sukayi suka kama gabansu
***********

Abbah beyi kwari a gwiwa bah ya cigaba da kiran number nata idan nashi ya shiga sena Adeel shima ya shiga haka suka ringayi can se doctor ya leko ya kirashi akan matanshi ta tashi mikewa yayi da sauri ya shiga dakin
A kwance ya sameta tanata faman ajiyan zuciya fuskanta ya jike sharkaf da hawaye karasawa yayi kusa da ita da sauri ya dafa ta
Kafin yayi magana se tace "Alhaji an dauko gawanta"
Dumm!! Yaji kirjinshi ya buga "Gawanta kuma" ya maimaita
Cire hannunta yayi daga jikinshi seya fara baya a hankali "Kema kim yarda ta mutu No!! Ameenah tana nan Ameenh bata mutu bah she's too young to die this not right No!!! Please Ameenah bata mutu bah"
Se yayi waje a guje mikewa tayi itama ta bishi da sauri
Suna shiga har a lokacin Mommy da safieyarh suna kuka kaman ransu ze fita tsayawa yayi yana kallonsu hawaye ne ya fara zubu mai kama hanya yayi ze fita Mami ta rikoshi itama tana hawaye "Alhaji ina zaka"
"Dauko maku Ameenah zanje nayi ku ganta dan bata mutu bah"
Mommy ce ta mike dakyar fitowa tayi kuma se duk suka biyota da doctor suka ci karo a bakin kofa
"Lafiya ina zaku haka dukkanku"
Bude gefan jakanta Mommy tayi credit card dinta ta ciro mika mashi kawai tayi danta san kudinsu yakeso
Beyi magana bah ya amsa saboda ba a wannan asibitin suka buse file ba a Giwa suka bude toh abunda ya kawosu nan shine dan yagi sauri yakeyi lokacin Hakeem a rude yake
Bata jira yayi wani magana bah ta wuce Mami na rikeda hannun Abbah suka bita while safieyarh na biye dasu itama a baya

Gun packing mota suka tsaya Abbah na kokarin ciro key ya shiga Mommy tace ya bata key din danta san baze iya tukawa bah
Mika mata yayi kaman robort
Goge hawayenta tayi seta amsa shiga tayi safieyarh ta shiga gaba Mami da Abbah kuma suna baya kwantar da kanshi yayi akan kafadanta kaman karamin yaro yana hawaye itama tanayi

Tada motan tayi suka fara tafiya
Kuka safieyarh keyi mara sauti sosai wayanta ta ciro messege ta farayi cewa Ameenah ta rasu a yau dinnan marking number Ameerah,fatye da Ummitarh tayi ta masu sending

Motan shiru se shan majina da kowa ke faman yi a cikin motan
Suna isa gidan har mutane sun cika dan dayawan mutanen unguwa sunji karan Ambluance dan haka aka leko se kuma sukaga an shigar da gawa
Wani wawan kuka Safieyarh ta sake saki
Gabadaya suka fito

Daddy ya rike hannun Mami se kace karamin baby
Cikin gidan suka wuce se kallon Abbah akeyi dan acikin 100% na mutanen gidan toh 80% duk sun dauka Abbah ne ya rasu basu kula kowa bah suka hau sama a zaune suka tarar da Daddy yana dafe da kanshi
Dagowa yayi da yaji motsin mutane fuskanshi sharakaf da hawaye
Kasa magana Abbah da Mami sukayi suna kallonshi kawai
Karfin hali yayi seya nuna masu kofan dakin kawai

Shiga sukayi dukkansu hadda shi a hankali Abbah ke tura kofan Hakeem ya fara hangowa ya rungumeta yana kuka amma ba'ajin komai dan muryanshi ta gama dashewa
Mami ce ta karasa gunta seta yaye abunda aka lullubeta dashi tana ganin fuskan a kune yake
Fashewa tayi da kuka se tayi waje a guje
Safieyarh kowa tana makale a jikin bangon dakin tana rera nata kukan Abbah kowa ya kasa komai yana tsaye kawai

Can ya kalla Daddy daketa kallon Hakeem yana share hawaye yace "Alhaji Adeel kowa ya sani?"
Girgiza mashi kai yayai alaman be sani bah dan haka se yace "Toh a kirashi ace ya dawo gida yanxin dan yayi ma matanshi addu'a kafin akaita final destination dinta"
Kallon Hakeem yayi yace "jeka kira liman"
Be tsaya yaji amsanshi bah ya fita daga dakin

Daddy yace ma Hakeem dake niyan tashi yana share hawaye " bari zan kirashi" seya fita
Wayanshi ya ciro kan Number Adeel har ze kira se kuma ya tsaya yana kallon number kawai ya kusan 10mins yana kallon number kawai se finally ya kira

Lokacin Adeel harya gaji da kiran number Ameenah ya kira na Hakeem shima yafi sau 10 be daga bah na safieyarh shima ya ringa kira bata dauka bah saboda wayan a silent yake toh se jikinshi ya fara bashi babu lafiya ya kira Number Mommy itama thesame answer dan haka kawai seya kulle gidanshi ya fito dagashi se wayanshi da passport dinshi se credit card

Airport ya nufa dan zuciyanshi na ayyana mashi kawai Abbah ya rasu yana isa Airport din jet ya sama wanda ze kawoshi kaduna direct (shata kenan inji mama πŸ˜‚)
Harya shiga sunyi nisa se wayanshi ya fara kara da sauri ya duba yaga manager shi dan yau da yamma yanada wani match din guntun tsaki yayi amma be daga bah
Yana gama ringing harzesa a Airplane mode seya kara ringing amma wannan karan Daddy ne
Da sauri ya dauka a kunne ya kara yace "Daddy"
"Uhmmm ka taho gida yanxin"
Gabanshi ne ya fadi dumm!!! "Lafiya Daddy? Meyafaru?"
Ka taho de kawai kuma meye zaka gani kuma kazo kaduna ne gidan Abbah ku.
Dumm!! Ya sake fadi
Daddy be tsaya yaji meze ce bah kawai yayi hanging up
"Innalillahi wa'inna"ilaihirraji'un " abunda ya fadi kenan a fili "Allah sarki Ameenah only god knows halin da take ciki yanxin i really want to be by her side right now" tunanin da yakeyi kenan yana ji kaman ya bace ya ganshi tare da ita
Kwantar da kanshi yayi a jikin sit din idonshi a kulle kawai se wayan ya sake ringing dagowa yayi ya duba kan screen din still it was his manager
Dugan tsaki yaja seya kashe wayan gabadaya ya saka a aljihu ya kumar da kanshi inda yake da yana tunanin yanzin dukka family kowa na nan shine kadai agogon hannunshi ya dago ya kalla seya leka window "God" ya fadi a fili gabadaya ya kago yaga sun isa ji yayi dama tun farko beyi wannan tafiyan bah "Mteww" ya sake jan wani

*********
Abbah daya fita daga dakinshi dakin Ameenah ya wuce yayi sa'a a bude yake dan da safe Mami ta bude ta dauka abu
Yana shiga ya maida kofan ya rufe hadda saka key
Kawai sake wani kuka yayi seya durkusa a kasa "How he wish all this was a dream ji yake dama shine ya mutu ba Ameenah ba cus she has a life ahead of her"

Kuka yake rerawa kaman yaron shekara 10 wanda mamanshi passed away recently

_Some hours later_

Lokacin har anyi mata wanka an sakata a likafani Hakeem na ganin haka kaman a mafarki kuka ya sake fashewa dashi yace "Be kamata a sata cikin wannan abun bah wlh bata mutu bah Ameenah is still alife bacci takeyi wlh bacci takeyi karku dauka hakkinta ku kasheta Ameenah please ki tsaki ki gayan masu ba mutuwa kikayi bah zasu kasheki da ranki fah"
Sanbatu yakeyi wasu ma gani suke kaman ya fara taubuwa Daddy ne ya kama hannunshi dakin Mami suka shiga ya zaunar dashi bakin gado kwantar mashi da hankalinshi ya farayi but it does'nt work shi kawai so yake yaga sistershi ta mike

Adeel ne ya sauka a Airport din kaduna taxi ya samo ba tareda bata lokaci bah ya shige koh ciniki basuyi bah
Saka shi yayi ya zinga gudu a titin nan kaman wanda saku haura sama.


πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
[21:36, 3/23/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: Suna isowa bakin layin motoci ne a cike a layin
Har kofan gida taxi driver ya ajiyeshi ya fito da sauri harze shiga cikin gidan driver yace mashi kudinshin fah
Dawowa yayi kawai ya cire designer watch dinshi ya mika mai dan koh biyar bedashi a hannunshi credit card dinshi ne kawai
Be tsaya jin me zece bah ya shige gidan
Motane ne cike a gidan tun daga bakin gate din aka fara mai gaisuwa
"Allah jikanta Allah sa ta huta"
Kallonsu kawai yakeyi amma beyi magana bah dan kanshi ya daure
Cikin mutane ya ringa shiga se "Allah jikanta" ake cemai amma se yayi ignoring dinsu

Sama yahau kawai se yaga Abbah ya fito daga dakin Ameenah
Wani wawan firgita yayi tsayawa yayi chak a wajan ya kasa motsawa

Abbah na ganinshi da sauri ya karaso yayi huging dinshi yana hawaye
Har a lokacin yana tsaye kaman kendil and ya kasa huging nashi back
Dagowa yayi ya kalleshi irin kallon da yake mai ya tabbata shima ya aza shine ya rasu girgiza kai yayi yana shafe hawaye seya wuce inda gawan yake dan yayi mata addu'a
Binshi da kallo yayi kawai ji yayi an fada jikinshi ana kuka juyawan da zeyi yaga Safieyarh tana kuka tana cewa "Ya Adeel, Why would this happen to her she don't deserve it"
Dagota yayi yace waye wai? Meke faruwa? Wait ina Ameenah take batazo bane

Kuka ta sake fashewa dashi ta kasa magana kawai sega Ameerah ta shigo tana hawaye gunta taje tayi huging dinta sunata kuka abun tausayi

Kallonsu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login