Showing 66001 words to 69000 words out of 94870 words

Chapter 23 - Umarnin Iyaye Book Complete By tyetyelorh.txt

yakeyi gabadaya kanshi ya dagule ya rasa tunanin me zeyi wai ina ma Ameenah take
Dakin da yaga Abbah ya shiga nan ya nufa jiki a sanyaye yanxin kuma seya fara tunanin koh Mami ce ta rasu
Tura kofan yayi se yaga Daddy ,Mommy, Mami da Hakeem a ciki da kuma Abbah daya juya ma kofan baya yana durkushe kaman mutum a gabanshi

A tare gabadaya suka juyo suka kalleshi banda Abbah
Dukkansu kuka sukeyi kallonsu shima yakeyi
Mami ce ta mike da sauri ta rungumeshi tana wani kuka ita kwata-kwata batayi wani kuka sosai ba seda taga Adeel kawai se taji tausayinshi

Chak ya tsaya can yace Mami ina Ameenah take ko bata iso bane har yanxin
Kuka duk suka sake sekewa a lokaci daya
Kwace kanshi daga runguman da Mami tayi mashi yayi yace "Can someone just tell me what the fuck is going on here why do you people keep crying and where the hell is my wife"
magana yake a tsawa ce abunda be tabayi ma babba ba kenan gashi kuma harya kaiga yima iyayenshi

Hakeem ne yace gatanan ya nuna mai gawanta
Kai kallonshi yayi zuwa inda ya nuna mai seyaga Abbah gaba ya karayi for better view mutum ya gani a lullube cikin likafani
"No!! No!!" Ya fada da karfi karasawa gun yayi da sauri se kuma ya tsaya can ya cigaba da tafiya daya isa gun durkusawa yayi a hankali yakai hannunshi ya yaye fuskanta
Kauda fuska yayi da sauri "No!! This not Ameenah wlh ba ita bace Ameenah fa yanxin zata iso ba ita bace wannan ba ita bace ita fah bata iso bah wlh bata iso bah No!!! You can't do this to me " seya saki wani kuka me tsuma rai kaman ba namiji bah

Mommy ce ta taso ta rungumeshi itama tana kuka
"Mommy kema kin yarda itace wlh ba ita bace ku dena mata kuka Ameenah bata rasu bah nasan bazata tafi ta barni bah you can't just live ki tashi ki gayan masu baki mutu bah i have so much to tell you bazan iya rayuwa ba tareda ke bah " kuka ne yaci karfinshi

Abbah ne ya taso ya rikeshi yana cewa "Adeel addu'a ya kamata kayi mata ba kuka ba saboda haka ya isa haka kuzo muje muyi mata sallah" karfin hali kawai yakeyi shima din
*******

An riga anyi mata sallah an ajiye ta akace family ta suzo suyi mata addu'a kafin akaita makwancinta haka akayi daga kan Abbah aka fara
Ya dade yana mata addu'a yanayi yana kuka Mamai itama tayi mata tasha kuka majina baja-baja a fuskanta
Se Daddy shima ya dade yana mata Mommy itama tazo tayi nata
Se Hakeem durkusawa yayi ya dade yana kuka kafin yayi mata addu'a sosai se safieyarh ita kasa addu'an tayi kuka kawai takeyi kaman za'a cire mata rai Mommy ce tazo ta dagata

Adeel shine karshe yana durkuse kusa da Mami yama kasa kuka binsu yake da ido kawai Daddy yace yaje yayi ma matanshi addu'a kafin akata makwancinta na hakika

Dakyar ya mike yana zuwa gabanta ji yayi wani kuka ya kwace mashi se kawai ya rungumeta kaman ze sata a ciki kuka yakeyi kaman ba namiji bah riketa yayi gagam

Dakyar ya saketa still yana kuka addu'a yashiga yi mata kusan 30mins yana mata addu'a sosai yake kuka
Matan wajan suma kuka suka shigayi saboda tausayi

Anzo daukanta dayake daman an sakata a makara
Riketa yayi yace kar wanda ya taba mashi matanshi ze cigaba da zama da ita karwanda ya tabata
Kuka yake abun tausayi shima haka su Hakeem da safieyarh
Abbah ne ya rikeshi yana bashi hakuri kan cewa ya bari a tafi da ita kwace jikinshi yayi da karfi
Yayi kan gawanta "Ameenah dan Allah ki mike ki tashi karsu tafi dake i love you so much wlh idan kika tafi kika barni zan kashe kaina na gwammace na biki mu tafi tare Ameenah ki tashi karkiyi min haka please"

Kukarin daukan gawan suka farayi Abbah yana hawaye yana kukarin rikeshi " Abbah dan Allah am begging you guyx ku barmin matana wlh zan iya zama da ita a haka ku barmin ita karku rabamu"

Su Mami kuka sukeyi sosai dan ya mugun basu tausayi kallon Daddy yayi seya je gunshi da sauri ya rikeshi "Daddy kayi masu magana su barmin matana zan iya zama da ita a haka wlh Daddy zan iya mutuwa idan suka tafi da ita"
Abbah ne ya bada izinin a tafi da ita Hakeem yana kuka yazo ya rike Adeel
"Hakeem kaima hadda kai kaima zaka bari a tafi da ita am really disappointed in you" juyawan da zeyi kawai yaga sun wuce da ita hadda Abbah da Daddy kama hanyan binsu yayi su Mami suka rikeshi suna bashi hakuri kallon gawan ya sakeyi kawai seya zube a kasa .....



IG.Tyetyelorh
[15:43, 5/6/2017] Rrspectable: [14:40, 3/26/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹UMARNIN IYAYEπŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹


WRITTEN BY:
TYETYELORH

EDITED BY:
AMEENATOU

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

_#I give zero fucks and i got zero chill in me_❣


*125*

_Some minutes later_

A lokacin su Afra sun iso layin dayake taxi suka sama Mama ce ta zauna a gaba tana hango mutane a kofan gidan kuka ta saki kawai
Afra ce ta fara tambayanta meyafaru shiru tayi still batayi mata magana bah
Parking taxi driver yayi yace gaskiya mota bazata iya wucewa ba daga nan dan haka bari ya taya su shigar da kayansu

Fitowa sukayi ya bude trunk din ya fara fito da kayan suna gaba yana binsu a baya
Jikin Afra da Afreen de ya fara sanyi da suka shiga gidan dan se kuke-kuke ake famanyi
Mama tana hango Mami aguje taje ta rungumeta suna kuka
Kallon juna twins suka se kuma suka maida kallonsu gunsu Mami
Can da suka saki juna se Afreen taje gun Mami ta rike mata hannu tace "Mami meyafaru wai meyasa kuke kuka meyasa kowa ke kuka?"
Itama ta rike mata hannu tace "Afreen ,Ameenah ce.Ameenah ta tafi ta barmu"
Da sauri Afra ta motsu kusa dasu "Mami what do you mean by that?"

"I mean Ameenah left us she left all of a sudden she's too young to die" ta gama tana kuka
Mama ce ta riketa tace Mami ke dena irin wannan maganan "kullu nafsin za'ikatul maut" so duk kankantan yaro dole ya mutu

"No!! Noh!!! Munyi da ita fah zamuzo why?? Meyasa zata tafi" seta fashe da kuka Afra ce me wannan maganan durkusawa tayi a kasa suka hada kansu itada Afreen suna kuka sosai
Durkusawa Mami tayi ta rungumesu tana tapping bayansu
While Mam tana tsaye ta saka hannunta akan baki tana hawaye
Shide driver ya gama ajiye masu kaya dayaga alaman rasuwa akayi seyayi masu gaisuwa ya tafi


Acan hospital din kowa Adeel rai a hannun Allah dan sun isa akayi emergency ward dashi abunda Alhaji yayi using ya daure mashi hannun dashi har ya kuma jajir dan farar shadda ce
Kuka Mommy keyi sosai Alhaji yana bata baki sesu Abbah suma suka iso
*******

Doctor ne ya fito da sauri sukayi kanshi suna tambayan jikinshi murmushi yayi "Allah de ya taimaka cut din da yayi be taba vein din nashi bah dan haka fatan hannunshi ne kawai ya yanke so yanxin de munyi mashi alluran bacci kuma an dinje wajan saboda yana cikin tashin hankali se maganganu yake akan...... Ameenah ryt ita"

Girgiza kai sukayi Alhaji ya mika mai hannu sukayi musabaha "toh mun gode sosai doctor yanxin mahaifiyarshi zata iya shiga ganinshi"

"A zata iya amma please kar ayi surutu sosai yadda ze huta sosai"
Mommy da sauri ta shige dakin
Su kuma suka dan zauna suna jiran ta fito dan kar suyi yawa a ciki
Tana karasawa bakin gadon kallonshi tayi har ya rame kaman wanda yayi kwana biyu yana jinya
Gashinshi ta shafa tana hawaye she really can't afford losing him
Ta dade a haka seta share hawayenta ta leko dan haka suma suka shiga sun tausaya mai sosai kuma haka ya tabbatar masu cewa yana son matanshi

_Two weeks later_

Kwanansu Adeel biyu aka sallamesu maimakon suyi gida se suka kuma gidansu Hakeem acan suke kwana dukkansu hadda Daddy
Su Afra ma anan suke kwana a cikin dakonan dake kasa
Yanzin Adeel ko magana bayayi be fitowa daga daki se daki anan yake sallah abinci ma ya yaye shi se idan Mommy ta sashi a gaba tana kuka yake ci duk ya gama lalacewa ya kare a lokaci daya kwata-kwata be bacci yana kwantawa tou dole yayi mafarkin Ameenah koma ya ringa kiran sunanta kenan

Idan Hakeem ya shigo dakin binshi yake da kallo yake kawai idan ya mashi magana kuma kaman da gwinki yake magana shi jiran mutuwanshi kawai yakeyi dan his life is totally over and is useless without Ameenah

Manager shi ya ringa kiran numbershi na can amma baya shiga ya fara trying na Nigeria shima thesame answer danshi yanxin ko wuka za'a saka mai a wuya ace ya gaya inda wayanshi yake bazeniya gaya bah
Da ya gaji seya kira na Daddyshi anan ne yake gayan mai ae Matanshi ta rasu ne
Yayi amshi ta'aziya bayan kwana biyu ya debo team mates dinshi dukka hadda ugansu da kadan daga cikin yan dayan team suka zo mai ta'aziya dukda kusan dukkansu arnayene dan a cikin 10% toh 8% duk kafirai ne 2% ne kawai musulmai

Duk sun tausaya mai yadda ya koma kwanansu daya suka koma
Office dinsu ma sunzo gasu Zaid da Fa'iz duk sun mai kara
Kuma duk wanda yazo sede kawai ya bisu da kallo be magana kaman kurma toh haka ya kuma duk wanda yasanshi a da toh idan ya kalleshi yanxin seya tausaya mai sosai


Dangi da sukazo daga gari daban-daban duk sun koma amma su Afra suna nan Baban su ma yazo lokacin anyi bakwai a washe gari ya kuma

Daddy ya yanke hukunci su kuma gida haka akayi duk suka shirya suka koma tun randa suka koma da Adeel ya shiga dakinshi yayi lockin be sake fitowa ba kwananshi biyu Allah kadai yasan me yakeci randa ya fito ma dakyar ya fito seda Mommy da safieyarh suka zauna a bakin kofan dakin suka ringa kuka sannan yazo ya bude ya kuma ya kwanta yana sana'arshi wato tunanin Ameenahshi
Cire keys din Mommy tayi ta tafi dashi

Da abun ya ishe Daddy masallatai ya saka aka ringa mashi addu'a sannan ruwan shan Adeel ya kuma ruwan rubutu da zam-zam amma dukda hakan ba nasara se kara tsotsewa yakeyi

Wata rana duk suna zaune a parlo Daddy suna shawaran akan abun Adeel se kawai suka ganshi ya shigo parlo kallanshi sukeyi da mamaki harya zauna
"Daddy daman inason kumawa Abuja ne dan nafison zaman can"

"Habah Adeel ae be kamata ka koma can ba kai kadai mukasan abunda zaka ma kanka a gaban mu ji abunda kayi balle ace kasan babu kowa sede gawanka ae" Daddy ne ke wannan magana
Dukar da kanshi yayi kawai beyi magana bah

Wa'azi suka shiga mai akan ya dugara ga Allah dan wannan JARABAWA CE wata kila Allah yana shirya mai wani abu ne anan gaba
Bece kala bah har suka gama ya mike ya kuma dakinshi Qur'ani ya dauko ya ringa karantawa da kira'arshi me dadi ya kusan Two hours yana karantawa daga baya ya kulle addu'a ya ringa ma matanshi dan ya saba tun randa ta rasu haka yake mata

_One month later_

Yau watan Ameenah daya da sati biyu da rasuwa
Har a lokacin Maman Afra sunki komawa Abbah yayi fadan harya gaji kusan kullum se Alhaji yazo shida wani danshi me suna _Marwan_ sun gaisa da Abbah sannan yaje ya gaida Adeel dan yana tausaya mai sosai

_Marwan_

Yarone dan shekara 22 kyakkawa ne sosai gashi kuma fari kaman balarabe dansun hada jini da larabawa saboda mahaifiyarshi balarabiya ce dan Alhaji Lawal bame zama waje daya bane yana tafiye-tafiye sosai saboda haka a dubai suka hadu da ita har sukayi aure dan haka ya saya gida a can yana xama da ita idan akayi hutu kuma sesu dawo gida har wata rana ta sama juna biyu
Ciki yayi girma ya isa haihuwa
A randa ta haiwa ta haifa danta namiji lafiyaye kafin ta daukeshi ta rasu Alhaji yayi suka kaman yayi hauka dan haka ya dauka Alkawari ze zame ma Marwan Uwa da kuma Uba baze taba neman abu a gunshi ya rasa ba kuma baze taba rashin uwa ba

Dan haka Marwan ya taso cikin so da kauna ga ilimin boko dana arabiya duk ya sani be taba kukan rashin Uwa bah amma yana mata addu'a sosai
*******
Ranan da Daddy yaje yaga yadda Adeel ya kuma har hawaye ya zubar mashi saboda haka ya zauna yayi tunani toh meze hana ya sake aure koh abun ze ragu
Da wannan tunanin ya sama Daddy shima yaji dadin shawaran nan haka duk aka zauna meeting hadda Safieyarh da Hakeem se Mamansu Afra
Amma banda twins

Kowa ya yarda da shawaran
Abbah yace shi harya saman mai mata a take kowa ya tambaya wacece ita
Yace "Afra"
A take gaban Mama ya fadi dan tasan kowa ze yarda amma ita Afra bazata taba yarda ba saboda tana bala'in son salman
Kallonta kowa keyi amma ita hankalinta baya wajansu
Mami dake kusa da ita tace lafiya kikayi shiru
"Aa babu komai zan kira Babansu anjima sena gayan maku yadda yace"

"Toh shikenan Alhamdullilah" Daddy yace yana jin dadi


πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
[15:58, 3/26/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: ***
Wuraren karfe takwas na dare Maman Afra ce ke kwance da waya a kunnenta tana waya da Babansu bayan yan gaise-gaise take gayan mashi halin da ake ciki
dan dumm yayi se kuma yace toh shikenan ae shima Babanta ne yanxin kin tambaya ta bakinta ne??

"Aa daman nafison idan ka yarda sena tambayeta nasan zatayi musu da UMARININ IYAYEnta bah"
"Toh shikenan ki bita da lallama ne dazin ma Abbah ya kirani yake gayan min toh amma nace mashi zanyi shawara. yanxi barin kirashi na sa'anar dashi daman na aza beyi maki magana bane"

Toh shikenan seda safe haka sukayi sallama ya kira number Abbah ya gayan mashi babu komai duk rannan da aka saka se a kirashi a gayan mashi da haka sukayi sallama
Abbah ba karamin dadi yaji bah

Hakeem kowa soyayya sukeyi sosai da Safieyarh yanxin kuma suna zama ayita wasa da dariya dasu Afra amma shi gabadaya abunda aka yanke na hadin auren nan shi beso bah besan dalili ba amma abunda ya sani kawai beson ayi wannan auren (ze taya yar'uwanshi kishiπŸ˜‚)

An sake taruwa amma wannan karan iyaye ne kawai aka yanke nan da two weeks (ya zama 2 months kenan da rasuwan Ameenah)
Aka kira Babansu Afra aka fadan mashi yace toh Allah sanya Alkairi ana gobe daurin aure zezo dan yanada aiyuka dayawa a gabanshi
*******

Daddy ne da Mommy a parlo suka aika Safieyarh akan ta kira Adeel
Tana shiga dakinshi a gaban dadduma ta sameshi ya gama sallah isha'i yanata addu'a hadda hawaye a idonshi zama tayi a kusa dashi harya zama addu'an ya shafa itama ta shafa
"Ya Adeel Daddy yace kazo zasuyi magana dakai"
Daga mata kai yayi kawai ta mike har zata fita seta dawo "Ya Adeel nasan kanason Ameenah but she's in a better place Allah ya fimo sonta shiyasa ya dauka abunshi but abunda take bukata a wurin mu yanxin shine addu'a shi kawai take bukata and ka sani we are all here for you we love you so much"
Daga mata kai ya sakeyi dan yasan yana magana kuka ze iya saki koma beson yayi kuka agaban kanwanshi (daga baya kenan)

Tashi tayi tayi huging dinshi seta fita
Hawaye ne kawai ya fara zubu mai kaman ruwan fanfo dakyar ya samo ya tsaya seya mike ya fito a hankali yake tafiya abun tausayi fuskan nan kowa har gemo ya taro sosai daman gashi da dan banxan gashi kaman mace

Yana isa besan dalili bah kawai se gabanshi ya fadi saboda kallon da suke mai samin waje yayi jiki a sanyaye ya zauna "Daddy gani"

"Yawwa daman kiranka mukayi dan na sanar dakai wani abunda muka yanke kuma nasan zaka bi Umarnin mu kaman yadda kabi a baya"
Kirjinshi ne ke bugu da saurin gaske amma be dago ba balle yayi magana

Daddy ya cigaba "Adeel mun gaji da ganinka haka kalla yadda ka kuma kaman ba kai bah munsan kana son marigayiya amma Allah ya fimu dukka sonta dan haka mun yanke hukuncin hadaka da Afra
Dagowa yayi da sauri ya kalla fuskanshi seya kalla fuskan Mommy sena Safieyarh duk shi suke kalla Safieyarh kowa har hawaye ya cika a idonta

"Haba Abbah so kuke ku kasheni bakujin tausayina yau kwata kwata ko wata biyu Ameenah bata shiga da rasuwa ba but you want me to get MARRIED AGAIN dan Allah ku taimaka min ask for something but not this anything zanyi maku but please banda wannan"

Shiru sukayi gabadaya suna kallonshi
Matsuwa yayi kusa da kafan Daddy ya rike gam yace "Daddy, Mommy dan Allah karkuyi min haka ku taimaka min ku barni a haka har nima na kuma ga ubangiji na idan bakusan zamana ne a gidan zan kuma can Abuja nayi zamana ni kadai harse Ameenah ta dawo Amma dan Allah i beg of you ku taimaka ku barni a haka wlh idan akayi auren nan dukkan mu wiya zamusha dan ni wlh bazan taba son wata mace bayan Ameenah bah and i believe wata rana zata dawo min wlh akan ku aura min wata gara ku kasheni"

Tashi Safieyarh tayi a guje tabar parlon tana kuka sosai saboda itama bata son auren kwata kwata
Mommy itama a lokacin kuka takeyi she can't bare to see her son suffering this way
Saukowa tayi ta rikeshi

"Adeel

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login