Showing 27001 words to 30000 words out of 88489 words

Chapter 10 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2066

ta shiga juya ta har Hamida ta fito daga ɗaki ta karɓi wayar a lokaci ɗaya ta karɓi kiran, bayan ta gama sauraron abin da ya faɗa ta sauke ajiyar zuciya, da guntun hawaye maƙale a idonta ta kafe Bintoto da kallo tana nazarin mafita. Saboda maigidan ne ya kira yana jaddada mata Bintoto ta bar gidan kamar yadda ya faɗa tun kafin ya dawo.

"Ke kam kin fi mijinki hali mai kyau. Dubi ki gani kallon da kika kunna mini ma yana shigowa ya kashe shi."

Zancen Bintoto kenan tana kallon Hamida da ko ƙiftawa ba ta yi. Hakan ya bai wa Hamida damar yin magana cikin sanyin jiki ta jawo wayarta ta kira Hajiya. Ringing biyu ta ɗauka suka sake sabuwar gaisuwa kafin ta sanar da ita abin da faru. Saboda har cikin ranta Hamida Bintoton ta kwanta mata, don zuciyarta ta tabbatar mata tsautsayi ne kawai ya jawo ta buge yarinyar ba da gayya ba. Hajiyar ma ba ta goyi bayan barin Bintoto gidan ba, domin kai-tsaye ta ce ta bar ta da shi za ta kira shi a waya.

Bayan ta sauke wayar ta miƙa kallon ta ga Bintoto da ta gama sakin baki tana sauraron abin da suke tattaunawa, a zuciyarta tana faɗin,

'Kambu! Ai wallahi babu ta yadda za a yi na bar gidan nan ni kam. Ya dai yi haƙuri ko Kandala ta ce haƙuri take yi da ni ba don tana son halina ba.'

Amma a fili ta ɓata fuska bayan ta cire tagumi ta isa gaban Hamida ta kai gwiwa ƙasa tamkar mai neman gafara tana cewa,

"Ni dai don Allah ki ƙyale mijinki ki sake kunna mini kallon kada su ɗauke waƙoƙinsu."

Wani kallo Hamida ta yi mata babu shiri ta saki 'yar dariya sannan ta ce, "Waton ke ta kallo ma kike yi ba ki damu da an ce ki bar gidan ba?"

"Ai ke ba za ki raba ni da gidan nan ba, don Allah ma ya sani ban so yarinyar ta ƙwale kanta ba saboda Allah ma ya sani har na fi shi son ta."

Miƙewa Hamida ta yi tana faɗin, "Sai ki ba shi haƙuri idan ya dawo na san zai haƙura. Amma ki kiyaye gudun matsalar ta sake faruwa."

Tana faɗar haka ta shige kitchen, Bintoto ta taɓe baki cikin murya ƙasa ta ce,

"Ai wallahi ni ko sai dai ya mutu idan aka ce sai na ba shi haƙur...hu'um! Kuma ni wallahi ba zan bar gidan ba sai dai ya kashe n..."

Zumbur ta miƙe jikinta yana rawa ta taryi gaban Hamida. Saboda ganin ta da plate shaƙe da shinkafa da miya har da kifi a sama. Bakinta a washe ta miƙa hannu tana cewa,

"Don Allah kawo na kai miki inda kike so kada ki wahala."

Hamida tana 'yar dariya ta sakar mata plate ɗin tana faɗin, "Naki ne ai, ki je ki ci zan shiga wanka kafin ya dawo mu ga yadda za a yi."

Bintoto baki har kunne ta karɓe plate ɗin, har da 'yar rawarta ta isa tsakiyar falon ta zauna saman carpet tana waƙe-waƙenta tana zuba loma. Don cire cakalin da ke ciki ta yi ta tsoma hannunta kamar yadda ta saba. A haka maigidan ya dawo gidan ɗauke da yarinyar, yana ido biyu da Bintoto dumu-dumu da abinci ya watsa mata muguwar harara ya wuce fuu zuwa ɗakinsa.

Mintuna a tsakani Hamida ta fito daga wankan da ta shiga ta yi ɗakinsa. Inda ta tarar da yarinyar a kan gadonsa sharkaf tana barci har da sauke ajiyar zuciya wata bayan wata. Cikin sanyin jiki ta fara magana a tsorace tana cewa,

"Don Allah ka yi haƙuri yarinyar can ta zauna Baban Baby. Saboda 'yar aikin da Hajiya ta kawo mana ce domin ta kula mana da Baby. Kuma ka sani idan aka kore ta ba za ta ji daɗi b..."

"Yar aiki ko mahaukaciya kamun yunwa? To bari ki ji; zan bar ta zauna kamar yadda Hajiya take so, amma daga yau kada ta sake taɓa Baby a cikin gidan nan! Domin ko 'yar'uwarki ce idan ba ta da hankalin da zan zuba ido na bar ta ta yi rainon Baby, ko a gabanmu ballantana a bayan idanuwanmu. Saboda ita kanta rainon take nema a yi mata, ta ya ya za ta iya rainon Baby? Haka kawai ta je ta kashe mana ita a banza. Ko so kike yi mu saka kuɗinmu mu sayo abin da zai jaza mana bala'i da hannunmu?"

Ya ƙare maganar a harzuƙe tamkar ya rufe ta da duka, baya ta ja cike da tsoro, duk da ta saba da halinsa jikinta yana rawa ta ce,

"Tsautsayi ne kawai amma ba za ta sake ba Baban Bab...."

Yi mini shiru ba na buƙatar wata kariya daga bakinki! Idan ma tsautsayin ne a kanta zai ƙare ba a kan Baby ba. Idan ta kuskura ta sake kuma za ki ga abin da zai faru."

Yana gama faɗar hakan ya shige toilet ya bar ta tsaye tana jimamin abin. A hankali ta fito daga ɗakin tare da ja masa ƙofa cikin sanyin jiki. Tana juyawa ta ga Bintoto tsaye a kofar ɗakin tana lasar plate da harshenta. Cikin rawar baki Hamida ta isa wurin tana cewa,

"Me kike yi a nan?"

Bintotona ta maƙale plate ɗin a hamatanta tana murza maiƙon miyar da hannuwanta tana faɗin,

"Sauraro na tsaya yi na ji idan za ki rama faɗan da yake yi miki, ko kuma za ki bar shi ya yi zaton tsoron sa kike ji. Ai ina ganin ki ɗazu har da hawaye kika yi a kan ya yi miki faɗa. To wallahi ki saki jiki ku daku kawai, idan ya ɗibi naman dafuwa ke ma ki ɗibi na gashi sai kowa ya ji a jikinsa. Amma haka kawai kina kallo yana ta miki masifa ke ba za ki iya ramawa b"

To fa🤔🤣

Princess Dija ✍️

17.

Hamida tana ƙoƙarin yin magana riƙe baki tsabar mamakin da Bintoton ta ba ta, ya buɗe ƙofar ɗakin ya fito idonsa a kan Bintoto ya ce,

"To ibilishiya! Ashe bayan haukar har da haɗin gurmin bala'i kike yi...to ba a gidana b..."

Yana maganar ya fisgo ta tana tirjiya da faɗin ya sake ta, a haka ya dinga jan ta har suka fice harabar gidan, Hamida tana bin su baya dariya fal cikinta ganin yadda Bintoton take tirjiya da ƙoƙarin ƙwace kanta amma babu dama, saboda ƙarfi ba ɗaya ba. Sai da ta ga ya buɗe gate ya wurgar da ita ƙofar gidan ya rufe ƙofa; sannan ta haɗe fuska cikin magiya tana cewa,

"Don Allah Baban Baby ka bar ta mu zauna, ni wallahi shirmenta ma dariya yake saka n..."

"Dariya ko? To wannan idan ta sha ruwan birni ta goge Allah kaɗai ya san bala'in da za ta tafka wa mutane. Amma tun da dariya take ba ki ki ɗauki shawarar da ta ba ki mu daku ni da ke ɗin, kamar yadda ta ce."

Tana rufe baki tsabar dariyar da ke taso mata ta ce, "Allah ya kiyaye wannan rana Baban Baby. Ita ma kamar shirme ne kawai da ya yi mata yawa ta yi wannan maganar, sannan da ƙarancin shekarunta ba ta fahimci mene ne aure da girman miji ba. Amma don Allah ka yi haƙuri saboda har zuciyata yarinyar ta kwanta mini, ina son mutum mai barkwanci saboda nishaɗi."

Da waɗannan maganganun ta rage girman fushin da Bintoto ta saka shi. Amma bai buɗe gidan ba ya yi cikin gida yana faɗin,

"Ki bar ta sai ta horu ko za ta dawo cikin gidan nan."

Ya shigewarsa ya bar ta tsaye tana sauraron dukan ƙofar da Bintoton take yi tare da magiyar da ta ƙara saka Hamida dariya har da hawaye.

"Don Allah Alhaji ka buɗe mini albarkacin uwata da ta rasu aka binne ta cikin ƙasa da ice, sannan aka lulluɓe ta da ganye. Ka yafe mini ba zan sake ba ko don albarkacin haƙorin Kandala mai kama da na giwa. Wallahi na yarda idan na sake ka saka wuƙa ka yanka wuyana ka sha jinina idan ya fit....amma gidan nan idan aka raba ni da shi an cuce ni wallahi, saboda matar gidan ta iya miyar shinkafa da soya kifi. Wayyo don Allah ka buɗe mini ga kare can yana kallo na..wayyo Allahna!"

Ta ƙwalla ƙara sanadin hango wani baƙin karen maƙotansu ya nufo inda take gadan-gadan yana zaro harshe. Hamida da ke leƙenta ta ramin ƙofar gate dariya take yi har da riƙe ciki. Musamman da Bintoto ta haye saman gate ɗin nasu ta maƙale, karen kuma yana ta haushi da tsallen son kamo ƙafarta tana kai masa harbi a kai yana kaucewa. Ga idonta a zare cikin matsanancin tsoro take ta kwarara ihun faɗin,

"Wayyo uwata wayyo ubana! Kandala! Kandala ki zo kare zai kashe ni!"

Da gudu Hamida ta koma cikin gidan tana sanar da shi ya zo ga black can zai haukata ɗiyar mutane. Duk da haushin ta da ke ransa cikin sauri ya fito ya buɗe gidan saboda karen har cizo yana yi. Sai da ya kora shi ya bar ƙofar gidan sannan ya koma tunanin yadda aka yi Bintoto ta haye gate ɗalam har da maƙalewa. Ƙugu ya riƙe fuskarsa a haɗe ya ce mata,

"Sauko Hajiya kada ki ɓalla mini gate. Kuma daga yau idan kika sake saka guntun bakinki a cikin harkar gidana da shi zan haɗa ki ya yagalgala namanki ki mutu kowa ya huta. Don na gano ba Allah kika sani ba ballantana ki ji tsoron saɓa masa."

Bintoto ta shiga rantsuwa har da ɗaga yatsan hannu sama bayan ta lasa yawu alamun ta yi ƙarshen rantsuwa tana cewa,

"Allah yana gani na yarda idan na sake ka kashe ni."

Ƙumshe da dariya ya yi, sannan ya yi yunƙurin komawa cikin gidan alamun bai yafen ba, kasancewar ƙafafuwan Bintoton sun yi sanyi kuma ba za ta iya dira ba akwai tazara. Bakinta yana rawa ta ce,

"Don Allah don Muhammadul Aminu ku saukar da ni!"

Kansa ya ɗaga yana kallon ta ya ce,

"Sauko da kanki, ai lokacin da kika hau babu wanda ya ɗora ki."

Idonta ya raina fata ta shiga rantsuwar ita ma ba ta san ta hau ba, wataƙila aljanun Kandala ne suka taimaka mata amma ba ita ce ta hau da kanta ba. Da maganar ido Hamida ta roƙe shi a kan ya bari ta sauko da ita saboda ta fara kuka, hakan ya sa ya yi cikin gidan ya bar su cikin dabara ta taimaka mata ta sauko tana ɗingisa ƙafa suka koma cikin gidan, sai matsar ƙwalla take yi tana shessheka.

Kai-tsaye wani ƙaramin ɗaki Hamida ta kai ta sannan ta tabbatar mata da shi ne ɗakinta, bayan ta zaunar da ita a kan ƙatuwar katifar da ke shimfiɗe mai kamar gado.

Bintoto baki har kunne ta shiga kallon ɗakin tana shafa gwiwar hannunta da ta gurje yayin hawa gate. Ranta fes ta yi magana cike da jin daɗi ta ce,

"Yanzu a nan zan dinga kwana?"

Hamida ta ɗaga mata kai tana murmushi ta ce, "Ta so ma na nuna miki yadda za ki yi amfani da toilet."

Bakin Bintoto a sake ta ce, "Mene ne tulit?"

Sai a lokacin Hamida ta tuna wace ce Bintoto ta ce, "Bayi nake nufi ai kin gane ko?"

Ta yi hanzarin ɗaga mata kai sannan ta bi bayanta har zuwa toilet ɗin, cike da mamaki take ta kallon Hamida da ke bayanin yadda za ta yi wanka da kashi, idan ta gama kuma da abin da za ta aikata. Tagumi Bintoto ta yi tana kallon kwalbar kashi ta ce,

"Yanzu shi wannan abin a kansa ake yin kashin?"

Hamida ta ɗaga mata kai, Bintoto ta sake cewa, "Daman ku a zaune kuke yin kashi a garin nan naku na 'yan birni?"

A nan ma ta sake ɗaga mata kai da murmushi a kan fuskarta ta kunna shower sai ga ruwa shaa yana sauka. Bintoto ta zabura tana ƙoƙarin ficewa cike da tsoro saboda ganin ruwan kamar almara. Idonta a kan shower ta yi hanzarin faɗin,

"Laa'ilaa! Ku kam dai kun ji daɗinku, har da ruwan sama kuna da kuɗin saya mala'ikun ruwa su yi ta zubo muku a lokacin da kuke so?"

Babu shiri wata ƙaƙƙarfar dariya ta suɓuce wa Hamida kafin ta ce, "Ba ruwan sama ba ne Fatima, daga ƙasa ake jawowa, shi ya sa ake yin amfani da shi a duk lokacin da ake so. Ai ke ma kuna da Bohol a garinku ko?"

Bintoto ta ɗaga kai, Hamida ta ce,

"To kamar haka ne ake zuƙo ruwan daga ƙasa ta hanyoyi da dama domin amfanin al'umma. Haka ma rijiya ai kin san ita ma daga ƙasa ruwan yake fitowa ko?"

Bintoto ta ɗaga kai, tana 'yar dariya ta ce, "Don Allah ɗan sake kunna mini na ga kalar ruwan."

Hamida tana kunnawa ta zura hannunta ta taɓo ruwan da sauri ta jaye hannun tana lasa ruwan tana 'yar dariya ta ce,

"Ashe ruwan ma bai da maiƙo."

Ta sake kai hannunta ta ɗebo ruwan ta kai bakinta tana sha ta ce, "Aradun Allah ruwan nan sun fi na garinmu daɗi."

A haka ta tara hannuwanta biyu a ruwan yana sauka tana zuƙa sai da ta ƙoshi sannan ta shafa ciki ta ce,

"Gaskiya ni ma idan na yi kuɗi sai na saka wa Kandala wannan ƙarfen a cikin ɗakinta. Da ta tashi son ruwa ta buɗa kawai ta ɗiba Kawu Mani ya daina yi mata jan rai idan ta ce ya ɗebo mata ruwa."

Hamida tana dariya ta ce, "Ai da ruwan famfo kawai ake yin amfani wannan a bayi yake na wanka ne kawai...zo mu je ki ga sauran abubuwan da ya dace ki sani kada ki tafka wauta ki ce don ba a nuna miki ba."

"Cabɗijam! Ku kam kun samu duniyarku ni ma Allah ya ba ni na rama wulaƙancin da Kulu take yi mini don ta ga ban tafi Makka ba. Amma na san dole idan ta gan ni da haƙorin Makka a bakina ta ce mini Hajiya"

Haka ta yi ta zuba wa Hamida surutu tana nuna mata tsarin gidan da jera mata abubuwan da ba a so ta yi gudun ta sake jawo fushin maigidan. Har ta gama nuna mata Bintoto ba ta daina hangen ayaba da lemun da ta hango a cikin wani ƙaramin firij ba. Tana ganin Hamida ta shige ɗaki bayan ta ce ita ma ta je ta yi wanka ta yi sallah. Zumbur Bintoto ta miƙe saɗaf-saɗaf ta koma inda ta ga firij ɗin ta jawo a hankali ya buɗe, nan take sanyi ya daki fuskarta ta fara lumshe ido tana zuƙo numfashi tana faɗin,

"Wayyo daɗi gidan 'yangayu."

Ta zura hannu ta ciro ayaba ƙwara guda ta fara ci tana lumshe ido har da bubbuga kai sanyi yana ratsa bakinta, motsin buɗe ƙofar da ta ji alamun za a fito ya sa ta yi hanzarin cinye sauran ayabar ta wurgar da ɓawo. A bisa tsautsayi maigidan yana taka ƙafarsa saman ayabar cikin rashin sani santsin ayabar ya ja shi, babu zato sai ga shi tim a ƙasan tayis.

Princess Dija✍️.

18.

Waige-waige ya shiga yi cike da jin kunyar faɗuwar, bayan ya tabbatar da babu kowa a wurin ya miƙe cike da jarumta yana riƙe ƙugu, fuskarsa a cure ya dinga wara ido don zuciyarsa ta ba shi aikin Bintoto ne, saboda ba halin Hamida ba ne kuma a tarihin zaman da yake yi da ita tun tana amarya har lokacin ba ta ajiye abu inda ba muhallinsa ba. Don mace ce mai tsananin tsafta da ƙoƙarin kauce wa abin da ta san ba ya so. Amma hakan bai hana shi ƙwala mata kira har sau uku a jere ba.

Kafin ya koma ƙare wa falon kallo a tsanake, caraf idanuwansa suka hango firij ɗin da Bintoto ta buɗe a wangale har lokacin, wanda ke ajiye a wata kusurwar da ke kai mutum kitchen ko hanyar ficewa ta bayan ɗakunan gidan.

Domin ita tana ganin aika-aikar da ta tafka kafin hankalinsa ya kai kanta ta yi bayan firij ɗin ta lafe tare da shan jinin jikinta ƙirjinta yana bugawa fat-fat.

A take zuciyarsa ta ba shi tana wurin, cike da tabbatacin ita ce mai aikin, amma hakan bai sa ya nufi wurin ba saboda bai san wane kalar duka zai yi mata idan ya damƙo ta.

Hankalin Hamida a tashe ta fito idonta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login