Showing 51001 words to 54000 words out of 88489 words
Chapter 18 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx
ta duba su ta cikin madubi sannan ta cire ta saka wasu.
Tafi-tafi sai ga ta har da buɗe ma'ajiyar tufafin Hamida. A nan kallo ya koma sama, saboda ganin kayan a tsare komai tsaf har da wani ƙamshi ya dake ta a lokacin da ta buɗe. Tsaf ta yi a ranta tana kallon wasu saitin kayan da suka ɗauki hankalinta tun kafin ta gama buɗe wadrobe ɗin. Hannu ta zura ta jawo su, ido ta zaro ganin aikin da ke gaban rigar yana walƙiya tsabar ya ji shuwari stone tamkar an yi ɓari ba hannu ya saka ba.
Jikinta yana rawa ta shiga warware doguwar rigar ta cire kayan jikinta ta saka. Nan take ta fara tsalle tana jujjuya jikinta a gaban madubi tare da ƙiƙƙifta ido ta rufe ta buɗe tana ɗaga ta gira. Daga baya ta koma fashewa da wata mahaukaciyar dariya.
Cikin sauri ta ɗauko ɗankwalin rigar ta dunƙula kamar yadda ta ga Hamida tana yi, sannan ta dinga fesa duk abin da ta gani a a gaban madubin, wanda take tsammanin turare ne. A cikin abubuwan da ta shafa har body lotion da ta gani a cikin kwandon shafe-shafen Baby, oil da cream duk ta goga wa rigar, hatta hoda sai da ta zazzaga a gaban rigar da hamata, fahimtar hoda ce ya sa ta shiga kakkaɓewa tana faɗin,
"Dalla ban da ke tafi can."
Saboda ganin kayan shafar da yawa, man gashi ma ba ta bari ba sai da ta zuba a hannunta ta goga wa rigar tana faɗin,
"Ita wannan komai sai ta nuna ta fi kowa iyawa, idan ba haka ba waɗannan kayan shafe-shafen duk me za ta yi da su idan ba ta yi ta kallon su a banza b...."
Ƙwanƙwasar gidan da ta ji ana yi babu shiri ƙirjinta ya buga dam-dam. Cikin sauri ta shiga mayar da komai a inda ta gan shi. Tana ƙoƙarin cire rigar wata zuciya ta ce da ita,
'Kada ki cire har sai ta gan ki da ita, wataƙila ta yi zuciya ta ce ta bar miki.'
Umarnin zuciyarta ta bi, cikin sauri ta kwashe kayanta da ta cire ta kai ɗakinta, sannan ta fito da takalmin Hamida 'yan tsini waɗanda ta manta shaf ba ta cire ba. Sai da ta fito harabar ta hango su ƙafarta, ta buga uban tsaki tana ƙara sauri ta ce,
"Ba za a cire ba, idan ta gani ta kashe ni."
Sai da ta leƙe ta kussuwar da ake ganin mutum kafin ta yi hanzarin buɗe ƙaramar ƙofar bakinta a washe. Cikin ladabi ta duƙa har ƙasa ta gaishe da matashin da ke riƙe da yarinyar da aka kawo a yi mata allura. Cike da jin daɗi ya amsa mata kafin ya ce, "Matar gidan tana nan?"
Bintoto ta yi hanzarin ɗaga masa kai har da nuna cikin gidan da hannu tana cewa,
"Tana ciki yanzu ta tashi daga barci."
"Yawwa, shi ya sa ba mu zo da wuri ba. Don Allah ki shiga da ita, ina nan ina jira, idan an gama yi mata allurar sai mu wuce. Tun da ita waccan wawuyar yarinyar ba ta san arziƙi ba. Haka kawai ta nemi faɗa masu gida daga taimako."
Maganganun da ya faɗa ya sa Bintoton ta gano da budurwar da suka yi faɗa yake, kuma tun da ta gan shi ta gano kamarsu. Hakan ya sa ta ƙara zama mutuniyar ƙwarai a gabansa tana sunkuyar da kai ta ja hannun yarinyar suka shiga gidan, sai da ta datse ƙofar da sakata sannan ta fara rawa har da ɗaga hannuwa tana faɗin,
"Daga ni sai ni sai ɗan ƙanen abokina ahayye."
Hannunta riƙe da yarinyar tana ta wara ido har cikin falon. Zama ta yi sannan ta karɓi ledar da ke hannunta ta fito da allurar da ƙaramin sirinjin da ta gani. Ranta fes ta shiga jijjiga ruwan allurar kafin ta saka bakinta ta fasa kwalbar, cikin rashin sa'a ta yanke mata leɓe da gefen harshe fashe. Babu shiri ta jefar da komai ta dafe kai tana kiran wayyo bakina. Nan take jini ya dinga fitowa cikin tashin hankali ta nufi ɗakinta da gudu. Bakin ta tara a fanfo tana runtse ido har sai da ta rage jin jogi jinin ya tsaya sannan ta tofar da ruwan bakin tana faɗin,
"Wai Allah, da na kashe kaina a banza. Amma fa dole ne sai na yi mata allurar nan."
Ta fito tana shafa baki ta isa falon, sai da ta zauna ta huta sannan ta ƙara ɗauko wata kwalbar da ta gani ta saka gefen ɗankwalinta ta fasa. Cikin sa'a ba ta yanke ta ba kuma ruwan bai zube ba.
Jikinta yana rawa ta nutsa sirinjin a cikin kwalbar ta zuƙo ruwan maganin. Cikin nishaɗi ta kwashe ruwan tana 'yan waƙe-waƙenta ta ajiye kwalbar ƙasa. Ba tare da ta saita ruwan ta cire iska ba, a yadda ta zuƙo a haka ta koma kan wata kujera tana nishi ta ce da yarinyar ta zo. Yarinya za ta yi kuka ta zare mata ido ta ce,
"Idan na ji kukanki har a cikin ido sai na yi miki allura. Ai da ma na faɗa, abin da yayarki ta yi mini sai na rama a kanki ko a kanta. Don haka ga shi Allah Ya kama mini ku har gida kin dawo kin same ni. Matso na ce!"
Ta ƙare maganar cikin faɗa, yarinyar ta ƙi zuwa, ta ƙame wuri ɗaya tana ciccika tare da kallon ƙofar shigowa. Bintoto ta taso ranta a ɓace ta dungure mata kai kafin ta ce,
"Wallahi ko mutuwa za ki yi sai na yi miki allurar nan. Da ma kin tsaya na yi miki a hankali."
Yarinya ta fashe da kuka, amma hakan bai hana Bintoto dunƙule ta ta ɗage mata riga da wando ba, kafin ta saita allurar daidai tsinin ɗuwawunta ta tura mata allura. Yarinya ta zabura ta ƙara taushe mata kai, sai da ta juye mata ruwan da iskan duka da ke cikin sirinjin sannan ta sake ta tana faɗin,
"Don ubanki ko gobe kika dawo ni zan yi miki allurar tun da na iya."
Yarinya tana ta kuka ta mayar mata da wandonta, sai da ta gyara falon tana yi wa yarinyar faɗa a kan ta yi shiru sannan ta ja ta tana sosa inda ta yi mata allurar, jini har ya ɓata doguwar rigar atamfar da ke jikinta. Amma ko kaɗan hankalin Bintoto bai kai can ba, a haka ta buɗe gidan tana ta rarrashin ta har gaban yayan nasu. Tana ɓata fuska ta ce da shi,
"Ashe kukan allura take yi. Gabaɗaya ma yau ƙin tsayawa ta yi da ƙyar Anti ta samu ta yi mata allurar."
"Ai babu komai tun da an gama. Ki ce da ita mun gode Allah Ya saka da alheri."
Ya ja hannunta tana ta kuka suka wuce, Bintoto ta rufe gidan tana ƙyalƙyala dariyar mugunta ta koma ciki.
kitchen ta nufa, a can ta tare tana ta tsince naman miyar da Hamida ta rage, wadda ta haɗa tun da sassafe, sannan ta yi pride rice ta cika kula ta tafi ta kai gidansu. Sauran kuma ta bari da niyyar idan ta dawo ta sarrafa ta a ci abincin dare.
Amma gaba Bintoto ta saka nama tas ta cinye, ta nemo wuƙa ta dinga yanka plantain tana ci haka nan ba tare da ta soya ba. Ta buɗe firiza ta hango soyayyen nama, jikinta har rawa yake yi wajen zura hannu fiddo bokotin. Zaman dirsham ta yi a gaban firizar tana tsoma hannu tana ciro shi yana hayaƙin sanyi, ɗaya bayan ɗaya ta dinga ci tana rawar baki tare da runtse ido. Sai da ta ji tana shirin yin amai sannan ta mayar da shi inda ta gan shi, ta rufe tana nishi ta fito kitchen ɗin. Daidai lokacin da ta ji ana ta bubbuga gidan, ƙirjinta ya ƙire ya faɗi dam-dam. Amma hakan bai hana ta buɗe firij ɗin falo ta sha ruwa ba kafin ta fice tana gyatsa.
"Innalillahi!"
Abin da ta furta kenan saboda ganin yayan yarinyar da Innarsu saɓe da yarinyar har lokacin ba ta daina kuka ba, tare da budurwar da suka yi faɗa ta riƙe ƙugu sai ciccika take yi tana bubbuga ƙafa ƙasa. Sannan da wasu mutane a bayan su sun yi cirko-cirko.
Bugun da aka sake yi wa ƙofar gate ɗin ya sa ta yi hanzarin faɗin, "Masu gidan ba su nan."
"Wurin ki muka zo ba wurin masu gidan ba!"
Yayan yarinyar ya faɗa cikin fusata. Bintoto ta leƙo kanta cikin kussuwar gate tana cewa, "To ni me na yi muku da za ku zo wurina? Idan ma allura ce ita yarinyar da kanta ta ce na yi mata tun da Anti ba ta gid..."
Wata kalar ashar da budurwar ta lailayo mata ce ta saka ta zura hannu ta kussuwar gate ɗin ta yi mata daƙuwa tana cewa,
"Ubanki dai ba ubana ba. Ai ba ni na ce ta ce na yi mata allura ba. Da za ku yo gayya kuna muzurai da ido wai har da Innark...."
"Kada ki faɗa mana maganar banza na diro cikin gidan na ci uban kakan Babanki! Wani za ki yi wa iskanci bayan kin gama yi wa yarinya mugunta! To wallahi ko ki buɗe gidan cikin mutunci ko na je na ɗebo miki 'yansanda. Da ma can darajar masu gidan ya sa ba mu ɗauki mummunan mataki a kanki ba, mun zo a yi magana kuma shi ne za ki raina wa mutane hankali don uban Babanki?"
Yayan yarinyar ya faɗa cikin tsananin fushinsa da Bintoto ta gama kai wa bango. Hango motar Aliyu da ya yi ya saka shi ja baya yana gyara rayuwarsa tare da sunkuyar da kai ƙasa. Bintoto kuma jin ya yi shiru tana kumbura leɓo ta ce,
"To ai haƙuri za ku yi. Saboda ni ma ba da son raina na yi mata allurar b..."
Tsayuwar motar da ta ji a ƙofar gidan hantar cikinta ta kaɗa, don a tsammaninta ko 'yansandan ne ya ɗebo mata kamar yadda ya yi iƙirari. Da sauri ta leƙa kanta ido tsakar ka ta dafe kai alamun haushi da takaici, don ba ta so su Hamida suka dawo gidan a daidai lokacin ba. Musamman da take tare da maigidan, saboda ta san ko Hamida ta tausaya mata shi ba raga mata zai yi ba.
Ganin mutane a ƙofar gidan tun daga nesa Hamida ta fara faɗin, "Wallahi yanzu haka Fatima ce ta sake jawo mana jarfa."
"Wace ce Fatima?"
Ya faɗa idonsa a ƙofar gidan, don har ya manta da wata Bintoto da suka bari a cikin gidan. Hamida ƙirjinta yana bugawa ta ce,
"Yar aikinmu mana."
"Mahaukaciyarki dai."
Yana maganar ya yi parking ya fito idonsa a kan mutanen da su ma shi suke kallo, kafin Hamida ta fito kallon ya koma kanta. Cike da mamaki ta dinga taku cikin sanyin jiki ta isa inda Mamar yarinyar tana faɗin,
"Mama lafiya na gan ku a nan haka?"
Kafin su ba ta amsa Bintoto ta buɗe gidan ta fito tana faɗin, "Ita fa ta ce na yi mata allura tun da ba kya gida, amma shi ne don kawai a ce na yi laifi aka zo har nan ana so a kai ni wurin 'yansanda.....yiiiii!"
Ta ƙare maganar cikin fashewa da wani kalar kuka tamkar wadda aka shaƙe wa wuya. Mamakin da ke fuskar Hamida ya ƙaru, ganin Bintoto da tsadaddun kayanta da take mugun so, sannan da takalminta na fita kunya. Ƙarin firgici jin abin da take faɗa, wanda alamu ya nuna ƙarara allura ta yi wa 'yar mutane da ba ta nan.
Kanta kawai ta dafe tare da yin baya taga-taga tsabar fita hayyaci tana faɗin,
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"
Cikin sauri Aliyu ya tare ta gudun ta faɗi. Idonsa a kan Bintoto ya dinga wurga mata wani kalar kallon da shi kansa bai san kalar hukuncin da ya dace ya yanke mata ba.
To ni ma na yi kudu🧑🦯
Princess Dija.
29.
"Fatima kin cuce ni. Ban taɓa tunanin haukarki da Baban Baby yake faɗa har ta kai haka ba. Yaushe kika iya allura da za ki yi wa yarinyar mutane?"
Bintoto ta yi tsuru-tsuru da iso tana turo baki tare da sosa kai alamun ta rasa abin faɗa da rashin gaskiya ƙarara. Haushin da ke shirin kai Hamida ƙasa ya sa ta ƙara yin magana a ƙufule tana kallon Mamar yarinyar tana faɗin,
"Mama, ku ɗauki duk hukuncin da kuka ga ya dace a kanta, wallahi babu ruwana saboda ban ma san ta aikata ba. Yanzun nan ma da kuka gan mu daga gidanmu muka fito, na je ganin Babana da ke fama da ciwo kwana biyun nan. Tun da har ta yi gaban kanta, ku ma ku yi mata duk abin da kuke so ita ta jawo wa kanta."
Tana gama faɗar hakan ta buɗe gidan ta shige, ta bar Bontoto da waɗanda ta yi wa laifin suna ta hararar juna, tana yi musu kallon ƙasan ido tana zagin su a zuciya, su ma suna aika mata mugun kallo mai ɗauke da harara, a ransu kuma suna jin kamar su rufe ta da duka har sai ta daina motsi.
Yayin da Aliyu yake gefensu yana waya, saboda tun da Hamida ta fara magana aka kira shi, yana gamawa ya juyo wurin su ransa a ɓace ya shiga ba su haƙuri yana cewa,
"Abin da ta aikata ganganci ne, don haka ko da zan ce ku yi haƙuri; ba zan hana ku ɗauki matakin da kuka ga ya dace ba, idan har kuna da ra'ayin yin hakan. Saboda ni kaina a yau kuma a yanzu za ta bar mini gidana, don na gaji da halinta. Amma idan kuka tashi har garinsu zan iya kai ku matuƙar kuna da buƙatar hakan. Da ma can zaman da muke yi da ita a cikin gidan ba don ina so ba, Hamida ce take son zamanta kuma yanzu ga abin da ta jawo mata. Don haka ku je ku kai yarinyarku asibiti a duba muku lafiyarta, duk abin da ke nan ni zan yi muku jagora har wurin kakartarta a yi duk abin da za a yi, idan ma rufe su kuke so ku yi kuna da damar hakan don sun cancanta."
Daga haka ya ja bakinsa ya tsuke, bayan ya ciro kuɗi daga aljihunsa ya bai wa yayan yarinyar, da nufin a kai ta asibiti gudun a bar abin daga baya matsala ta biyo. Mamarsu ta ce babu komai, amma fuskarta cikin rashin walwala suka tafi, budurwar kuma sai da suka yi gaba ta dawo a fusace ta dinga kai wa Bintoto duka. Kafin ka ce me suka dinga kokawa, nan take ta kai Bintoto ƙasa ta taushe, ko da aka raba su tana saman cikin Bintoto tana ta duka. Don da ma can ta ci burin sai ta dake ta ganin yadda aka bar ta babu wanda ya yi yunƙurin saka mata hannu.
Mutanen da suka taru ƙofar gidan suka dinga yi wa Bintoto saukale kowa da abin da yake faɗa a kan rashin hankalin da ta aikata. Aliyu dai cikin gidan kawai ya nufa, mintuna a tsakani ya fito da jakar kayan Bintoto ya wurga mata a jiki. Ta ƙara fashewa da kuka tamkar wadda aka yi wa mugun naushi. Hamida da ke bayansa ta rufe gidan sannan ta shiga mota, cikin ɗaga murya Aliyu ya leƙo kansa yana faɗin,
"Za ki shigo ko sai na taka kanki wurin nan?"
Sanin da ita yake, ta tallabi jakarta tana haɗe rai ta buɗe motar ta shiga ta zauna rungume da jakar kayanta. A ranta tana faɗin,
'To don kun kore ni sai me? Ai dai ba shi zai sa na mutu ba. Ni ma zama gidan naku ya fita kaina tun da ba mutunci ne da ku ba. Abu kaɗan ku saka mutum gaba ku yi ta masa faɗa sai ka ce ku kuka haife ni"
"Mitsss!"
Ta ƙare zancen da jan ɗan ƙaramin tsaki, wanda ya sa Hamida faɗin,
"Kanki kika cuta Fatima, don wallahi kin gama sire mini a rai gabaɗaya. Wai ma saboda tsabar kin raina ni har ɗakina kika shiga kika ɗauko mini kaya kika saka. To ki je an bar miki idan kika tashi mutuwa a rufe ki da su cikin ƙabarinki."
Aliyu ya yi hanzarin ƙumshe dariyar da Hamida ta so ba shi yana cewa, "Tun farko sai da na ce miki yarinyar nan mahaukaciya ce, amma ba ki yarda ba. Babu yadda ban yi da ke ba a kan ta bar gidan kika ƙi yarda, to ai ga inda rashin hankalinta ya kai ki. Don ta saka ki jin kunya da mutanen da ke ganin mutuncinki,