Showing 21001 words to 24000 words out of 88489 words
Chapter 8 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx
ta yi matashi da cinyarta.
Ganin hakan ya sa Hari ta kasa haƙuri ta fara tayar da ita daga barcin saboda ita ma kanta minsharin ya dame ta. Firgigit Kandala ta yi tare da yin miƙa da salati mai ƙarfi a bakinta, salatin da ya janyo Bintoto ta yi zumbur daga saman cinyarta, a bisa tsautsayi kanta ya daki bakin Kandalar, inda kai tsaye tsinin dogon haƙorin nata ya kai wa Bintoto sukar ba zata a cikin tsakiyar kai, babu shiri ta ƙwalla ihu tare da faɗin,
"Wayyo Allahna! An soka mini mashi a cikin kain..."
Kandala ta yi saurin lalabo kan nata cikin tausayawa tana faɗin,
"Yi haƙuri to! Ai duk ke ce kika jawo haƙorin nawa ya soke ki, amma tun da har Allah ya tsare wurin bai fashe ba ai sai ki gode wa Allah."
Bintoto ta yi saurin kallon bakin Kandalar tana cewa,
"Kandala yanzu kina nufin haƙorin giwarki ne ya cake ni haka tamkar an soka mini mashi!?"
Kandala ta kai wa Bintoto wani mangari a kai cike da jin haushin maganar ta ce,
"Kibiya ce ba mashi ba! Ƙaramar mara kunya waton a nan ɗin ma ba za ki bar ni ba sai kin sa na yi hargowa da ke ko? Toki gode wa Allah na taimake ki kin shigo motar nan da yanzu kina can an baro ki kina fama da kajin Kulu, idan kina bacci su yi maki kashi a baki."
Bintoto ta turo baki waje tana cewa,
"To ai ke ma ina ga har faɗuwa kika yi garin shiga motar aka tallabo ki kamar 'yar yarinya."
Wasu daga cikin mutanen motar suka fara dariya, saboda tun da suka fara musayar bakin suka shiga ƙumshe dariyar amma zancen Bintoto ya saka su dariyar dole.
Musamman waɗanda Kandala ta faɗi warwas a gabansu a lokacin da za ta shiga motar, wasu shaƙiyai har da riƙe ciki yayin dariyar tasu saboda tuno irin yakicewar da zaninta ya yi har sai da aka yi mata rumfa ta saya jikinta.
Yawan dariyar da suke yi Kandala ta fara tsarguwa ta shiga sababin faɗa tana cewa,
"Duk wanda ya yi mini dariyar na faɗi Allah ya sa shi ma wajen fita motar bakinsa ya karci ƙasa."
Wata sabuwar dariya matasan cikin motar suka sake kwashewa da ita, masu hankalin cikinsu kuwa suka fara nuna musu rashin dacewar abin da suke yi, amma duk da sun rage dariyar hakan bai hana ta ci gaba da faɗan ba, faɗan da fiye da rabinsa na saka mutum wata dariyar ne, da haka har suka fara jan ta da wasa tun tana ɗaure fuska har ta fara sakewa da su ana ta hira.
Hari dai alla-alla kawai take yi su sauka lafiya tun kafin Kandala ta yi wani sabon barci, hakan ya sa da ta ga ta fara gyangiɗi take kiran sunanta tana cewa,
"Inna! Inna! Kada ki yi barci mun kusa isa cikin garin fa, ki bari ki ga yanayin birnin da kyau ta yadda za ki bayar da labari."
Kandala ta yi saurin goge fuskarta tana kallon gefen titin tare da goge baki, amma duk da hakan minti biyu tsakani ta ƙara komawa wani sabon gingiɗin, haka Hari ta sha fama da ita har suka shiga cikin cikin garin. Bintoto da Kandala sai kalle-kalle suke yi yayin da motar ta shiga babbar tasha.
Mutane suka fara fitowa Hari ma ta fito aka bar Bintoto da Kandala suna tunanin yadda za su fito daga motar, Hari ta koma ta riƙo hannun Bintoto ta fito da ita, Kandala ta koma zarar idanuwa saboda a rayuwarta kaf ba ta taɓa shiga irin motar ba sai a wannan karon.
To fa! A samu wata jaruma ta fito mana da Kandala kada ta sake faɗuwa ta yi walle a shiga uku😂
*Princess Dija ce✍🏻*
*SHAGALALLIYA!*
*HADIZA D. AUTA*
*1k kacal, 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. Shaidar biya 08022014771.*
*LAMBA SHA UKU.*
Da dabara aka samu Kandala ta fito daga motar tana ɓarin jiki da sambatu kafin ta koma yi wa Allah godiya har da shafa addu'ar a fuskarta. Hari ta nemo musu ɗan baron da zai fitar da kayansu zuwa bakin tashar, bayan ya gama loda kayan suna ƙoƙarin bin bayansa; suka hankalta da Bintoto ba ta tare da su.
Kandala ta fara kuka tana kururuwar sai an nemo mata jikanyarta idan ta ɓata kuma sai masu tashar sun biya ta Bintotonta. Cikin tashin hankali Hari da wasu masu tausayi suka fara neman inda take lungu da saƙon cikin tashar ana bayanin siffarta da kalar kayan da ke jikinta.
Babu zato Hari ta hango ta a bakin shagon wata Hajiya mai abinci da ke cikin tashar. Hankalinta a kwance tana zaune saman dogon bencin Hajiyar tana ta guma lomomin shinkafa, jikin Hari yana rawa ta isa wurin tana faɗin,
"Haba 'yata, ashe kina nan kika sa hankalinmu duk ya tashi? Sai neman ki ake ta yi lungu da saƙo, to yi sauri ki gama ga Inna can tana kururuwar sai an nemo mata ke."
Bintoto tana dariya tana guma lomo ta ce mata,
"Share ta kawai Inna, don ba ta san daɗin da na zo sha ba ne shi yasa take kuka."
Hari tana tsaye kusa da ita tana dariyar yadda take guma loma sai ta ciko hannu, har ta cinye abincin da zuƙa-zuƙan naman da ke saman shinkafar tsoka ta kusa goma, tana gamawa ta je gaban mai abincin ta ajiye mata robarta tana cewa,
"Na gode miki da yawa wallahi, ni zan tafi Allah ya yi albark..."
Tana maganar ta juya da nufin tafiyarta, mai abincin ta zabura jikinta yana rawa ta miƙe, babu zato Bintoto ta ji an cafko rigarta ta ta baya, waigowar da za ta yi ta yi ido huɗu da Hajiya mai abincin tana aika mata muguwar harara, domin yanayinta ya nuna ƙiris ya rage ta kifa mata hamshaƙin mari. Bintoto ta yi saurin kai kallonta ga bayan Hari da ta ɗan yi misu nisa kaɗan, sannan ta yi saurin ƙwala mata kira tana cewa,
"Inna! Don Allah ki zo wannan ƙatuwar matar tana so ta kashe ni!"
Haushi ya sa mai abincin tsumar jidali ta ɗaga hannu ta kai mata bahagon mari tas, Bintoto ta yage baki ta fara zuba ihu iya ƙarfinta hannu biyu a ka, Hari ta yi saurin waigowa tana salati cike da mamaki ta ƙaraso wurin tana tambayar matar abin da ya faru. Sai dai kafin mai abincin ta haɗiye fushinta ta yi magana; Bintoto ta riga ta faɗin,
"Abinci take rabawa kyauta, kuma a gabana duk wanda ya ci ko godiya ba ya yi mata yake tafiyarsa, amman ni kina gani sai da na gode mata amma shi ne don ta gan ni baƙuwa za ta ce duka na za ta yi, to ai don ban san ba ta son godiyar ba ne yasin da ina gama ci zan yi gaba kamar yadda na ga wasu suna yi mata."
Ta ƙare maganar tana kallon ƙatuwar matar tana turo baki, nan take Hari ta fahimci inda zancen ya dosa tana haɗe dariyarta ta ce da mai abincin,
"Na nawa ne kika saka mata?"
Mai Abincin ta ƙara tsuke fuska tamau sannan ta gyara tsayuwarta ta ce,
"Abincin dubu ɗaya ne naman dubu biyu."
Hari ta yi saurin kai kallon ta ga fuskar Bintoto saboda mamakin wautar da ta tafka, ba tare da ta ce komai ba ta ciro kuɗin a jakarta ta miƙa mata, amman tsabar haushin da Bintoton ta ƙumsa mata; garin sakin ta sai da ta cillar da ita ta faɗi ƙasa, sannan ta fara ƙirga kuɗin tana haɗe rai daidai lokacin da Kandala ta iso wurin idonta a kan matar tana faɗin,
"Wannan ai rashin daraja ne! Kina ɗirkekiyar ƙatuwa da ke haka don lalacewa ki koma faɗa da wannan 'yar tsakon yariya? Wallahi kin ji kunya da yawa kuma ki gode wa Allah da ba garinmu kike ba da sai na la'ance ki gaba da bayanki bak'ar almura mai fuskar maza da mazaunai kamar ƙaton masak...."
Haka ta dinga cin zarafin mai abincin Hari tana jan ta tare da roƙon ta yi haƙuri saboda ganin cikin ɗan lokaci ta tara musu jama'a, amma Kandala sai da ta kai ayar zancenta. Mai abinci kam ƙanzil ba ta ce mata ba saboda ganin ta tsohuwa, bakin aikinta kawai ta koma ba tare da ta kula da duk abin da take faɗa ba.
Hari da wasu mutanen da cikin tashar suka taru a kan Kandala ana ta ba ta haƙuri, sannan ta riƙe hannun Bintoto suka bar wurin. Amma ba ta daina tsine wa mai abincin albarka ba. Mai baro a gaba suna bin shi a baya har zuwa bakin tashar, inda Hari ta tsayar da napep suka shiga duka da kayansu suka nufi unguwar da Harin ta sanar da shi. Amma har lokacin Kandala ba ta daina sababin faɗan da take yi ba kamar ta ci babu, Hari tana dariya ta ce da ita,
"Inna fa abincin siyarwa ne Bintoto ta je ta ci, saboda ta zaci kyauta take bayarwa, shi ne fa da ta ga za ta tafi ta riƙe ta ta ce sai ta biya ta kuɗin abincinta."
Kandala ta yi saurin kai wa Bintoto ƙoso a kai sannan ta ce,
"Kaɗan daga aikinta, ke kam idan ba ki daina kwaɗayi ba sai kin ciyo wa kanki wutar lahira watarana."
Bintoto ta turo baki tana cewa,
"To ita ma tun da ta san ba na sadaka ba ne ai sai ta faɗa mini gaskiya tun kafin na ci. Amman don mugunta har da tambaya ta tsoka nawa za ta saka mini, ni ko na ce ta saka dozin kafin na cinye idan ban ƙoshi ba sai ta ƙara mini."
Hari da mai Napep suka fashe da dariya, yayin da Kandala ta yi gefe da kanta tana kallon bakin titin fuskarta a haɗe tana cewa,
"Ai da na san haka ne wallahi da na bar ta ta yi wa bakinki darzar man ƙuliƙuli, baƙar fitinanniyar yarinya! Sai gobe mu ga da wane bakin za ki je wurin kwaɗayin jarabar da kika saba."
Haka suka ci gaba da rikicin da suka saba yi a tsakaninsu, don bakin Bintoto ba ya mutuwa wajen ƙara tunzura ta, hakan ya sa ta sha kalolin faka da mangare kai har suka isa gidan da Hari take haya ba su daina musayar yawun ba, bayan an sauke su Bintoto ta fara waige-waige fuskarta a yatsine take kallon gidajen cikin unguwar tana cewa,
"Amma dai wannan unguwar taku ta talakawan birni ce ko Inna?"
Hari ta yi murmushi kawai ba ta ce mata komai ba, kai-tsaye ta buɗe gidan da makulli sannan ta ce su fara shiga za ta sa a shigo da kayansu. Wasu yaran unguwar da ke murnar ganin ta suka riƙa mata kayan har cikin gidan suna yi mata sannu da zuwa. Cikin sakin fuska ta fito da jakar ƙolon daɗin da ta riƙo musu ta dinga raba musu, suna ta murna suka fice suna godiya. Bintoto ma sai kallon ledar take yi tana tunanin ita jakar ya dace ta ba ta, kafin ta ciro guda uku ta miƙa mata tana cewa,
"Karɓi ke ma ki sha, kafin wasu su shigo su karɓi nasu, don na san muddin yaran unguwar nan suka ji na dawo gidan nan ba zai sake zama shiru ba."
Bintoto ta karɓa tana gunguni Hari ta mayar da sauran a jakarta sannan ta buɗe ɗakinta ta fito musu da tabarma ta shimfiɗa, sai da ta shigar musu da kayansu ciki sannan ta fito da nufin fita, Kandala tana jefa goro a bakinta ta ce,
"Wai ke kam ba ki da ɗan farau-farau na ɗan kora? Wallahi maƙoshina har ciwo yake yi mini saboda jarababbiyar 'yar nan taki."
Bintoto ta yi karaf tana cewa,
"Ko saboda faɗanki da kika saba ba! Ai na so kin ci abincin ƙatuwar matar nan ki ji yadda yake da mugun daɗi, alƙur'an da haƙorin giwarki sai ya koma inda ya fito ba tare da kin sani ba, saboda kiran sallar da za ki yi ta jin ana yi miki a cikin kunnuwa tsabar daɗin miyar da tsokokin naman."
Hari ta girgiza kai kawai tana 'yar dariya sannan ta ce da Kandala,
"Ai Inna furar ce zan aikawa a siyo miki yanzu nan, don na san kin fi son ta da komai."
Bintoto ta sake karɓe zancen tana kallon Kandala ta ce,
"Ba fa komai ba Inna! Don wallahi tana cin nama da irin abincin matar can sai ta rasa inda kanta yake."
Hari ta fita tana dariya ta ce,
"To ni dai bari na bayar a siyo mata furar yanzun nan, tun da ke kin gama ƙoshi tun a tash... "
*Princess Dija✍🏻*
*SHAGALALLIYA!*
*NA HADIZA D. AUTA*
*Wannan shi ne fejin ƙarshe. Domin ci gaba da bibiyar littafin a biya 1k kacal ta wannan account; 9032685442 Opay Hadiza Ibrahim Ɗan Auta. Shaidar biya ta wannan lambar 08022014771.*
*LAMBA SHA HUƊU.*
Haka Hari ta dawo da abinci mai rai da lafiya da furar Kandala, suka baje a kan tabarma suka ci suka ƙoshi, Kandala sai lasar leɓo take yi da dogon haƙorinta mai tsini saboda jin daɗin jar miya. Bintoto kuma tsabar lasar hannu har zuwa gwiwa tana rawa da kai don ita ma ba ƙaramin daɗin abincin ta ji ba, saboda takanas Hari ta saka maƙociyarta ta dafa musu abincin tun kafin su iso garin, gudun su zo suna jin yunwa a koma a neman abinci.
Da dare ma a nan suka baje tsakar gidan dukansu suka yi barci, saboda yanayin zafin da ake ciki a lokacin, bayan sun gama shan hira da matan da ke zuwa yi wa Hari barka da dawowa. Sai da sawunsu ya ɗauke hira ta koma tsakanin Hari da Kandala, a nan Hari ke sanar da ita washegari idan Allah ya kai su za ta je ta kai Bintoto gidan aikin da ta samo mata. Sannan ita ma za ta haɗa ta da matar da za ta yi wa aikatau a goben duka. Shiru kawai Kandala ta yi tana nazari kafin ta ce,
"Wai ni kam me zai hana mu yi aiki a gida ɗaya ni da Bintoton? Ni fa Hari ba na fatar duk abin da zai sa a ce na yi nisa da Bintotona gaskiya, don haka a duba dai idan akwai inda za a karɓe mu mu biyu a ɗan rakuɓa mu mu yi maneji."
Hari ta yi murmushi sannan ta ce,
"Ai Inna da ke za mu je ki ga gidan, duk lokacin da kika buƙaci ganin ta sai ki je ki dubo abarki babu wanda zai hana ki zuwa inda take."
Kandala ta taɓe baki cike da rashin jin daɗin maganar Harin sannan ta ce,
"Yanzu ba za su ɗauke mu mu yi musu aikin tare ba?"
Hari ta yi shiru sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce,
"A yadda na ji wata ma'aikaciyar asibiti ce Bintoto za ta dinga yi wa rainon 'yarta mai wata bakwai da haihuwa, saboda tana fita aiki kullum shi ya sa take buƙatar mai kula mata da yarinyar, don ita kaɗai ce a gidan mijinta ma ɗan kasuwa ne ba zama yake yi gidan koyaushe ba. Sannan uwar yarinyar za ta a samu nutsuwa da yin aikin gidanta cikin lokaci."
Kandala ta yi murmushi mai sauti sannan ta ce,
"Allah ya sa 'yar taki za ta yi abin da ake buƙata to, saboda ina tsoron ta je ta yi musu rashin jin da ta saba a koro ta ko'ina ba a je ba."
Hari ta yi dariya sannan ta kai kallon ta ga Bintoton ta ce,
"In sha Allahu ma za ta yi duk abin da ake so."
"Allah ya sa!"
Shi ne abinda Kandala ta iya faɗa saboda gabaɗaya jikinta ya gama mutuwa da rabuwar da za ta yi da Bintoto, Hari tana 'yar dariya ta ce,
"Amin Inna."
Da haka suka kulle hirar kowa ya yi shiru yana tunanin abin da ke ransa, Bintoto kam tun ƙarfe takwas na dare ta baje tana shaƙar barci baki buɗe, tsabar gajiya minsharinta kawai ke tashi tare da sauke numfashi kala-kala tana canza giya.
Tun da sassafe suka shirya sannan Bintoton ta ɗauki kayanta da ke ƙulle a ɗankwali suka fito. Kandala jiki babu kuzari take bin bayan Harin har suka hau adaidaitasahu zuwa unguwar da za a kai Bintoton, sai murna take yi tana ta kalle-kalle saboda mamakin manyan gidajen da ke cikin unguwar da suka zo, har suka shiga gidan idonta ba su daina waige-waige ba a zuciyarta tana murnar ita ma ta kusa zama mai kuɗi.
Kandala ma sai mamakin ganin ƙaton gidan take yi tana jinjina mulki da iko na Ubangiji tana ji kamar a mafarki ne ta hango suna shiga aljanna, musamman da ta tuna irin ginin gidajen garinsu, a take