Showing 75001 words to 78000 words out of 88489 words
Chapter 26 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx
na yi su na huta."
Kandala ta dungure mata kai tana cewa, "Sannu wadda ta fi kowa sanin yadda ake yin sallah."
"To ai na fi ki, don wani lokaci ma ba duka kike yi ba."
Harara take wurga mata tana muzurai ta ce, "Ku ji mini masharranciyar yarinya. Sai ka ce idan zan je wurin aikina da ke nake zuwa. To na ƙi cika sallar idan ke za ki saka ni aljanna ki fasa."
Hari dai ko shiga maganar tasu ba ta yi, don ita ma ta fahimci Kandala ba kowace sallah take yi a wuni ba. Wani lokaci ma tana jin ana kiran salla amma ta yi zamanta har sai Harin ta yi arwala ta yi sallah ba ta motsa daga inda take ba. Kuma idan ta tashi ma ba sallar za ta yi ba, hidimomin gabanta kawai za ta yi babu zancen yin sallah.
Sau da yawa sai ta so sanar da ita gaskiya, amma tsoron yadda za karɓi abin yake sa ta ji gara yin shiru da fadar abin da zai jawo mata ɓacin rai. Sai dai a hakan watarana take kannewa ta ce,
"Inna ki tashi lokacin sallah ya yi ana ta kira a masallatai."
"Ai ko ba ki ce ba, yanzu nake da niyyar yin ta. Idan ba kafuri ba wa zai ƙi sallah a duniya?"
Hari ta ja bakinta ta yi gum, amma kuma babu jinkiri Kandala take yin sallar saboda gudun sa ido irin na Hari mai gani har hanji.
Bintoto ma mai haɗa sallah wuri ɗaya, idan Hari ta ce ta tashi ta yi sallah, arwala kawai take yi ta dinga doddosawa kamar mai yin sallar gaske. Amma ba ta cewa komai kuma ba ta karanta komai ko a cikin zuciya. A cewarta sallarta ta riga ta kowa kai inda ake so, saboda ta haɗa su gabaɗaya tun asuba ta miƙa.
Ana haka watarana Bintoto ta tashi yin sallar asuba ta ga jini duk ya ɓata mata jiki. Ihu ta fasa tare da ɗora hannu a ka tana kururuwar wayyo ita Allah wani namiji ya shigo cikin dare ya yi mata iskanci.
Hari da Kandala a take suka gano jinin al'ada ne ya fara zuwar mata. Amma ita duk yadda suka so kwantar mata da hankali ƙi ta yi. Kuka ta dinga yi kamar wadda aka ce za a yanka, tsabar tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki. Ta kira innalillahi ta fi sau ashirin tana faɗin don Allah a bincika a gano wanda ya yi mata iskanci, don tsabar rashin imani ya lalata ta cikin dare ba tare da kowa ya sani ba.
Hari ta ja ta zuwa bayi ganin da gaske ba za ta nutsun ba, ballantana ta saurari bayanin da take son yi mata. Ruwan zafi Hari ta saka ta yi mata wanka tas tamkar wata ƙaramar yarinya, ta wanke mata kayan da jinin ya ɓata ta shanya, sannan ta nuna mata yadda za ta kimtsa jikinta, gudun jinin ya ƙara lalata mata kaya ko wuri idan ta zauna.
Bintoto ta shiga tashin hankali sosai, ta yadda ko motsi mai kirki ba ta son yi, ganin jinin ya ƙi tafiya duk ta duba sai ta gan shi. A rana tana shiga bayi ya fi sau goma saboda dubawa ta gani yana nan ko ya tafi.
Kuka kuwa ta sha shi tun suna ba ta haƙuri har suka yi banza da ita. Abinci ma ƙin ci ta yi duk shegen kwaɗayinta tana kallon abincin take yin banza. A cikin kwana ukun da ta yi jinin ko makarantar cewa ta yi ba za ta je ba a dinga kallon ta a ce ga 'yar iska can wadda aka yi wa lalata a cikin dare, har jini ya fito a jikinta.
Don a wunin ranar da abin ya faru zazzaɓi sosai ya rufe ta, ta dinga rawar ɗari bayan Hari ta gama yi mata wankan. Har sai da aka kai ta chemist aka yi mata allura biyu sannan aka samu zazzaɓin ya lafa mata. Sauran allurar ma rantsuwa ta yi a kan ba ta so saboda mai allurar ya leƙa mata ɗuwawu ya gano an yi iskanci da ita.
Ranar da ta kammala kwanakin al'adar kuma Hari gaba ta saka ta da bayani dalla-dalla. Sannan ta nuna mata duk yadda za ta yi wankan tsarki, tana gunguni tana turo baki ta yi wankan tare da cin alwashin duk jinin ya sake zuwa kamar yadda Hari ta sanar da ita zai zo duk wata; ta rantse da Allah sai ta bar shi ya yi ta zuba a ƙasa tun da mugunta ce kawai za ta sa ya dawo bayan ya tafi.
Ranar da ta koma makaranta faɗa sosai malamai suka yi mata. A kan me ya hana ta zuwa, babu kunya ko ɓata lokaci ta faɗa musu wani mugu ne ya shigo gidan Hari cikin dare ya yi lalata da ita, jinin da ya dinga zuba ne ya sa ba ta samu zuwa makarantar ba. Ganin ya ɗauke ta yi wankan tsarki ta zo, inda ta ƙara da cewa,
"Amma don Allah kada ku ce mini 'yar iska, wallahi daga ni har Kandala da Inna duka ba mu san lokacin da aka yi lalatar da ni ba. Sannan kuma gidanmu a rufe ɗakin ma an rufe da makulli, amma saboda rashin imani sai ya hudo ta bango ya shiga ɗakin ya yi mini iskanci."
Princess Dija.
37.
Mamaki da ikon Allah ya kama su, bayan dariyar da ta bai wa malaman ganin tana hawaye suke ƙoƙarin danneaa. Saboda a bayanin nata sun so su fahimci abin da ya faru. Amma don ƙarin tabbatarwa suka kira wata malama aka ce ta je da ita ta ƙara yi mata bayanin yadda abin ya kasance.
Bintoto tana matsar ƙwalla malamar ta shigar da ita wani ofishinsu ta zaunar da ita sannan ita ma ta zauna. Cikin dabara da nuna damuwa ga halin da take ciki ta dinga yi mata tambaya tana amsawa. A nan malamar ta gano al'ada ce kawai ta zo mata, duba da yanayin girmanta da shekarunta da ta ƙiyasta a ranta.
Duk da ita ma ƙarfin hali ne kawai take yi tana sauraron Bintoton ba tare da ta yi dariyar ba, ganin yadda take ta kuka alamun mai yin iskancin ya ɓata mata rai sosai. Hakan ya sa ta ƙare bayanin nata da rantsuwa tana faɗin,
"Na rantse da Allah duk azzalumin da ya sake dawowa gidanmu ya yi mini iskanci har jini ya fito mini a jiki; ni ko ba zan saka abin da Inna ta saka mini a wando ba. Sai dai jinin ya yi ta zuba tun da so ake yi na mutu a banza jinin jikina ya ƙare."
Dariyar dole malamar ta yi ba don tana so ba, sai da ta gama murmusawa tana ƙoƙarin danne dariyar da ke son haɗa ta da Bintoto. Gudun ta gano abin bai dame ta ba dariya ma take yi. Dole ta saka juriya ta shiga nutsuwarta ta fara yi mata bayanin yadda jinin al'adar yake a ilmance da Addinance. Sannan da dabarar yin sa ga kowace 'ya mace a kowane wata, da kuma yadda za ta dinga tsaftace jikinta idan ya zo kamar yadda Hari ta sanar da ita a gida.
Shiru kawai ta yi tana sauraron malamar, duk da ta so ta amince da zancen nata, amma tuna labarin wata yarinya da aka taɓa yi wa fyaɗe a ƙauyensu, da yadda su Jamila suka ba ta labarin jini ya yi ta fitowa a jikinta yana bin ƙafafuwanta; ta ji a ranta ba gaskiya malamar ta faɗa mata ba. Ita ma kamar Hari ce tana faɗar maganganun ne kawai don ta daina tayar da hankalinta kuma ta bar kuka.
Hannunta malamar ta ja suka fice ofishin, bayan ta ba ta umarnin ta tafi ajinsu za a yi mata karatu. Sannan ita ta koma wurin malaman tana yi musu bayanin yadda suka kwashe. Dariya suka dinga yi dukan su, inda wani daga cikin malaman ya ce, yana ganin kamar kan Bintoto da motsi ba ta da cikakken hankali. Malamar da wasu malaman suka dinga bayyana zallar ƙauyanci ne kawai da ƙurciyar da ke damun ta, don kowa da yadda take zo masa.
A nan hirar tuna baya ta taso a tsakaninsu kowa yana faɗar irin wauta da rashin hankalin da ya tafka ana ta dariya. Shugaban makarantar ya bai wa Malamar nauyin kulawa da Bintoto domin ta wayar mata kai ga duk abin da ya shige mata duhu. Saboda Jabir ya sanar da shi matarsa ce da zai aura lokaci kusa.
Kwanaki da sati-sati suka dinga zuwa suna wucewa. Har ranar da jinin al'adar Bintoto ya sake zuwa bagatatan babu zato. A nan ma an sha fama da ita kafin ta haƙura ta saka audugar da Hari ta tanadar mata saboda irin wannan lokacin. Kandala dai sai murna take yi tana tarairayar ta, har da yi mata farfesun kayan ciki saboda kawai ta rage ƙiyayyar jinin a ranta, bayan ta tabbatar mata duk lokacin da jinin ya zo ba ta tayar da hankalinta ba; sai ta dinga yi mata farfesun kuma ta saya mata duk abin da take so.
Da dabara Bintoto ta saki jikinta har da zuwa makaranta, amma kuma a takure take zama ko fitsari sai ta ji zai ɓalla mata mara ya fito sannan take zuwa ta tsiyaye shi dolenta.
Wasa-wssa Bintoto ta kwashe shekara ɗaya a makarantar ba tare da ta yi wani babban laifin da za a yi mata faɗa ko a ce za a kore ta ba. Saboda su ma malaman kulawar da suke ba ta ba irin ta kowa ba ce, duba da yanayin girmanta a cikin manyan mata, sannan da ƙauyancin da suke so su goge mata shi da ilimin Addini.
Ana haka watarana Kandala ta yi wa Jabir maganar aure, saboda ta matsu ta aurar da ita ganin ta fara hankali ta rage wasu abubuwan da take yi na rashin gaba. Jabir ya gyara zamansa yana yi wa Kandala bayanin halin da yake ciki.
"Ni kaina abin da nake kwana da shi ina tashi kenan. Saboda haka idan kin lura ko gidan nan na rage zuwa. Fafutukata duka ta rataya a kan yadda za a yi na samu abin da zai ishe ni a yi komai a gama. To kin san yanayin kasuwar a yanzu ba kamar baya ba, wani lokaci wuni nake yi ina yawo a cikin rana ba tare da na yi cinakin kirki ba. Amma in sha Allahu a cikin kwanaki kaɗan za a yi komai a gama. Saboda haka a ɗan ƙara mini lokaci."
Kandala tana ƙoƙarin yin magana Hari ta riga ta da cewa, "Babu komai ya ci gaba da nemansa kafin lokacin auren ya yi Bintoton ma ta ƙara hankali."
Jiki babu kuzari ya fice ya bar gidan, ganin yadda Kandala ta damu da dole sai an yi auren a lokacin. Ya shiga nazarin yadda zai samu kuɗi ya gama gyaran da ya ɗebo a cikin gidansu, sannan ya haɗa mata kayan lefen da ya yi niyya.
Zama na musamman ya yi da ahalinsa, suka yi shawara da mahaifiyarsa da ƙanwarsa da ke gidan aure a kan yadda za a ɓullo wa lamarin. A take suka nuna masa kawai ya yi abin da ya gani kada ya jira sai ya yi abin da bai da shi. Amma tuna kalolin daɗin bakin da ya dinga yi wa Bintoto da alƙawari kala-kala; yake jin fargaba a duk lokacin da ya tuna ta. A haka ya yi ƙarfin halin ture komai ya nemi a saka masa rana. Cike da jin daɗi aka saka lokacin auren wata ɗaya da kwanaki kamar yadda ya nema ba tare da an ja lokaci ba.
Sannan ya haɗa mata kayan fitar biki daidai abin da ya samu ya bayar aka kai mata. Mutanen ƙauyen da dama sun yi ta sam-barka ganin kaya masu kyau irin na 'yan birni, har da akwaitinta guda biyu masu kyau da wata ƙaramar jakar da aka sako kwalin takalmi taki biyu da jakarsu mahaɗi.
Amma Bintoto tana buɗe ido ta hango kaya kala biyar kacal sai tarkacen su man shafawa da sabulai. Ta fara tijara da borin faɗin ita ba irin kayan take so ba, akwatuna da yawa take so ya kawo mata kowane ya cika shi da sutura.
Ta shiga ɗaga kayan tana faɗar maganganu har ta ci karo da bireziya biyu da ke ciki. Cikin zaro ido ta ɗaga bireziyar sama tana rufe baki ta ce,
"Kan uban nan! Kandala duba ki gani ashe shi ma dai ɗan iska ne. Wai ni ya saya wa bireziya sai ka ce na ce masa ina so. To wallahi ni na ma fasa auren ya zo ya ɗauki kayansa tun da ni zai yi wa rashin mutunci. Bayan maƙon kayan lefen da yake son yi mini har da kayan 'yan iska a ciki. To ba zan aure shi ba ya je wurin 'yan iskan da ya gani suna saka bireziya ya kai musu kay...."
"Wai ke yaushe za ki yi hankali ki gano gaskiya? Ita bireziyar ce iskanci bayan kin gani da idonki ni ma ina sakawa?" Hari ta yi maganar tana haɗe rai ganin abin nata yana ƙoƙarin wuce gona da iri.
" To ai ke ma Inna babba ce ko kin yi iskancin ma ba zan faɗa ki ji da bakina ba. Amma ni yaushe na ce masa ina son bireziya ko ya taɓa ganin ina sakawa da zai siyo ya kawo mini? Gaskiya sai dai ki yi haƙuri Inna amma sai na faɗi gaskiya, duk mai saka bireziya ɗan iska ne."
A fusace Kandala ta mayar mata da amsar cewa, "Ita vest ɗin da kike sakawa tana rufe miki kanun mangwaron da ke ƙirjinki ai a matsayin bireziya take."
"To ke me ya hana ki dinga sakawa? Ai ban taɓa ganin kin saka ta ba shi ne sai ni ake so a mayar 'yar iska haka kawai ina gani na yi shiru a cuce ni a banz...na rantse da Allah ba na son ta sai dai ya zo ya karɓi kayansa."
Ta miƙe cikin fushi tare da ture kayan da ke jikinta ta yi gaba tana turo baki. Kallon takaici Kandala ta bi ta da shi, kafin Hari ta sauke ajiyar zuciya ta magantu cikin wani yanayin damuwa ta ce,
"Ina murna 'yata ta fara girma haƙorin hankali ya fara fito mata ashe har yanzu da sauran aiki a gabanmu. To, bari na cire bireziyar na adana, duk ranar da kika gane gaskiya na san da kanki za ki neme ta."
Daga can inda take tsaye rungume da hannu tana aika wa kayan harara ta ce, "Har da wando fa ya saya mini, sai ka ce an faɗa masa ban da wanduna. Wannan fa wallahi ko ba a so na faɗa sai na yi magana. Kowa ya san akwai iskanci a cikin sayen kayan nan, sai dai kawai a ga laifina a banza. Don ko Babana bai taɓa sayo mini wando ba, Kandala ma wando ɗaya ne ta taɓa saya mini, kuma tun da ya tsufa har yanzu ba ta sake saya mini ba. Sai ke da jini ya fara fito mini a jiki kika sayo mini guda uku. Amma shi yana namiji ko kunya ba ya ji ya saka kuɗinsa a banza ya sayo bireziya da wando don kawai ya raina ni. To ba za a saka su ba, ya je da tsiyarsa tun da kayan ma sai da ya saka maƙo da talauci a ciki. Ko kuma wallahi idan na je gidansa ni babu ruwana duk abin da nake so sai ya saya mini tun da shi ne ya yi mini alƙawari."
"Tun da uwarsa ce ke ai dole ya yi miki duk abin da kike so."
Kandala ta faɗa tana aikata mata harara, "Idan ya ƙi ai sai na dawo gida na fasa zaman auren. Ni fa auren ma ya fita kaina ba na son sa, idan na samu wani Alhaji wallahi ko zai yi kukan jini ba zan taɓa aurensa ba. Sai ya je wurin 'yan iskan da suke saka bireziya ba dai ni ba."
Haka ta dinga surutunta ita kaɗai babu wanda ya bi ta kai, saboda fahimtar halin nata ne ya motsa don da ma can ba inda ya je, ta dai ƙara da sababbin halayen da ta samu suna ƙoƙarin ɓoye na asalin.
Ranar da Jabir ya zo ma da faɗa suka rabu, don kai-tsaye ta nuna masa kayan ba su yi mata ba, kuma ba irin su take so ba. Sannan ta ƙara da bayyana masa abin da ke ranta a kan wando da bireziyar da ya haɗo a cikin kayan, inda ta tuɓure masa da masifa tana faɗin ba za ta aure shi ba, tun da ashe kallon 'yar iska yake yi mata shi ya sa ya saka mata wando da bireziya.
Tana gama faɗar maganganun ta shigo gida ta bar shi a soro da