Showing 45001 words to 48000 words out of 88489 words
Chapter 16 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx
marin da ta yi masa ya saka shi yin cikin ta da naushi mai haɗe da harbi da ƙafa. Amma duk da haka tun da ƙarfi ba ɗaya ba, ko'ina kokawar ba ta je ba Bintoto ta kayar da shi ƙasa ta taushe tana ta duka. Yayin da wasu abokansa suka shiga faɗan su ma suka dinga kai mata harbi da ƙafa masu sakar mata duka a baya suna yi. Hakan ya sa ta sake shi ta koma kan wanɗanda suka shigar masa faɗan tana dukan su bayan ta ci kwalarsu. Amma nan take suka kai ta ƙasa saboda ƙarfinta ya gama ƙarewa, da ma can zawo ya cinye rabin ƙarfin. Kafin malamai su shigo a raba har sun jigatar da ita, don bayan mazan da suka shigar wa abokinsu faɗan har da wasu matan ajin sun afka faɗan.
Hakan ya sa ba a ba su gaskiya ba, duk da bayanin da suka yi wa malaman a kan cewa ita ce ta fara jawo faɗan. Ganin yadda suka saka ta yin laushi ko tafiya sai an riƙa ta take yi. Sunan Kandala ko ta kira shi ya fi sai hamsin. Har da hakan ya sa yaran da ke wurin sulhun suka dinga dariyar shirmen da take yi da surutan da take faɗa.
A nan aka yi wa yaran da suka yi faɗa da ita bulala goma-goma, sannan aka ce duk wanda ya sake taɓa ta ko ya yi mata rashin kunya ko dariya a cikin ajin sai an kore shi ya bar makarantar bayan an gama hora shi. Yan ajin ma da babu ruwansu sai da aka yi musu bulala biyar-biyar, a cewar malaman ita Bintoto sabuwar zuwa ce ba za a buge ta ba, sannan kuma dukan da aka yi mata ya wadatar ba sai an ƙara mata ba. Nan take zazzaɓi ya rufe ta, ko da aka tashi makarantar ko idonta ba ta iya ɗagawa. Waɗanda da suka dake ta suka dawo jin tausayin ta suna faɗin ta yi haƙuri, ganin yadda take rawar sanyi da kakkarwa alamun ita kaɗai ta san me take ji. Kasancewar Makarantar haɗe take boko da Islamic, ƙarfe biyu daidai wasu daga cikin 'yan ajin suka kai ta Clinic ɗin makarantar. A can aka yi mata allura biyu tana ta ihu da raki kala-kala yara suna yi mata dariya.
Ƙarfe biyar motar Makarantar ta ajiye ta a bakin titin gidansu Hamida. Ta fito tana jin jiri ta dinga bin bangon gidajen mutane tana tafiya, idan ta gaji ta tsaya ta huta, haka ta dinga yi har ta isa bakin ƙofar gidan. Tana ƙoƙarin bubbuga gate ɗin ta ji wata murya a bayanta tana yi mata sallama. Cike da matsanancin tsoro ta yi hanzarin juyawa tare da faɗin,
"Innalillahi!"
"Yi haƙuri don Allah, ni ma ban yi zaton ke ce ba, sai daga baya na tabbatar da ke ce sannan na biyo ki. Saboda na san za ki tuna ni idan kika gan n...."
"To ban tuna ka ba! Ka tafi kawai ba na tsayawa magana da talakawa."
Cike da mamaki ya dinga kallon ta, saboda ba ƙaramin naushi maganarta ta yi wa zuciyarsa ba. Don tun ranar da ya fara haɗuwa da ita yake fatar Allah Ya mayar da shi garinsu ya nemo gidansu. Sannan bayan barin su garin ya samu damar komawa, amma labarin da ya ji ya saka shi barin garin cikin alhini. Don an sanar da shi wani ya nemi lalata mata rayuwa shi ya sa aka kai ta birni aikatau. Amma abin haushi, yana murnar ganin ta ita kuma ta zo masa da abin da ya jijjiga tunaninsa.
"Yanzu da gaske ba ki gane ni ba Bintoto? Ni ne fa wanda na zubar miki da goro a garinsu kika ce sai na saya duk..."
"Kai ka tafi na ce! Ban gane ka ba, ni ban ma san lokacin da aka yi haka ba. Sannan ka ga ban da lafiya ma, ko magana da kai ni ba na son ma na yi. Ka tafi don Allah."
Ta ƙare maganar da bubbuga gidan tana ƙwala kiran "Anti don Allah ki zo ki buɗe mini zan faɗi."
Ta ɗauki lokaci tana bubbuga ƙofar kafin Hamida ta zo ta buɗe mata, shi kam kansa kawai ya saka cike da baƙin cikin wulaƙancin da ta yi masa. Sannan kuma da alwashin sai ya samo kanta tun da har ya fahimci inda hankalinta ya fi karkata.
Princess Dija.
26.
Kuka ta fashe da shi iya ƙarfinta tana kiran sunan Kandala tun da ta yi ido biyu da Hamida. Saboda takaici goma da ashirin da ya haɗe mata, ga zafin zazzaɓi, ga rashin kuzarin zawon da ta sha da na dukan da 'yan ajinsu suka yi mata. Don ba ta yi tsammanin za su yi mata taron dangi ba, hakan ya sa ta so nuna musu halinta don su dinga jin tsoron ta kamar yadda ake tsoron ta a ƙauyensu. Sai ga shi duk da ƙarfin da take kuri da shi an goge mata harda, da ma an ce taron yawa ya fi taron ƙarfi.
Kallo mai cike da mamaki Hamida ta dinga aika mata don ta kasa barin bakin ƙofar gate ɗin, ganin yadda Bintoton ta zube tana ta kuka da gurje-gurje a ƙasa.
"To ni dai na gaji da tsayuwa, idan ba ki tashi shiga gidan ba na rufe ƙofar, lokacin da kika gama abin da kike yi ki sake bugawa na zo na buɗe."
Bintoto ta yi banza da ita tare da ƙara volume ɗin kukanta dafe da kanta da ke mugun sarawa. "Wannan haukar taki za ta jawo Black ya tashi daga barci, kuma wallahi idan ya zo ko kin bubbuga mini ba zan buɗe ba."
Zabura ta yi cike da matsanancin tsoro ta juya tana kallon ƙofar gidan da karen yake, tana ciccika da shesshekar kuka ta faɗa gidan har tana ƙoƙarin ture Hamida. Ba ta tsaya bi ta kan abin da ta yi mata ba, ta rufe gidan tana faɗin,
"Allah dai ya dawo da maigidan nan lafiya, na gaji da halinki, Allah ma ya san na yi abin da zan iya."
Bintoton da ke ƙoƙarin shigewa cikin gidan ta waigo tana turo baki ta ce, "Don ba ki san abin da ya faru ba ne shi ya sa kike ganin laifina, to sanyi nake ji, har da allura aka yi mini a muguwar makarantar da kuka kai ni. Sannan wasu 'yan yara suka yi mini taro a cikin ajin suka yi ta duka na. Idan kuma kin ɗauka ƙarya nake yi ki je makarantar ki tambayi malamai."
Tana gama faɗar maganar cikin muryar kuka ta yi cikin gidan ta bar Hamida tsaye cikin sanyin jiki. Don yanayinta ya nuna zazzaɓi ne ya kafce ta, duk da ba ta yi mamakin dukan da ta ce an yi mata ba. Saboda ba kowa zai iya jurar halinta ba, ita kanta ba don tana kai zuciya nesa ba da tuni ta karya mata hannu ko ƙafa.
Kai-tsaye ta nufi ɗakinta, ta ɗauko wasu magunguna sannan ta je ta haɗa mata tea da ruwa ta kai mata. Inda ta hango Bontoton ta dunƙule bisa gadon jikinta yana ta ciccira haƙoranta suna kakkarwa, cikin sauri ta zauna bakin gadon tana kiran sunanta. Da ƙyar ta samu ta sha ruwan shayin da maganin, Hamida ta jawo bargon da ke gadon ta lulluɓa mata kafin ta ce,
"Ki yi barci da kin farka za ki ji kin wartsake. Tun da kin ce an yi miki allura a makaranta."
"Kan....Kandala za a kira mini, wur...wurin.... ta na...nake so na kom..."
Sosai ta bai wa Hamida wani kalar tausayi saboda tuno artabun da aka sha da ita a kan ba za ta bar gidan a ranar da su Kandalar suka zo. Har cikin ran Hamida, ta ji kamar abin da take yi mata a cikin gidan ba ta kyautawa, tun da har Bintoto ta iya furta cewa a kai ta wurin Kandala ta manta da abincinta da take maita. Jiki babu kuzari ta miƙe ta fice, tare da ja mata ƙofar ɗakin, bayan ta gyara naɗin atamfofin da Bintoton ta watse. Zuciyarta cike da burin ta ga Bintoto ta samu lafiya idan ana gama ɗinkunan ta fara gayu.
Bubbuga gate ɗin gidan da ake yi ya sa Hamida ta yi hanzarin kammala sallar da take yi ta shafa guntuwar addu'ar da ta yi a gaggauce gudun ta tashi ba ta yi kowace addu'a ba Mala'iku su jefo mata sallarta. Saboda tun tana yarinya ta wannan fatawar kafin malamai da ya tunatar da ita cewa, "Duk wanda ya yi sallah bai tsaya ya yi addu'a ba ba za a karɓi sallarsa ba. Mahaifiyarta ma cewa ta yi a fuska a jefa wa mutum kayansa yana tashi ya watsar da ita a nan, saboda babu fiffiken da za ta tashi sama ta je inda ake.
Cikin sauri ta isa bakin ƙofar ta buɗe bayan ta ce waye, ya sanar da ita shi saurayin Bintoto ne. Mamakin da zancen nasa ya sa ta buɗe ƙofar tare da ƙare masa kallon sama da ƙasa kafin ta ce,
"Kai ne saurayin Fatima?"
Yana washe baki tare da sosa kansa da makullin mashin ɗin da ya zo da shi ya ce, "I Bontoto ba, ai na san ta tun a ƙauyensu kafin ta zo gidan nan aiki. Har garinsu na yi neman ta aka ce da ni ta dawo nan birni tana aikatau."
"To ya aka yi ka san tana gidan nan?"
"Ɗazu na gan ta lokacin da motar makarantarsu ta ajiye ta, har magana ma mun yi da ita ta ce mini ba ta da lafiya."
"Ikon Allah."
Hamida ta faɗa cikin sakin fuska, saboda yanayinsa ya nuna gaskiyar abin da yake faɗa. Ledar da ke hannunsa ya miƙa yana cewa, "Don Allah a ba ta, ni zan wuce Allah Ya ƙara afuwa."
Ta zura hannu ta karɓi ledar tare da rufe ƙofar, daidai lokacin da motar Aliyu ta durfafo unguwae tare da sakin titin ta isa bakin ƙofar gidan ta tsaya. Saurayin Bintoton yana ƙoƙarin juyawa da mashin ɗin sa Aliyu ya fito daga motar a zafafe ya shaƙo wuyan rigarsa, yana ƙoƙarin kai masa naushi saurayin ya yi hanzarin cewa,
"Wurin Bintoto na zo, ni saurayinta ne tun tana ƙauyensu."
Ran Aliyu a matuƙar ɓace ya sauke hannunsa tare da hankaɗa shi gefe yana nuna shi ya ce, "Daga yau kada ka sake zuwa gidan nan! Idan ba haka ba duk abin da ya samu iyalina kai ne. Ita ma wadda ka zo wurin ta kora ta zan yi, sai ku je can ƙauyen ku dinga haɗuwa amma ba a gidana ba. Idan kuma na sake ganin ƙafarka a nan sai na yi maka abin da za ka yi mamaki."
Har ƙasa saurayin ya kai yana roƙon Aliyu ya yi haƙuri ba zai sake zuwa ba. Tare da sanar da shi yanzun ma ba ta da lafiya shi ya sa ya zo yi mata ya jiki.
"Na dai faɗa maka kada ka sake zuwa."
Daga haka ya bar wurin ya koma cikin motarsa, kansa a duƙe yana kiran wayar Hamida saurayin ya wuce aguje da mashin ɗin sa a cikin firgita da kalaman Aliyun.
"Buɗe mini ƙofa!"
Iya abin da ya faɗa kenan a cikin muryar da tana jin sautinta ta ji ƙirjinta yana dakan kuguden uku-uku. Don ba ta yi tsammaninsa ba a lokacin, sannan jikinta ya ba ta cewa wataƙila ya ga saurayin Bintoto a ƙofar gidan shi ya sa kansa ya fara hayaƙi tun kafin ya shigo gidan.
Sanin zafin kishinsa da yadda suke hawa sama su faɗo ƙasa da shi a kan ko 'yan'uwanta maza ba ya so suna zuwa gidan.
Da sassarfa ta isa bakin ƙofar gate ɗin ta buɗe masa, maimakon ya shigo kamar yadda ta tsammata, sai da ya ja lokaci a cikin motar yana ta danne-danne da wayarsa, duk da ya hango ta riƙe da gate ɗin tana jiran shigarsa.
Amma ko kaɗan abin ya yi bai sa ta yi fushi ba, ta fito gidan tare da doso motar tasa don ta ga me ya hana shi shigowa. Sai dai tun kafin ta isa ya fisgi motar da ƙarfi ya raɓa ta gefenta ya shige. Nan take haushi ya kama ta, tana shiga gidan ta rufe gate ɗin zuciyarta babu daɗi.
Lokacin da take ƙoƙarin isa inda motar a cikin rumfa, ya yi hanzarin fitowa ɗauke da jakunkuna biyu ya yi cikin gidan. Babu jinkiri ta rufa masa baya ranta a ɓace ta shiga ɗakinsa, a nan ma yana jin ƙarar buɗe ɗakin ya miƙe daga kan gadon da ya faɗa yana sauke numfashin gajiya. Sannan ya koma cire agogon da ke hannunsa ya yi toilet.
Zaune ta yi a kan gadon cikin sanyin jiki tana jiran ya fito, amma tuno yana buƙatar abinci ta fice da sassarfa ta yi kitchen. Nan take ƙamshin girkinta ya game gidan, saboda ba ta san zai dawo ba, sannan ganin Bintoto babu lafiya ya sa ko girkin ma ba ta yi ba, don da ma ita ce mai cin abincin, ita kuma ba ta cika cin abincin dare ba sai a lokacin da ta ga dama.
Bayan ta gama kammalawa ta ajiye masa centre table, inda ya saba cin abincinsa koyaushe. Sannan ta koma ɗakin ta tarar da shi har ya yi wanka ya sauya kaya kuma yana sallah, jira ta yi har ya gama addu'a ya shafa, sannan ta fara yi masa sannu da zuwan da babu shiri ta tsuke bakinta ganin irin kallon da yake yi mata kafin ya ce,
"Sau nawa zan sanar da ke ba na ra'ayin kowane namiji ya zo mini gida?"
"To ai wannan mutumin Bintoto ne tun a ƙauye. Kankana, lemu da ayaba ya zo kawo mata saboda ba ta da lafiy...."
"Wallahi ko mutuwa ta yi ba a gidana zai zo gaisuwar ta ba! Ballantana wani ciwo can! Ke har yanzu fa ban manta da ɓawon ayabar da ta jefar na faɗi ba. Da ma can jira kawai nake yi na dawo na mayar da ita wurin Hajiya. Saboda ni ba zan iya zama da ita ba watarana ta sa mu karye ko ta zuba mana guba a abincin da muke ta kashe m..."
"Haba-haba Baban Baby, wallahi Bintoto ba za ta kashe mu b..."
Cikin sauri ya katse ta da cewa, "Sau nawa muka ji labarin 'yan aiki suna zuba wa masu gida guba? To idan ma ba ki yarda za ta aikata ba ni dai ba zan iya zama da ita ba gaskiya. Sannan wancan ɗan ƙauyen idan ya sake zuwa wallahi sai na sa an ɗaure shi. Saboda wani lokaci da an san maigida ba ya gari ɓata-garin mutane suna zuwa yin ɓarna, musamman a wannan ƙarnin da muke fama da rashin tsaro. Ko shi kansa ɗan ƙauyen za a iya turo shi don ya san wani abu dangane da gidan a yi makami da shi. To da muguwar rawa gara ƙin tashi, duk wanda ya zo matuƙar kika leƙa kika ga namiji ne, kuma ba ki san shi kada ki buɗe gidan. Ni na ce ki koma kawai idan da hali ma ki ƙara saka kwaɗo ki datse gidan. Saboda shi mugun bai da kama."
Ajiyar zuciya Hamida ta sauke kafin ta ce, "In sha Allah! Ga abinci can yana jiran ka."
Maimakon ya tashi su je sai ya ɓuge da cewa, "Ina Baby?"
"Barci take yi."
Ta amsa masa a daƙile tare da miƙewa ta fice daga ɗakin. Shi ma ya rufa mata baya, yana fita ɗakinta ya nufa, sai da ya dudduba a ya gano babu wani sabon rauni a jikinta, sannan ya yi mata kiss a goshi ya ja ɗakin a hankali ya fice.
Sosai hankalinsa ya kwanta, saboda tunanin da ke ransa a koyaushe, don har mafarki ya taɓa yi a kan cewa Bintoto ta sako ta daga bayanta, tana faɗuwa ta mutu.Tashin hankalin da ya shiga a ranar tamkar ya rufe ido ya buɗe ya gan shi cikin gidan. Amma saboda bai gama abin ya kai shi ba ya dinga damun Hamida a waya, tare da kashedin kada ta kuskura ta bai wa Bintoto ita bai yarda da ita ba, duk kukan da za ta yi ta bar ta a hannunta, sannan ta ƙara ba ta kulawa.
A daren ranar sun nuna juna kaunar ma'aurata, sannan sun nuna sun yi kewar juna, hakan ya sa da safe Hamida ba ta sha wuya wajen shawo kansa ba. Duk da ya so ya yi tirjiya, amma da dabara ta saka ya aminta da zaman Bintoto har zuwa wani ɗan lokaci, don kai-tsaye ta sanar da shi ita ma Bontoton ta ce ta gaji da zama gidan a kai da wurin kakarta. Sannnan ta ƙara da cewa,