Showing 84001 words to 87000 words out of 88489 words

Chapter 29 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2061

da Allah Ya hore musu na gado da kujeru daidai ƙarfinsu sun aika mata kuɗin tun lokacin da aka ɗaura auren.

Hari kuma ta kai ta wurin masu gadaje aka zaɓar mata gado na daidai kuɗinsu har da kujerunsa guda uku, kujera ɗaya mai zama mutum biyu, sai ƙwara biyu masu zaman mutum ɗaya-ɗaya. Hari ta ce a bar musu kayan har zuwa lokacin da aka tashi buƙatarsu a karɓa.

Hakan ya sa Kandala ta bar mata sallahun ta yi komai a can birnin yadda ya dace. A nan garin nasu kuma aka fara shagali nan take aka raba goro da alawa. Mutane suka dinga kawo wa Kandala gudunmawar bikin tamkar ba ta taɓa aurarwa ba sai a kan Bintoto. Saboda mace ce mai ƙoƙarin miƙa abin ta a duk inda ta ji hidima ta tashi. Da ma can al'ada ce irin ta mutanen garin duk wanda ya yi maka kai ma idan tasa hidimar ta tashi sai ka mayar masa. Don wani lokaci ma har gida ake zuwa a yi wa mutum takakkiya idan bai biya bashin bikin da aka yi masa ba lokacin hidimarsa. Gudun jin kunya ke sa kowa yake yin ƙoƙarin rama biki tun kafin a yi wa mutum tonon sililin da zai jawo masa ɓacin suna, wanda zai sa a daina ba ka bikin idan an gano kana da matsala ba ka mayarwa.

Tsakanin atamfofi, kuɗi, shinkafa ɗanya, farin wake, manja, manƙuli da dawon fura; haka aka bai wa Kandala su har sai da ta rasa bakin godiya, tsabar ganin su a baje kowa da kalar tasa bajinta. Tukuici ta dinga bayarwa cikin farinciki da jin daɗi, bakinta ko rufuwa ba ya yi ganin duk wannan taron na Bintoto ne.



Ga al'ada irin ta ƙauyen ba sa komai na shagulgula a aure sai a ranar wunin bikin. A safiyar bikin aka dinga ɗora manyan tukane ana ta girka wa mutane abinci. Bayan an gama masu kiɗan ƙwaryar da aka gayyato suka baje tsakar gidan Kandala suna ta kiɗa, mata suna rawa gwanin burgewa. A gefe ɗaya kuma amarya ta ci kwalliyarta tare da ƙawayenta suna cikin ɗaki ko kallon masu rawa ba a bari ta fito yi. Saboda a wurin su amarya ba ta rawa, ko fitowa tsakar gida ba ta yi sai dai mai son ganin ta ya shiga ɗakin da take ya gan ta ya fito.

Bintoto kam duk da ta sha kwalliyarta irin ta amare mai ɗige-ɗigen baƙin kwalli da janbaki a saman goshi da kumatu, bayan ƙamshin da ke tashi a jikinta, amma fuskarta a cure take ko magana ba ta yi wa kowa, har ƙawayen nata su Jamila ƙirjin biki. Kwanciyarta kawai ta yi tana ƙunci saboda tun abin da Kandala ta yi wa Alhajin da ya rage mata hanya, ba ta sake sakin jiki ta yi hira da ita sosai ba. Harin ma ban da ina kwana da sallama da ta yi mata lokacin da za su baro garin ba ta ce da ita komai ba. Duk yadda ƙawayenta suka so ta saki jiki ta ba su labarin birni ƙin kula su ta yi. A haka suka zauna cikin ɗakin jugum-jugum tamkar masu zaman makoki. Sai idan an shigo ganin amarya idan an ce ina take su nuna ta.

Da marece bayan 'yan kiɗan ƙwarya sun haɗa kayansu masu kalangun suka dasa nasu kiɗan a ƙofar gida.

A nan ma mata suka firfito bakin ƙofar gidan suka fara rawa ana zuba musu liƙi. Kandala ta yi ɓarin kuɗin liƙi a ranar kamar ba ta san zafinsu ba. Tsabar jin daɗi da farincikin ganin Allah Ya gwada mata auren Bintoto.

Kula ma da ɗan cikinta amma sai da ta fito ta yi rawar kalangu saboda kawai ta faranta wa Kandala ta ji daɗi. Ganin yadda tun da ta zo garin babu wata matsalar da ta haɗa su. Lafiya lau take yi mata magana cikin fuska tamkar ba ita ba, ganin haka ya sa ita ma ta shiga duk dafe-dafen da aka yi sai da ta sa hannunta. Bintoto ce kawai har lokacin magana ba ta haɗa su ba, asali ma ko inda take ba ta zuwa gudun ta ce ga wani laifin da ta yi mata ta sa Kandala ta ci mata zarafi a cikin jama'a. Mani kuma sai kwanonin abinci yake fitarwa a waje da tire-tire yana kai wa abokansa ganin banza ta faɗi gasasshiya.

Sai da aka kira sallar magriba sannan masu kiɗan kalangun suka kwashe kayansu. Taron bikin ya fara watsewa ana ta yi wa Kandala sallama, saboda ba garin za a kai ta ba, don da a ce cikin garin za a kai ta ana gama sallar Isha mata za su dawo a yi sabon zama don zuwa yi wa amarya rakiya zuwa gidan mijinta idan 'yan ɗaukar amarya sun zo biko.

****

A can birni kuwa, Jabir ya nemo babbar mota aka kwashi kayan Bintoto zuwa gidansa, tare da Hari da wasu mutanen arziƙinta. Maza aka nemo majiya ƙarfi suka shigar kayan gadon da kujerun har cikin ɗakin da Jabir ya nuna musu. Hari ta jinjina wa Jabir ganin yadda ya shafe gidan fes da siminti tare da sabon fenti har a cikin ɗakin Innarsa. Gidan ƙarami ne amma an keɓe wa Bintoto ciki da falo har da madafi da ban ɗakinta cikin ƙuryar ɗaki.

A gefe ɗaya kuma ɗakin mahaifiyarsa ne a jere da nasu katanga kawai ta shiga tsakaninsu. Innarsa tana ta yi wa su Hari sannu har aka gama saka gadon da kujerun da labulanta guda huɗu, aka koma ɗauko kwalayen kuloli aka dinga jerawa cikin madaidaicin kitchen ɗin, sauran kwanoninta cikin ƙuryar ɗakinta aka saka cikin wardrobe don babu wurin ajiye su.

Hari ta shimfiɗa ta sa aka share ɓangaren duka suka saka turare aka rufe aka bai wa Jabir makulli. Sannan ta sallami abokan aikin da abin da ya samu Jabir, Innarsa da ƙanwarsa suna ta godiya. Tare da wasu daga cikin danginsa da suka zo gidan suna ta hada-hadar nasu shagalin bikin da za su yi washegarin ranar, wato ranar da aka yi shagalin bikin Bintoto a ƙauyen nasu.

Tun da safe Jabir ya samo mota uku aka ɗauko Hari daga gidanta suka nufi ƙauyen. Kasancewar mota biyu bus ne na jigila, ɗaya ce kawai wadda ya aro a inda ake bayar da hayar motoci, don a saka masa Bintoto a ciki. Haka suka ɗunguma zuwa ƙauyen Maidala, misalin ƙarfe goma na safiya. Zuwa lokacin gidan Kandala ya ɗauki taron mata ana zaman jiran zuwan 'yan ɗaukar amarya.

Ihu da sowar yara ta sa aka gano sun iso. Nan take gidan ya ɗauki guɗa mata suka cika gidan da guɗa ta ko'ina ana kiran ina amarya ta fito ga masu kai ta nan sun zo. Bintoto da ke cikin ɗakin Kandalar ƙunce saman gado ta dunƙule tana ƙunci. Wata ƙanwar Amadu waton gwaggonta ta isa bakin gadon cikin farinciki ta fara kiran sunanta. Ganin ba ta motsa ba ta jawo ta jikinta tana faɗin,

"Tashi 'yar albarka mai goshin arziƙi ga mijinki nan ya aiko da motoci. Ki gode wa Allah duk ƙauyen nan ba a taɓa samun miji irin naki ba. Don ita uwar Jabirun a bakin titi aka nemo motar da ta kai ta gidan miji. Amma ke ga motoci can a ƙofar gida har guda uku an turo duk wanda yake son zuwa zai samu mazauni."

Tsaki kawai Bintoto ta yi ta yunƙura gwaggon tata ta sauko da ita daga kan gadon tana faɗin, "Ina turare a ƙara fesa miki?"

Kandala ta yi gaba tana tura baki saboda ba ta da niyyar yin magana. Ganin za ta fice fuskarta a buɗe saɓanin lulluɓin da ake son gani ta yadda babu mai ganin fuskarta. Ta yi hanzarin riƙo ta baya tana rufe mata fuska ta ce,

"Don Allah tsaya kada ki jawo mana abin gori a cikin garin nan. Kowace amarya tana kukan barin gida ke idonki ƙamas kuma ki fita haka?"

Tana ƙoƙarin fita da ita Inna Hari da Kandala tare da wasu yan'uwa na jini suka kutso ɗakin. Hari ta ce da da ƙanwar Amadun ta mayar da ita a yi mata huɗuba. Aka zaunar da ita bakin gadon Kandala kowa yana ta faɗar abin da ya iya dangane wa'azin aure da nasihohin zama da miji. Yayin da Kandala ta koma gefe tana ta sharar ƙwalla cike da kewa da alhinin rabuwa da ita.

Sai da kowa ya tofa albarkacin bakinsa a kanta tare da bayyana mata gidan miji ba kamar gidan da ta bari ba ne. A can dole ta yi wa mijinta biyayya matuƙar tana so ta gama da duniya lafiya. Komai ya ce ta yi masa ta yi ba tare da ta yi jayayya ba. A ƙarshe suka rufe nasihohin da yi musu addu'ar zaman lafiya.

Princess Dija.

40.

Kandala tana ta sharɓar kuka tamkar wata ƙaramar yarinya ana ta rarrashin ta. Haka aka fito da Bintoto daga gidan zuwa gidan Amadu. A can ma wasu nasihohin aka yi mata kafin a kama hanyar birni. Ganin da gaske an rabo ta da garinsu kuma an raba ta da Kandala, ta tuɓure wa mutane a cikin mota da borin ita sai an mayar da ita gida, tana ihun kiran wayyo ita Kandala take so ta gani.

Gwaggwanninta ne suka dira kanta da faɗa tamkar za su cinye ta da ranta, yayin da Hari ta koma 'yar kallo. Saboda ganin yadda suke sakin maganganun da ke nuna ƙarara su ba za su ɗauki iskancin da take yi wa Kandala ba.

Tana sharar hawaye da gunguni a bakinta har aka isa birni. Sannan ta ware tana kallon garin tana ƙiyasin yadda unguwar da za a kai ta take, cikin takaici ta ja tsaki saboda ganin sun saki titi da wucewa unguwannin masu kuɗi, sun kama wani lugu mai gangara suna ta gangarawa. Sannan suka dinga bi ta bakin ƙofar wasu gidaje, waɗanda a ranta ta dinga faɗin,

'Mutanen wannan unguwar ko ya ya suke iya rayuwa a cikin ta?'

Tamkar za ta yi ihu, a lokacin da ta ga mai motar ya tsaya a cikin unguwar, a gefen wani gida mai dogon kwatami, wanda ya ratsa tsakanin gidajen da ke layin har zuwa bakin gidan. Cike da mamaki ta kai kallonta ga Inna Hari, bakinta yana rawa tana cewa,

"Inna wurin wa muka zo a baƙar unguwar nan?"

Hari wani kallo ta yi mata kafin ta girgiza kai ta yunƙura za ta fice ta ce, "Fito mu je ki ga inda muka zo da idonki ki huta da tambaya."

Babu shiri ta ɓata fuska tana yatsine-yatsinen ta ce, "A'a ku tafi dai, zan jira ku a nan."

"Ke dalla fito malama kada ki raina wa mutane wayo. Gidan uban wa n muka zo ba gidan mijinki ba? Ko so kike yi ki nuna wa mutane halinki tun a nan ƙofar gida ki nemi tara mana jama'a? Wallahi ki shiga hankalinki saboda yanzu da baya ba ɗaya ba ne girma ya hau kanki."

Zancen wata ƙanwar Amadu kenan tana maka mata wata kalar harara, da ma can ba sa shiri da Bintoton, saboda ko a cikin dangin Baban nata ita ce masifaffiya kuma ta jima da sanin ba ta son ta.

'Ki ci kanki ba dai ni ba uwar masifa.'

Abin da Bintoto ta faɗa kenan a ranta tana fitowa daga motar, saboda mugun kallon da take wurga mata mai kama da shirin kai mata duka. Inna Hari ta rufa mata fuska sannan ta ja ta sauran matan suka rufa musu baya. Bintoto da ƙyama ya tsallake kwatamin ƙofar gidan tana toshe hanci har suka shiga cikin gidan. Ƙamshin fentin da gidan ke yi ya sa ta ɗan ware bayan an kai ta ɗakin Innar Jabir an zaunar da ita. Mata suna ta guɗa ana ta ihu sannan ana ta leƙen ta saboda kowa yana so ya ga fuskarta.

Kanta a duƙe tana sauraron muryar Innar Jabir da wasu daga cikin danginsu suna ta zuba addu'a da nema musu zaman lafiya da albarka a cikin auren nasu. Kafin wata taubashiyar Jabir ta isa inda take ta yaye rufin fuskarta tana faɗin,

"Ke buɗe idonki mu gani wa kike jin kunya a nan?"

Bintoto ta ɗaga kai tana wurga mata harara da jajayen idanuwanta da kuma ruwan hawayen da ya gama ɓata mata fuska. "Ashe amaryar ma ta Jabir ƙwaila ce, to kalle ni da kyau kafin ki ba shi abinci sai kin fara zuba nawa kin aika mini har gida. Ba harara ba ko cire idon za ki yi babu ruwana tun da kika yi gangancin aurens..."

"Na rantse da Allah ki rufe mini fuskata ni ba na son rashin hankali. Tun da na zo kike ta mini surut... wallahi zan cire mayafina mu dambatu da k..."

Kukan da ya taso mata gabaɗaya ya hana ta ƙarasa maganar. Cike da mamaki sauran mutanen da ke cikin ɗakin suka dinga kallon ta. Yayin da kunya ta rufe danginta da suka kawo ta har cikin ɗakin. Inna Hari ta miƙe da hanzari bayan ta wayance maganar da cewa,

"To tashi mu je tun kafin tsautsayin amarci ya sa garin damben a buge miki fuska."

Tana gama maganar ta mayar mata da lulluɓin fuskar, sannan ta kama ta suna ƙoƙarin ficewa daga ɗakin. Abokiyar wasar Jabir ta biyo su tana faɗin,

"Idan damben kike son yi ki jira mijinki ya dawo ku yi ta fama, ni kam ba zan yi kokawa da ƙwaila ba ta cije Ni a banza ta bar ni da allurar totunos."

Dariya wasu suka saka, yayin da suka bar wasu da tunanin Bintoton wace irin kala ce a cikin mata. Saboda ganin yadda ta furta maganar cike da rashin kunya, babu shayin kowa ballantana ta ji nauyin surukantaka.

Har ƙuryar ɗaki Inna Hari ta kai ta, mata da yara suka dinga tururuwar zuwa ganin ta. Aiko ta shiga aika musu harara duk wanda ya haɗa ido da ita a kallo ɗaya yake juyawa, saboda mugun kallon da take bin kowa da shi tana kumbura fuska.

Da dabara Inna Hari ta samu yaran suka fice daga ɗakin ta rufe ƙofar ƙuryar tana haɗe fuska ta isa gabanta tana faɗin,

"Wallahi-wallahi sai kin gyara halinki matuƙar kina so ki yi zaman lafiya da kowa a cikin gidan nan. Saboda rashin hankalin da kike yi a can gida wannan gidan babu wanda zai ɗaukar miki shi. Ki duba ki gani tun kafin a je ko'ina har kin fara raba wa kanki abin magana cikin dangin mijinki. Yanzu idan ban da rashin mutunci ita wannan baiwar Allah da kika gwaɓa wa magana tsararki c....?"

"To ita ba ki ji irin maganganun da take yi mini ba? Haka kawai har da ce mini ƙwaila."

"To ai ke ƙwailar ce, don kin tabbatar mata ba ki da cikakken hankali ta hanyar amsar da kika ba ta. Tun da ke ba ki san wasa ba, daga magana ki hau kanta da zancen dambe a gaban sarakuwarki? To billahillazi idan ba ki iya sarrafa fushinki da kame bakinki ba ke ce a ruwa. Don mu tafiya za mu yi mu bar ki da su, ba zama za mu yi muna yi miki nasiha ko rabon faɗa ba idan kin jajibo. Sannan Kandala da ta saba tare miki rigima ba ta san ma an yi ba, ke kaɗai za ki zauna kuma ke za ki ji da kanki, mijin ma da kike gani ba zai taɓa shiga cikinki ba ya bar 'yan'uwansa. Sannan ba ki kyautata musu ba shi ma ba za ki ji daɗin zama da shi ba. Saboda haka tun wuri ki kama kanki da aikata abin da zai dame ki, kuka ki kulle bakinki matuƙar kika san ba alheri ne za ki faɗa ba."

Zancen wata yayar Amadu kenan saboda ita kanta ba ta ji daɗin abin da Bintoton ta faɗa ba. Haka suka saka ta gaba kowa yana tofa albarkacin bakinsa. Kafin su buɗe ɗakin a dinga shigowa ana yi mata Allah Ya ba da zaman lafiya.

Da misalin ƙarfe ɗaya na rana aka kawo musu abinci. Suna ci suka yi sallah kowa ya fara haramar tafiya. Daidai lokacin Jabir ya shigo gidan mata suka dinga yi masa guɗa, abokiyar wasarsa kuma ta dinga tsokanar sa da mijin ƙwaila. Yana ta dariya baki har kunne ya isa sashensa, inda aka sanar da su Hari ga shi nan ya zo su yi sallama. Da ma can ita ta kira shi saboda kunyar mutane ta hana shi shiga gidan.

Kansa a ƙasa ya shiga gaishe da su suna ta amsawa cikin sakin fuska. Kafin su koma ba shi amanar Bintoto tare da nuna masa sai ya yi haƙuri kuma sai ya dinga ɗora ta a hanya. Duka ya ce ya ɗauka ai aikinsa ne tun da shi ne mijinta. Ya ciro kuɗi ya damƙa musu suna ta godiya ya ce idan sun tashi tafiya motocin da za su mayar da su suna ƙofar gida. Suka shiga yi wa Bintoto huɗubar zama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login