Showing 48001 words to 51000 words out of 88489 words

Chapter 17 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2071



"Yanzu idan ta tafi a wannan lokacin, na san bakinta ba zai faɗi alheri a kanmu ba, kuma babu kalar sharrin da ba za ta iya maƙala mana ba. Sannan Hajiya za ta ce cutarta muke yi shi ya sa ta guje mu. Amma idan muka bari ta warware ciwon, kuma ta dawo nutsuwarta ba za ta ta so barin mu ba. Ko gidan muka tura ta, sai ta yi boren a dawo da ita. Kuma daga haka za a gano ba ma cutar ta."

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce, "Wannan shawara ta yi. Amma ki ce don Allah babu ruwanta da Baby."

"Babu damuwa."

Daga haka suka jingine zancen Bintoton, ya shiga ba ta labarin tafiyar da ya yi da abubuwan da suka faru. Amma ko kaɗan bai faɗa mata mafarkin da ya yi ba, saboda ba ya so ya tayar mata da hankali a kan shirmen mafarki.

Princess Dija ✍️

27.

Kwana biyu Bintoto tana fama da kanta Hamida tana ta ƙoƙarin ba ta kulawa har ta samu lafiya. Don ko ɗakinta ma ba ta fita ballantana ta yi abin da zai sa a ce ba ta kyautawa. Abinci ma sai Hamida ta matsa take ɗan tsakura, cike da jin daɗi Hamida ta dinga ba ta kulawa, tare da cika baki a wurin Baban Baby a kan cewa Bintoto ta shiryu duk rashin jin da take yi yanzu ta daina. Shi dai kallo ne kawai nasa a duk lokacin da ta faɗi hakan ba ya cewa uffan, saboda har cikin zuciyarsa bai da nutsuwar zama da ita a cikin gidansu.

Malaman makaranta ma da suka kira shi a waya, suna tambayar kwana biyu ta daina zuwa makaranta, bai ja zaren da tsawo ba, cewa kawai ya yi,

"A yi haƙuri zazzaɓi take yi. Idan ta ji sauƙi za ku gan ta."

Daga haka ya datse kiransa, saboda duk abin da ya shafe ta ba ya son shiga, makarantar ma da ya kashe kuɗinsa matsin Hamida ne ya sa ya biya kuɗin don ya faranta mata. Sannan da Hajiyarsa da kullum suka yi waya ba ta bari a kammala lafiya ba tare da ta sako zancen a kula da Bintoton ba. Har da haushin hakan ya sa yake rage manyan ƙudurin da yake da su a kanta, don a ranar da ya faɗi ba don tafiyar gaggawar da ya yi ba; ya so yi mata mugun dukan ko ganin sa ta yi sai ta dinga firgita.

Hakan ya sa tun da ya dawo ko hanyar ɗakinta bai kalla ba, duk da Hamida ta faɗa masa ba ta da lafiya, amma hakan bai sa ya rage jin haushin da take ba shi ba. A gefe ɗaya kuma tsoron ta illata masa Baby.

Kwana biyun da ta yi a kwance ita kaɗai ake bari gidan a kulle ta ta baya, amma tana ɗakinta ko'ina ba ta zuwa. Sai a rana ta huɗu da ta ji sauƙi wato ranar Asssbar. Daga Hamida har Aliyun duka suna gida, shi ma bai fita kasuwa da wuri ba yana ta barcinsa a ɗaki.

Bintoto ta fito daga ɗakinta jiri yana ɗan ɗibar ta saboda ciwo ya tafi da kuzarin. Ta zauna falo tana wara ido zuciyarta cike da son ganin Kanlada.

Ko da Hamida ta fito daga ɗaki ta tarar da ita zaune ta yi tagumi, Hamida ta ƙaraso inda take fuskarta cike da jin daɗin ganin ta wartsake ta zauna tana faɗin,

"Fatima, ya ƙarfin jikin naki?"

Bintoto ta matse hawayen idonta kafin ta ce, "Ni dai don Allah a kai ni inda Kandala. Idan ma mutuwa ce zan na yi a hannunta."

Dariya ta bai wa Hamida, amma ta fuske tana cewa, "Ke da za ki gode wa Allah kin samu lafiya shi ne za ki dinga kiran mutuwa bayan kin ji sauƙi?"

Shiru ta yi mata kafin ta sake share hawaye ta ce, "To ni dai makarantar nan da kuka kai ni ba zan koma ba, tun da yaran nan suka dake ni kuma suka dinga yi mini dariya. Sannan wannan yaron da ya ce shi saurayina ne ƙarya yake yi, don Allah ma ya sani ni ba 'yar iska ba ce."

Dariya Hamida ta fara yi riƙe da baki tsabar mamakin furucinta na ƙarshe, kafin ta ce, "Wa ya ce da ke 'yar isk...?"

"To ai duk macen da take da saurayi 'yar iska ce."

"An shiga uku ko Fatima, shikenan da mace ta yi saurayi ta zama 'yar iska? Ko kin manta ke ma kin sha faɗar kina so ki yi aure ki je Makka?"

"Ai ni miji na ce, miji nake so ba saurayi ba. Amma shi wannan don kawai ya sa a ce ni 'yar iska ce zai zo gaban mutane yana cewa wai saurayina. Uwanin Jimmai Jarka ta garinmu ma ai saurayinta ne ya yi mata ciki har ta haihu. Shi ne ni yanzu zai zo ya yi mini ciki ya ɓata mini suna a banza....yiiiii!"

Ta fashe da kuka iya ƙarfinta, tsabar takaicin da ke cin ranta, tun a ranar da Hamida ta sanar da ita abin da ya faɗa take cike da haushin saurayin da ya kira. Don ita gabaɗaya ta ɗauki zunubi mai girma ta ɗora ga sunan saurayi, saboda a garinsu mijin wance ake cewa, ko a ce mai son ta.

Hamida kallon ta kawai ta dinga yi tana dariya, kafin ta ji motsin Baban Baby zai fito daga ɗakinsa; ta yi hanzarin kai kallonta gare shi dariyar a kan fuskarta.

Cikin falon ya ƙaraso tare da nufar TV ya kunna ya dawo kan kujera ya zauna, ba tare da ya bi ta kan kukan da ya ga Bintoto tana sharɓa ba.

Sai da ya gama kamo tashar da yake son kallo ya kai kallonsa ga Hamida yana cewa, "Ki ce ta bar falon nan idan ba za ta yi mana shiru ba."

Bontoto ta yi masa wani kallon gefen ido mai ɗauke da harara, kafin ta karkace gefe ta sako tusoshin da take ta ƙoƙarin dannewa a gaban Hamida.

Hamida ta ja hannunta cikin sauri suka nufi kitchen, da niyyar su bar masa falon. Bayansu ya bi da kallon yana yatsinar fuska tare da faɗin,

"Kada ta shigar mini kitchen ta je ta yi wanka. Gabaɗaya wari take yi."

Yana gama maganar ya miƙe ya ƙara ƙarfin Ac da fesa abin ƙamsasa wuri. Bayan ya gama ya yi tsaki a ransa yana cewa,



"Fitinanniyar yarinya, ita koyaushe sai ta saka mutane aiki."

Kamar yadda ya hana su shiga kitchen, haka Hamida ta ja ta suka yi ɗakin Bintoton. Bayan sun zauna Hamida ta ce,

"Ba ki yi wanka ba ne?"

Bintoto ta kai mata harara tana faɗin, "Na yi wanka."

"To me ya sa ba ki fesa turarenki ba?"

"Shinshina ni ki ji sau biyar ina tatso shi a jikina. Idan ma kin ji ina wari tusa ce maigidanki ya yi."

"Maigidana kuma?"

"E, tun da ya shigo falun ɗin nake jin wari. Amma shi ne zai ce ni nake wari kada na shigar muku kicis."

"Ke matsalarki shirme ya yi wa kanki yawa. Wa ya faɗa miki babban mutum yana tusa a gaban mutane? To ba shi ba ne, kuma kada na sake jin irin wannan maganar daga bakinki."

"Na bari."

Ta faɗa tana yi mata wani kallon gefen ido mai ɗauke da harara. A ranta tana tuna yadda Kawu Mani ke buga tusoshi a gaban kowa. Har sai Kandala ta kora shi tana faɗa sannan yake barin wurin, amma shi ne za ta ce wai babba ba ya tusa.

"Fatima."

Kiran da Hamida ta yi mata ne ya sa ta kai kallonta gare ta. "Mu dawo zancenmu na farko wanda shi ne ya sa kika ga na zo nan. Saboda ba na so na bar ki a duhu, shi saurayi ba wai yana nufin ɗan iska ba, mu a nan wanda yake son auren mace shi ake kira saurayi kafin su yi aure, amma da an yi auren shikenan ya zama miji. Sannan kuma ita ɗiyar Jimmai Jarka da kika ce an yi wa ciki, ita ce ta so saurayin ya yi mata cikin, don duk macen da take bari namiji ya taɓa jikinta dole ne watarana sai ta yi ciki. Na san ke kuma babu yadda za a yi don kawai wani saurayi ya ce yana son ki ki bar shi ya yi ta taɓa miki ƙirji da wurin fitsari. Don haka kada ki ji wani wuri an ce saurayi ki munana zato ga mutane tun da idan za a yi iskancin ma ba a gabanki za a yi ba, kuma shaidar zur haramun ne. Sannan na san halinki sarai za ki iya jawo mana fitina muna zamanmu lafiya. Kin gane abin da na faɗa ko ƙara yi miki bayani?"

Bintoto ta ɗaga kai cikin sanyin jiki, Hamida ta miƙe da sauri saboda kiran da maigidan ya ƙwala mata. Jin kukan Baby ya sa ta gano dalilin kiran, cikin sauri ta karɓe ta daga hannunsa ta zauna ba ta abincinta. Daidai lokacin aka dinga bubbuga musu gate, Hamida ta ƙwala wa Bintoto kira ta ce ta je ta je ta gani.

Ta fita tana gunguni ta buɗe gidan, wata budurwa ce ta gani riƙe da yarinya. "Lafiya." Ta faɗa tana haɗe rai.

"Wurin Anti muka zo."

Suna ƙoƙarin kutsa kai Bintoto ta sha gabansu tana cewa, "Shin ku dakata na ce, idan ba ta nan wurin wa za ku shiga idan kun je ciki?"

Sai a lokacin budurwar ta ɗan ja ta tsaya tana yi mata wani kallo kafin ta ce, "Allura za a yi wa ƙanwata. Idan tana ciki ki faɗa mata. Don yau Assabar babu inda take zuwa."

Sai da Bintoto ta yi mata wani kallo kafin ta yi ƙwafa ta ce, "To sai me don allura za a yi wa ƙanwarki? To barci take yi, kuma maigidan ma yana gida suna tare. Don haka ki jira na ce na sanar da ita, idan ta amince shikenan."

Budurwar ta yi mata wani kallon raini sannan ta riƙe ƙugu ta ce, "Ke nake jira 'yar aiki. Don dai na san ke 'yar aiki ce daga ganin ki ba ku haɗa komai da ita ba."

Har Bintoto ta yi gaba ta waigo tana faɗin, "Ni kike kira 'yar aiki? Yaushe kika ga na yi miki kama da masu aiki? To billahillazi ban yafe miki ba!"

Ta ƙare maganar cikin ƙwafa ta yi ciki, amma maimakon ta shiga ta faɗa wa Hamida saƙon sai ta ƙi, sai da ta ja sakonni a tsaye sannan ta fito tana haɗe fuska ta ce,

"Ta ce wadda za a yi wa allurar kaɗai za ta shiga cikin gidan."

"Kya ji da shi ciwon ajali a ɗan yatsa. Matsalar baƙauye duk inda yake sai ya nuna halinsa."

Bintoto ta yi kamar ba ta ji ta ba, suna shigewa ta sakar wa ƙanwarta ƙoso biyu a tsakiyar kai. Yarinya ta tsala ihu Bintoto ta toshe mata baki tana zare mata ido kafin ta koma faɗin,

"Ku ji yarinya da sharri, ki buge kanki a bango shi ne za ki yi wa mutane kuka a ce ni ce na dake k..."

Fisgar da ta ga budurwar ta yi wa ƙanwarta ya sa ta tsaya tana kallon ta, a ƙufule budurwar ta ce,

"Dukan ta kika yi ko?"

"A'a kashe ta na yi ta dawo duniya. Daga ke har ita sai na haɗa ku na tumurmusa a wurin nan. Ta buge kanta shi ne za ki ce ni na dake ta? To an dak..."

Ba ta kai ƙarshe ba ta ji budurwar ta shaƙo wuyan rigarta. Daidai lokacin da maigidan ya ƙaraso saboda kukan yarinyar da daɗewar Bintoto sun saka shi fitowa bai shirya ba. Ganin budurwar tana ƙoƙarin kai mata duka ita ma tana harbinta da ƙafa ya daka musu tsawa. Suka rabu babu shiri, bai tsaya binciken komai ba ya hau yi wa Bintoto faɗa, saboda zuciyarsa ta ba shi ita ce da laifi. Hakan ya ba budurwar damar yi masa bayanin komai. Kunne Bintoto ya murɗe tana ihu da roƙon ya yi haƙuri har ta kai ƙasa sannan ya sake ta.

Cikin fushi ya dinga faɗa tamkar ya rufe ta da duka. Saboda yana sanin ko dawowa ba ta yi ba amma ta ce an ce yarinyar kaɗai za ta shiga ban da budurwar. Takaici ya sa ta fashe da kuka ta yi ɗakinta da gudu. Hamida da ke ƙoƙarin lallaɓawa ta ajiye Baby a kan kujera ta tafi ta ga abin da ke faruwa, babu shiri Baby ta farka daga barcin da ta fara, firgicin kalar kukan da Bintoton ta shigo da shi ya sa ita ma ta ci gaba da nata kukan. A kiɗime ta saɓa ta a kafaɗa ta nufi hanyar fita, ganin budurwar da ƙanwarta a bayan Baban Baby ya sa ta gano Bintoto ce ta sake haddasa wani abu.

Babu ɓata lokaci ya yi mata bayanin komai, ranta a ɓace ta yi wa yarinyar allura tare da bayar da haƙuri. Saboda ba ƙaramin mutuncinta 'yan unguwar suke yi ba, musamman ma gidan su yaran, kuma sun saba zuwa tana yi musu allura har Mamarsu ita take yi mata allura. Wani lokaci idan ciwon ya yi nauyi gidan take zuwa ta yi musu komai suna jin daɗi suna saka mata albarka. Amma shi ne Bintoto za ta sa mutuncinta ya zube a kan shirmenta.

Bayan tafiyarsu ta kira ta tana ta yi mata faɗa, Baban Baby gidan ya bar musu don ba ya ƙaunar buɗe ido ya gan ta a tsakiyarsu. Bintoto ko ta ci buri da alwashin sai ta rama duk abin da aka yi mata a kan budurwar ko ƙanwarta. Tun da aka nuna su ake so ita kuma ba a bakin komai ba. Da takaicin abin ta kwana, da Alla-Alla a kan ganin safiya ta waye su dawo gidan, don ta ji Hamida ta ce gobe ma a dawo da yarinyar akwai sauran allurai.

Uhum🤦🏻‍♀️

28.

Ranar Lahadi, tun da safe aka kira Hamida ana sanar da ita Babansu bai da lafiya. Hakan ya sa ta fara shirin tafiya gida cikin tashin hankali, duk da an sanar da ita da sauƙi, ko a waya tana iya kira ta yi masa sannu ba sai ta je ba. Amma Aliyu ya ce ta dai shirya su je har da shi ya yi masa ya jiki. Ko da ƙarfe goman safiya ta yi har sun gama shiri, Hamida ta so su tafi da Bintoto amma Aliyu ya ce ba za ta shigar masa mota ba, ta ce to ya tafi su biyo shi da motarta ya ce sam bai san da zancen ba. Don tafiyar ce kwata-kwata ba ya so a yi da Bontoton, a cewarsa ba a shiga gidan kunya da ita, saboda kafin a fito ta tafka wata ta'asa.

Ba don ta so ba, haka suka bar Bintoto a gidan tana ɗaga musu hannu, a gefe ɗaya kuma tana aika wa Baban Baby harara a duk lokacin da ta faki idonsa tana muimui da baki.

Bayan sun wuce ta rufe gidan, har da yin tsallen jin daɗin ganin an bar ta ita kaɗai ta yi abin da take so. Cikin sassarfa ta nufi ɗakin Hamida, da ma can tana so ta shiga ta ga ya yake, amma ba ta ga fuskar hakan a wurin masu gidan ba. Tsaye ta yi tana kallon komai na daki-daki riƙe haɓa tana faɗin,

'Hu'um! Lalle ma matar nan, ashe ta san nata ɗakin ya fi nawa kyau, shi ne ko sau ɗaya ba ta taɓa bari na shigo na gani ba. Ji wasu jakunkuna don Allah, sai ka ce sayarwa take yi."

Cikin sauri ta isa ma'ajiyar takalmin Hamida ta tsaya riƙe da ƙugu tana faɗin, "Kai-kai-kai Waɗannan takalman duk me za ta yi da su haka da yawa? Gaskiya matar nan muguwar gaske ce, yanzu tana da irin waɗannan takalmin da yawa shi ne ni ba za ta ba ni ko da huɗu ba? To billahillazi sai na saka su na gani idan suna yi mini kyau, ita komai nata mai kyau sai ka ce ita kaɗai ake so a cikin duniya."

Haka ta dinga saka takalmin ɗaya bayan ɗaya tana gwada tafiya da su a tsakiyar ɗakin. Da abin ya yi mata daɗi har jakunkunan ta dinga saƙalawa tana yarfi da hannu da yatsine-yatsinen fuska tana ɗage hanci sama tamkar wadda ta ratsa a tsakiyar mutane tana jin warinsu, tsabar kaifi da kurin da take bazawa daga ita sai ɗaki da madubin da take yada zango a gabansa. Don takalmin ma sai ta ɗaga ƙafa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login