Showing 42001 words to 45000 words out of 88489 words

Chapter 15 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2077

ta tsamuko naman ɗuwawun Baby da ƙarfi. Yarinya ta fasa ƙara tare da zabura tamkar wadda aka tsirawa allura. Cikin sauri ta rufe mata baki idonta zare tana faɗin,

"Laalaalaa! Me aka yi miki ke kuma kike kuka? Yi shiru...daina kukan to kada a ɗauka na ci zalinki n..."

Karaf ta haɗu da ƙanen mijin Hamida zai fito daga cikin gidan, cike da tsoro ta zabura tana faɗin,

"Wallahi ni ban yi mata komai ba, idan na yi ƙarya kuma ka tambaye ta ka ji gaskiya."

'Yar dariya kawai ya yi tare da karɓar Babyn ya koma cikin gidan yana jijjiga ta da buga bayanta yana faɗin, "Shiiii...yi haƙuri Baby...kurrrr.." Haka ya dinga yi mata a kunne har ta rage kukan Bintoto tana biye da shi har cikin babban falo. Inda suka ci karo da Hamida tana ƙoƙarin fitowa cikin sassarfa tana duba agogon hannunta.

Ba ta tsaya bi ta kansu ba ta fice tana faɗin, "Sai na dawo."

Hajiya ta karɓi Baby idonta a kan Bintoto tana faɗin, "Maraba da mai sunan manya, sannu da zuwa uwata."

Sai a lokacin Bintoto ta saki ranta ganin yadda Hajiyar take farincikin ganin ta tamkar wata mai babban matsayi a cikin danginsu. Har ta zauna kan kujera, ta tuna huɗubar da Hari ta yi mata a kan gaishe da mutane, hakan ya sa ta zame ƙasa tana gaishe da Hajiyar cikin ladabi. Cike da jin daɗi Hajiya ta amsa tana tambayar lafiyarta, da yanayin zamanta cikin gidan Hamida. Bintoto ta nuna mata babu matsalar komai don kada ta faɗi wani abu Hamidar ta kore ta. Amma hakan bai hana ta cewa wani abu ba.

"Gaskiya Hajiya matar gidan tana da kirki, amma tana yi mini faɗa idan na yi laifi."

Hajiya ta faɗaɗa fuskarta da murmushi tana cewa, "Faɗan ma za ta daina yi miki idan kin daina laifin uwata. Ki nutsu da kyau Hamida ba ta da matsala, shi ya sa aka kai ki wurin ta kuma za ki ji daɗin zama da ita fiye da yanzu..."

Haka ta dinga yi mata nasiha a fakaice tana jan ta wasa da barkwanci har Bintoton ta fara warewa, har da nemo tsintsiya tana share filin gidan don kawai Hajiya ta yabe ta. Da abin ya yi ma daɗi har da aikin bai wa fulawowi ruwa, da wanke wata tsohuwar motar da ke ajiye cikin rumfar gidan. Sai dariya 'yan aikin gidan maza suke yi mata ganin yadda ta dage sai darzar motar take yi da tsalle tana 'yan waƙe-waƙenta na shirme.

Jin daɗin aikin da ta sha, Hajiya ta sa aka cika mata ƙaton plate da abinci ta lamushe tana lasar hannu, ganin kamar ba ta ƙoshi ba ta ajiye mata kula ta ce ta ɗibi iya son ranta. Bintoto ta baje sai da ta ji za ta yi amai sannan ta bar abincin dolenta ba don tana so ba. Ta shiga nishi jingine da kujera tana hamma, kafin ka ce me barci ya yi awon gaba da ita tana jan minshari tamkar wata raƙuma.

Ko da Hamida ta dawo ƙarfe biyu tana ta barcin, don hannun da ta ci abincin ko wanke shi ba ta yi ba ta ɓingire. Hajiya ce ta sa mai aikinta ta wanke mata hannun aka shafe mata baki tare da gyara mata kwanciya. Sai faman yabon ta take yi da jinjinawa ga irin aikin da ta sha. Hamida dai ba ta ce komai na kushe ba, sai dariya take yi tana girgiza kai ganin yadda Hajiyar ta taƙarƙare tana ta yabon Bintoton babu ruwanta, sannan kuma ga ta da son aiki.

Ba su bar gidan ba sai yamma, sannan da abincinsu na dare da aka haɗo su da shi aka hutar da Hamida shiga kitchen. Hajiya ta yi wa Bintoto kyautar atamfofi da dogayen riguna ta ce a ɗinka mata ta samu na gayu ko za ta samo mata Baba, a matsayin da ta ba ta na uwa mai darajar da ba ta son abin da zai taɓa mata ita. Bayan ɗan kunne da kayan kwalliya har da turare ta saka mata cikin kayan. Ga lemun Shani da ta zuba mata gwangwani uku a leda, bayan ƙaramar gorar Pepsi-Cola guda biyar da fanta biyu. Amma hakan bai hana ta gane-gane a kan titin komawarsu gida ba. Don duk abin da ta gani ana sayarwa a bakin titin sai ta ce, 'Anti ga kaza can ki saya mini don Allah. Wayyo gwaba ta nuna yawuna ya tsinke Anti. Laa! Kin ga kifi can an wuce da kin saya mini shi don Allah.'

Sai da Hamida ta gaji da halinta sannan ta ci birki a bakin wani bahon mai kilishi ta saya musu, kowa da ledarsa, sannan ta daina damun ta suka isa gida lafiya ba ta sake cewa komai ba. Saboda auna kilishin kawai ta dinga yi a baki tana kurɓa Fanta har da rufe ido tare da waƙa, da rawa da kai alamun banza ta gama samuwa.

Kayanta ta ɗauka cike da jin daɗi ta nufi ɗakinta ta datse ƙofa. Gado ta faɗa tana birgimar jin daɗin kayan da Hajiya ta ba ta. Ta shiga haukar ta ita kaɗai tare da kiran Kandala da kwalbar turaren da ta mayar waya tana faɗin,

"Hilo! Hilo Kandala kina ji na? Shin ba kya ji kika ce? Yawwa to gara da kika fara jin me zan faɗa miki. Da ma cewa zan yi ki taya ni murna na zama 'yar gayu har da atamfofi Hajiyar nan ta ba ni wai a ɗinka mini na samu miji mai kuɗi....Wayyo daɗi."

Ta yi wani tsalle ta sake faɗawa gadon ta baya da kwalin turaren a kunnenta tana sake cewa,

"Ni fa wallahi sai na yi abin da duk nake so. Kin ga idan na fara zuwa makaranta zan iya Turanci, idan na je America a can zan siyo miki takalmi mai tsini. Ko ba kya so?"

Ta ƙare maganar tana ɓata fuska kamar gaske kafin ta sake cewa, "To ki ce da Kawu Mani ya kora Kulu gidansu tun yanzu kafin na zamo Hajiya. Don wallahi sai na sa an yi mata bulolin tsiya a duk ranar ta bari muka sake haɗuwa. Baƙar muguwa mai fuskar tumaturi. Ai an bar mata gidan ita kaɗai sai ta ci kanta baƙar mayya. Wai Allahna! To ni dai sai anjma Kandala tun kafin ki cika mini kunne da hawayenki."

Ta danna kwallin wayar kamar gaske wayar ce ta gama, don yadda ta ga Hamida tana yi ne take kwaikwayo saboda ta zama 'yar gayu kamar ita.

Ba ta daina shirmen da ta saba ba sai da ta ji Hamida tana ƙwala mata kira a falo, saboda sai da ta yi wanka ta yi wa Baby sannan ta fito da niyyar su ci abinci. Amma har lokacin ita Bontoto babu abin da ta yi, don bayan wayar kwalin da ta yi ta koma baje atamfofi tana ɗaurawa a gaban madubi, don tana so ta gano wadda ta fi yi mata kyau a cikin su. Hakan ya sa gabaɗaya ta yamutse atamfofi ta jibge wuri ɗaya tamkar kayan wanki. Doguwar rigar da ke ciki kuma ta saka tana juyi gaban madubi tare faɗin,

"Ai wannan duk ta fi yi mini kyau."

Tuno kiran da Hamida ta yi mata ya sa ta zabura ta nufi falon. Ganin tana cin abinci ta tuno ashe ita ma ba ta ci abincin daren ba, duk da ba ta jin yunwa, don tsiren da Hamida ta saya mata duka ta cinye har ƙulin tun kafin su ƙarasa gidan.



Next page🙋

25.

Kallo ɗaya Hamida ta yi mata ta ɗauke kai, duk da ta so ta yi mata faɗa a kan doguwar rigar da ta gani a jikinta. Amma tsabar ba ta son surutu ta yi banza da ita, har sai da ta gaji da zaman tana satar kallon kular abincin da wanda take ci, sannan ta gyara zamanta tana cewa,

"Anti wai da gaske rigar nan ta yi mun kyau ko?"

Ba tare da ta ɗaga kai ta kalle ta ba ta ce, "Musamman idan kika bar ta a jikinki kika kwana da ita, za ta fi yi miki kyau."

Ta miƙe cike da jin daɗi tana kallon jikinta ta, saboda ko kaɗan ba ta fahimci gatse ne ta yi mata ba. Baki har kunne ta ce da Hamida,

"Gaskiya ni kaina na san ta yi mini ɗan banzan kyau. Amma kin san mene ne? Idan Kandala ta gan ni da ita zan ce mata rigar Saudiyya ce na sayo a lokacin da na je aikin Hajji."

Dariyar da ta so kufce wa Hamida ce ta sa ta ƙware, ta shiga tari tana bubbuga ƙirjinta har ta sha ruwa ta samu tarin ya lafa. Amma Bontoto ko sannu ba ta ce mata ba, sannan ba ta daina juye-juye tana kallon rigar ba.

"Ki ci abincin ni ba na son sakarci da yawan surutu."

Bintoto ta zuba abincin tana 'yan waƙoƙinta. Jin daɗin girkin ya saka ta shiga jujjuya kai tana rangaji tana ci gaba da waƙenta.

"Ke kina da matsala wallahi, wai wa ya faɗa miki ana magana idan ana cin abinci? To ki ci gaba, idan kika sarƙe wallahi ko sannu ba zan yi miki ba tun da ba ki da hankali."

Tana gama faɗar maganar ta miƙe tare da plate ɗin da ta gama cin abincin ta nufi kitchen tana sake cewa,

"Idan kin gama ki tabbatar kin kwashe komai kin wanke. Yau da wuri nake so na yi barci, ke ma ki kwanta cikin lokaci, don idan kika yi lattin tashi a goben ma ba zan kai ki makarantar ba."

Maganganun da ta yi kenan har ta wanke plate ɗin ta ajiye ta fito ta nufi ɗakinta da niyyar shigewa. Bintoto ta yi hanzarin miƙewa tsaye tare da ɗaga murya tana lasar hannu ta ce,

"Anti kallon fa! Ba ki kunna mini ba."

"Ba zan kunna ba, tun da barci kike yi ki bar shi har safe yana aiki."

Daga haka ta shige ɗakinta ta rufo ƙofa. Bintoto ta riƙe ƙugu tana aika mata harara ta ce,

"Wallahi idan ba ki bi ni a sannu ba sai na yi miki abin da maigidan nan zai ya mayar da ke gidanku. Na san a can babu tirbin kallon, sannan kuma tuwon dawa ne ake ci a shari malmala ba irin abincin gidan nan mai shegen daɗi ba. Tana wata tafiya haka....haka...tamkar za ta karye don lauɗi. Ni wallahi gabaɗaya ma haushi take ba ni yanzu."

Ta ƙare maganar bayan ta gwada yadda Hamidar take tafiya tana yatsine fuska, tare da yarfa hannu tana aika wa ƙofar ɗakinta harara.

"Ke kika sani."

Ta murguɗa baki tana kwashe kayan abincin ta yi kitchen. Har za ta juyo ta fito, ta tuno da umarnin da ta ba ta a kan ta wanke komai. Tana tsaki da gunguni ta wanke ta ajiye inda ake tsane kwanoni. Maimakon ta fito kitchen ɗin sai ta koma wasa da ruwa tana yi tana wanke fuska da ƙafa kamar mai arwala. Sai da ta jiƙe kitchen ɗin ko'ina sannan ta kashe fanfon ta fito, tana bubbuge ruwan da ya ɓata mata riga.

"Wayyo sabuwar rigata ta jiƙe, kuma ga shi masifaffiyar matar can ta ce na kwana da ita. To amma ni ko wallahi sai na cire ta babu yadda za a yi na kwana da ita a jikina ta jiƙe. Sai dai komai za ta yi ta yi ba zan yi abin da ta ce ba."

Daga haka ta sauya rigar ta jawo lemunan da Hajiya ta ba ta ta dinga kwankwaɗa, sai da ta ji babu wani sauran fili a cikinta sannan ta ajiye saura tana zuba gyatsa kala-kala. Atamfofin da ta dunƙule wuri ɗaya ta ɗora hilo a kansu ta kwanta tana zuba hamma. Daga nan sai barci.

Asubar farin Hamida ta tayar da ita, tun kafin a yi sallah. Sai da ta tabbatar ta tashi sannan ta koma tana sabgoginta a kitchen. Ganin yadda ta ɓata kitchen ɗin ta ji a ranta ina ma ba ta ce ta yi wanke-wanken ba.

Bintoton kam kamar kada Hamida ta tayar da ita, tana shiga bayi ta dinga kwarara zawo. Kafin ka ce me ta jigata, ko da ƙarfe shidan safe ta yi gabaɗaya ta zuge a lokaci ɗaya. Amma a haka ta yi ƙarfin halin shiryawa gudun ta yi laifin da za a fasa kai ta makaranta. Hamida kanta tana ganin ta ta ce,

"Ke lafiya me ya same ki haka duk kin yi laushi?"

Tana turo baki ta ce, "Ba zawo nake yi ba!"

"Da ma shegen kwaɗayinki ai dole ki yi zawo. Ke komai kika gani sai kin ci, to garin ciye-ciyenki sai kin yi zawon hanjin cikinki gabaɗaya kowa ya huta da halinki."

Ta dangware mata plate ɗin Irish da ƙwan da ta soya, sannan da kofin shayin da ke hannunta ta yi ɗakinta. Mintuna a tsakani ta fito, cike da mamaki ta dinga kallon Bintoto da abin da ta ajiye mata, don kafin ka ce me har ta cinye ta koma lasar hannu. Hamida tana isowa wurin Bintoto ta bazama da gudu ta yi ɗaki. Saboda wani arnen zawon da ya taso mata wanda tun kafin ta isa bayin ya dinga bin ƙafafuwanta.

Hamida ta biyo ta, ganin inda ta nufa da warin da ke tashi ta tabbatar da wani zawon ne za ta yi. Kafin ta ankara da wanda ya bi ƙafafuwanta duk inda taka. Cikin sauri ta fice tana duba jikinta ranta a ɓace ta yi ɗakinta.

'Allah Ya gani ni dai na gaji da zama da yarinyar nan. Tsabar ƙazanta har da kashi za ta dinga yi mana barbaɗe a cikin gida?"

Sai da ta wanke jikinta ta kunna turaren ƙamshi a gidan ta ko'ina, sannan ta ƙwala mata kira daga inda take tana cewa,

"Wallahi sai kin gyara duk inda kika ɓata. Kuma idan kika sa na yi lattin fita na rantse da Allah sai kin bar gidan nan don na gaji da zama da ke."

Bintoto ta fito bayan ta cire kayan da ta ɓata ta wanke, sannan cikin rawar jiki ta dinga gyaran duk inda ta hango zawon. A bisa umarnin Hamida da ke faɗa mata kaza za ta yi ta saka kaza ta barbaɗa kaza har ta gyara wurin tsaf. Cike da ƙyama Hamida ta miƙa mata wasu magunguna ta ce ta shanye su duka. Jikin Bintoto yana rawa ta kora su da ruwa.

Misalin ƙarfen bakwai da mintunan safiya suka bar gidan. Bayan Hamida ta tabbatar da jikin Bintoto babu inda yake wari. Don turare ta yi mata kala-kala sannan ta bar ta shiga motarta. Amma duk da hakan idan ta tuno da halin Bintoton tana jin ba za ta iya ci gaba da zama da ita ba.

Gambo Academy, sunan Makarantar da aka saka ta, saboda da ma can sun biya kuɗin komai kai ta kawai ya yi saura, ba tare da dogon turanci ba aka ba ta uniform da littafai, saboda makarantar kuɗi ce komai su suke bai wa ɗalibansu. Amma aji biyu aka ajiye ta na Firamare, saboda wasu tambayoyi da aka yi mata ba ta amsa su ba. Hamida ta tafi ta bar ta bayan an kai ta cikin aji ta zauna. Bintoton ta dinga kallon yaran da ke cikin ajin 'yan kuci-kuci duka ba su wuce shekara bakwai zuwa takwas ba, a ranta ta ce,

'Cabɗijam! An ma raina mini wayo. yanzu waɗannan yaran ne 'yan ajinmu? Ai kuwa dole a ba ni monita, idan ba haka ba wallahi duk sai na ci ubansu."

Tana zaune tana wara ido bayan ta dawo daga tunanin da ta lula, ta fahimci yaran ajin duk ita suke kallo suna dariya, ganin ta gandama a cikin su. Hakan ya ƙara ɓata mata rai, ta shiga aika musu harara kafin ta miƙe ta tsaya gaban ajin riƙe da ƙugu tana cewa,

"Da wa da wa ne suka yi mini dariya?"

Cike da mamaki 'yan ajin suka dinga kallon ta kafin wani daga cikin yaran ya ce, "Me za ki yi idan an faɗa?"

"Idan ka sani kawai ka sanar da ni, yanzu babu ɓata lokaci zan sanar da kai abin da zan yi."

Sai da ya isa gabanta da wata kalar tafiya sannan ya tsaya gabanta ya ce, "Ni ne nan! Me za ki iya y...."

Kafin ya rufe bakinsa ya ji saukar mari fau! Takaicin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login