Showing 57001 words to 60000 words out of 88489 words
Chapter 20 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx
ta bari idan Jumu'a ta yi sai ta je can ta yi hutun ƙarshen mako. Amma atafau ta ce ba ta san zancen ba, ita lalle sai sun tafi da ita. Sai da Hari ta haɗa mata da jan ido sannan suka tafi suka bar ta. Bayan ta sake yi mata faɗa da jan kunne a kan ta nutsu ta yi abin da ake so, idan kuma ta sake yin wani laifi ƙauye za su komawa gabaɗaya a fasa zaman birnin.
Har sun fice gidan Bintoto ta ƙwala wa Kandala kira suka tsaya, ta isa inda suke da gudu ta kama kunnen Kandala tana yi mata raɗar cewa,
"Wani ya ce yana so na, amma talaka ne ba na son shi."
Kandala ta dungure mata kai tana faɗin, "Sannu ɗan wake ka fi ubanka. To Amadun Jaririy ma har gobe da riga ɗaya yake yawo a gari. Amma ke har kin samu wuri kina kiran wani da sunan talaka. To ki jira mai kuɗin da bai da hankali ya zo ya ce ke yake so."
"Ni wallahi sai mai mota zan aura."
"Ki so mai jirgin sama ba mota ba. Mu tafi Hari, wannan 'ya taki watarana sai na ɓalle mata haƙarƙari idan ba ta bi ni a sannu ba. Wai ita nan da ita har ta san ta ce ba ta son talaka, saboda ƙaruna ne uban da ya kawo ta duniya."
Hari dai biye take da Kandala kawai tana dariya, ganin yadda Bintoto ta dinga aika mata harara tana turo baki tun da ta kira sunan Babanta. Da ma ita idan ana son ganin ɓacin ranta a lokaci ɗaya a kira sunan Amadun Jaririya.
A ƙufule ta juya bayan ta ɗaga murya tana cewa, "Na fasa zuwa gidan naku ma ko an kai ni ba zan zauna ba."
"Kada Allah Ya sa ki zo mashirmanciyar banza."
Haka suka rabu suna faɗa, amma hakan bai hana Kandala waigen gidan ba bayan Bintoto ta shige. Da kuɗin da Hajiya ta ba su suka hau abin hawa har suka raba canjin da ya rage. Bayan sabulu da klin da ta ba su ta ce su yi wanki. Har cikin zuciyar Kandala, ta yi farinciki da albishirin da Bintoto ta yi mata a kan mai son ta. Da ma ita babu burin da take kwana take tashi da shi kamar a ce Allah Ya ara mata rai ta aurar da ita, ko da za ta ga ɗiyan da za ta haifa da idonta.
Hakan ya sa tun a kan hanya ta fara yi wa Hari zancen auren Bintoto da abubuwan da ya dace ta saya da ɗan abin da take samu a inda take aiki. Hari ta ba ta shawarar su fara sayen tukane da wasu abubuwan da ba za su yi saurin lalacewa ba. Ai kuwa Kandala ta kwance ƙullin zanenta da ke maƙale a ƙugunta tana faɗin,
"To ke zan bai wa kuɗin ki sayo mata ko tare za mu je na zaɓo waɗanda nake so?"
Hari tana dariya ta ce, "Ƙafata ƙafarki Inna, ai da ke za mu je a yi komai da ke ki gani da idonki."
"To, shikenan Hari. Hakan ma ya fi mini gaskiya, idan kuma sai na koma gida na sayar da akuyoyina da tumaki sai na haɗa kan kuɗin wuri ɗaya mu ga abin da zai samuwa."
Hari ta ba ta shawarar ta bari sai Bintoto ta zo gidan, sai su haɗu gabaɗaya su tafi ƙauyen su yo ganin gida, sannan duk abin da ta ga ya dace ta yi kafin su baro garin sai ta yi. Da haka suka tsayar da magana, ran Kandala fes tsabar farin ciki da jin daɗin ta kusa aurar da Bintoto. Bayan ko mijin ba ta sani ba, sannan kuma ba ta san komai a kansa ba hatta sunansa.
Bintoto kam, ba ta tashi jin kewar Kandala ba sai da dare ya yi. Lokacin da ta kwanta bayan dattijuwar mai aikin Hajiya, ganin ta ɗora mata ƙafa a jiki ta ture ta tana faɗa, sai abin ya ba ta haushi. Cikin fushi ta tashi ta bar mata ɗakin, a ƙarshe a falo ta kwana kan kujera tana juyi tare da mafarkin Kandala kala-kala.
Da safe ma ba don tana so ta je makaranta ba. Gabaɗaya karatun ya fita kanta, saboda matsa mata da ake yi sai sun yi sallar Zuhur da Asr a cikin jam'i. Sannan ga shi ba komai ta sani ba, malamai su yi ta matsa mata da tambaya yara suna yi mata dariya. Amma tana tuna kalolin abincin da take ci daga ɗanɗane ta yi musu wayo; ta dinga murna har da tsalle-tsallenta ta isa bakin titi. Inda Bus ta ajiye ta a nan ta zo ta ɗauke ta suka wuce.
Lokacin da aka tashi ma tana fitowa ta hango wata mota ta nufo ta. Cike da tsoro ta ja baya, abin mamaki ta ga an yi gaba an tsaya, idonta a kan motar har wanda ke ciki ya fito. Babu shiri ta zaro ido tana nuna shi da hannu tana faɗin,
"Wai da ma kai ne?"
"Ni ne."
Ya faɗa yana wani boƙarewa tare da murmushi a kan fuskarsa. Bakinta ya kasa rufuwa har ta isa jikin motar ta shafa ta tana faɗin,
"Wannan motarka ce?"
Ya ɗaga mata kai yana ci gaba da murmushi ya saka hannu cikin aljihunsa ya fiddo dubu biyu 'yan ɗari biyu guda goma ya miƙa mata. Jikinta yana rawa ta karɓe tare da yin wani tsallen jin daɗi tana faɗin,
"Yaushe ka yi kuɗi kai kam?"
"Tun a ranar da kika ce mini ba kya son talaka."
"Innalillahi!" Ta faɗa tare da rufe bakinta cikin tsantsar farinciki tana kallon kuɗin kafin ta koma lissafawa.
"Yanzu don Allah duk ni kaɗai ka bai wa waɗannan kuɗin?"
Ya ɗaga mata kai yana murmushi cike da jin daɗin ya samu kanta cikin ɗan lokaci. Kafin ya nufi motar yana cewa,
"Zo mu je na ajiye ki gidan."
Babu dogon nazari ta buɗe motar ta shige tana kallon sa, cike da mamakin ganin ya yi kuɗi kamar almara. Hakan ya sa ta sake kallon cikin motar da kujerun baya kafin ta dawo da kallonta gare shi ta ce,
"To amma yaushe za mu yi auren?"
"Ko gobe kike so zan aure ki. Saboda ina da ƙaton gidana, kuma ga mota na saya, kuɗi ma ina da su ko nawa kike so zan ba ki."
"Da gaske."
Ta faɗa tana wata zabura, tsabar ya gama kai ta maƙurar daɗi ganin burinta ya cika za ta auri mai kuɗi. Tuno abin da ke ranta ta yi hanzarin gyara zamanta tana cewa,
"Za ka kai ni Makka?"
"Abu mai sauƙi. Har wasu ƙasashen ma zan kai ki mu je mu yi yawon shaƙatawa idan kina so."
"Yeeee!"
Ta yi ihu mai cike da tsalle, daidai lokacin da ya ajiye ta a ƙofar gidan ta fita da gudu, tana ƙoƙarin shigewa ta dawo da sassarfa tana haki ta ce da shi,
"Ba ka faɗa mini sunanka ba."
Yana 'yar dariya ya ce, "Sunana Jabir."
Sai da ta kira sunan sannan ta rufe fuskarta ta buɗe, tana wasar baki ta ruga da gudu ta faɗa cikin gidan. Ko sallama ba ta yi masa ba ballantana godiya saboda murnar banza ta samu burinta ya cika cikin sauƙi.
Baki sake ta samu Hajiya har cikin ɗakinta ta sanar da ita aurenta ya kusa. Mamaki da al'ajabi ya kama Hajiya, saboda ganin idonta ƙyam a kanta babu kunya ko shayi, ta sanar da ita ba za ta sake zuwa makaranta ba ta samu miji mai kuɗi za ta yi aure. Da dabara Hajiya ta nuna mata ai aure dole ne sai ta yi. Amma makarantar ma ba za ta fasa zuwa ba ko da ta yi auren. Kuɗin da ya ba ta ma ita ta miƙawa ta ce ta ajiye mata a hannunta. Hajiya ta karɓa tana dariyar shimenta ta ce ta je ta cire kayan makaranta ta ci abinci. Idan ta gama ta zo su yi labarin ta ji wane ne mijin kuma ɗan wane gida ne a garin. Amma saboda ba ta san komai a kansa ba Hajiya ta tsoratar da ita sosai, gudun ta faɗa matsala idan ba mutumin kirki ba ne a shiga uku. Amma daga bayanin da ta yi mata ne ta fahimci shi ne wanda Aliyu ya ba ta labarin ya je gidansa. Hakan ya sa ta ce mata idan ya dawo ta ce ya zo tana neman sa.
Washegari kuwa, ana sauke ta ya zo da motarsa ya ɗauke ta. Bayan sun isa ƙofar gidan ta sanar da shi saƙon Hajiya. Babu ko ɗar ya fito ta yi masa jagora har cikin gidan, Hajiya ta fito suka yi magana a keɓe, a nan ta fahimci lalle shi ma da tasa hujja karɓaɓɓiya. Ta yi masa addu'a da godiya sannan ta sanar da shi wasu abubuwan da da ma can ya san su. Saboda komai na Bintoto yana biye da shi sau da ƙafa tun daga ranar da ya yi tozali da ita a ƙauyensu har zuwa birnin da Allah Ya sake haɗa su.
A daddafe Bintoto ta ga Jumu'a ta zo, saboda ta matsu ta ga Kandala ta fesa mata labari. Hajiya ta shirya mata tafiyar sosai don Hari ta kira a waya ta sanar da ita za su je ƙauye. Hamida ta karɓo mata ɗinkunanta da ta bayar aka ɗinka mata, amma ko da ta kawo mata ba ta gidan. Don kullum sai ta kawo Baby wurin Hajiya take zuwa wurin aiki, amma da yake Bintoto tana makaranta ba su taɓa haɗuwa ba. Lokacin da za ta dawo gidan kuma Hamida har ta tsufa da barin gidan ta koma gida, don da ƙarfe biyu zuwa uku na rana take tashi daga aiki. Yayin da ake tayar da su Bintoto da ƙarfe biyar na yamma.
Misalin ƙarfe huɗu da rabi na yammacin ranar Jumu'ar, Hajiya ta sa direbanta ya kai ta har gidan su Hari, domin ta kai Bintoto. Sannan kuma da niyyar ta yi musu bayanin saurayin Bintoton mai suna Jabir, don a san abin yi tun kafin tafiyar ta yi ƙwari.
Murnar ganin ta ya sa Kandala fashewa da kuka tana faman fyace majina da gefen zaninta. Saboda ganin ta cikin sabuwar shigar kamala, ta yi kyau tubarakallah a cikin hijabinta sabo tamkar ba Bintotonta ba. Hari ma kanta ta yi farinciki da ganin sauyin da ta samu, shiriyar da take so ta samu Allah Ya fara kawo mata ita.
Bayanin Jabir da suka ji a bakin Hajiya abin ya ƙara faranta musu rai. Bintoto dai sai faman wasar baki take yi, amma ta kasa cewa komai sai ƙunshe fuska take yi alamun kunya.
Hajiya ta sa aka shigo da kayan tsarabar da ta haɗa wa Bintoto, sannan ta kawo kuɗi ta ba Hari ta ce ga shi nan ladar 'yan kujiba-kujibar da take yi musu a cikin gida, saboda watan da suka ɗauke ta aiki ya cika har ya haura, tun daga barin ta hannun su zuwa gidan Hamida da dawowarta hannunta. Duk da ba wani aikinnkirki ta yi ba, amma hakan bai hana Hajiya yi mata ihsani ba.
Su Kandala suna ta godiya da sa albarka, saboda su kansu sun san abin da Hajiyar ta yi mata; ko rabinsa Bintoto ba ta cancanci a ba ta ba. Amma saboda karamci irin na gidan girma da waɗanda suka san darajar mutane, ta linka musu ladar aikin cike da kyautatawa.
Ashe Bintoto kawaici ne take yi wa idon Hajiya, a lokacin da tana nan shiru take ba ta ko motsin kirki, amma kamar jira take yi ta tafi ta zare hijabin ta jefar tana faɗin,
"To ni Kandala wai yaushe ne za a yi mini auren."
Kangala da Hari suka zaro ido, cikin ƙufula Kandala ta wurga mata daƙuwa a fusace ta ce,
"Ranar da duk Amadun Jaririya ya saya miki gado mai fameka."
Na yi nan 🏃🏻♀️
Princess Dija ✍🏼
31.
Nan take Bintoto ta haɗe rai tana kumbura fuska ta ce, "Wai ke Kandala komai aka yi sai kin kira sunan Babana! Wallahi fa idan ba ke ba ce kowace ce sai na rama. Nan fa Abu na gidan su Jamila daga ya ce Ɗan'agunde shikenan kika yi ta faɗa har da kai shi wurin 'Yansandan bakin titi. Amma ni ki yi ta kiran sunan Babana ai ni ma na san zafins...."
"Ni ma ki kai ni wajen 'yandandan tun da kin san zafin a kira sunan ubanki Amadun Jaririy...."
Babu shiri Bintoto ta fashe da wani kalar kuka tare da dunƙulewa wuri ɗaya tana faɗin, "Wallahi-wallahi idan ba ki daina zagi na ba sai na rama."
"Ramawa na nawa kuma? Ai ina jin yanzun nan kika gama kiran Ɗan'agunde ko kuma kina nufin ni ce ban san zafin nawa uban ba?"
Hari ta yi hanzarin shiga tsakani gudun abin ya yi ƙarfi ta raba faɗan, saboda fahimtar idan ta yi shiru rigimar tasu ba mai ƙarewa ba ce. Suna tsaka da harhaɗa kayansu wani yaro ya shigo yana faɗin, an ce Bintoto ta fito ƙofar gida saurayinta kuma wanda zai aure ta ne ya zo. Kandala ta yi tsam da rai cikin faɗa tana cewa,
"To ba za ta zo ba! Shikenan shi ba zai shigo ya gaishe mu ba sai dai ya laɓe ƙofar gida yana mana aike? To ka ce na ce ba za ta zo ba! Ko ita ce za ta aurar da kanta ba mu za mu yi mata auren b...."
"Inna ki sassauta kada ya ji k..."
"Yo idan ma ya ji ni sai me Hari? Ai shi ma ya san bai kyauta ba! Mu ya dace ya zo ya gani ba ita ba, don mu ne za mu ba shi ita, ba za ta iya aurar da kanta gare shi ita kaɗai b...."
"Wai ya ce wurin ku ya zo ba wurin Bintoto ba."
Wani yaron da ya biyo bayan wanda aka fara aikowa ya faɗa yana ƙumshe dariya. Ganin tana lasar bakinta da ya yi dagaje da goro, don garin faɗanta goron da ta kwance a gefen zaninta tana ƙoƙarin kaiwa baki ya faɗo ƙasa, ta sake ɗauka ta nufin bakin a nan ma ya sake faɗuwa, ta duƙa da niyyar ta ɗauke shi cikin rashin sani ta shura shi da ƙafa ya yi nisa. Sai da ta bi shi ta ɗauko tana faɗin,
"Wallahi sai na ci ka. Ku ji mini la'anannen goro!"
Kafin ta dawo bai wa yaron amsa tana cewa, "Ya dai fi masa. Amma tun da yarinya ba ita ce za ta ba da kanta ba ai mu ya dace ya nema ba kowa b..."
Hari ta yi hanzarin tare zancen da cewa, "To ai ke Inna wataƙila niyyarsa sai ta fita sai ya aiko ta a ba shi izinin shigowa, idan ta faɗa mana ga shi nan ya zo. Don na tabbatar da ko shi ba zai zo ya tafi ba tare da ya neme mu ba."
"Ke dai kin kare surukin naki kawai Hari. Amma ni tun yanzu na fara jin kamar kishinsa nake yi."
Hari ta yi hanzarin yin dariya, saboda fahimtar Kangala ta sauko daga dokin fushin da ta fara hawa, sai da ta shimfiɗa masa tabarma sannan ta ce da yaron ya ce ya shigo. Bintoto kam tana ɗaki tun da ta ji shi ne ya zo ta hau sauya kaya, har da shafa hoda da fesa turare kamar yadda Hajiya ta ce ta dinga yi, idan ya zo hira sannan da ƙauyensu idan sun je, kada wani ya ji jikinta yana wari a ce a can birnin ba a koya mata komai ba.
Hakan ya sa ta baje kayan kwalliyarta ta dinga zuba kwalliya har Jabir ya gama gaisawa da su Hari ba ta gama ba. Sai da Kandala ta ƙwala mata kira sannan ta fito tana ɗaura ɗankwali ta tsaya gabansa ko mayafi babu tana kumbura fuska. Hari ta ja ta zuwa ɗakinsu tana yi mata raɗar,
"Saka hijabinki ya daina ganin ki babu abin rufawa a jikinki."
"To ai ni babu komai a jikina Inna."
Ta faɗa tana dudduba jikin nata, Hari ta yi hanzarin miƙa mata hijabi tana faɗin, "Na sani, ke dai saka hijabin kada ya kalle miki ƙirji a banza."
Sai a lokacin Bintoto ta yi dariya tana rufe fuska, bayan ta kai kallonta ga matasan nonuwanta da suka fara kumburowa a cikin riga. Sai da Hari ta ƙara gyara mata ɗaurin ɗankwalin sannan ta ce, ta ɗauki kujerun roba guda biyu ta ajiye cikin a soron gidan, kada su fita waje wani ya gan su suna hira.
Kandala kam gaba ta