Showing 78001 words to 81000 words out of 88489 words
Chapter 27 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx
tagumi. Sai da ya kira Hari ya yi magana da ita a kan don Allah ta wayar mata da kai ba wani abu ne mai illa ba. Sannan ya tafi da tunanin yadda za su kwashe da ita idan an yi auren ya nemi kusantar ta.
Kwanakin bikin suna ta ƙaratowa ita ma tana ta ƙara borin ba ta son auren. Har aka zo wata rana tana kan hanyar dawowa gida a cikin adaidaita sahu, jar danja ta tsayar da su suna jiran a ba su damar wucewa. Garin kalle-kallenta kawai sai ta hango Jabir rungume da kayan da yake sayarwa, bulawus da moper tare da makwashin shara da tsintsiya. Yana ta kutsawa cikin abubuwan hawan da ke wurin yana yi wa mutane talla. Ƙara gwalalo ido ta yi tana kallon sa har ya kusa isowa inda adaidaitasahunsu. Daidai lokacin aka ba su damar wucewa mai adaidaitar ya yi gaba tana ƙoƙarin yi masa magana ba tare da ya ji ta ba. Saboda hankalinsa gabaɗaya ya tafi a kan neman halaliyarsa da yake yi babu safiya babu rana, ruwa ko sanyi ba sa hana shi fitowa neman na kansa.
Yatsa ta dinga cizo tana ƙwafa har aka ajiye ta ƙofar gida. Ta fito ranta a matuƙar ɓace ta shiga gidan tana ranste-rantsen ba za ta taɓa auren Jabir ba. Kandala wani mugun kallo kawai ta yi mata ba tare da ta ce mata komai ba. Hari ce kawai da ke ƙulƙulen daddawa a cikin turmi ta samu tambayar wa ya taɓo ta.
Bintoto da ta yi zaman dirsham a tsakiyar gidan ta haɗa kai da gwiwa tana matsar ƙwalla ta fara magana cikin muryar kuka tana cewa,
"Ashe ma ba mai kuɗi ba ne tsintsiya yake sayarwa da wani abu dogo da wani a cikin leda. Na rantse da Allah ba zan aure shi ba don ni mai kuɗi nake so ba irin shi b....."
Kukan da ta fashe da shi ya sa Kandala jefa goro a bakinta tana faɗin,
"Sannu ɗanwake ka fi ubanka! Hamshaƙiya mandiya! To billahillazi ko Habi ta dawo duniya ta ce ba za a yi auren nan ba sai dai ta koma inda ta fito, amma sai kin aure shi. Ba tsintsiya ba ko kashi kika ga yana kasawa a kan hanya sai kin aure shi mara kunyar banza da ta wofi. To sai in ga uban da zai sa a fasa auren tun da kin raina mutane. Haka kawai za ki saka mu zama ƙananun mutane bayan an gama magana? To ai mu mun jima da sanin sana'ar da yake yi, ke ce kawai dogon burinki ya hana ki gano irin baiwar da a Allah Ya yi miki kina ta hauka. Buɗe kunnuwanki da kyau ba za a fasa auren ba! Uban da duk ya fasa rashin mutunci a kan auren nan malfar ubansa uban da haife sa shi ma ubansa!"
Haka Kandala ta saka ta gaba da masifa tamkar za ta cinye ta da rai. Don da a ce kusa da ita take babu makawa sai ta kai mata hannu ba tare da ta san ta aikata ba. Bintoto ta ja jakar makarantarta ta shige ɗaki tana rantsuwar da take ji a ranta ita ce kaɗai makaminta da za ta nuna ba ta ra'ayin auren.
Tuwon dare ma da Hari ta zuba mata ƙin ci ta yi. Sai da fitsari ya sa ta farka tsakiyar dare ta buɗe kwanon ta cinye abincin sannan ta sha ruwa ta koma ta kwana. Da safe Hari tana ganin babu tuwon ta yi dariya, don ko ba a faɗa ba ta san aikin Bintoto ne. Saboda Kandala ba koyaushe ta damu da cin abincin ba, wani lokaci fura kawai take sha ta yi kwanciyarta.
Bintoto har ta gama shirin zuwa makaranta ba ta ce da kowa komai ba. Sai da za ta fita ta tsaya kan Kandala da ke ta shirin ficewa wurin aikinta ita ma, kai ta juya gefe ta rungume hannu a ƙirji tana cewa,
"Ba ni kuɗin tafiya zan yi."
"Au! Ashe fa kina magana ba kurma kika koma ba."
"Ni dai ki ba ni."
Kuɗin kawai ta wurga mata a ƙasa ta duƙa ta ɗauka ta fice. Sai da ta fita sannan ta dawo tana haɗe rai da maƙale murya ta ce da Hari,
"Inna na tafi."
"Allah Ya kai ki lafiya 'yata."
Hari ta faɗa cikin sakin fuska. Bintoto ta fice bayan ta ce da ita a faɗa wa Kandala ta tafi. Hari tana 'yar dariya ta sake cewa da ita,
"Ita ma ta ce Allah Ya dawo mana da ke lafiya ya ba da sa'ar karatu."
'Amin.' Ta faɗa a zuciya ta fice tana haɗa rai har ta samu abin hawan da zai kai ta makaranta. Lokacin da aka tashi kuma ta jima a bakin titin tana neman abin hawa ba ta samu ba. Tana tsaye rataye da jakarta wata mota ta yi gaba, sannan ta dawo a hankali har ta tsaya daidai saitinta aka fara zuge gilashi. Wani babban mutum kuma dattijo ta gani, mai farin haƙorin Makka biyu a bakinsa yana ta murmushi kafin ya ce,
"Sannu ustaziya. Zo mu je na rage miki hanya."
Jikinta yana rawa cike da jin daɗi ta buɗe gaban motar ta shige babu ɓata lokaci ko wani jinkiri. Fuskarta a sake take kallon sa yayin da shi kuma ya koma kallon titi yana faɗin,
"Ya sunan Malamar? Kuma ina ne unguwarku?"
Sai da ta gyara zamanta cikin zumuɗi sannan ta faɗa masa sunan unguwar su Hari kafin ta koma faɗin,
"Amma ni ba malama ba ce. Malamanmu sun fi ni girma."
Wata kalar dariya ya yi kafin ya kalle ta ya sake cewa, "Da alamu kamar kina da aur...."
"A'a ban taɓa aure ba, ko miji ma ban da shi sai Allah Ya kawo."
Amsar da ta ba shi kenan da hanzari ganin har ya fassara ta bayan ba ta yi auren ba.
"To amma ya na gan ki da kayan makarantar masu aure?"
Sosa kai ta shiga yi kafin ta ce, "Wani ne ya saka ni makarantar, wai don an taɓa kora ta a wata makaranta."
"To fa!"
Dattijon ya faɗa yana 'yar dariya saboda a lokaci ɗaya ya fahimci ƙaramar yarinya ce kuma mai shirme. Ganin yadda ba ta ɓoye masa komai ba, har abin da bai tambaya ba sai da ta faɗa masa. Tun daga kan laifin da ta yi a gidan Hamida har zuwa saka wa malami cinnakun da ya yi sanadin aka kore ta, Hajiya ma ta kore ta gidanta, duk sai da ta faɗa masa.
Dariya ya dinga yi ita ma tana taya shi ta hanyar ƙara yi masa bayanin wace ce ita da faɗace-faɗacen da ake yi da ita, har suka kai bakin jar danja. A daidai lokacin da Jabir ya iso wurin motar saitinta yana faɗin,
" Hajiya ga shi a yi wa gida tsarab...."
Bakinsa ya datse sauran maganar ta maƙale ganin Bintoto a cikin motar Alhajin suna ta dariya.
Princess Dija.🧑🦯
38.
Cikin sauri ta juya kanta suka haɗa ido. Ƙirjinta ya faɗi dam-dam! Amma hakan bai hana ta buga wani kalar tsaki tana maka masa harara ta juya masa baya ba. Daidai lokacin da aka ba da hannu Alhajin ya ja motar cike da mamakin ganin yadda Jabir ya saki baki yana kallon su, yayin da ita kuma yanayinta ya nuna masa ƙarara akwai wani abu a tsakaninsu.
"Wancan kin san shi ne?"
Abin da ya faɗa kenan bayan ya kama titi yana zuba gudu. Hannuwa ta rungume a ƙirji tana huci kafin ta ce,
"Ban ma taɓa ganin mai irin fuskarsa ba."
"Allah Sarki, har na tsammanin yayanki ne. Ganin yadda ya yi kamar akwai wata alaƙa a tsakanink...."
"Babu alaƙar komai ban san shi ba. Wataƙila kuma kama na yi da wadda ya sani."
"Ok."
Alhajin ya faɗa, amma bai yarda da zancenta ba. Saboda ya sani ruwa ba sa tsami a banza. A take ya saka wa ransa Jabir yayanta ne ko kuma saurayinta. Hakan ya sa ya juya kansa yana ƙare mata kallo kafin ya yi dariya. Saboda gabaɗaya ta canza a lokaci ɗaya ta ji ranta ya ɓaci, hakan ya jawo ta haɗe fuskarta tare da cika kumatunta da iska hannuwanta a rungume tana kallon abubuwan hawa ta gaban motar ko ƙiftawa ba ta yi.
Dariyar da Alhajin ya ya sa ta lalle shi ta gefen ido kafin ƙara tsuke fuska ta ce, "Wallahi wancan mutumin ko kaɗan ba na son sa. Ko ganin sa na yi haushi yake ba ni. Kamar na samu ƙaton dutse na fasa masa kai sai ya fashe ya mutu kowa ma ya hut...."
"Subhanallahi! Wane mutume ne ba kya so har haka?"
Alhajin ya tambaye ta cikin sauri saboda mamakin furucinta. Banza ta yi da shi ba ta ce masa komai ba, ganin fuskarsa a cure kuma ta ƙi cewa komai, ya yi shiru bai sake tankawa ba. Har ya shiga unguwar su Hari ta nuna masa ƙofar gidan ya durfafi wurin.
Motar ya tsayar daidai bakin gidan yana kallon ta da riƙe baki ganin sun kawo amma ba ta yi yunƙurin motsawa ballantana ta fice ya juya.
"Tun da ba za ki faɗa mini wane ne za ki fasa wa kai ba, ki shiga gida kada a yi miki faɗan kin shiga motar wanda ba ki sani ba."
Hawaye ta fara gogewa kafin ta kai kallonta gare shi ta ce,
"Don Allah za ka aure ni?"
"Aure?" Ya faɗa cike bakinsa a buɗe tsabar mamaki. Kafin ya ji wata kalar dariya ta zo masa babu shiri. Kallon sa ta dinga yi hawaye yana zuba a kan fuskarta ya ce mata,
"Ni ba yaro ba ne, kin ga na tsufa har da hurhura a kain..."
"Ai kuma kana da kuɗi. Ni kuma mai kuɗi nake so na aura wanda zai kai ni Makka."
"Wata sabuwa yanzu ni za ki aura?"
"E, saboda ba na son na auri wanda bai da kuɗi."
"To ya yi, ki shiga gida idan na yi shawara zan dawo mu ƙarasa maganar."
Cikin zumuɗi ta ɓalle murfin motar ta fice, shi ma ya yi ribas ya juya tana ɗaga masa hannu har ta daina ganin motarsa. Juyawar da za ta yi ta ci karo da Kandala da ke bayanta tsaye cike da mamaki. Saboda ta ji tsayuwar mota a ƙofar gidan, fitowar da ta yi don ta tabbatar gidan ne aka zo ka ya ya, ganin Motar ta juya Bintoto tana ɗaga hannu zuciyarta ta ba ta ita aka kawo a cikin motar.
Sandarewar da ta yi ne ya sa ta kasa furta mata komai. Zabura Bintoto ta yi cikin matsanancin tsoro ganin Kandala a wurin. Fuska ta haɗe tana turo baki ta nemi raɓawa ta gefenta ta wuce. Caraf Kandala ta cafko hijabinta tana faɗin,
"Wancan da ya kawo ki ƙanen Amadu ne ko yayansa?"
Wani kallo Bintoto ta yi mata kafin ta ƙwace riƙon da ta yi wa hijabinta ta yi ciki tana cewa, "Taimako na ya yi don haka ki daina kiran sunan Babana, amma kuma ni aurensa nake so na yi alamunsa ya nuna mai kuɗi ne."
"Tabbatacciya! Ai har kin aure shi ma ba za ki yi ba! Wallahi na rantse da Allah idan na sake ganin shi a ƙofar gidan nan; ko kuma kika sake shiga motarsa sai na yi miki abin da ba ki yi zato ba. Idan ban da kin rasa mafaɗi wancan garsaƙeƙen ƙaton shi kike kwatantawa da mijin da za ki aura?"
"Yaushe kika gan shi da za ki ce masa ƙato?"
"Na hango gingimemen kansa da ya kusa yin girman motar tasa baƙar kwaɗayayyiya!"
"Wallahi kanki ma ya fi nasa girm..."
"Ke! Ko ma wane iri ne daga yau kada na sake jin ko hirarsa a bakinki, ballantana ya sake yi miki taimakon. Don idan ba ki sani ba ko sani, wallahi zai iya yi miki fyaɗe ya tona masa asiri muna zamanmu lafiy...."
"Ni da ma zai yi mini fyaɗen ina so in dai zai aure n...."
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'una! Yanzu Bintoto ke kike faɗar wannan maganar a bakinki? Kin ko san ma'anar fyaɗen da kike zance? To daga kada na sake jin irin wannan mummunan lafazin daga bakinki, Allah Ya daɗa ba ki kariya da duk abin da zai jawo miki naƙasu a rayuwa mu ma ya jawo mana fitina da jin kunyar duniya. Zo..zo na ji me ke faruwa?"
Hari ta ƙare maganar tana jan hannun Bintoto suka zauna, don dawowarta gidan kenan ta ji maganganun da suke yi, amma ba ta fahimci komai a kan rikicin nasu ɗan kullum ba. Don babu safiyar da za ta zo ta wuce ba tare da sun yi abin da suka saba ba. Bayani Bintoto ta fara yi mata tana hawaye.
"Wai Inna wani ne fa ya kawo ni gida, saboda ban samu abin hawa ba ya taimaka mini. Shi ne fa Kandala ta dinga zagin sa wai zai ɓata ni. Bayan shi har furfura na gani a kansa da gemunsa. Amma motarsa mai kyau kuma yana da kuɗi."
"Tooo! Yanzu na gano silar faɗan naku. Wato saboda yana da kuɗi kika shiga motarsa ya kawo ki gida. Ita kuma Inna tana faɗa saboda ba ta so a ce wani abu ya same ki. To bari ki ji, ire-iren waɗannan masu motar a garin nan su suke yanka 'ya'yan mutane. Yanzu idan aka yanka ki mu shiga ina fisabilillahi?"
"To ai ni aurensa nake son yi."
Hari ta ja numfashi kafin ta ce, "Irin su ai ko auren ba sa yi, don duk wadda suka aura sai dai su kashe ta sun sha jininta namanta karnuka su cinye, shi ya sa ma ko auren ma mata ba sa yi da su. Kowa tsoron take yi a kashe ta."
"To ni dai gaskiya ba na son wancan mutumin."
"Wane mutumin kike zance kuma?"
"Talakan da yake so na."
"Amma kuma shi ne masoyinki na gaskiya. Saboda shi yake ƙoƙarin sada ki da rahamomin Allah ga shi kina zuwa makaranta kina samun lada. Sannan kina yin sallah kowane lokaci, to me ya rage miki a yanzu ban da ki yi aure ki haihu mu ci naman suna?"
Cikin sauri Bintoto ta rufe fuskarta da hijabi saboda kunyar zancen nata, musamman da ta ce wai ta haihu. Fuskarta a lulluɓe ta ce,
"To ni Inna ina ma na iya haihuwar."
"Idan lokaci ya yi zan gwada miki yadda ake yi. Don ki haifa mana 'ya'ya goma sha biyu mu yi ta shagalinmu mu kaɗai."
A haka Hari ta ture zancen mai motar suka koma hirar da ta fahimci ta samo kan Bintoto da dabara. Kandala dai tana gefe tana aikin maka wa Bintoto harara zuciyarta tana zafi, a ranta tana ji kamar ta nemo bulala ta zane ta. Saboda rashin hankalinta da dogon burinta ba ƙaramin ƙona mata rai suke yi ba.
Marece sakaliya Jabir ya diro gidan, don ba ƙaramin ƙarfin hali ya yi ba da da bai biyo matar Alhajin ya murɗe masa wuya ya mutu ba. Saboda zuciyarsa babu abin da ba ta nuna masa ba tsabar zafin kishin da ya rufe shi ya haifar masa da zazzaɓi babu shiri.
Kai-tsaye gida ya koma ya kwanta, sai da ya ji ƙarfin jiki da kuzari bayan fushinsa ya faɗa, sannan ya yi wanka ya fito zuwa gidan. Bai nemi ganin Bintoto ba, Hari ya nema, ya bayyana mata abin da idanunsa suka gani. Sannan ya nemi alfarmar yana so a rage kwanakin bikin saboda tsoron abin da zai je ya dawo. Ko kuma a ɗaura auren kafin zuwan lokacin haka zai fi kwantar masa da hankali.
Hari ta faɗa wa Kandala buƙatar da ya zo da ita, ita ma ta yi na'am da zancen, saboda ba ta da nutsuwar zuciya ganin mutumin da shigar ɓurtun da yake son yi a rayuwar Bintoto.
Nan take Jabir ya aika ƙauye wurin dangin Amadu. A gaggauce cikin kwana biyu aka ɗaura auren, ba tare da an sanar da Bintoto ba. Makaranta ma daina zuwa ta yi kwana biyun sai da aka ɗaura ya zo tun da safe ya ɗauke ta ya kai ta. Kuma ya ce idan an tashi ta jira zai zo ya mayar da ita gida. Amma saboda ba ta son ya ɗauke ta, ta fito bakin