Showing 63001 words to 66000 words out of 88489 words

Chapter 22 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2075

gidan, inda mutane suke zazzaune ana hirar kuɗin auren da suka ji labarin har an biya. A nan ya saka hannu aljihu ya fito da kuɗi 'yan naira ɗari sababbi ya dinga raba wa mutanen da ke wajen suna ta murna. Kandala kuma dubu biyar ya ba ta ita kaɗai, suna fita ya damƙa wa Bintoto bandur ɗin naira 'yan ɗari-ɗari sababbi fil tana ta jin daɗi.

Tana tsaye jikin motar yana ƙoƙarin tayarwa su Jamila suka iso wurin cikin sauri suna faɗin, "Mu ƙawayen Bintoto ne, mu ma ka ba mu kuɗin kafin ka tafi."

Sai da ya kai kallonsa ga Bintoto da ke riƙe da ƙugu tana hura hanci sannan ya ciro kuɗin daga aljihunsa ya miƙa wa Jamila. Sai dai kafin su isa hannunta Bintoto ta wafce kuɗin tana aika mata harara tana cewa,

"Ai wallahi ba za a ba ku ba. Ni zan haɗa duka na riƙe tun da ba wani ya samo mini mijin a cikin ku ba!"

Cike da muguwar kunyar waɗanda ya zo da su Jabir ya dinga dariyar yaƙe yana cewa da su Jamilar, "Ku yi haƙuri wasa take yi za ta ba ku idan mun tafi."

Daga haka ya tayar da motar suka bar ƙofar gidan, tana ɗaga masa hannu har suka sha kwana. Kafin ta koma rungume hannu a ƙirji tana kallon Jamila ta ce,

"Wai ke ba ma Innarku ta raba ki da ni ba? Yanzu don yana kwaɗayi shi ne kika ce da mijina ke ƙawata ce. To ni na daina ƙawancen da ke, karɓi ɗaya Amo ke ma Zulai karɓa, ku kaɗai zan bai wa kuɗin ba da ita ba. Idan Innarta ta isa gobe ta sake cewa ta raba mu ƙawancen mu gani."

Haka ta rabar da kuɗin amma ko ficika ba ta bai wa Jamila ba. Takaici ya sa ta yi nesa da ita kafin ta fara ja mata Allah Ya isa tana aika mata daƙuwa tare da faɗin,

"Allah Ya sa yaya Habu ya dawo ya tarar da ke a garin nan ki ga abin da zai yi miki. Don ya ce duk ranar da ya sake kama ki sai ya cire ladar ƙazafin da kika yi masa. Saboda ke ya bar garin nan, don zalunci irin naki kika yi masa sharri kika sa mutane suna ta yamaɗiɗi da zancen har da masu yi masa gori a garin nan. Mijin naki ma da zai aure ki Allah Ya sa kullum ya yi ta dukan ki sai kin some, baƙar muguwa."

Haka Jamila ta dinga jifar Bintoto da maganganu, a ranta tana ji kamar ta bi ta har gidansu ta dake ta kamar yadda suka saba.

Haƙurin da sauran ƙawayen nata suka dinga ba ta ya sa ta yi banza da Jamila, ta shige gida suka rufa mata baya, saboda jin daɗin kuɗin da ta ba su suka tsaya suna ba ta labarin kashin da Innar Jamila ta sha a hannun Jimmai Jarka, a kan kuɗin dashen da ta cinye wa mutane kuma ta ƙi biya.

Dariya suka dinga yi har da riƙe ciki a cikin soron gidan. Saboda Lami ta dinga kwatanta yadda Innar Jamila ta dinga wutsil-wutsil da ƙafa bayan Jimmai Jarka ta taushe mata ruwan ciki daga ita sai buje. Sannan ta yi mata ɗuren garin tuwo har bisa gashin kanta tamkar an barbaɗa mata hoda a kai. Aka yi dace kan nata a kwance yake, wannan dalilin ya sa gabaɗaya Jimmai Jarka ta hautsine shi garin ɗura mata gari a baki ta zuba mata shi har saman kai.

A can cikin gidan kuma Kandala ta fito da kwanoni tana salati. Salatin da ya jawo hankalin Bintoto ta faɗa cikin gidan, hango kwanonin ta isa wurin tana haɗe rai ta ce,

"Ai sai da na duba na gani gabaɗaya sun cinye komai don baƙin kwaɗayi. Ni wallahi da na san duka kika ba su da na shiga na same su na ce su rage mini. Amma yanzu fa sun cinye komai har da miyar duk sun lashe kwanon kamar ba masu kuɗi ba. Wannan ai idan ba don an san suna da kuɗi ba da sai a ce 'yan yunwa n...."

"Ke sun cinye a yi abin da za a yi! Da ma ai don su aka yi." Kandala ta faɗa tana murguɗa baki kamar wata ƙaramar yarinya.

"Ku ji Kandala, ke fa kika fito da kwanonin kina salati. Kuma shi ne don na yi magana za ki ce sun cinye?"

Bintoto ta yi maganar tana aika mata harara. Tsabar ta ji haushin abin da ta yi mata a gaban mutane. Kandala kam barin wurin ta yi ba tare da ta sake cewa komai ba, saboda ranta a ɓace yake da takaicin ganin baƙin sun lashe komai tas ba su bar mata naman ko ɗan kaɗan ba. Don sai da babbar 'yarta ta ce su rage kowa ya saka wa bakinsa, Kandala ta ce ai 'yan gayu ne ba su damu da cin nama ba. Saboda ganin yadda masu sayen wainar Hajiyar a birni wani lokaci ko sun sa an zuba musu naman ba duka suke cinyewa ba. Wainar ma ragewa suke yi a bai wa almjirai ko ita ta ɗauka idan tana so. Naman ma har tara shi take yi wani lokaci ta ƙulle sai ta dawo gida ta ci. Wannan dalilin ya sa ta yi tsammanin su Jabir ma za su rage idan sun tafi kowa ya saka wa bakinsa. Amma maganar da Bintoto ta yi ta saka ta nuna ba ta ji komai ba, saboda gudun munafurcin mutane su je su kai maganar gidan hakimi.

Da dare Hari ta yi gida, bayan sun gama tsayar da maganar komawarsu, da zummar tun da safe za su tafi saboda su isa cikin lokaci. Hakan ya sa ta lissafa kuɗin dabbobin da ta sayar ta bai wa babbar ɗiyarta wani abu ta ce ta riƙe ta ja jari. Tun da abinci ma wuya yake yi mata ita da yaranta, zuwanta gidan da ganin yadda ta koma ɗan lokacin da ba sa tare, hakan ya sa ta ƙara jin tausayin ta a ranta. Sannan ta ci alwashin ko tana can idan ta samu ɗan saƙo za ta dinga aiko mata abin da Allah Ya huwace.

Mani kam, duk nacin da ya yi mata da magiya a kan ta ba shi wani abu a cikin kuɗin; bai sa ta ba shi ko ficika ba. A cewarta kuɗin akuyar da ya ci shi ne rabonsa. Haushin bai samu yadda yake so ba ya bar mata gidan tun kafin su tafi, Kulu ce ta yi musu rakiya har bakin gida tana faɗin Allah Ya kiyaye. Kandala ta shiga maƙota yi musu sallama Bintoto ta tsaya ƙofar gidan tana ta aika wa Kulu harara, sai rufe hanci take yi tana faɗin,

"An bar miki gidan ki ci kanki ke da ƙazantar yawun da kike ta zubarwa."

"Ke ma ai kin kusa yin auren, za ki ji idan da daɗi." Kulu ta faɗa cike da jin haushin rainin da ta yi mata. A fusace Bintoto ta ce,

"Allah Ya raba ni da yin ciki. Ai duk wanda kika ga ya yi ciki ɗan iska ne. Ke ma da kika yi Allah Ya shirye ki ba don halinki ba."

Murmushi Kulu ta yi kafin ta ce mata, "Da iskancin ne ai da ke ma ba a haife ki ba."

Wani kallon sama da ƙasa Bintoto ta yi mata kafin ta ba ta amsa da cewa, "Lelle ma, ni wa ya faɗa miki cikina aka yi? To idan ba ki sani ba ki sani ni daga sama na faɗo Innata da Babana suka tsince ni a daji. Ke kuma a haka za ki ƙare kawu Mani ya mayar da ke 'yar iska har kin bari ya yi miki cik.."

Hango Kandala ta fito daga gidan da ta shiga ne, ya sa ta ɗauki jakarta da ke ajiye tana faɗin, "Mu za mu tafi, ku ma idan ba ku bar garin nan ba sai talauci ya kashe ku."

Wasu yaran da Kandala ta nemo suka riƙa masu wasu kaya suka nufi bakin titi. Inda a can suka iske Hari tana jiran su. Cikin ɗan lokaci suka samu mota Bintoto tana tsaki ta ce,

"Da na sani da ma ni da na ce wancan yaron ya zo da motarsa ya ɗauke ni."

Hari tana daidaita zamanta a cikin motar ta ce, "Wane yaro ne haka?"

"Mai motar da zai aure ni."

Ta ba ta amsa tana kallon gaban motar tare da motocin da ke gabansu suna ta wucewa. Kafin Hari ta yi magana Kandala ta riga ta da cewa,

"To ai ki kira shi ko yanzu ya zo ya ɗauke ki, tun da haifar sa kika yi ai dole ki kira shi yaro."

Hari ta shiga zancen tana faɗin, "Ai ke Inna soyayya babu abin da ba ta sakawa. Kada ki sha mamaki idan ta kira shi ki ga ya dawo ɗaukar ta. Don dai kawai ba ta ce ya zo ba da ya ɗauke ta, ai haka ne ko 'yata?"

Hari ta ƙare maganar tare da kai kallonta ga Bintoto tana janyo ta jikinta cikin kulawa. Bintoto ta lafe tana turo baki ta ce,

"Ki ƙyale Kandala Inna, bayan ya faɗa mini har ƙasar waje zai kai ni na sayo takalmi idan muka yi aure. Shi ne don na ce masa yaro za ta ce ni na haife shi. To ai ko Innarsa ma ya fi so na a kanta, don ya ce a duniya babu macen da yake so kamar ni. Amma dai ita Kandala na san ba za ta yarda ba, za ta ce ƙarya nake yi masa bai faɗa ba, bayan a gaban abokinsa ma ya ce bai taɓa son kowa kamar yadda yake so na b...."

"To shashasha! Wannan son da yake faɗa daban da wanda yake yi wa uwar da ta haife shi. Don babu ɗan da zai ce ya fi son wata ƙatuwa a kan wadda ta kawo shi duniy..."

"Ai ke ma sau nawa kike faɗar Kawu Mani ya fi son Kulu a kanmu? Kuma wallahi ni na yarda da ya fi son ta, tun da har ciki ya yi mata ya sayar miki da uwar garke aka yi mata magani. Idan ba ya fi son ta a kanki ba yaushe zai sayar miki da akuya a kan ya nema mata magani? To ni dai ko za ki ji haushi na sai na faɗi gaskiya wancan yaron ya fi so na a kan Innarsa, kamar yadda Kawu Mani ya fi son Kulu a kan mu ni da k...."

"To na ji kin faɗa, saura cikin ke ma ki je yaron ya yi miki tun da Mani ya yi wa Kulu, saboda ya fi son ta a kaina."

Wani mugun kallo ta wurga wa Kandala tsawon mintuna ko ƙiftawa ba ta yi kafin ta yi magana cikin murya kuka ta ce,

"Ai ni kuma ba 'yar iska ba ce! Allah ma ya sani ban taɓa yin iskanci ba."

Daga Hari har mutanen cikin motar da ke sauraron su gabaɗaya suka saka dariya. Kandala ce kawai ta yi ƙarfin halin danne ɓacin ranta ta ɓalli goro tana tauna tana faɗin,

"Tun da cikin kike so ai za a yi miki, gaggawar me kike y...."

"Ni ko na rantse da Allah duk wanda ya yi mini ciki sai na kashe shi!"

Ta yi maganar cikin kuka da ɗaga sauti alamun ranta ya kai ƙololuwar ɓaci da maganganun Kandala. Kafin ta dunƙule jikin Hari ta yi ta gunjin kuka ganin har lokacin mutanen cikin motar ba su daina yin dariyar da suke yi ba.

Princess Dija ✍️

33.

Da haka suka isa cikin birnin bayan Hari ta shawo kan Bintoto ta daina kukan. Kandala ma da ke ƙara tunzura ta ta sauko daga dokin fushin da ta haye ta rarrashe ta. Tare da sanar da ita babu wanda ya isa ya yi mata ciki har sai idan Allah ne Ya nufa. Daha haka ta kulle mata baki ta koma share hawayenta tana faɗin,

"Ni da mun je ba zan kwana wurin ku ba gidan Hajiya zan wuce."

Kandala tana yi mata hararar gefen ido ta jefa goro a bakinta tana faɗin, "Ki je wurin Alhaji ma idan kina iyawa, ai mu ma ba son zaman naki muke yi ba."

Mai adaidaitasahu yana kai su gidan Hari ta kira Hajiya tana sanar da ita sun dawo. Marece sakaliya Hajiya ta turo aka tafi da Bintoto, da tsarabar ƙauyen da suka yo mata mai yawa saboda jin daɗin yadda take ɗawainiya da su babu nuna ƙyama irin ta masu kuɗi.

Baki har kunne Hajiya ta dinga yi wa Bintoto maraba saboda jin daɗin ganin ta da abin alherin da ta kawo mata. Sai da ta ci abinci ta ƙoshi sannan ta yi wanka ta yi sallah tana ta zuba hamma. Sallah ma sai da ƙyar mai aikin Hajiya ta tirsasa ta yin ta, tana gamawa ta baje a wurin sai barci, ko da asuba ma da ƙyar aka tayar da ita ta yi shirin makaranta.

Cikin zumuɗi da ɗoki ta isa makarantar da kwandon abin breakfast ɗin ta kamar yadda kowa yake zuwa da abin sa. Tana ƙwambo da zuƙe wuya ta shiga ajinsu, ba ta yi wa kowa magana ba ta isa kujerar da take son zama ta zauna tana hararar mutane. Zamanta babu wuya malami ya shigo ajin ya fara yi musu karatu. Amma ko kaɗan hankalinta ba ya kai, hannunta yana ƙasan benci a cikin kularta tana tsamo Irish tana ci da ɗaya-ɗaya, da niyyar idan ta cinye ta koma kan kulolin mutane da take hange tana son ta gano mene ne a ciki.

Hakan ya sa tana cin Irish ɗin tana kallon ƙasan ƙafafuwan masu kulolin, a gefe ɗaya kuma ta koma kallon taga da mutanen da ke wucewa jefi-jefi.

Rubutun da malamin yake yi ya hana shi gano wainar da take toyawa, yana gamawa ya juyowa ya hango kanta a duƙe tana faman tura dankali a bakinta, wanda ta kwaso cike a hannunta don ta matsu ta cinye shi ta ajiye kular.

Babu zato ta ji an daki bencin kujerar da take kai, tana ɗaga kai a firgice ta ga mutum a kanta yana huci. Ita ma ranta a ɓace ta saki kular ɗan sauran dankalin ya zube, tana aika masa harara tare da turo baki ta ce,

"Ni wallahi ka ma ba ni tsoro! Kuma duk abin da ya same ni kai n...."

Cakumar da ya yi wa hijabinta ya jawo ta, ya sa ta yi shirun dole ta koma kokawar ƙwace riƙon da ya yi wa hijabinta. Amma hakan bai hana shi kai ta gaban ajin ba ya wurgar, cikin fusata ya ce ta duƙa, Bintoto ta yi tsaye tana hararar sa tare da rungume hannunta a ƙirji ta ƙi yin abin da ya ce.

Jikinsa yana rawa ya ɗauko bulalar dorinarsa ya shiga zabga mata tana ta tsalle, bayan ta yi durƙushen cikin azama tana roƙon ya yi haƙuri. Amma saboda ta gama ɓata masa rai sai da ya gama sauke fushinsa a kanta, sannan ya jefar da bulalar yana faɗin ta same shi ofis.

Bintoto ta dinga kuka tana tsine masa tare da rantsuwar Wallahi-wallahi ba ta yafe masa ba, kuma ba za ta je ofishin ba. Wasu daga cikin 'yan ajin suka iske malamin har ofishinsa suka sanar da shi abin da ta faɗa. Ransa a ɓace ya nemo wasu manyan prefects ya ce su je su ɗauko masa ita a ka idan ta ƙi zuwa da ƙafarta.

Masu biɗa a duhu ballantana a haska musu, mugayen prefects ɗin suka yi mata kama-kama bayan sun gama zabga mata buloli, suka fito da ita ajin tana ta tirjiya suna jan ta, yayin da masu tura ta ta baya ma suka dinga aikinsu.

A haka suka kai ta har bakin ofishin malamai da ƙarfin tsiya suna nishi. Malamin ya fito yana ba su umarnin su saka ta kamun kunne, azabar da suke ba ta ce ta saka ta yin kamun kunnen dole tana kuka tana faɗin ba ta yafe ba.

A nan suka bar ta cikin rana tana kamun kunne tana kuka, shi ma ya shige ofishinsa yana barci. Tsabar ta ba shi haushi ya kasa yin komai ya koma nazarin wace irin yarinya ce aka kawo musu a matsayin ɗaliba. Saboda ba wannan ne karon farko da suka fara ganin rashin ɗa'a daga gare ta ba. Akwai ranar da 'yan ajin nasu suka kai wa malamai ƙarar tana cinye musu abinci.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login